Zakaran da Allah ya nufa da Cara complete Document

Zakaran da Allah ya nufa da Cara complete Document

 

Baban Sojoji

ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA.....🐓*

( _Ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai Yayi_) 

Na 

*Nuceeyluv😘*

*Alhamdulillah Allah ya sake dawo Dani a sabon littafi na me suna a sama👆🏻, Bayan dogon hutun zango da mukaje💃🏻 yaudai gamu tsundum mun dawo, Ina masoyan Dangin Na fulani😂 kun gane ai😉 @SIRRIN ZUCIYA😜 da fatan Baku manta ba🤣 toh yanzun ma Nuceeyluv batayi kasa a gwiwa ba Dan ta sake zuwar muku da Wanda yafi SIRRIN ZUCIYA😋 karki Bari a baki lbri 'yar uwa💃🏻 karki Yi sake a barki a baya💃🏻 masu iya mgn kance sawun giwa ya take na rakumi🏌️‍♂�? toh wollah haka abun yake dokin Wannan littafin ya take SIRRIN ZUCIYA nesa ba kusa ba😍 haba madarar dadin ma ai sai mun luntsuma cikin lbrin...*✍�? 

1....

Tafe yake cikin takun sa na kasaita Yana me kokarin zare labcoat dinsa cikin wani irin salo me matukar birgewa, *DR. UMAR SALEES* kenan matashin Dr. Me jini a jika Yana da cikar sura irinta mazanta, Idan Yana tafiya sai kace basarake kazalika idan Yana mgn tamkar Jinin saura Kai kace Dan sarki ne, Jajir yake idanunsa dara-dara lumsassu Wanda suke yanayi da kamar yanajin bcci, kwayar idanun sa fara ce tass tamkar Madara Dan haske yyinda bakin dake tsakiya ya Kara kawatu, Yana da saje irin na isassun 'yan gayu da hancin sa Wanda ya dace da kyakkyawar fuskar sa, a takaice dai UMAR Yana da kyau da cikar sura shiyasa dayawa Mata ke kware masa, maza ke jin kishin sa, toh da Allah yasa shi bana matan bane sai ya kasance bema San sunayi ba Dan Abinda ke gabansa ya ishe shi, Wani abun mamakin shine Koda yaushe fuskar Umar a dinke take is hardly aga Yana dariya saita kure idan abin yakai dole yyi dariyar kaga yadan murmusa kadan, hakan ma sai idan tare yake da abokin sa Sadeeq,


 Sadeeq shine kadai best frnd dinsa tun yarinta har kawo yanzu tare suke, Bayan shi baya yiwa kowa dariya fuskar San Nan a dinke take, shiyasa dayawa 'yan Mata saidai su kware masa daga nesa badai a kusa dashi ba Dan kowacce ganin sa take tamkar Namijin Zaki. Huh! Kada na cika ku da surutu domin idan nace Zan zayyano Sura da Kamala irinta Umar Zan rubuta littafi guda ban gama ba#lol😜. 


Cikin sauri ya Isa cikin office dinsu direct inda ake rataye labcoat ya nufa Nan ya rataye tasa a wajen, a gurguje yyi sallama da Prof Sa'idu dake kan kujera Yana duba system, Prof Sa'idu ya dago Kai Yana duban Umar hade da kokarin zare glass dinsa yace, 


"Saurin me kke haka Umar?"


Umar yadan Sosa keyar sa cikin girmamawa yace, 


"I'm sorry an kirani a gida ne emergency before mu shiga theater room"


Prof ya girgiza Kai Dan yasan Umar Kai tsaye zai Gaya maka gsky komai dacin ta, shiyasa ya yadda dashi Dan yasan karya ba dabi'ar sa bace, 


"Okay you can go, But u make sure ka dawo akan lkci kasan yanzu zaku koma school"


"Insha Allah I will try best"Girgiza Kai Prof Sa'idu yyi, yyinda Dr. Umar ya juya da sauri yabar cikin office din, budewar kofar sa keda wuya daidai lkcn Dr. Sadeeq ya taho office din shima, Kadan ya rage basuyi Karo ba, Dr. Sadeeq ya dubi Omar da mmki yace,


"Kai lpy?"


Ya tmby Yana wara ido, dafa goshin sa Omar yyi Yana me dawo da hannun ya hade su waje daya👏🏻 yyima Sadeeq haka bece masa komai ba ya raba zai wuce, da sauri Sadeeq yasha gaban frnd din nasa yace, 


"haba Omar wani lkcin fa wulakanci ne dakai wlhy, tmbyr ka fa nake Amma ka wani hade min hannu kamar wani ba'indiye"


yyi mgnr cikin tsokana Dan ya Saba fada masa hakan sbd kamar Al'adar sa ce mgn wahala take masa gara yyi maka nuni da hannu, Dan cije lips dinsa yyi Yana me shafa lumsassun gashin kansa cikin nutsuwa yace,


"sorry Sadeeq Ina sauri ne"


cikin kulawa Sadeeq yace,


"Ina zakaje haka kke sauri?"


Sake shafa sumar sa yyi yanaji kamar ya make Sadeeq din Amma ya Sansa da naci idan be Gaya masa ba yanzu zai Dame shi da tmby, cikin nutsuwa yace..... 

Domin cigaba da karatu danna download dake ƙasa.


Download 

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post