Sarkin Bichi ya kai wa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ziyarar Sallah

Sarkin Bichi ya kai wa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Gida-Gida ziyarar Sallah
BBC/Kano State Government

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf (na farko daga dama) ya karɓi baƙuncin Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero a gidan gwamnati a wani ɓangare na gaisuwar Sallah.

Shugabannin sun tattauna kan al'amura da dama da suka shafi jihar, musamman tun bayan da Abba ya karɓi ragama a farkon watan Yuni, inda gwamnatinsa ke ci gaba jawo muhawara game da rushe-rushen da take yi.

Cikin abubuwan da suka tattauna har da batun sabon tallafin karatu da gwamnatin ta ɓullo da shi wanda kuma zai fara aiki a watan Satumba, a cewar gwamnan.

Sarkin wanda ƙani ne ga Sarkin Kano Aminu Ado, ya gana da gwamnan bayan yayan nasa ya kai irin wannan ziyarar a ranar Juma'a yayin Hawan Nassarawa.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post