Bukukuwan Hausawa Na Gargajiya Kafin Zuwan Baƙi

Bukukuwan Hausawa Na Gargajiya Kafin Zuwan Baƙi

Bukukuwan Hausawa Na Gargajiya Kafin Zuwan Baƙi

Buki ko biki na nufin taro na mutane da suke shiryawa domin nuna farin cikinsu a kan wata baiwa da Allah ya yi wa wani ko wasu daga cikinsu.


Ana gudanar da biki domin tunawa da wani abu muhimmi ko zagayowar wata rana. Biki al’ada ce wadda take da asali tun iyaye da kakanni. Kasancewar al’ummar Hausawa masu ƙauna da girmama junansu, ya sa idan wani abu na farin ciki ya faru ga ɗayansu sai su taru su taya shi murna, ta hanyar gudanar da shagulgula iri daban-daban da dai ire-iren bukukuwan Hausawa.


BUKUKUWAN HAUSAWA NA GARGAJIYA KAFIN ZUWAN BAƘI


1.Bikin Aure

2.Bikin Suna

3.Bikin Sallah

4.Bikin Shan Kabewa

5.Bikin Cika Ciki

6.Bikin Takutuha

7.Bikin Naɗin Sarauta

8.Bikin Kalankuwa

9.Bikin Buɗar Daji

10.Bikin Hawan Daba

11.Bikin Maulidi

12.Bikin Hawan Daushe

13.Bikin Saukar Al-Kura’ni

14.Bikin Mutuwa

15.Bikin Walima


MENE NE AURE?


Aure yarjejeniya ce tsakanin namiji da mace ko amincewar dangi bisa wasu ƙaidoji na al’ada ko na addini. Bayan zuwan addini wannan yarjejeniya kan ginu a kan wasu sharuɗɗa ko ƙa’idoji da suka haɗa da, waliyyai da shaidu da sadaki da kuma lafazin yarjejeniya.


Kafin zuwan addini riƙon aure ya na hannun mace, haka kuma mutum ya na da ikon ya auri mata ko nawa yake so, domin yawan matanka, yawan arzikinka. Haka kuma, ita ce za ta yi ayyukan gona ko kasuwanci da kuma ayyukan cikin gida kamar; Girki da kula da yara, da kula da cikin gida, da kuma kula da maigida da kuma kanta.


Bayan zuwan addini hakkin ciyarwa da shayarwa da tufatarwa da ilimantarwa da muhalli da tsaron lafiya duk sai suka koma a kan namiji.


Masana da manazarta sun bada ma’anar aure kamar haka:


1. Bunza, (2006) ya ce, “Aure wata hanya ce ta ƙulla zamantakewa tsakanin namiji da mace, wadda babu abin da zai raba su sai mutuwa, ko kuma idan matar ta gaji ta yi tafiyarta ta samu wani mijin.”


2. Yahaya, (2001) ya ce, “Aure wata hanya ce ta ƙulla zaman tare tsakanin namiji da mace, ba tare da iyakancewa ba sai idan mutuwa ta raba. Kuma a kan tabbatar da hakan a bisa amincewar ma’aurata da kuma waliyyansu tare da kafa shaidu.”


NEMAN AURE


A zamanin da can, Hausawa sukan gudanar da neman aurensu a bisa tsari na al’adunsu daga lokacin da iyayen yarinya ke amincewa mai neman auren ɗiyarsu wato saurayi, zai tabbatar da soyayyarsa ga yarinya ta hanyar yi mata kyauta da abubuwan nuna ƙauna. Wato, zai rinƙa yi wa yarinya liko a lokacin wani biki da ke tara ƴanmmata da samari ko a dandalin da ake rawa da waƙa.


Haka kuma, zai dinga taimakon iyayenta wajen aikin gona ko wasu ayyukan ƙarfi.


A kan kai kayan fira wanda a kan ƙumshewa a ba wata tsohuwa ko wani dattijo ya kai gidan iyayen yarinya.

< p>

Sannan idan daga baya an tsaida magana, sai saurayin ya kai dukiyar aure a raba wa dangi, saboda kowa yasan cewa, ɗiyarsu ta samu miji, sai a tsayar da ranar aure (baiko).


BAIKO


Shi ne tsayar da ranar da za a ɗaura aure, in da za a aiko da kayan sa rana daga gidansu Ango wanda za a rarraba wa dangi domin kowa ya tabbatar da cewar an tsayar da ranar ɗaurin auren su, bayan nan sai saura mako guda ko biyua ɗaura aure a kan aiko da Lefe daga gidan su ango.


LEFE


Shi ne wanda a kan sami akwatin kaba wanda aka saka aka yi masa ado da kalaluwan zanzahur a zuba zannuwa irin na saƙi da ƴan kayan kwalliya na mata, a wannan lokacin, dangin Ango kan ɗauko kayan su kai gidan su amarya.


A lokacin da za a kai waɗannan kayan al’ada, ƴan kai kayan za su rinƙa tafiya su na guɗa da shewa domin nuna murnar su, su kuma gidan su amarya za su tare su da murna da karramasu da abinci da abun sha, daga bisani su kawo tukwaici su ba su, daga ƙarshe taro ya watse.


TURGEZA


Yadda ake gudanar da ita, za a je gidan waɗansu mata guda Goma Sha Biyu waɗanda aka tabbatar ba su taɓa yin yaji ba bare ma har a kai ga batun saki, za a ɗebo ruwan waɗannan gidajen sai a samo koko a zuba a ciki a haɗa lalle da turaruka a gauraya, a fito da amarya tsakar gida, yayyan mamanta ko na babanta za su yi mata wannan wankan za a tuɓe ta, a kifa turmi a tsakar gida ta hau a samo Goro guda Uku manya a saka mata a baki, ɗaya a gefen dama ɗaya a hagu, sai ɗaya kuma a tsakiya don gudun kar ta yi raki ko ta yi magana, ana wankewa ana durzawa har sai ya ƙare.


KAMUN AMARYA


Ana yin sa ne a ranar ɗaurin aure, Amarya takan gudu ta bar gida, za ta tafi can wani wuri ta ɓoye in da ba wanda ya sani, daga nan uwar ɗakinta za a tafi nemanta za a rinƙa bin gidaje gida-gida don neman Amarya, ƙawayen amarya za su biyo ta a baya idan uwar ɗakin ta gano ta, haka za ta damƙo hannunta ta na kuka, ƙawayenta kuma su na rera mata waƙa.


ƊAURIN AURE


Ya na nufin tabbatar da saurayi da budurwa a matsayin ma’aurata a bisa wasu dalilai, ɓangaren iyayen Amarya da na Ango za su gayyato ƴanuwa da abokan arziki da kuma makaɗa da maroƙa a ranar ɗaurin aure.


Za a taru ne a ƙofar gidan maɗaurin auren yarinya, in da za a kawo abinci iri daban-daban, gefe kuma ga makaɗa da maroƙa sa’annan ana gudanar da wasu al’adu a wurin kafin ɗaurin aure, wanda uban Ango zai ba uban amarya kaya irin su Bokiti, Buta, matashin Kai da Fitila, idan har ya kasance ba a zo da irin kayan ba to har auren ana iya fasawa.


Za a ba uban amarya waɗannan kayan sannan a ɗaura aure.


JERE/DANKI

Al’adar Hausawa ce wadda ake yi bayan an ɗaura aure, jere ya na nufin ƙawata ɗakin da za a kai amarya, iyayen amarya da ƴan uwanta sukan sai mata kayan ɗaki na al’ada kamar; Gado, Katifa, da sauran tarkacen ɗaki da na ayyukan cikin gida a je a jera a ƙawata ɗakin da ango ya tanada.

BUƊAR KAI

Shi ne a cire kayayyakin da aka lulluɓe amarya da su. Ana rufe fuskar amarya ne domin a ranar ake kammala yi mata gargaɗi da nasiha, a wasu lokutta idan gidan Ango ɗaya ne da na mahaifansa ana damƙa amarya ne hannun iyayensa, sai a yi buɗar kai a nan tare da ƴanuwansa.

A wasu wurare kuwa, ko da gidan Angon daban ne da na iyayensa ana aiko wata yar uwarsa da za ta karɓi Amarya da ƴan rakiyarta. Dangin Ango sukan biya kuɗi yayin da dangin Amarya za su karɓa sai a cire wannan lullubin da aka yi wa Amarya shi ne an yi buɗar Kai, wasu kuma daga nan sai a yi wa Amarya kitso da kwalliya da sauransu.

KAI AMARYA

Bincike ya gano cewa, a wurin rakiyar Amarya a kan haɗa mutane da yawa tun daga mata dangin Amarya da ƙawayenta da abokan miji da dai sauran su.

Sai kuma a nufi gidan Ango ana tafe ana raira waƙa iri daban-daban waɗanda suke da taken karantarwa ga Amarya, kuma wannan waƙa ta na ɗauke da saƙon ban haƙuri ga Amarya, domin an raba ta da iyayenta an kai ta can wata duniya daban.

Haka dai za su ci gaba da waƙensu har a kai Amarya ɗakinta, bayan nan sai ƴanmata su tsaya a yi sayen baki.

SAYAN BAKI

A wannan lokacin ana ciniki ne tsakanin ƙawayen Amarya da na Ango kafin abar Amarya ta yi magana, idan aka sami daidaiton abin da za a biya, sai kuma kowa ya tafi ya bar miji da matarsa, kuma mafi sayan baki da daddare ake yin sa.

Source: Taskar Nasaba

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post