*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:huguma*
Page 57
To tun daga wannan rana kwananta ya dawo dakinsa,saidai tana kammala sallar asuba take komawa dakinta ta shirya shirin makaranta,wani lokaci shike kaita,wani lokacin kuma samuel ko daya daga cikin yaran dake qarqashinsa.
Aikin da yakeyi yasa a yanzun zamansa a gida yafi yawa,wannan ya fara haifar da shaquwa a tsakaninsu,duk da baya barin kowa ya rabi inda yake wannan aikin amma yawancin lokuta suna tare,badai hira sukeyi da ita ba,amma zata dauki littafinta ta zauna a wajen,ko ba komai tana jin motsinsa bata da kewa,lokaci bayan lokaci tana barin karatunta tadan zuba idanu tana kallonsa,idan sun hada ido kuma sai ta basar,murmushi kawai yakeyi ko yayi kamar bai gani ba yaci gaba da abinda yakeyi,aikin nasa ke bata sha'awa yake kuma burgeta,tanason masa tambaya amma kuma tana jin nauyi,don har yanzu bata gama sakewa dashi ba.
A lokacin yayi qoqari matuqa ya koya mata abubuwa da dama,har ya fara sakar mata,don majority ita ke dafa musu abincin rana,kuma ya ciyu saboda gyaran bashi da wani yawa.
Wannan karon ma bai samu zuwa bauchin ba sai bayan sati biyu,tanata hada kaya ta zaci da ita zaya je,sai yace a'ah,tayi zamanta,ta dinga masa kuka amma daga baya dole ta haqura,ya yiwa mai gidan magana matar gidan ta bata 'yar tayin kwana suke kwana tare,friday ya tafi ya dawo sunday da magariba,saita samu kanta cikin murna da farinciki ranar daya dawo din,wanda ita kanta batasan dalili ba,tunda dai ya tafi taji gaba daya bata da sukuni.
Zuwansa bauchi a yawancin lokuta bacin raine,yana zuwa ne kawai don ya sauke nauyin da Allah ya dora masa,ya kuma kwatanta adalci,amma baya ga haka baiga wani alfanu da yake samu ba,hafsat din ta yita mita da nunqufurcin bai taho da weedad ba,don ta tara ayyukanta jingim suna jiranta,gidan ya hada mugun datti da qura yadda ya kamata,to koda yaje ma kusan washegarin ranar a aikin kintsa gidan ya qarar dashi,daga qarshe sassan weedad din ya bude ya kwanta yayi baccin gajiya a falonta,ki sashen nata da babu dan adam baiyi wannan qazancewar ba,da yamma ya fice wajen hajiyarsa,wadda ta dinga jajjabin abinda yasa baizo da weedad din ba,a haka dai ya qare weekend din nasa a gantale babu wata kyakkyawar maraba.
Haka kawai ta samu kanta da son masa gwaninta,yana fita sallar magariba din a gurguje ta shiga kitchen,ta hada masa simple spaghetti jallop,da murmushi yake kallonta sanda ta dire masa ita,taliya ba cimarsa bace,amma kuma sai yaji ta burgeshi dari bisa dari,ko babu komai tafi hafsat din wadda a qalla nata shekarun sun ninka na weedad din,amma ko irin hakan batasan tayi masa ba,don haka yaji bazai iya watsa mata qasa a ido ba,yaja taliyar ya soma ci,taste dinta sai ya bashi mamaki qwarai,har ya kasa jurewa
"Yammata irin wannan abincin fa?,a ina kika koyo shi?" Sunan daya kirata dashi ya bata kunya,saita kifa kanta saman pillow tana dariya,batasan sanda suka fara irin wannan wasan dashi ba
"Kaine ka koyamin" kai ya girgiza yana sakin murmushi
"Wannan kaman ba aiki na ba" kuma ya fada dinne har zuciyarsa,saboda dandanon ya zarta yadda ya koya mata din.
Daya tashi komawa bauchi da ita ya tafi saboda hajiyarsa dake ta tambaya,hakan ya yiwa hafsat dadi,ta sake miqa dukka wasu ayyukan gida ga weedad din,bata samun zama ko hutu saita gama dukka wasu aiki na sassan hafsat din,hakanan hidimar yaran gaba daya ta dawo hannunta,wankansu wanki cire pampers,basu abinci da sauransu,tun tana jin gajiya da wahala har ya soma zame mata jiki ta saba.
Wani zuwa da sukayi,ranar asabar da azahar,tana kitchen din hafsat din tana gogeshi bayan ta gama wanke kwanukan da suka cika babban sink din kitchen din,cikin ranta cike fal da mamakin yadda take barin kitchen ya hada wannan uban datti da kayan wanke wanken kamar na gidan biki ko suna,mimi da nawwara na falon data gama gyarawa suna wasa,ta kadasu can don su barta ta gyara nan din a nutse,a dole ta sake qwarewa ta samu kuma experience sosai akan harkar kitchen da kula da yara.
Sau biyu anty ummee na sallama sai surutansu mimi,har sai data bude qofar falon ta shigo,tabi falon da kallo zuciyarta cike fal da mamakin yaushe hafsta ta koyo tsafta?,yaran da suka ankare da shigowarta suka watsar da kayan wasan suka taho da gudu suka rungumeta
"Ina babarku?"
"Tana dakinta,ta kwanta tace kada a tasheta"
"Babanku yana nan ne?" Kai ta girgiza
"Ya fita a mota"
"Muje cikin" ta fada tana kama hannunsu,har yanzu tana mamakin kintsuwar falon,duk da tazo kwana hudu da suka wuce amma ba haka ta samu falon ba.
Tana kwance male male saman gadonta tana sana'artata wato chart,harta bude baki data ji an bude qofar zata hau masifa,a zatonta weedad ko yaran ne saita maida maganar dake cikinta tana murmushi ta miqe ta zauna saman gadon ganin anty ummee ce
"Daga ina haka ba kira ba sanarwa?" Harara ta balla mata tana samun gefan gadon ta zauna
"Kedai baki da hali,don zanzo gidanki saina gaya miki?" Dariya tayi
"Allah ya baki haquri ba haka nake nufi ba" bedroom din nata anty ummen ta sake kalla
"Nace ba,wai yaushe kika fara tsafta ne?,don nidai banga haka a jikinki ba" tafadi tana kallon jikin hafsat din,wadda ko brassiere babu,sai wata t-shirt data mata yawa da zanin atamfa,kanta kuma tsifa ce rabi da rabi.
Fuska ta tsuke tana kallonta,tasan halin anty ummee idan ya motsa in ba cin mutunci tataba mata ba bata jin dadi
"Ni dadina dake wlh cin fuska,aidai jikin nawa babu qazanta ko?"
"Nima bance akwai ba" ta amsa mata tana boye dariya,sai hafsat din ta gyara zama tana cewa
"Yarinyar nan ce sunzo weekend,ai na gayamiki indai sukazo bani da matsala,nima nawa weekend din nakesha"
"Kina shan weekend dinki amma na ga kanki rabi da rabi,a haka mai gidan yazo ya sameki?" Kan nata ta shafo
"To mene?,kitso naso azo ayimin kuma na kasa qarasa tsifar tun shekaran jiya"
"Allah ya tsinewa qazantarki" anty ummee ta fada cikin ranta,amma a fili saita mirgina kai kawai,tasan kome zata gaya mata abanza,tunda ba yau farau ba,indai akan tsaftane
"Amma dai ya kamata kiyi amfani da damarki duk sanda yazo weekend ya zamana kin qara kawo kusanci tsakaninki dashi"
"Manta da wannan anty ummee,kome zakiyi masa baki taba burgeshi" baki ta tabe
"Ai shikenan,Allah ya kyauta" daga haka ta maida kallonta ga dakin,ta fara bin ko ina da kallo tana neman abinda zata rabauta dashi,ganin haka sai hafsat din ta tsuke fuska da kyau,tasan yanzun zata rabata da wani abu,don haka ta zamo daga gadon tana daura zaninta
"Muje falo anty ummee,kada a shigo gidan babu kowa a daukemin wani ita tana ciki tana aiki bata sani ba" ta fahimceta sarai,bata ce komai ba tadauki jakartata suka dawo falo,amma cikin ranta taci alwashin sai fa ta fita da wani abu daga gidan
"A banza zan dinga baki shawari" ta fadi a ranta.
"Nifa dadina dake rowa wlh,ko ruwa ki kasa bawa mutum?" Anty ummee ta fada ganin sunata zuba zance amma ko ruwa bata mata tayinsa ba,kusan wannan din dabi'ar hafsat ce,bawai wani abu bane a wajenta
"Kai anty ummee,kedai kin cika qorafi wallahi"
"Ahto ai gaskiya ce" daga nan inda take zaune ta qwalawa widad kira tace ta kawo ruwa,ajjiye mop stick din hannunta tayi,ta samu plate ta hado ruwa da kuma lemo babba da qarami me sanyi da cup,kamar yadda ta saba gani a gidansu ummu nayi,ta nufo falon.
Idanun anty ummee a kanta harta qaraso,ta tsugunna ta ajjiye kayan sannan ta gaidata ta miqe ta koma ciki.
Sai data koma sannan ta dauke idanunta daga kanta ta maida ga hafsat
"Hafsatu,ya naga yarinyar nan tana girma ne?,kinga yadda take canzawa?" Baki hafsat ta tabe
"Na gani,nima abun yana dan damuna,duk da dai nayi mata dashen dana tabbatar bazai barsu suyi kowacce irin sakewa ba,kai qarshe ma idan ya matsa nasan rikici za'a yi ba dan qarami ba,namiji kuwa kinfini sanin ba haquri gareshi ta wannan bangaren ba" kai ta jinjina
"Eh da haka kam,amma dole mu sake lalubo wata hanyar kafin ta fahimci duk gaibu kike gaya mata" mugun tsaki hafsaa din taja
"Kuma dai?,ni na fara gajiya,haka kawai kana zaman zamanka banda namiji matsiyaci ne ya dauko abinda zai hanaka sakewa,shi bai amfana ba kai baka sake ba,aikin banza kawai" ta sake fada tana jan mugun tsaki, idanunta har sun sauya launi,da kallo anty ummee ta bita tana fasa lemon da aka kawo mata,a baqin kishin hafsat dinma bata dauka za'a kai warhaka gayyar bata watse ba,saidai tana alaqanta dadewarta akan plan din da morar yarinyar da takeyi.
Bayan ta shanye ta dauki dayan ta jefa a jakar hannunta,don tunda ta samu wannan damar ba zata barta ba,hafsat din kuwa ta bita da kallo cikin ranta tana fadin
"Kwadayayya hadamammiya" yayin da anty ummee din ta waske da cewa
"Karki damu,kafin lokaci ya qara turawa za'a samo wata mafitar".
Sannu a hankali rayuwa ta dinga juyawa,watanni suka fara shudewa,tsakanin widad da abbas yanzun akwai sakewa da sabo ba kamar baya ba,duk da cewa ba wata mai yawa bace,don bata bari ya kusanci inda take sosai,idan ka gansu zakayi tsammanin yaya ne da qanwarsa da yake matuqar bawa kulawa,zuwa sannan weedad din ta fara girma ita a karan kanta tana ganin wasu sauye sauye,ta fannin girki ta iya abubuwan da baza'a rasa ba,sosai kuma takejin dadin makarantar ta,ta fara sabo da mutane,ta kuma fara karantar rayuwa da yadda mu'amala take tsakanin mutane
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥