Tabarmar Ƙashi page 28 by H U G U M A

Tabarmar Ƙashi page 28 by H U G U M A

 

Tabarmar Ƙashi page 28 by H U G U M A

*H U G U M A*


*_TABARMAR ƘASHI_*💔

https://arewabooks.com/u/huguma


Page 28



         Dif dakin yayi na wasu mintuna,kafin anty farheen ta tattara hankalinta sannan tace


"Me ya faru daya kawo wannan ajjiye aikin rana tsaka haka?" Qwalla idanunta suka kawo,tayi qoqarin maidasu ta kuma kawo dakiya ta azawa ranta,sannan ta fara basu labari daki daki,daga qarshe ta qarqare da fadin


"I can't take it anymore anty,how can he humiliate me like that?yana tunanin ina da interest ne akan dukiyarsu?,ya dauka ni na kawo kaina nayi begging a bani aiki,kamar yadda sauran wulaqantattun matan dake mutuwar masa soyayya sukayi aka basu gurbin aiki yanzu haka a company din ba,baisan tilastani yaa muhyi yayi ba shima don kawai yayi alfarma wa mahaifinsa?" Shuruu anty farheen tayi tana jinjina kai,sosai taga zallar bacin rai saman fuskarta,afifa zatayi magana tayi saurin dakatar da ido,sannan ta fara magana


"Gaskiya bai kyauta ba,baisan mace 'yar tarairaya bace?,so amma duk da haka,ina roqar masa afuwa ummin abba,sannan on my own view akwai dalilin da yasa yake behaving haka.....but kafin sannan,dole na gaya miki gaskiya ummin abba,kema kina da naki laifin"


"Yes" afifa data kasa jure rashin saka bakinta ta fada,har sai da sãahar ta waiwaya ta dalla mata harara da fararen idanunta dake da raguwar danshin hawaye. Juyawa farheen tayi


"Afifa,i beg you..." Yatsunta tasa ta kame bakinta,sanann ta koma ta kwanta,saidai duk da haka kunnuwanta da hankalinta yana kansu din tana ci gaba da sauraron abinda anty farheen din taci gaba da gaya matan.


              Mai da kai farheen tayi ga sãahar tana dubanta cikin kulawa


"Don ba dai dai ba anyi miki,ya bata miki rai na yarda,kuma ya miki laifi,tunda har abun yakai ga taba lafiyarki......to amma abinda nakeson ki sani,shi babba duk inda yake babbane,koda babban nan ba musulmi bane Christian ne,abu na biyu ko babu komai ai ya girme miki ya kuma baki shekaru sãahar,ina cewa ma zaid ya miki magana akan kiyi haquri kiyi aikinki?,ki kuma bashi girma ko don daddyn aleena?,sannan karki mata,namiji ako yaushe sarki ne,ke macace dole ko yaushe a qasansu kike....."


"Ni ba a qasan wanan nake ba anty,ni a qasan abba dasu ya muhyi kawai nake a yanzun,amma babu wani namiji a samana" ta fada da sauri,da alama an tabo mata bangaren da tafi adawa dashi. Karamun murmushi ta saki


"To shikenan,amma dai kamata yayi ace,tunda kinsan halinsa kici maganin zama dashi ,magana ta Allah kuma babu namijin da yasan abinda yakeyi wanda zai yarda da wannan,kina qasa da shekarunsa,sannan kina qasa dashi a aiki sannan kuma ya dauki rani?,bazai yiwu ba,kiyi tunani da kyau,a yanzun kina cikin fushi,yanke hukunci ba naki bane" taji duka maganganun farheen,amma batajin akwai wata sauran shawara data rage,gaba daya ta gama tsanarsa da dukkan wani abu da ya shafeshi,ajjiye aikin shine kawai maslaha a wajenta saboda muddin zasu ci gaba da haduwa,zaici gaba da yi mata haka,ita kuwa ba zata taba jura ba,saita maida masa dai dai da abinda yayi matan.


***********Tun washegarin ranar da abun ya faru bata sake batu ko yunqurin zuwa aiki ba,sunyi waya da miss sameera,tana tambayar lafiyarta jin shuru bata shigo ba,tace mata bata jin dadi ne. Cikin alhini tayi mata sannu,tare da shaida mata zata shigar da report


"Da kin barsu ma sameera,basai kinyi reporting ba". A kan hakan suka rabu,amma duk da haka bata fasa yin report din ba,duk sai taji ba dadi rashin zuwan sãahar din,kirkinta yana da yawa,tana kyautata mu'amala sosai a tsakaninsu.


             Tun daga ranar har zuwa satin gaba gaba daya tayi qaura daga zuwa aiki,duk da cewa zuwa lokacin ma qafar ta warke sumul,koda maama ta tambayeta dalili ce mata kawai tayi hutu ta dauka,sai bata sake yi mata zancan ba.


**********Karfe hudu na yammacin ranar litinin ne,wanda ya kama shigarta sati na biyu rabonta da MT JARMA GROUP OF COMPANY. Tana zaune cikin farfajiyar gidan,guri na musamman da aka kebe saboda hutawa. IG ta shiga tana duba hotunan styles na dinkuna da takeso takai,tayi scrolling down kenan hotonsa ya mamaye fuskar laptop din nata. Faduwa gabanta yayi,cikin sauri ta furta


"A'uzubillahi minash shaidanir rajim" ta sake maimaitawa kusan sau uku,kafin daga bisani ta bude idanun nata a hankali tana jan tsaki,ji take kamar ta fasa computer din gaba daya,sam bata qaunar ganinsa har can cikin zuciyarta,ko yanzun data aje aikin ta daina zuwa ji takeyi kamar tayi nesa da wani baqin maciji. Tana shirin sauka daga IG din gaba daya idanunta ya fada kan sunan me account din MEENAL YA'AQOUB AJI(AJI). 


"Banzaye marasa kishin kansu" ta furta tana qoqarin karanta rubutun dake qasan hoton nasa. Kamar dai wancan karon,itace wadda ta wlafa hoton nasa tare da kalmomi na yabo tare da nuna zallar madarar soyayya da qauna a gareshi,sauran 'yammatan da suka zube comment sama da dubu uku suna sake yaba kyanshi haiba da kamalarsa,tare da sake kodashi. Baki sãahar ta tabe


"Ko meye abunso a nan?,a green snake under green grass kenan"


"To tunda bakison kalla ki sauka mana,naga kema kallon nasa kikeyi" muryar afifa taji daga bayanta. Wani irin fatali tayi da system din kafin takai ga waiwayowa ga afifa wadda ta rugo tana fadin


"Subhanallahi" ta daga system din tana fatan batayi komai ba,saboda tasan nawa ta sanya ta siyeta,system ce me tsada ta kamfanin apple,kuma ko shekara batayi ba sukayi order dinta ita da afifan.


           Sai data tabbatar ba abinda ya sametan sannan ta fita ta kashe mata ita gaba daya,kafin ta maida hankalinta akan sãahar din.


            Manyan idanunta ta kafeta dasu,bacin ranta yana bayyana sosai saman fuskarta,suna hada ido tadan kauda idon don ta samu damar gayawa afifan abinda yake ranta


"Bestie...."


"Me yasa kika tsaneshi har haka sãahar?" Afifan fa katsi numfashin sãahar din daga abinda tayi niyyar gaya mata,ba tare da ta barta ta bata amsa ba ta sake cewa


"Ina jiye miki tsoron hadisin ma'aiki yayi aiki a kanki fa?,yace kada ku zurfafa soyayya don tana iya juyewa qiyayya,kamar dai tsakaninki da adam,sannan kuma yace kada ku zurafaf qiyayya saboda watarana zata iya juyewa zuwa soyayya".


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,bestie bansan bakya qaunata ba sai yau" sãahar ta fada da muryarta data canza saboda tsananin bacin rai,duk duniya afifa dince kawai take zata iya gaya mata hakan ta qyaleta. Kowanne yana shirin sake magana qarara wayar sãahar dake kan cinyoyinta ta katseta,maida dubanta tayi ga wayar tana tsammanin mahmud ne,amma sai taga mutumin da bata taba zaton kiransa ba,Dr mahmud JARMA.


          Cikin matuqar mamaki da kuma girmamawa ta daga kiran hadi da yin sallama


"Waalaikumus salam diyata"


"Barka da yammaci abba"


"Barka kadai,kin yini lafiya?"


"Alhamdulillah abba"


"Ayimin afuwa,inata son na kirayeki naji ya qafar taki,sai kuma sabgogi suka riqeni,to amma shekaran jiya munyi waya da muhyiddeen,yace kin warke tun cikin wancan satin ma" cikin jin nauyin afuwar da yake bida a wajenta tace


"Na warke abba,alhamdulillah"


"To ma sha Allah,nayi zaton ciwon ne ya hanaki komawa aiki,ina fatan za'a daure a koma din"


"In sha Allah" ta samu kanta da furtawa saboda yadda yayi mata kwarjini take kuma jin nauyinsa,duk da cewa babu plan na komawarta aikin kwata kwata. Addu'a sosai yayi mata,cikin jin dadin irin girman da take bashi,qaunarta da kimarta data iyayenta suna sake qaruwa a ran Dr mahmud JARMA.


           A sanyaye ta sauke wayar daga kunnenta tana tuhumar kanta dalilin da yasa ta amsawa dr jarma cewa zata koma bakin aiki?,me yasa bata gaya masa cewa tabar aiki ba?.


"Yanzun nan ya zaid ya shigo,nayi masa zancan ankon bikin fatima,yace cikin week din nan container dinsa da yayi order laces daga china zata iso,akwai wasu colors guda goma na musamman da su kadai ne a ciki,zai cire mana"


"Yayi,amma duk wani event da tasan akwai maza a ciki a cireni" ta fada tana gyara zamanta,can qasan ranta alqawarin komawa bakin aikin da tayi ba tare data shirya bane yake damunta.


              Sanye yake da yadin lallausan yadi da aka saqa da ainihin zaren guanaco me taushi da tsada,an shirya masa dinkin da yayi masifar dacewa da darajar yadin da martabarsa,ya kuma dace da jikin mamallakin yadin. Rufaffen takalmin qasar italy ne a qafarsa me asalin kyau da tsada,wanann kusan al'adarsa ne,komai nashi designer ne,komai nasa na musamman ne. Kansa babu hula,sai sassalkar sumarsa daketa qyalli,da wani irin gyara dake nuna tana samun kulawa,hakanan yana amfani da tsaftatattun tsadaddun mayukan gyaran gashi na maza. Zallar kyau da kwarjinin dake shimfide a fuskarsa dake da qarancin fara'a a bayyane yake muraran,kwarjinin da yake hanawa mata da yawa kallon fuskarsa kai tsaye.


          Shi da angel din nasa suke takowa zuwa inda motocinsa suke jiransa,akwai baqi da sukazo daga qasar tokyo da zasu karbesu shida daddyn nasa,wanda a yanzun haka suke bristol suna jiransu.


            Daga daya bangaren nasa kuma hajiya qarama ce,riqe da wata doguwar takarda


"Zaki bani aron lokacin daddyn naki muyi magana kuwa?" Hajiya qarama ta fada tana duban fadeela. Siririyar dariya yarinyar tayi tana dora kanta saman hannun daddyn nata da yake riqe da nata hannun,sai ya saka hannunsa ya dauketa cak ya a zata saman kafadarsa,wani miskilin murmushi na fita daga labbansa.


"Wannan sune list na mutane cikin dangi da za'a bawa zakkar wannan shekarar" hajiya qarama ta fada tana duban takardar. Kadan ya waiwaya ya kalleta,sannan yace


"Mu qarasa ki bawa jibril ko elyas"


"To yayi" ta fada tana ninke takardar.


           Dukkanin motocin an shiryasu kamar yadda aka saba,ya qare musu kallo a nutse sanann yace


"Da mota biyu kawai zamu fita yau"


"Me yasa?,baka tsoron lafiyarka?, idan baka qara guards ba ai ba zaka rage ba,yadda yanzun duniyar nan ba amana ba gaskiya" kai ya kada,shi dukka guards da yake fita dasu badon komai bane,don kawai ya samu sauqin tafiyar da aikinsa ne,bashi da wata alaqar gaba da kowa, hakanan dukiyarsa da guminsa ya tara,halas dinsa ce,so bayajin akwai wata barazana da zaiji tsoron fuskantarta


"Ba komai,fi amanillah" ya furta calmly,baki tadan kyabe kadan,yana da wani irin tauhidi da wani lokaci yakan bata tsoro,zata sake magana cook dinsa ya iso,yadan tsaya daga nesa nesa yana jiran izinin qarasowarsa,sai yasa hannu ya yafitoshi,wannan ya bashi damar qarasowar yana cire zungureriyar hular chief dake kansa


"Sir,you didn't choose what you want to eat" yayi maganar yana miqawa jibril takardar dake dauke da jadawalin abincin wata guda.


"Bashi takardan mu wuce,i want something lite,banason abu me nauyi yau,coz zan dawo gida late" yayi maganar yana sauke fadeela. Dai dai sanda wayarsa ta dauki tsuwwa.


            Sunan Dr mahmud din da ya gani ya sanyashi daga wayar da hanzari


"Ka taho ne?"


"On my way dad"


"Good,ka tsaya ta gidan Dr Mamman girema,ka duba jikin president dinka,ya kamata ka dinga kyautata mu'amala da employee dinka toufeeq"


"Alright dad" ya amsa masa yana sauke wayar daga kunnensa. Zazzafar iska ya furzar daga bakinsa yana zube hannayensa cikin aljuhun wandonsa,me yasa dad zaiyi masa haka?,wannan umarnin da ya bashi dai dai yake da yace masa yabi jirgin sama ya kamo masa shi,wannan yarinyar maras kunya?,me dagawa da izza zai taka ya sake zuwa gidansu a karo na biyu da sunan dubata?,bayan wancan karon dad din ya sakashi kaita asibiti ya kuma kaita har gida ya sauketa?. Duk yadda yaso ya qirqiri wani uzuri da zai hanashi wannan zuwan amma abun ya faskara,sun riga sunyi magana da dad din yace masa ya gama komai yana hanyar zuwa,so babu wani excuse ya tabbatar da zai bashi ya karba.


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post