Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 14 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 14 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 14 - Novels Elite

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 

 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽

By

            *Nusaiba Alkamawa*

Dedicated to my bloody sister *jiddah alkamawa* 🥰

                  And yaya *jamal* 

 Free page 14

******

Har Hassana ta kule Asabe bata daina kallonta ba ashe kiyayyar da takeyiwa Jidda har takai tanaso yaranta su kashe ta jiki a sanyaye ta fito daga falon, "Asabe lafiya kuwa na ganki jiki a sanyaye haka","wllhi Garzali su Al'amin ne suke naiman kashe jidda a gidan nan" nan dai ta bashi lbr abinda ya faru har abinda likita yace da kuma abinda Hassana ta fada yanzu, ransa a matukar bace yake kallon Asabe, "saide mu cigaba da hakuri kawai Asabe bamuda yadda zamuyi kawai dai abinda nakeso dake shine ki daina barinta tana fitowa idan baki nan, in kuma a madafa kike wannan zaki iya fitowa da ita sai kina barinta a kofar madafar saboda zaman kullum a daki bazai mata dadi ba, Allah yana sane da komai kuma insha Allah komai ya kusa zuwa karshe da izinin ubangiji" daga haka suka wuce zuwa dakin Jidda ya dubo jikin ta har kuka saida Garzali yayi ganin yadda sukayi mata gaba daya fuskarta a kumbure take kamar ba ita ba, lokacin ma bacci takeyi shiyasa Garzalin ya fito daga dakin yana komawa wajan aikin sa.

Jamal wai ina zakaje ne haka naga sai sauri kaketa zubawa" kayataccan murmushi ya sakarwa mahaifiyar tasa da yake bala'in sonta da kaunarta, cikin daddadar muryarsa mai sace hankalin yammata yace "Mommy zanje asibiti ne zamu shiga da wani mutum tiyata ne karfe bakwai shiyasa kikaga inata sauri, yafada kamar baya son yayi magana " cike da so da yadda yake taimakon alumma itama take kallon sa, "to amma dai ka farayin breakfast kafin ka tafi" ya mutsa fuska yayi yana duban kyakkyawan diamond din agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa, "Mommy gaskiya na makara innace zan tsaya nayi breakfast to zan makara innaje chan kawai zanyi" ya fada yana mikewa, "dama ai haka kake kullum bakason cin abinci banason wannan banzan ciwon na zamani fa ya kama min kai nasan kasan yadda ulcer takewa mutum idan ta kama shi ","insha Allah Mommy babu abinda zai sameni" ya fada yana karasa ficewa daga falon, "nide zan bawa idi driver ya kawo maka saura kuma kaki ci" murmushi kawai yayi saboda yana sauri sosai, da sauri Idi driver ya taso ya bude masa back set ya Shiga Sannan shima ya shiga suka bar gidan, suna zuwa asibitin ya fito da sauri saboda saura minti daya bakwai ta cika kuma yasan bazasu taba fara aikin ba dole sai yazo saboda ya fisu sanin makamar aikin, da sauri_ sauri gudu_ gudu yake tafiya duk inda ya wuce Nurses sai gaishe sa sukeyi amma ko kallo basu ishe sa ba, Fadeela ce ta tabo Yesmeen saboda ta juya baya tana waya batasan da tahowar Dr Jamal ba. 

A hankali Fadeela ta rada mata a kunne, "gafa mutumin naki yau yayi sammakon zuwa watakila ko wani aikin zaiyi shiyasa yazo da sassafen nan" da sauri Yesmeen ta juyo jin abinda Fadeela ta fada tasan ta akwai tsokana yanzun ma ta dauka tsokanar ta takeyi ai kuwa tana juyowa idonta ya sauka akan kyaukyawar fuskarsa ta gabansu yazo ya wuce, ba tare da ya kalli kurarsu ba, lumshe ido tayi jin daddadan kamshin turaran daya bakunci kofofin hancin ta mai dadin shaka, "kee malama ai sai mu tafi aikin dake gaban mu ko ya tafi ai" firgigit Yesmeen tayi jin abinda fadeela ta fada itakam harta tafi tunani wata duniyar hangosu kawai takeyi sunyi aure ita da Jamal gashi ma wai suna shan soyayya abinsu shine Fadeela ta katse mata tunanin nata gaba sukayi sunata zanchen Jamal dan kaf asibitin nan mata daddaya ne basuce suna son sa ba amma shi mata basa gabansa sam.

Yana shiga office dinsa ya chanza kaya zuwa na aikin tiyata cikin azama ya fito daga office din saida yayi yar tafiya sannan ya karaso tiyata room din takalmin kafarsa ya cire ya saka wasu farare sol sannan ya shiga, suna ganin sa sukayo masa chaaa akai akan ya makara da yake duk abokansa ne su uku, Muhseen, Umar Farouq, sai kuma Khalid sai kuma shi Jamal din, saida suka shafe awa daya da rabi sannan cikin nasara suka kammala tiyatar, akan gadon marasa lafiya aka turo mutumin zuwa dakin hutu, fitowa sukayi suna tafe suna dan taba hira a tsakanin su har suka karaso zuwa wajan office dinsu kowa ya shiga nasa, Jamal na shiga toilet ya shiga ya wanke hannun sa sannan ya fito ya zauna a kan kujerar sa yana duba wusu file da ya gani akan table dinsa, ko minti goma baiyi ba da zama Yesmeen ta shigo sai faman girgiza jiki takeyi tana wani yauki wai ita a dole son Dr Jamal takeyi bai dago ba haka zalika baiyi magana ba tafi minti biyar a tsaye amma ko uhmm baice mata ba, saboda a duniya in akwai abinda ya tsana shine mace marar kamun kai, ita kuma Yesmeen kwata _kwata batasan wani abu waishi kamun kai ba, "Dr" ta kira sunan sa da wata iriyar murya mai jan hankali

"banza yayi mata ya cigaba da aikin da yakeyi saboda bashida lokacinta, "Dr kasan fa abinda nake nufi kusan shaikara biyu kenan ina fama da dakon soyayyar ka kuma nasan ka fahimta amma saika rika nunawa kamar baka gane abinda nake nufi" banza ya kumayi a karo na biyu kuma har zuwa lokacin bai dago ya kalle ta ba kamar ma baisan da tsayuwarta a gurin ba, "nifa Dr ba dole ne saika aure ni ba indai zamuna hutawa tare ni ko sau daya ne ya kamata ka sanni a matsayin diya mace nima na sanka a matsayin dana miji hakika nasan zakayi jarumta yadda nake bukata" ta fada tana cisge dan mililin hijabin dake jikinta tana matsowa kusa dashi hannu ta mika da niyyar shafo sajen fuskar sa da yake kwance luf akan fuskar sa, wani irin kululun bakin ciki ne ya taso masa, cikin zafin nama ya rike mata hannu tare da bankara sa, karar azaba ta saki a wahalce, "wannan shine babban kuskuran da zakiyi a rayuwar ki yanzu haka zan iya karya wannan dan iskan hannun naki anan wajan kuma babu abin da zai faru na karya banza, kuma bari kiji ni kamilin mutum ne ban taba zina ba kuma wllhi bazan fara akan ki ba, kuma ma in inayi wllhi babu abinda zanyi dake, kije na kore ki daga asibitin nan domin zaki gurbata mana sauran yaran da wannan gurbatacciyar tarbiyar taki" dan Allah Dr kayi hakuri" banza yayi mata wayar sa ya dauka yana kokarin barin office din ta rike kafa tana masa magiya hanbarar da ita yayi yana watsa mata wani kallo da saida yasa hantar cikinta kadawa, "na baki minti biyar kibar office dinnan in ba haka ba na kira security su fitar min dake" yana gama fadin haka ya fita daga office din zuciyarsa na radadi.


Daga alkalamin nusaiba ✍️

Shere fisabilillah.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post