IZZA DA FARIYA
*BY*
*NUSAIBA* (Nuseey Yar Amana)
ASSALAMU ALAIKUM MASOYANA INA MAI FARIN CIKIN KASANCEWA TARE DAKU BAKI DAYA INA MATUKAR GODIYA GA ALLAH DA YABANI DAMAR FARA WANNAN LITTAFI MAI SUNA *IZZA DA FARIYA* KU KASANCE DANI HAR KULLUM NICE TAKU YAR AMANA WATO NUSAIBA KUBIYO NI DAN JIN WANNAN LABARI NAWA MAI SUNA *IZZA DA FARIYA* WANDA YAKE KUNSHE DA DARUSA DA ABIN AL'AJABI DA KUMA SON ZUCIYA 🙏🏻✍🏻
INA MATUKAR GODIYA AGAREKU TARE DA JINJINAWA MASOYANA DA ABOKAN ARZIKI INA MATUKAR ALFAHARI DA RUBUTAN HAUSA NI MARUBUCIYACE KUMA INA FARIN CIKIN HAKAN.
*IZZA DA FARIYA*
Page 1
Manyan motocine ke shiga harabar gidan sunkai guda hudu masu tsada da kyau har suka gama shiga aka maida get aka rufesa bayan sun gama parking ne motar dake gaba suka fito suka nufi motar dake biye dasu da zimmar budewa yan bayan ma sun fito suka nufi motar dake gaban su suka budeta wani hamshakin saurayi nagani kyakykyawa fari dashi yana latsa wayar sa can yadago kai sannan yazira kafarsa da bisimillah yafito haka ma motar ta biyu bayan anbudeta wata budurwa ce cikinsa hadaddiya mai kyau sosai tana taunar cingum abakinta yatsina fuska tayi tana zubawa wanda yabude mata kofar harara kamar wacce zata cinyesa da idanu baima yarda sunhada ido ba kansa yana kasa har ta karaci zamanta da wani karemai kallon walakancinta tagaji ta zira kafa tafito tana takawa daya bayan daya mummy da daddy suka fito tarbanta dan daman shi hashim yadade da shigewar sa abinsa rungume mummy tayi tana shagwaba,,
""Mumm I really miss you""☹️ ta kalli daddy ""dadd miss you so much '"" murmushi sukayi dukkan su mummy tace ""we miss you more dear mushiga ciki kafin ki gama bademu da shagwabar taki da bata karewa"" dariya daddy yayi suka shiga ciki tana ta shagwaba tana narkewa jikin mummy suna isa ta zauna saman kujera ita da mummy,,
'""Kinga tashi tashi kishiga ki watsa ruwa kishirya kifito kici abinci yana jiran ki"" mikewa tayi tana fadin ""mumm"" murmushi mummy tayi kawai rigima ta dawo fana dai rokon Allah yasa bata dawo da wannan halin nata ba hashim ne yafito a dan hanzarce da dan saurin sa yana gyara links din rigar sa mummy ta kalle sa tayi mai alama to sai ina haka,,
""Mummy bara nazo zanje na dauko farida a school nayi mata alkhawari kuma yanzu lokacin fashin su yayi bara na hanzarta saina dawo"" yashafa kumatunta baibata damar yin magana ba tana kokarin maganar ma yafita yana fadin,,,
'""Please mum nasan kina da magana amman kiyi hakuri if am back zanyi miki bayani sai nadawo asa mana Albarka mummy "" yafita murmushi mummy tayi tana girgiza kai tace,,,
""Allah yayi muku Albarka Allah kuma yasa itace abokiyar zaman taka hashim kenan Allah nagode maka da ka nuna min wannan rana ban mutu ba ya Allah kamar yadda kanuna min naji da kunnena ya Allah ka nuna min da idanuwata"" ta shafa,,
'"Amin ya rabby Allah yanuna mana tare dukda bansan menene ba"" daddy yafada yana murmushi zama mummy tayi tabashi kanun labarin yadda sukayi da hashim dukda sunan kawai sukaji basusan ko wacece ba amman sai addu'ah sukeyi masa dasanya Albarka,,
✍🏻✍🏻✍🏻
Tsaye take ita da kawarta suna fira fitowar su kenan daga class din antashe su motar sa ta tsaya gaban su murmushi tayi suka isa gun motar bude musu yayi suka shiga,,
""Ina yini"' suka fada lokaci guda "lafiya lau ya kuke ya lecture "? Alhamdulillah suka amsa daga babu wanda yakara magana har ya sauke su a kofar gidan nasu sukayi masa godiya yace sugaida masa da umma da abba suka amsa masa da to suka shige ciki saida yaga shigewar tasu sannan shima yatada motar sa yayi na gidan su muheed abokin sa kuma amininsa,
Bilkisu saida ta shafe 1hr sannan tafito sanye da riga da wando wadanda suka dan kamata babu kallabi a kanta kallonta mummy tayi tace,,
""Haba bilkisu wannan wani irin dressing ne haka ina kallabin ki ki kalli kanki gashin dokine fa akanki kuma kina yar musulma haba"" bata rai tayi ta dawo kenan za'abi atakurawa rayuwar ta gaskiya ita shiyasanya bata son dawowa nigeria sabida bata son ire iren wannan batare da ta bata amsa ba ta nufi dinning table ta zauna girgiza kai mummy tayi daddy ma yakasa magana dukkan su suka isa gun dinning din mummy ta dauki wayar ta takira hashim yanajin ring din yasan mummy ce yasa hannu ya dauko wayar yana murmushi lokacin suna tare da muheed,,
""Assalamu alaikum" Amin wa'alaikassam ku muke jira kuna inane "" muna hanya mummy munkusa" owk sai kun iso" suka katse kiran muheed yace ""uwar mu maganin kukan mu kenan nazaku nima naje naci girki mai dadi" murmushi hashim yayi baice komai ba har suka isa koda suka isa mummy tazubawa daddy kenan sukayi sallama suka shigo bilkisu bata ko daga kai ta kalle suba bare susa ran zatayi musu magana ma tana cin abincin ta zama sukayi mummy ta zuba musu suka faraci muheed ya diba yakai bakin mummy yana murmushi budar bakin tayi yasanya mata shi kuma hashim yabaiwa daddy mummy tadiba ta ba bilkisu daddy ma gaba mummy dariya su muheed suka sanya sabida yadda mummy taji wani kunya daddyn ma dariya yakeyi kama kai bilkisu tayi irin suna cika mata kunne ta aje spon dinta tamike mummy cikin dariya tace,
""Kada kice min kin koshi"" gyada kai tayi alamar yes tana son ta huta ne ta gaji da yawa sannan ta wuce duk babu wanda bai lura da ita ba daddy ya girgiza kansa yace Allah yashirye ki bilkisu " suka amsa da amin suka cigaba da cin abincin su suna nishadi.
Zaune suke suna fira da umma suna kuma a'iki farida na yankar alaiyahu zarah na tsintar shinkafar tuwo umma na jajjaga kayan miya suna fira,
""Yawwa umma wai inji ya hashim yana gaida ku keda abba"" Zarah tafada umma ta kalle ta tace ""Allah sarki yaron kirki yauma halan shi yadawo daku ko"? Eh umma a'i yana matukar son Aminiyata sosai ki duba fa kigani duk matan dake masa shawagi baya kallon su ita kawai yake kallo a'i tasamu miji wallahi kuma gasu da kudi mu baiduba yadda muke ba Allah sarki bamu da bakin godiya agaresa wallahi Allah yajikan baba nasan da yana raye zaiji dadin wannan mu'amalar sosai wall..... kawai sai kuka yasubuce mata ta tashi ta nufi daki farida ta bi bayanta da gudu itama tasanya kukan suka taru a daki suna kuka babu mai rarrashin wani itama kanta umma saida tayi kwallar bata tanka musu ba har sai da suka gaji dan kansu sukayi shiru bacci ne yayi awangaba dasu lokaci daya umma ta cigaba da a'ikin ta har ta hada miya ta daura tukunyar tuwo tazuba shinkafar ta tattare gun da sukayi a'ikin ta duba su taga suna bacci tayi murmushi tasakan musu labulan tacigaba da duba girkinta har ta tuka tuwon ta basu suka farka ba har saida umma ta kammala aikin tas ta tsaftace gun farida ta fara farkawa tayi salati tamike tafita taga tsakar gidan fesfes tashiga dakin umma tayi mata sannu da a'iki ta zauna suna fira zarah tashigo itama abincin farida ta zuba musu dukkan su suka zauna suka faraci harda umma bayan sun gamaci suka tattara kayan sukayi na gun wanke su sannan sukayi sallah suka fara wankewa
TAM ANAN NAKAWO . NA LITTAFI NA DAYA MU HADU A NAGABA TAKE YAR AMANAR KUCE NAKE MUKU FATAN ALKHAIRI🙏🏻🙏🏻❤️❤️