💖💖 NIHAAD 💖💖
Page 48
NIHAAD
Nihad ta fito bandaki kenan taga mutum zaune edge din gado wayarta a hannunsa yana dube duben wayar with full concentration, lokaci daya mamaki da tsoro suka cikata, gashi bata san for how long yake dakin ba don tana dawowa daga amso charger wajen Mimi ta jona wayar sannan ta shiga wanka, tana tafiya a hankali taje inda Hijab dinta yake ta dauka ta saka don towel ne kadai jikinta, ta juya tana kallonsa, she don't think ya san ta fito daga bandakin ma don gaba daya fa hankalinsa na kan wayarta, tana jan kafa ta tafi can karshen gado ta tsaya tana ɗan leka wayar trying to see what he is doing with it, a kan WhatsApp ta gansa yana duba duk chat dinta da Ayman tun daga farkon sa, sosai taji gabanta ya fadi, and she started thinking of what to do next, though ba wai dirty chat suke da Ayman din ba, but he use to chat romantically sometimes saboda wayayye ne gayen, ta kalli fuskarsa taga babu yabo babu fallasa yana ta scrolling chat din slowly, a hankali Nihad ta nufi kofar dakin gabanta na faduwa ta murda taji a kulle sannan ba makullin a jiki, ta juyo tana kallonsa kamar zata yi kuka, gaba daya hankalinta yayi mugun tashi, har at last ya gama karance kaf chat din ya ajiye wayar staring at the wall still fuskarsa babu yabo babu fallasa, hankalin Nihad ya kara tashi, she wish kofar a bude yake da tuni ta fice ta koma parlon Mami, shi kam for the next 2 minutes bai ko kalleta ba, ko tunanin me yake oho, sai kuma taga ya tashi ya dau wayar ya saka aljihu ya nufi kofa, ta bi sa da kallo har ya isa kofar yana kokarin budewa, da sauri tace "Ina zaka je da waya...." Bata kai karshe ba ya juya ya sauke mata wani lafiyayyen mari a fusace, ta dafe kuncinta da sauri with shock tana kallonsa baki bude, sai a sannan taga idonsa da ya koma kamar garwashi, ya fasa bude kofar ya fixgota ya hadata da bango cikin husky voice yana mata wani mugun kallo yace "I thought iskancin da kika yi a baya ya isheki ai? I thought it was enough for you ashe i was mistaken, ta waya kika ci gaba da iskancinki daga inda kika tsaya...." Nihad ta fashe da kuka sosai tace "Ni ban ta6a iskanci ba, ni ba er iska bace...." Ya daka mata tsawan da ya firgitata yace "Meye ban sani ba a kanki? Tell me, meye ban sani ba akan kazamin rayuwar da kika yi a baya? Idan zaki ma wani karyan baki bi maza ba don baki da kunya har ni za ki ma? Ke din da kika mayar da kanki taxi no garage, leaving home at night and returning back early dawn, kece warce naga kayan maye da Prophylactics a jakarki, what were you doing with them??? bayan haka har alcohol you do take..., bana tunanin akwai hotel ko club din da baki sani ba a garin kano, At times if i think of ur past life i regret my destiny of having to accept ur marriage for the sake of ur parents, i so regret that, ƙyamarki nake don ma ki ji ki sani babu yanda xan yi da aurenki ne, you are not worth being married to me, na fi karfinki ta ko ina, and i can never be comfortable to present you to anybody as someone i am marrying, kwanciyar hankalina kawai shine in dinga kawar da tunanin akwai aure tsakanina da ke, no responsible person will be proud to have u as the mother of his kids..... You have a dirty past, still not considering that shine kike chatting da wani katon banza har kina ce masa you have neva kissed all ur life, telling him no one have ever touched you before, ain't you ashame of lying? Ke da kika gama rabar da mutuncinki a hotels? Ina ce garin haka ne har aka samu wanda ya maki video ya sakar ma duniya, nasan duk zaman da kike yanzu u are uncomfortable without a man tunda kin riga kin saba, shine kike biye wani namijin da aure a kanki ku ke chatting har da phone calls saboda ke baki san darajan aure ba" Nihad ta daga kai hawaye na sauka idonta tana kallonsa tace "Duk na ji, ka rubuta min takardata ka bani" Ya wani fizgota yana mata mugun kallo yana huci yace "Who are you to tell me what to do?? To baxan bayar ba, idan kin isa ki rubuta ma kanki takardan" Yana fadin haka ya turata har sai da ta kusa faduwa, ya nufi kofa kamar zai tashi sama ya bude kofar ya fice daga dakin. Hajiya Amina na parlonta tare da Aunty Hassana dake cin fruit salad, Hajiya Amina tace "Ke kin ta6a jin inda aka kai kudin aure har dubu dari bakwai, ba wai sadaki ba, sannan a hada da buhunhunan shinkafa? Wallahi abun yayi mugun daure min kai" Aunty Hassana ta ajiye bowl din hannunta tace "Toh ke kuwa ba mayunwata bane, ai ita fatiman ce xata ce a hada da shinkafar, ni fa ko a gyalena batun auren nan, don in dai wannan auren ne wallahi baxa ayi sa ba ina da assurance din hakan, don da dai Khalil yayi aure a waje gwara ya dauwama haka ba aure, in ma duniyanci xai yi shi yafi komai sauki wallahi" Hajiya Amina dai ta tabe baki bata ce komai ba, Aunty Hassana tace "Banda babana ya tsaya shiririta ai shi zai fara auren a gidan, kuma yanzun ma bai baci ba ya dawo shima yayi auren kawai shi ma ayi masa abinda xa ayi masa" Hajiya Amina tace "Ba gobe kika ce yana hanya ba?" Aunty Hassana tace "In sha Allahu kuwa" Hajiya Amina tace "Toh kuwa baxai juri ganin sabon walakancin khalil a gidan nan ba, dama can kinsan ba jituwa suke ba" Aunty Hassana tace "Ai dalilin da yasa na takurasa kenan ya dawo, Babana ne zai raga masa? Sai dai in bani na haifesa ba kuma" Hajiya Amina ta kyalkyale da dariya tace "Yana dawowa ki takura masa ya fiddo mata shi ma a masa auren tunda abun en aure aure ne" Aunty Hassana tace "Ke dai ki zuba ido mana, gwara shi auren zai yi, can kuwa kashe kudin xa ayi a banza babu zancen auren" Sallama aka yi bakin kofar duk suka yi shiru. Umma ce zaune dakinta tana magana da Nihal, Umma tace "Ke in zaki bude baki ki min magana ki bude, meye kuma ana maki magana kiyi ta amsawa mutane ciki ciki, ko baki da lafiya ne dai?" Nihal tace "Ce maki nayi ya turo min daxu" Umma tace "Nawa ya tura maki?" Nihal tace "Dubu hamsin" Umma ta tabe baki tace "Me dubu hamsin xai maki, ko dai baki ce masa kayan abinci xa ki siya ba?" A hankali Nihal tace "Na gaya masa" Shiru Umma tayi, don da Nihad ce ai dubu dari zai saka mata ko fiye da haka, shi sa fa ita bata jin ko dar akan abinda ta aikata, don akan Nihad sun ga abubuwa iri iri a wajen Abba a gidan nan ita da yaranta, haka ya kwashi kudi ya kai ta Maryam Abatcha dab da bikin Kamila bayan ga kayan gadon da kamila ta zaba ya ki siya mata wai yayi kudi, wanda a lokacin ko dubu dari takwas kayan gadon basu yi ba, tana ji tana gani kuma ya tura mata Nihal dinta Zaria, kuma ko nunawa a fuska Umman bata yi ba balle a gane taji haushi, Umma tace "Toh ai Shikenan, kawai ki kira farooq ko Usman su kara maki, ita er son ma ko biyar ta daina samu ai yanzu, wa ma yasan isilinta" Nihal dai bata ce komai ba, Umma tace "Ke in fa baki da lafiya ne nasanki da zurfin ciki ki dawo gida a maki treatment kar kije ki jaza min jaraba, lafiyarki kuwa?" Nihal tace "Lafiya ta kalau ni" Umma tace "Toh ai shikenan, Kina da labarin Nihad?" Nihal ta girgiza kai tace "Aa" Umma tace "Allah sarki, kamar ba ayi ta ba, ko ana wani kauyen yanzu kuma, yanzu kenan wayar dreban baya shiga?" Nihal tace "Ehh" Umma tace "Toh Allah ya kyauta, ya wannan saurayin naki ɗan senator, in ji dai kin ci gaba da kulasa banda walakanci ko?" Nihal tace "Eh" Umma tace "Yana zuwa wajen naki?" Nihal tace "Eh" Umma tace "To madallah, ki dai kula banda cewa xaki bi sa ko ina komin takuraki da zai yi, kuma ban amince da tadi a mota ba, sannan iyakan ku cikin makaranta, ko wajen makaranta ban yarda ki bi sa ba, banda dai mata sun zama abinda suka zama da sai ince ko hira xaki fita in ya zo ki dinga fita da roommate dinki wannan da kika raka garinsu, to yan matan ne sai su maka snatching" Ita dai Nihal bata ce komai ba, Umma tace "Ki dai kula don Allah kin ji Nihal?" Nihal tace "Toh" Umma tace "Naga kamar bacci kike ji sai da safe" a hankali Nihal tace "Allah ya tashe mu lafiya" Umma tace "Ameen auta" Daga haka ta katse wayarta, ta shiga neman number Husnah, ita kam tana son taji wani hali Nihad take a kauyen da dreba ya kai ta, yana fara ring Husnah ta daga, Bayan sun gaisa Umma tace "Kwana biyu ko leko mu kun daina" Husnah tace "Wallahi kuwa, nima ai banji dadi ba kwanaki, na ma kwana biyu a asibiti da kamar xa a min aiki a ido sai kuma Allah ya takaita, wallahi ban dade da fara fita ba yanzu haka, don idan na fita cikin rana idon kamar ya cire don azaba" Umma tace "Subhanallahi, to Allah ya tsare, Allah ya kara lafiya, gashi bamu da labari ai da ko dubaki ne sai in zo inyi" Husnah tace "Ameen Umma, ya mutanen gidan?" Umma tace "Lafiya lau wallahi, nace dai yau bari in kiraki in ji ko kina ji daga wajen kawarki, kamar anyi ruwa an dauke yau wata daya kenan ni Sumayya" Husnah tace "Wallahi jiya jiya su Naf suka gama wannan zancen, Umma kinsan wani abun mamaki kuwa??" Umma tace "Aa me ya faru?" Husnah tace "In gaya maki kafin su bar garin nan ina kwance asibiti sun je dubani, turanci a bakin dreban nan kamar bature" Umma tayi shiru, can tace "Turanci kuma?" Husnah tace "Wallahi" Umma tace "Aa to ai dama yace yayi sakandari, dama dole xai iya turanci ai in dai ba dakiki bane, amma tabbas iyakarsa dai sakandari" Husnah dai tayi shiru, can tace "Yanzu ko Abba baxa kice ya tuntubi...." Da sauri Umma tace "Aa ko xancen su bai so gaskiya, yanzun nan hawan jininsa sai kiga ya tashi, shi yasa na daina gaba daya, dama wai inji inda suke ne" Husnah tace "Shekaranjiya saurayin Nihad din ɗan janar jikamshi ya kira Naf asking for her whereabout, muka ce ai mu ma bamu sani ba gaskiya..." Umma tayi shiru, can tace "Shikenan dai, shi banda abunsa ko da ba a mata aure ba ta ina iyayensa xa su amince da auren wata Nihad, ai da ko Aminata ce sai ya nema tunda ita Nihal na da wani saurayi, ko ɗan minister ne ko sanata ni dai na manta yanda tace min, kuma yana sonta sosai sai kinga kudin da yake kashe mata, don da bata ma kulasa ni ke ta tursasata ta dinga kulasa bata san waye mijinta ba, kwanaki har mota yace xai bata taki, nima kuma ban goyi bayan hakan ba" Husnah tace "Gaskiya kam" Umma tace "Shikenan, sai dai yanda ta yiwu" Husnah tace "Muna nan dai muna binciken inda xa mu samota in sha Allah" Umma tace "Toh don Allah ku kokarta" Nan suka yi sallama Umma ta katse wayarta. Da safe Mimi ta gama shiryawa zata tafi makaranta wajen karfe goma, bayan ta sallami Mami ta kalli Khalil dake parlon yana danna wayarsa tace "Yayanmu sai na dawo" ya kalleta yace "Isn't ur frnd going to lectures?" Tace "I met her lying down tace baxata ba, i don't think she is even okay" Bai ce komai ba har ta fita daga parlon, Bata jima da fita ba Noor ma ta shigo parlon ta je ta sallami Mami sannan ta fito, tana kallonsa tace "Yayanmu amma dai yau zaka je wajen Nadeeyah ko? You know u didn't try yesterday, she made all u requested but u ended up not coming, you just spoilt her mind" Yace "Zan je" Tace "Better, cause she is so sad" Shi dai bai kara ce mata komai ba har ta fita daga parlon, wayarsa ne ya fara ring ya duba yaga Nihal ce, tun jiya da daddare ya kirata to check on her ya ji ta on another call kuma bata kirasa ba sai yanzu, Bayan sun gaisa jin she sounds dull yace "Are you okay Nihal? You sound stressed out" Nihal tace "I am fine, i just woke up, ya Nihad?" Yace "Alhamdulillah, yaushe za ku fara exam?" A hankali tace "There is still time, CA muka gama yanzu" Yace "Are you sure baxa ki je gida ko weekend ba so that u can get enough rest? Naga kamar wannan semester din da zafi" Nihal tace "Toh xan je" Yace "Or will you like to come over to ur sister?" Nihal ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "I will love that" Yace "Ohk then, i will talk to farooq about it later, idan ya amince sai in zo Zarian gobe in daukeki" a hankali tace "Okay, i am grateful" Yace "Take care dear" Tace "Sure" Daga haka ya katse wayar, Mami ta fito, Khalil na kallonta yace "Mami are you going out?" Tace "Ehh xa mu fita da su Amina, xa mu je wani gaisuwa ne..." Yace "Ohk, are you staying long" Tace "Not at all, but i might branch Hajiya Safeenah's place" Yace "Ohk Allah ya tsare" Tace "Ameen, ina da magana da kai idan na dawo" Yana kallonta yace "Maganar me Mami?" Tace "Sai dai na dawo" Ya bi ta da kallo har ta fita daga parlon, yana jin fitarsu daga gidan with escort bayan kusan minti sha biyar, mikewa yayi ya fita daga part din Mami. Dakinsa ya koma ya kwanta, deep in his thought, kiran Nadeeyah ne ya shigo wayarsa, ya dinga kallon wayar har ya katse, can ya dauka ya kirata, kamar me bacci yace "I will call u later Nadeeyah, i am still on bed..." Jin bata ce komai ba yace "Hello" Tace "Ohk" Katse wayar yayi ya mike zaune, bayan kusan minti biyar ya kalli agogon dakin dake nuna karfe goma da rabi, tashi yayi ya dau wayar Nihad dake gaban mirror dinsa ya fita, daren jiya Ayman ya kirata yayi sau biyar, yau da safe ma still sai da ya kira duk Khalil na kallon kiran, direct ya nufi dakin da Nihad take ya bude kofar ya shiga, kwance ya sameta ta rufe har kanta da duvet, ya karasa ya cire duvet din ya jefa mata wayar a gefenta, fuska daure yace "Kirasa yanzun nan kice kada ya sake kiranki, do that immediately...." Ko bude ido Nihad bata yi ba balle ta kulasa, ya wani hade rai yace "Ba dake nake ba?" Tashi tayi ta sauka daga kan gadon zata nufi bandaki ya fizgota, ta fashe da kuka tana turasa da dashashiyar muryarta tace "Ni ka kyaleni wallahi, kai me bakinka yake yi da baxa ka gaya masa da kanka ba sai ni??" Yana mata wani kallo yace "Ni kike gaya ma haka?" Cikin tsawa tace "Na fada maka din, tell him ur self and stop bothering me, ko kuma ka kira Aunty Maryam ka gaya mata ita ta gaya masa" Sai kuma ta fashe da kuka ta durkushe wajen, tayi me isanta duk yana kallonta sannan ta mike ta figi Hijab dinta zata fita ya fixgota, ta buge hannunsa cikin rawan murya tace "Ni ka kyaleni, baxan sake kwana a gidanku ba, gwara in tafi wajen grandma dita nasan she will accept me, it's not as if I don't have anywhere to go...." Yana mata wani kallo yace "Da izinin wa zaki je wajen nata??" Cikin kuka tace "Wallahi idan baka barni na tafi ba sai na gaya ma kowa a gidan an mana aure da kai, kaji har na rantse" Da mamaki yake kallonta baki bude, xata kwace kanta ya riketa gam yace "Ohk, kinsan an mana auren kike kula wani farin katon banza a waya har kike ce masa you love him too?" Ta hadiye kukan da take ta kallesa tace "Kai kuma da kake kula wata farar katuwar banza fa? Sai ni ce baxan kula wani ba...." Duk da dariyar da ta basa ya kara murtuke fuska yace "Ohh kika ce sai kin kulasa?" Tace "Kuma baka isa ka hanani ba, don bansan da auren kowa a kaina ba, i neva accepted ur marriage even for one second, nasan kuma da shi ne he is too gently and calm to raise his hand on my face, and dole ka sakeni in auresa because i am beginning to love him...." Kuka take sosai tana son kwace kanta amma yaki saketa yana kallonta babu ko kiftawa, ta fara kai masa duka a kirji ganin ya ki saketa, lokaci daya ya dauketa cak ya nufi saman gado da ita ya jefata kai, ta hadiye kukan da take tana kallonsa tana komawa baya ganin yanda ya daure fuska yace "I will show you ni mijinki ne yau, and you have nothing to do about it" Kawai taga ya juya ya yaje ya sama kofar dakin key, ta yi wani tsalle xata shiga bandaki, yayi hanzarin fizgota kafin ta shiga.....
TWINS NEEE.... BIYU TA FI DAYA