A Rubuce Take (K'addarata) page 8 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 8 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 7 Hausa Novel - Novels Elite

 


 H U G U M A

A RUBUCE TAKE

       (K'addarata)


Page 08


        Cikin dakinta take tsaye,sanye da uniform na islamiyya,farin riga da wando da kuma hijab ne,sai baqar abaya da suke dorawa a sama,idan ta saka kayan sai ka dauka ita daya aka kebe aka yi uniform din don ita,tana da wani irin kyau da yasha banban da na yaran gidan dukkansu,innocent face ne da ita,duk da cewar a zahirance din ma bata fiya hayaniya ko rigima ba,bata da abokin fada idan bawai taso ba ko quruciyar ta motsa.

          Dukka jakar tata ta zazzage saman gadon tana kwashe tarkacen dake ciki gami da kauda su gefe daya,ta maida alqur'aninta ciki,tana shirin rataya jakar ummu ta leqo


"Kin fasa zuwa islamiyyar ne?" Da fuskarta dake da qarancin walwala ta waiwayo tana dubanta,ssnnan ta buda baki a nutse


"Zani"


"To ai gwara ki hanzarta kada ki makara" ummu ta fada tana sakin labulen gami da juyawa,har cikin ranta bata jin dadin rashin walwalar widad din sam,gaba daya tun ranar ta koma wata sukuku.


        Plate takalmanta masu igiya ta daura,baqaqe da suka zauna suka yiwa fararen qafafuwanta kyau,saita fito a dakin,ta yiwa ummu dake zaune a falon sallama sannan ta fito farfajiyar gidan.


           Tana tsaka da tunanin ta tsayawa koda Aafiya ne su wuce tare ko kuma tayi tafiyarta hon din mota daga waje ya cika harabar gidan,ba tare da jinkiri ba baba awwa ya miqe ya bude gate din,baqar motar dake daukan idanu da sheqi ta sako kanta zuwa cikin gidan,hankalin widad ya dauku kan motar,kamar taso ta gane motar waye?,tunaninta yazo dai dai sanda baba awwa ya qarasa ga motar bayan ya rufe gate din yana fadin

"Barka dai da sauka,barka da sauka mai gida muhsin" wani murmushi ne ya qwace mata,uncle muhsin?,uncle muhsin ne yazo?,mutumin dake cikin jerin sahun mutanen dake da girma da matsayi a rayuwarta,mutumin dake nuna mata kulawa kamar yadda yaga ummu nayi mata,gaba daya ta sha'afa ma da batun makaranta ta fito,gaba daya hankalinta ya tattara ga uncle muhsin din,wanda ko second daya bata qara a tsaye ba ta nufi inda ya faka motar tasa harda sassarfarta.


             Suna tsaka da gaisawa da baaba awwa din ya tsinceta a wajen,bakinta har kunne


"A'ah,yammata sai ina?, islamiyya za'a je?" Farincikinta ya gaza boyuwa,ta gyada kai tana dariya gami da fadin


"Uncle muhsin ka shammaceni,dama zaka zo?"


"Gani kuwa widad,bakiji wajen alhaji ko ummu ba?" Kai ta girgiza still dai tana dariyar.


          Kafarta kafarsa suka shige gidan,sai daya fara shiga sassan 'yan uwan nasa suka gaisa,tana biye dashi qafa da qafa,duk da hararar da take samu daga wajensu amma bata damu ba,anty madina ce ma ta tsokaneta


"Batun tafiya makaranta ya tashi kenan?". Dariya widad din tayi,sai uncle muhsin din ya juya ya kalleta


"A'ah,ai ba za'a fasa zuwa makaranta ba saboda zuwa ne,kije ki dawo,ina nan ai" cikin shagwaba ta narke fuska


"Don Allah uncle,yau kadai.....kuma ma lokaci ya wuce,na makara,idan ma naje bulala zaayimin Allah" kai ya jinjina kawai,widad din ta daukeshi da wani matsayi sosai,haka suka wuce sassan ummun tare.


        Ina ka saka ina ka ajjiye ummu keyi da dan autan nata,wanda take lelensa kamar kowanne auta a wajen iyayensa,duka su ukun suna falon suna hira,ita widad da kuma uncle muhsin din,sai da ummu ta korata tace ta fidda uniform din daga jikinta tunda taqi makarantar sannan ta miqe da jakarta a hanzarce ta wuce daki.


          Dauke dubansa muhsin yayi daga dubanta sanda ta bacewa ganinsa ya maido ga ummu


"Me ya samu widad ne?,ko tayi ciwo baya bayan nan?" 


"Me ka gani?" Ummun ta tambayeshi itama


"Ramewa naga tayi,ko girma ne ya kawo hakan?" Kai ummun ta girgiza tana tabe baki


"Batun aurenta ne yaketa zuwa da mishkiloli kawai"


"Aure fa ummu?,widad din?"


"Eh baqon abu ne?,naga kusan duka 'yan bayanta ma haka aka musu" zamansa ya gyara,har cikin ransa bayaso a aikata wannan dabi'a ga widad din,yana jin yarinyar har ransa,saboda baya mancewa da yadda mamarta ta daukeshi a sanda take auren dan uwansa,saboda da shaquwa ne sosai tsakaninsu da ita,ta daukeshi kamar qaramin qaninta


"Amma ummu sunfi widad datawa ai,duka duka ita din shekararta nawa ne?,sha hudu fa?"


"To mahaifinta dai ya tasamma aurar da diyarshi,mahfood ne akayita gwagwarmaya akan lamarinsa tace bataso,muka saka baki ni da alhaji aka ajiye zancansa,ya dauko ma'aruf to yanzu akan batunsa ake,shima din kuma ba so take ba" sosai fuskar uncle muhsin ta sauya


"Amma ummu shikam yaaya meye haka?,tunda bataso duka basai a qyaleta ba?,nawa widad din take?,naga batayi girman da zai daga hankalin kowa ba saboda batayi aure ba ko?"


"Duk yadda nake da iko dashi da ita dole akwai huruminsa na uba daya zama dole na bashi,nidai abu daya na sani bazan bari ayi mata auren dole ba" dan qaramin tsaki yaja abun yana bashi haushi,ko da shi dabi'arsa ta daban ce,bare a yanzun da ya zama riqaqqen dan boko


"Wannan maganar a barta kawai,indan tace taji ta gani tana so ne ma shikenan sai ayi zancan aure,amma ni sha'awar karatu nake mata,karatu nakeso tayi,bari zamu hadu da yayan,ya bani ita kawai mu wuce gida tare"


"Bazan iya baka widad ba,zan maka lamuni dai taje zuwa sanda komai zai lafa" murmushi yayi


"Zahra ta dade tana nacin a bata widad ummu,su kansu su nujood zancansu yaushe zatazo,tunda anyi haka kawai ki haqura ku barmin ita"


"Banyi alqawari ba" ummu ta shaida masa kai tsaye.


         Sanda widad din ta dawo falon bayan ta sauya kaya ummu ta shiga ciki ta duba dashishin da za'a girkawa alhajin,har yau har kwanan gobe tsufa jin dadi ko wadata bai hana dattijuwar matar aikin abincin mijinta ba.


          Cikin hikima uncle muhsin yake bugun cikin widad kan batun,tuni ta fara share qwalla,sai ya ajjiye spoon din hannunsa


"Kinga share hawayenki,ba wanda zai miki auren dole,dake zan koma ma na kaiki wajensu nujood,ai zaki je ko?" Duk da nisa da ummu shine abu da tafi tsana,amma a yanzun sai takejin shine mafi dacewa,kawai tabi uncle muhsin din,tayi nisa da garin ko abbanta zai haqura da qudurinsa,bata da zabin da ya wuce wannan,don haka ta gyada kai hadi da cewa


"Zanje uncle"


"To shikenan,share hawayen ki bani labarin izifinku nawa yanzu a islamiyya" hira ce ta barke tsakaninsu,harma ta manta da fargabar tafiya tabar ummu,saima zumudin matsawa daga garin,ko banza ta gujewa wani ma'aruf abbanta dama auren da ake shirin qaqaba mata.


           Uncle muhsin shine auta ga ummu a maza,daga shi sai halimatu kenan,kuma qani ga abbanta da suke uwa daya uba daya,shi din ba mazaunin kano bane,yanayin aiki ne ya kaishi bauchi,da farko ma kamar bazaije ba,saida ummu ta qarfafa masa gwiwa,ta kuma nuna masa aiki ba inda baya kai mutum,yanzu haka shekararsa kusan goma sha uku da aure,yana da yara hudu,diyarsa ta farko widad ta girmeta da shekara kusan daya,dan boko ne sosai,yana da sauqin kai som mutane da kuma kirki,widad na ji dashi cikin dukka tulin qannen da mahaifinta ke  dasu,saboda yadda yake nuna mata kulawa da kuma janta a jiki.


          Da kansa uncle muhsin din ya zauna da yayan masa mahmudu,ya sha fama sosai kafin ya gane abinda yake kwatanta masa,don daga bisani dole ummu da alhaji suka sake shiga maganar sannan ya janye qudurin nasa,ba kuma wai don ya haqura da maganar bane gaba daya,wannan ya sake qarfafawa uncle muhsin gwiwar tafiya da widad din


"Taje dai ta huta,amma ban bar muku ita ba,kada ma kazo kace min ga zance ga magana".


            Kamar wasa sai ga widad tana murnar tafiya,har ta fara hada kayanta da kanta ma,latifa ita da anty madina sunata dariya


"Ba cinya ba qafar baya,Allah dai yasa a qarke qalau kada ku dawo ranar da kukaje" suke tsokanar uncle muhsin sanda sukaga widad din nata shiri.


           Kwana uku kacal ya qara suka tattara sai bauchi,ranar da zata tafin gaba daya 'yan rakiyarsu har bakin motar uncle muhsin din,latifa ke riqon jakarta,tana ta tsokanarta


"Uwar dakina kada dai zama yayi dadi a manta dani" widad dake sanye da atamfarta dinkin doguwar riga tayi dariya tana qwamewa gaban motar uncle din


"Bazan manta dake ba inna latifa,kedai ki zuba ido zakisha tsaraba" dariya ta saki


"To Allah yasa" itama ta amsa tana dariyar,suna dakon uncle muhsin ne,yana rabawa yaran gidan da sukayo masa rakiya kudi,'yan dari dari ne sababbi qar,baya rabo dasu,ya kammala ya dawo cikin motar ya zauna yana sake waina injin motar sosai,ummu ta zagayo ta durqusa tana musu addu'ar sauka lafiya,sannan ta zura hannu saman cinyar widad ta ajjiye mata kudi


"Gashinan,kada kije baqon guri hannunki babu komai" murmushi uncle muhsin yayi bayan ya kalli kudin


"Banda abinki ummu me zatayi da kudi?"


"Ina ruwanka kai dai?" Ta amsa shi,tana gyara yafen mayafin dake saman kanta


"Nidai bance a riqemin yarinya acan ba,aro na baku" ta sake jaddada masa abinda yake ranta,sai yayi dariya kawai yana tayar da motar,dai dai sanda widad kema ummun godiya,duk da itama din batasan amfanin me kudin zasuyi mata ba.


           Har motar ta fice daga harabar gidan suna waigen juna ita da ummun


"Zauna sosai kada ki baro kan naki a gida kije bauchi da iya gangar jiki" uncle muhsin ya tsokaneta,sai tayi dariya tana zama sosai din,saidai tun a lokacin taji ta fara kewar gida,taji kamar ta koma,to amma idan ta tuna abinda ta gujewan sai taji dadi,hankalinta kuma yadan kwanta,ko ba komai za'a daina zancan,tana saka ran maganar ma tabi ruwa ta huta.


         Suma shirin ficewa a unguwar motar ma'aruf din ta sako kai,uncle muhsin yadan dakata kadan,sai ta lafe sosai ta kwantar da kanta saman  cinyoyinta ta yadda bazaya ganta ba,ma'aruf din ya gaidashi sukayi sallama,uncle muhsin yaja motar sukayi gaba yana dariyar widad din cikin ransa,quruciya sai abarta.ZAFAFA BIYAR 2023


IDON NERA Mamuhghee


KI KULANI miss xoxo


A RUBUCE TAKE Huguma


RUMBUN K'AYA Hafsat rano


DAUDAR GORA Billynabdul


Account number


0022419171

Maryam sani

Access bank


Saiki tura shaidar biyanki ga

09033181070


VTU OR MTN RECHARGE CARD

09166221261


AL'UMMAR NIJER SU TUNTUBI WANNAN NUMBER


+227 90 16 59 91


Thanks for choosing us

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post