Tabarmar Ƙashi page 17 by H U G U M A

Tabarmar Ƙashi page 17 by H U G U M A

 

Tabarmar Ƙashi page 17 by H U G U M A

*H U G U M A*


_*TABARMAR ƘASHI*_💔

 

*Arewabooks: huguma*

https://arewabooks.com/u/huguma


Page 17



         Wani abu ne ya tasowa saima,yayi mata tsaye a wuya,ta riga ta saka hannu kan dokar yin biyya ga wanda yake sama da office dinka,me yasa bata nema matsayin president ba?


"Neman kusanci da taoufeeq" zuciyarta ta bata amsa kai tsaye,ajiyar zuciyar baqinciki ta sauke,ta koma tayi relaxing cikin kujerarta tana qarewa qofofin guda biyu dake facing dinta kallo, zuciyarta na wani irin tsalle cike da luguden kishi,har tsahon wani lokaci toufeeq din zai kwashe kebance da wannan kyakkyawar halittar data bar mata sassanyan turarenta na yawo cikin dukka qofofin hancinta?.


           Cikin nutsuwa kuma dauke da sallama ta tura qofar office din. Kyakkyawan dattijone da shekaru sam basu samu nasarar ture kyakkyawan fuskar da Allah ya mallaka masa ba,fari ne sol,farin dake gwada tashen kyau da farin daya zuba zamanin quruciya,yana zaune saman sofa qwaya daya dake cikin office din,ya dora qafarsa daya kan daya,system dinsa na saman qafar tasa yana dannata cike da qwarewa.


           Cikin kamala ya waiwayo yana amsa sallamar tata,idanunsu suka gauraya,kwarjininsa da kuma kamalarsa suka cika idanun sãahar,yayin da murmushi ya wadaci fuskarsa


"Lale maraba da 'yata,president dinmu" dattijon da shekarunsa suka suka rufa sittin ya fada yana sauke qafafunsa qasa. Da dan sauri ta daga kanta daga sunkuyar dashi din da tayi da farko tana duban dattijon duba na mamaki,ita dai zata iya cewa kaf rayuwarta yaune karon farko data fara ganinsa ma gaba daya,sani kuwa saidai na fatar baki kawai wajen yaa muhyi,to amma shi din ya akayi yasan wace ita


"Daina mamaki diyata,kamanninki da d'ana muhyiddeen ta bayyana sosai a fuskarki....." Cikin girmamawa qaramin murmushi ya subuce mata,bata taba jin ance suna kama da yaa muhyi ba sai yau,tana shirin gaidashi ya tareta


"Koma ki shiga resting room ku jirani keda d'an uwan naki" ya fada cikin kulawa. 


"Dan uwana?" Ta tambayi kanta cikin mamaki,waye cikin gidansu yazo company din ba tare data sani ba?,kodai yaa muhyi ne bai nutsu ba sai daya biyota?,bata sani ba,saita juya a nutse taja masa qofar ta fito.


           Qofa ta biyun ta dosa tana takawa a nutse,zuciyarta na qawatuwa da karamcin tsohon da kuma kirkinsa. Tsaiwa ta danyi kadan tana sauraren muryar dake fita daga dakin,wata irin husky voice me zurfi da wani irin amo,cikin fada da kuma tsawa muryar ke fita,saidai kuma a nutse sautin yake fita kuma a jejjere,cikin ginshiri da wani abu da yayi kama da QASAITA.


        Hannunta ta sauke daga kan handle din,tadan yamutsa fuskarta kadan,zuciyarta na mata fatan Allah yasa ba halittun maza aka tara a dakin ba,muddin hakan ta kasance bata jin zata iya dogon zama a tattaunawar tasu. 


          Cikin bawa kai qwarin gwiwa ta sake dora hannunta saman handle din,kalmar da taji ta fita a bakin mamallakiyar fusatacciyar muryar me zurfi yasa ta sake dakatawa


"You are fired,stupid woman" cikin qasa da second biyar qwaqwalwarta tayi mata rewinding,sak irin muryar da taji tana magana da wata mace cikin tsawa a bristol palace kwanakin da suka wuce,daga bisani kuma qarar mari ya biyo baya,qarar marin da ko a yanzun sai data sanyata rintse idanunta kamar a lokacin ake yinsa,ta kuma damqe hannunta abinda ya sanyata murda handle na qofar ba tare data shirya ba,saiji tayi ta tafi kai tsaye zuwa cikin dakin.


         Cak ta tsaya daga bakin qofar,idanunta yana nutsawa ga tsakiyar dakin. Kallonta bai sauka a ko ina ba sai akan budurwar dake sharban kuka,kyakkyawar budurwa wadda zubin dressing dinta ke nuna zallar iya gayunta da kuma wayewarta. Dauke idanunta tayi daga kanta tana jin zuciyarta na zafi,ta sauke a hankali a kansa. Tsayyayen namiji sosai mai cikar haiba izza da kuma kamala,hannunsa daya yana sanye a aljihun wandon suit dinsa,daya hannun kuma yana danna wayarsa da zafi zafi. Dai dai sanda yake sanya wayar a kunnensa ya juyo,idanunsu suka sarqe guri daya.


          A tare suka sake janye idanunsu kamar dai wancan karon,zuciyar sãahar cike da wani irin tsanarsa da kuma jin haushinsa,ko kadan maza basu da tausayi bare imani,suna amfani da raunin mata suna cutara musu,hakan wani karatu ne da take yawaita bitarsa a kwanyarta a duk lokacin da taga ire iren wadan nan rashin imanin na maza akan mata,saidai a yanzun shi din tamkar yana sake jaddada mata cewa haka tunaninta yake,karo na biyu data taba saninsa a rayuwa,amma duk sanda zata ganshi din cikin wulaqantawa da wofantar da kimar mata yake


"Ka sallameta da albashinta na wannan watan,ka hada dana watan gaba,banason ka nemeni akan wannan issue din,case closed" ya fada da murkakkiyar fuskarsa wadda ko kusa batayi kama data mutumin daya taba gwada yin dariya ba arayuwarsa,ko da yake a wajen mutane da yawa da suka sanshi haka suke kallonsa,sukan tambayi kawunansu harma da abokan huldarsu


"Wai shin yana dariya?"


"Shin wai ya taba dariya kuwa?"


"Ka taba ganin dariyarsa?".


           A nutse ta taka ta yiwa kanta mazauni saman daya daga cikin couches din dake zagaye da qawataccen dakin,wanda aka yiwa tsari me ma'ana da baiwa ruhi kwanya harma da zuciya hutu. Dai dai lokacin daya kammala wayar,a karo na biyu ya sake daga kai ya sauke sexy eyes dinsa a kanta,wani fushi ne ya sake taso masa,wacece ita da har zata shigo masa dakin hutawa a sanda yake da buqatar hutu ba tare da izininsa ba?,wacece ita da zata shigo dakin da ba kowa yake baiwa izinin shigowa ba,har ta yiwa kanta da kanta mazauni ba tare data nemi yardarsa ba?,me ta dauki kanta?,dukka wadan nan maganganun dake ransa,shigowar Dr mahmud JARMA ya datsesu daga kwanyarsa,sai ya maida dukka hannuwansa cikin aljihun wandonsa,ya tattara hankalinsa ga mahaifinsa.


           Sosai yake mata kwarjini da wani irin haiba dake bayyana a fuskarsa,don haka ta miqe tsaye sanda yake shigowar,cikin nuna girmamawa


"D'iyata ina fatan ban bata lokacinki ba ko?" Kanta a qasa tana murza zara zaran yatsun hannunta,cikin siririyar muryar nan dake da wani irin taushi da amo tace


"Babu komai abba" a hankali ya lumshe idanunsa yana zuqar numfashi da kyau zuwa hunhunsa,lokaci daya yaji wani abu me kama da rashin jituwa ya darsu a ransa,fitar sautin muryarta kawai yaji a ransa yarinyar batayi masa ba kwata kwata


"I hate it" ya fada can qasa yana sauraren muryar tata sanda take magana da abban nasa a karo na biyu. Haka kurum yaji zuciyarsa tana zafi,sai ya koma a hankali ya yiwa kansa mazauni akan daya daga cikin kujerun da aka tanadesu domin hutawar,wadanda zasu bawa gangar jiki qafafu da kuma baya daman zama Sosai su samu nutsuwa.


         Yana jinsu sanda dr mahmud yake zama saman daya daga cikin sofa din dake dakin,har zuwa sanda yake umartar sãahar data zame ta zauna saman lallausan carfet din da aka ajjiye tsakanin kujerun


"Tashi ki zauna saman kujera mana,wannan meeting ne zamuyishi tamkar sa'anni,bawai na uba da 'ya'yansa ba" yayi furucin sãahar din na sake shiga zuciyarsa,d'a'arta nutsuwarta da tarbiyya girmama na gaba data samu suna sake saka mata qaunarta tare da jinta a zuciyarsa tamkar TOUFEEQ dinsa. Murmushi ta danyi kadan,sannan ta koma saman kujerar kamar yadda ta buqata.


            A nutse ya waiwaya ya dubeshi,sai ya zuba masa idanu,yadda yayi kamar baya gurin da lumsassun idanunsa da eyelashes suka yiwa ado ya tabbatar 'yan halin sun motsa ko suna kusa,don haka yayi gyaran murya,ya kuma kirayeshi da sunansa na aihini


"Muhammad" kiran sunan da ya sanyashi ware idanunsa a hankali,a nutse ya rabo bayansa da jikin kujerar,ya zauna sosai hadi da crossing qafafunsa dake sanye da wata shiny black socks guri daya


"Ga khadijatou,itace sabuwar president na kamfanin nan da zakuyi aiki a tare,nake kuma fatan zaku kai kamfanin zuwa tudun mun tsira,inaso ka dauketa tamkar NADEEYA,infact....na damqa amanarta a hannunka kamar yadda yayanta na damqamin" idanunsa yadan lumshe kadan sannan ya budesu lokaci guda,yana jin maganar abban nasa wani iri,ba aiki tazoyi don a biyata ba?,ko raino aka kawota da za'a buqaci a bata kulawa?,kudi tazo nema fa,an yarda za'a biyata ita kuma ta yiwa kamfani aiki,fine.......ba shikenan ba?.


"Na yarda da kaifin basirarta,na tabbatar kuma idan kuka hada gwiwa,kuka hada qarfi da qarfe za'a samu kyakkyawan result din da akeso" maganar abban a gaba ta biyu ta sake katse masa tunaninsa. Baiko tsaya din ta bakinsa don yasan halin kayansa,ya waiwaya ga sãahar data nutsu tana sauraren maganganun dattijon,duk da tafin hannunta take murzawa a hankali 


"Khadijatou,ga MUHAMMAD nan,a matsayin yayanki yake,kada kiji nauyi,idan kina da buqatar wani abu,koma meye ki tambayeshi,bashi da maraba da muhyiddeen,kinji ko?" Kai ta gyada masa,a taqaice tace


"In sha Allah,we will do our best"


"Barakallahu lakuma,zanyi alfahari da hakan".


           Duk su biyun ya saka a gaba yana nuna musu wasu muhimman abubuwa da suka shafi company din wadanda su basusan dasu ba,toufeeq na hannun damansa,ita tana daga hagunsa,a lokacin idan ka shigo zaka dauka duka 'ya'yansa ne,shi kansa cikin zuciyarsa sai daya ji hakan.


           Tsahon wasu mintuna kusan arba'in da wani abu sannan ya dakata yana dubansu bayan ya kalli tsadajjen agogon hannunsa,ya dan saki murmushi saman dattijuwar fuskarsa


"Inajin a nan zan tsaya,kusan muhammad kasan komai,zan barka da khadijatu,sauran abinda ya rage saika qarasa nuna mata kayi mata bayani,for the first time zatayi aikin kamfani,but tana da talent sosai,zan wuce kada nayi missing flight" ya furta yana miqewa. Dai dai lokacin da daya daga cikin guard dinsa yayi knocking qofar bayan ya samu alert dake nuna Dr din yana buqatarsa. Komai ya tattarawa uban gidan nasa,dr ya miqe yana duban toufeeq da shima ya miqe


"Koma ka zauna,ku qarasa kada lokacin tashi yayi" yadda yayi masa sallama haka itama sãahar,cikin girmamawa da ganin kimarsa,ya juya ya fita a office din,yana jin farinciki har cikin zuciyarsa.


           Shuru ne ya ratsa office din tamkar babu sauran wani me rai,shi din yana daga saman kujerarsa,yayin daya dora sambala sambalan qafafunsa akan leg rest na jikin kujerar,yana kuma sarrafa computer dinsa cikin qwarewa da hannu daya. Ko sau daya bai dago kai ko yayi wani motsi da zai nuna yasan da mutum cikin office din ba,dai dai lokacin da sãahar ke zaune don cika umarnin dattijon,wayarta itama take sarrafawa,lokaci lokaci tana duba agogon hannunta,tana jiran kuma lokacin data dibawa kanta ya cika tabar masa office dinsa.


          Kowanne a cikinsu jin kansa ya hanashi ya fara tankawa dan uwansa,cikin zuciyar sãahar tsanarsa da haushinsa ne fal suka danqare mata,ba tun yau ba tasan baisan darajar diya mace ba,bai martaba kimarta sam,a nasa sashen kuma ji yake sam batayi masa ba,tunda suke da Dr bai taba ganin mutumin daya jawo jikinsa har haka ba,farat daya ya maidashi tamkar ahalinsa,ya bashi dukkan yarda ya bude masa sirrinsa,yasan halin mata sarai,basu da kirki ko kadan muddin suna da wata manufa akan abu......tofa basa ji basa kuma gani harsai sun cimma muradinsu,suna iya komai,hakanan suna kuma iya jure komai har sai sun cimma gaci,musamman akan KUDI DA DUKIYA,suna sa masifar son kudi,tamkar wata halitta ce aka dasata cikin jininsu,basayin komai don Allah,bayason shi ko wani nasa ya sake fadawa MASIFA DA TARKON MACE,wannan wani HUKUNCI ne nashi da ya jima da yankewa akan kowacce mace idan ka debe MUTUM UKU RAK cikin rayuwarsa.


          Sai da ya mula don kansa sannan ya janye hannuwansa da idanuwansa duka daga kan computer din,ya sarqe yatsunsa cikin na juna yana fitar da sassanyar siririyar iska daga bakinsa,ya maida shanyayyun idanunsa dake da wani irin qarfin fusgar hankali a muhallin da take sai kuma ya janye yana jin wani qyashi yana kamashi,dai dai sanda take miqewa a nutse cikin nata jin kan,ta zura takalmanta a nutse ta fara takawa zuwa bakin qofa


"Hey,da alama bakisan policies na aikin kamfani ba" ya jefa mata magabarya nutse ba tare daya kalli inda take ba,tsaiwa tayi cak,sautin muryarsa data tsana tana ratsa kunnuwanta,kamar tayi gaba,sai taga ya kamata atleast ta tsaya ta fuskanci wannan izzar tasa,don haka ta waiwayo cikin nutsuwa ta zube idanunta fes cikin nasa


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post