Rumbun Qaya Page 50

Rumbun Qaya Page 50

Rumbun Qaya  Page 50

Rumbun Qaya  Page 50

***Wajen karfe uku da rabi na dare ya farka daga baccin da ya dauke shi. Kansa ne yayi masa wani irin nauyi har zuwa idanun sa. Shi kadai ne a saman gadon tana k'asa ta shinfida sallaya ta kudundune a cikin Hijab dinta tana bacci. A hankali ya zuro kafafun sa ya sakko ya dagata daga k'asan zai maida ita sama ta bud'e idon ta da sauri dan ba wani bacci me nauyi tayi ba. Be lura da ita ba, ya ajiyeta a gadon ta yi saurin maida idonta ta rufe tana jinsa ya zare mata Hijab din jikinta sannan ya tashi ya nufi toilet din. Wanka ya fara yi sannan ya dauro alwala ya fito ya haye sallayar da ta tashi daga kai ya shiga raya daren cikin neman taimakon Allah a abinda yake shirin yi. Karfe hudu da rabi akayi kiran farko ya dauko wayarsa ya bud'e application din alqur'ani me girma ya kunna ya dan rage volume din ya jinginar da kansa a jikin gadon yana sauraron karatun yana shiga chan cikin zuciyar sa yana saukar masa da nutsuwa. Yana zaune har aka yi kiran sallar, ya duba time din yaga biyar da kwata. Sai ya mike tsaye yana gyara zaman rigar jikin sa. Ya kalle ta tana bacci hankalin ta kwance. Sai ya sunkuyo kanta yayi kissing dinta a saman goshin ta a hankali sannan ya bud'e kofar ya fita daga dakin. A gate suka hadu da Dr Farouk ya kalle shi da mamaki dan be yi tunanin a gidan ya kwana ba duk da yaga motar sa amma be kawo yana nan ba, Sai dai yana ganin shi yasan dalilin da ya kawo shi dan shi kansa sai da yayi wa Ya Nabeela fadan akan me zata dauko masa mata ta ajiye ta dai kawo excuse dinta amma shi sam be gamsu ba, dan be ga amfanin zaman ba. Ganin da yayi wa Aryan din a yanzu ya bashi dariya ganin yadda ya Nabeela ta hakikance jiya akan maganar ashe Aryan din na cikin gidan ma a lokacin. Lallai shaanin maza sai a barsu kawai. Gaishe shi yayi ya amsa yana tsokanar sa yayi murmushi kawai dan yasan bazai fadawa Ya Nabeelan ba. Tare suka je masallacin sukayi sallar sannan Aryan din ya tafi shi kuma ya shiga ciki yana murmushi shi kadai. Ganin yadda yake ta faman smiling yasa Ya Nabeela tambayar sa dalilin Murmushin sa amma sai yace mata sirri ne ba zai fada mata ba, sai an kwana biyu idan ma zata ji abinda ya faru. Tasan halin shi sarai ko me zatace ba fa zai fada matan ba tunda yayi niyya shiyasa sai ta kyale shi ta nufi dakin Raihanan taga ta tashi. 

   Ta riga ta tashi tana ma toilet sanda Ya Nabeelan tayi Knocking a kofar sai kuma taji alamun ruwa sai ta juya kawai tasan ta riga ta tashi. Yana fita tana tashi ta shiga toilet din dan yin alwala tayo alwalar tazo tayi sallah bayan ta idar ta zauna tana azkar tunanin abinda ya faru tsakanin su na dawo mata a kwakwalwa. Bakin ta, ta dan shafa sai taji ya saki ba kamar jiyan ba. Samun kanta tayi da yin murmushi kawai ta chusa kafarta a tsakankanin cinyoyinta kunyar abinda yayi matan na kamata. Zai yi wuya ta iya kallon sa face to face a yanzu dan jiyan nan sosai ya wuce gona da iri da wasu irin salo da kwanyar ta, ta gagara dauka sam. Sake dawowa Ya Nabeela tayi dakin ta tashi taje ta bud'e mata ta shigo ta zauna Raihanan ta gaishe ta, ta amsa a sake tana tambayar ta bakunta. Amsawa tayi a kunyace ta dan zauna a dakin har garin yayi sha sannan ta tashi zata fita Raihana tace ko akwai aikin da za'a yi? Girgiza mata kai tayi tace


"Akwai masu aiki karki wahalar da kanki, idan kin gama sha'awa zata shigo ta gyara miki dakin."


"Zan iya gyarawa ma Anty."


"Ban saki ba, kar ace ina wahalar da amarya." Tace tana dariya murmushi Raihanan tayi itama 


"Kinsan halin mutanen naki, jiya ma munsha fama da Daddyn su Amna wai akan me zan dawo dake, haka Kamal ma yayi ta mita suji kuma yanzu na barki da aiki ai sai kiji an aiko min da sammaci."


"A ah dai Anty."


"Ahaap, baki san halin su ba ai, sun iya son kansu."


"Me zaki ci breakfast, ko da yake ma nasan me ya kamata na baki." 


Ta juya ta fita ita kuma Raihanan ta hau zare zanin gadon da duk ya yayyamutse kamar an yi dambe a kansa.***Bacci ne a idon sa dan haka yana isa gidan tubewa kawai yayi ya haye gadon ya kwanta. Ba shi ya farka ba sai kusan sha daya, shima knocking ne ya tashi shi ya mike da k'yar muryar sa a chunkushe yace waye


"Bud'e ka gani mana." 


Adam yace da full confidence. Muryar sa Aryan yaji, yayi tsaye cikin tunanin abinda ya kawo shi a lokacin bayan sai da ya tabbatar ya kwashe kayan sa tas daga gidan. Sake knocking yayi da dan karfi, Aryan din dake tsaye ransa ya soma baci ya isa kofar ya bud'e yana kallon sa. Kallon sama da k'asa Adam din yayi masa sai kuma ya bushe da dariya yana rik'e baki


"Ina matar? Ko ba aure kayi bane ba? Naji ance kayi auren boye."


"Me ya kawo ka?" Yace a fusace fuskar sa na sauyawa nan da nan zuwa bacin rai 


"Relax." Yace yana wara hannun sa. 


"kamar yadda kake da iko da gidan nan haka nake dashi, so karka daga min murya please. Zuwa nayi na maka murnar aure a matsayi na, na dan uwanka. Sai kuma nagan ka a haka."


"Kana tunanin wai kana da waje a gidan nan Adam?"


"Yes ofcouse, baka sani ba? Ko da yake ba zaka sani ba nasan. Kamar yadda kake da iko da right da gidan nan haka nake dashi nima."


Tabe baki Aryan yayi yace 


"Ok yayi, zaka iya bani waje ko?"


Ya kama kofar zai rufe Adam din ya rik'e da sauri


"Ina matar wai? Ko dai ka kasa... Nooo don't tell me baka da wannan energy din, nooo." 


Sai ya rufe bakin sa da sauri yana dariya. Rufe kofar Aryan kawai yayi ba tare da yace komai ba. Yana jin dariyar Adam din cikin izgilanci ya wuce toilet ya sakarwa kansa shower ruwan ya dinga shiga simar kansa yana ratsa shi sosai. Ya dade a haka kafin ya dawo daidai sannan ya fito ya hau shiryawa a tsanake tamkar wani abu be faru ba. Shigar kananan kaya yayi masu kyau da aji ya saka sandal ya fito ya fice daga gidan yana jin hayaniyar Adam din kamar ba shi kadai bane a gidan ba ko kuma waya yake. Gidan Kamal ya wuce kai tsaye ya kirashi yana hanyar yace zai karaso. Lokacin Khadija na tayashi had'a kaya domin tafiyar tasa ta dawo yau saboda wayar da ya samu daga chan sama dole a yau zai wuce dama hutun nasa yaso yayi yawa dan dai shugaban su mutumin sa ne sosai. Zuwan Aryan din yasa ya bar ta, ta karasa hada kayan ya dawo falon wajen Aryan din da zuwan nasa haka urgent ya bashi mamaki. Sai dai a yadda ya ganshi a nutse tsaf ya samu kwanciyar hankali sosai har yayi masa maganar tafiyar sa da ta taso wanda da yaso sai yaje zai gaya masa amma ganin komai normal yasa kawai ya sanar dashi. Aryan din be nuna komai ba yayi masa addu'ar nasara sannan suka dan taba hira har suka gangaro kan shari'ar da za'a zauna gobe wanda Kamal din yaso yana nan za'a yi. Sam Aryan be fada masa abinda yake shirin faruwa ba, ya barshi kawai a goben suke saka ran za'a gama komai. 

   Har bayan azahar suna tare a gidan Kamal din, sai da Habeeb yazo daukar Kamal din sannan Aryan yayi masa sallama ya tafi. Company ya wuce duk da yau ba ranar aiki bace ba, ya bud'e office dinsa ya shiga ya rufe ta ciki, ya dade sosai har kusan tara yana wajen sannan ya fito ya wuce gidan sa dan ba zai koma main house din ba yasan Adam yana chan. Shiryawa yayi ya saka kayan sa da yasan zai bukata a booth din motar sa, wajen sha daya ya fito ya nufi main house din ya ajiye motar tasa ya dauki kayan ya saka a motar Daddy sannan yasa Yahya ya kaishi gidan Ya Nabeela. Kiran ta yayi suna daf da gidan ta kalli wayar ta kalli Ya Nabeela da ta shigo suna maganar abubuwan da take da bukata duk da tana jin nauyi da kunyar ta amma haka ta dan dake ta fada mata, sun so tsayawa yau ma bayan sun baro wajen gyara jikin amma babu lokaci tunda kuma suka dawo Ya Nabeelan ta sake fita tare da Dr Farouk din sai past 10 suka dawo abinda ya sa suke maganar a lokacin kenan. Da wuri Ya Nabeelan zasu tafi Lagos da safe tare da Dr Farouk din zata rakashi wani taro shiyasa kuma bata so a sake bata lokaci. Sake kira yayi a tunanin sa ko tayi bacci jin bata daga ba sai tasa wayar a silent ta tura masa text suna tare da Ya Nabeelan. Bayan kusan 30min ya Nabeelan tayi mata sallama ta tafi ganin dare yayi sosai. Fitar ta da minti biyar taji yana kwankwasa kofar, sai da tayi wani irin jan numfashi kafin ta tashi ta bud'e masa ya shigo ciki. Kofar da Ya Nabeelan tabi ta fita ya nufa ya murda key sannan ya dawo cikin dakin. Gaishe shi tayi a hankali maimakon ya amsa sai ya zauna ya jawota ta zauna a saman cinyar sa.


"Ya Nabeela tasa duk sauro ya gama cinye miki kafar miji." Yace yana zuro hannun sa ya zagayo dasu ta cikin ta ya hade su waje daya. 


"Ka dade sosai?" 


"Umm, kusan 40min."


"Da ka tafi gida."


"Me yasa?" 


"Dare yayi ai toh."


"Na sani ai, ke nake so na gani." 


"Sai Ka tafi?"


"Sai na kwana dai, dare yayi ma gashi da wuri zan fita, kinyi min addu'ar da nace kiyi min?"


"Um nayi." 


"Good girl, ki cigaba kinji?"


"Tam."


"Me zan samu?" Yace yana mata wani shu'umin kallo, irin kallon da in dai yayi mata shi toh fa shikenan. Wasa da yan yatsun ta da suka sha gyara dazu ta hau yi  ya kalli hannun da suka kasance dogaye zara zara ya rik'e su yana shafa fatar hannun da yaji tana wani irin sulbi da taushi. Gefen wuyan ta ya shafo a hankali ya yi baya da jikinsa suka fada saman gadon yana rik'e da ita. Batayi yunkurin tashi ba dan tasan ba zai taba bata dama ba, sannan a k'asan zuciyar ta tana son abinda yake wakana a tsakanin nasu sai dai ba zata nuna ba saboda kunya irin ta mace wadda shi namiji babu ruwansa da wani abu wai shi kunya musamman sababbin auren nan. Yau ya lura duk karantun da ya biya mata jiya ta dauka dan har wani bashi support take yi duk da tana cike da tsoro amma ganin ko kama hanyar abinda bata so din ma bayayi yasa ta saki jikinta sosai har ya samu damar yin yadda yaso da ita. Burin sa kenan dama, ta saki jiki dashi ko babu yawa domin yasan a duk ranar da me gaba daya ta faru akwai aiki babba. 

 Kamar jiya yau ma da asubah ya tafi sai dai basu hadu da Dr Farouk ba dan ko jiya yaji nauyi da kunyar sa sosai shiyasa ya fito yau da wuri akan sanda yake fitowa ya kuma chanja masallaci ba wanda Dr Farouk din yake zuwa ba. Daga nan ya wuce main house dinsu wanda daga chan ne zai karasa shirin sa kafin lokacin da za'a shiga court din yayi.

  Sanda ya koma Adam baya gidan, be san ko be kwana a gidan ba ko kuma ya fita da wuri bane saboda shari'ar oho, shirin sa kawai yake a tsanake ba tare da ya saka kayan su na lauyoyi ba, dan ba shi da plan din halartar zaman kwata kwata. Bayan ya gama shiryawa ya dauki motar Daddyn wanda ta jima ba'a hau ta ba, ya fice daga gidan.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post