Kurkukun Ƙaddara page 37

Kurkukun Ƙaddara page 37

Kurkukun Ƙaddara

 💋KURKUKUN ƘADDARA💋


E37


Daga alƙalamin Boss Bature writer of Abban sojoji


Sun ɗauki tsawon lokaci rungume da juna suna ta kuka, Sai da suka yi mai isar su tukunna kowa Ya yi shiru, ba tare da sun raba jikinsu daga na juna ba, Muryar deeja a disashe tace"Na gaji da irin wannan rayuwar angel, bazan iya jure ganin ƴan uwana suna shan wahala ba, tun da ba yanzu suka fara ba, zasu ci gaba da zuwa suna ɗaukar mu ne ɗaya bayan ɗaya har sai sun ƙarar damu, nayi tunanin cewa gata ne ake nuna mana acikin kurkukun nan ashe ba haka bane, tsohuwa ta yi mana ƙarya da tace mana gidan marayu ne, za'a gatanta rayuwarmu, ta yaudare mu ta cuce mu, ba zamu ta6a yafe ma duk wanda yayi silar sadaukar damu zuwa cikin kurkukun nan ba......."


katse maganar ta yi, batare da ta kaiga ƙarasa ta ba, saboda wani irin ƙululun baƙin ciki da ya tokare mata maƙoshinta, Sai lokacin angel ta iya buɗe baki tace"Dama ni nasani tun farkon zuwana kurkukun nan na gane cewa Ba orphanage home bane, Tun daga kan sunanshi, shiyasa nayi ta ƙoƙarin in fahimtar daku, saboda ni nayi rayuwar ƴanci da hankalina da wayau na, sihirin tsohuwa tamira bai yi tasiri a Jikina ba, shiyasa Tunina bai gushe ba, dama taya za'ae Gidan marayu ya kasance Kurkuku? Kuma ba shige ba fuce, Abinci sau ɗaya arana! Uniform kala ɗaya, sai dai idan munyi wanka mu cire mu wanke mu maida a jikin mu? Ga shi babu wani mai kula damu, Rayuwa muke yi kara zube, wlh ko dabbobin dake garari acikin daji sun fi mu ƴan ci, koba komai zasu yawata inda suke so, Kai ni da irin rayuwar nan ma ƙwara mutuwa, saboda ɗaci ne da ita, rayuwar kulle, babu wanda zaiso ya kasance cikin irin wannan makauniyar rayuwar, Ai ko maƙiyi na bazan yi ma fatan shigarta ba....." Sai lokacin angel ta raba jikinta daga na deeja, Idanuwan kowannan su ya yi jawur saboda tsabar kukan da suka sha, Cikin karyayyiyar murya deeja tace"Ni bana Jin ma zanyi tsawaicin kwana, Gani nake kamar nice gawar fari acikin mu...." kafin ta karasa maganar angel ta yi saurin sanya tafin hannunta ta toshe mata baki, tana girgira kai, Hawaye na bin fuskarta tace"in sha Allah ba ke bace gawar fari, wlh bana Yi mana fatan mu rasa rayuwar mu acikin kurkukun nan, ina matuƙar so inga kuma kunyi rayuwa kamar kowa, Idan ma mutuwar ce na ƙwammace ni in fara yinta, saboda bazan Juri rashin wani acikin ku ba, bakisan yarda nake jinku ba, akan ku bana jin tausayin kaina, saboda ku ne abun tausayi" Daƙyar takai ƙarshen maganarta, hawayen deeja duk sun wanke hannunta data rufe mata baki dashi, 


  "Kowani ɗan adam da irin tashi ƙaddarar rayuwar, kowani bawa da irin ƙalubalan da yake fuskanta acikin rayuwarshi, Allah yana jarabtar bayin shi  ba dan baya sonsu ba, face don ya jaraba imaninsu, babu wanda zaice maka 100% yana rayuwa Cikin jin daɗi, dole akwai ranakun farin ciki da kuma na baƙin Ciki, wani farkon rayuwarshi Jin daɗi ne, tsakiyar rayuwarshi wahala ce har zuwa ƙarshenta, wani kuma da farko zai ci baƙar wahala amma daga ƙarshe sai kaga Ya samu farin Ciki, Akwai wanda kuma Kaf rayuwar shi tun daga zuwanshi duniya Allah zai fara jarabtar shi, har zuwa ƙarshen rayuwar shi bazai ta6a jin daɗin duniya ba, zai fuskanci ƙalubale iri iri wanda idan Baida ƙarfin imani da tawakkali zai fidda rai da rahamar ubangiji ne, Zaiyi tunanin cewa ko Allah baiso na ne? At end har yakai ga tunanin salwantar da rayuwarshi don ya huta, wanda yin hakan kuma zai ƙara Jefa kanshi Cikin matsala ne, Kazo duniya a wahalce kuma ka koma a matsayin zero duka kayi asara, Amma idan kayi haƙuri ka miƙa lamurranka ga Allah subhana'hu wata'ala Koda baka ji daɗi anan ba, acan ana kyautata zaton zaka dace, akwai wanda kuma bai ta6a shan wahalar duniya ba, gatanci ta ko'ina, wahalarta kaɗan ya sani,  in kaga 6acin ranshi to wani Ya rasa na kusa dashi, aduk halin da bawa ya tsinci kanshi Ya kasance mai godiyar Allah, Kafi wani, wani yafi ka, yanzu kamar rayuwar waɗannan bayin Allah, tunda suka zo duniya A garƙame suke kamar dabbobi, An tauye musu duk wani haƙƙinsu na rayuwa, basu son komai game da jin daɗin duniya ba, sun yi rayuwa acikin duhun jahilci, Basu son iyayensu ba, Basu son danginsu ba, su kansu basu Su wanene su ba, Haba jama'a, wannan rashin imanin har ina? A haka ake so su mutu su fuskanci mahaliccinsu, ai ƙwara wanda ke rayuwa acikin mutane yana fuskantar jarabawar rayuwa, Amma akwai imani azuciyarshi, Atlease Ya tsira da wannan idan yayi tawakkali, amma waɗannan bayin Allahn fa? Ba don zuwan angel acikin rayuwarsu ba da shikenan An kashe su da ransu an gama dasu, yakamata mu ƙara jin tsoron Allah acikin zukatanmu, mu kasance masu tawakkali, kuma mu kasance masu godiya ga Allah aduk halin da muka tsinci kanmu, tun da bamu rasa komai na rayuwa ba, ka kwana ka tashi da ranka da lafiyarka, ka je inda kake so, Ka ci mai kyau kasha mai kyau, ka sanya sutura mai kyau, kana a tare da iyayen ka ko babu su akwai danginka, kai idan ma babu dangin naka Allah Yana atare dakai, Zaka Iya rayuwa ko babu su, da daɗi da ba daɗi, Allah ya baka rai da lafiya, Amma sai kaga bawa yana Ƙorafi don ya rasa wani abu ƙalilan, ko angaza biya mashi buƙatarshi, dayawa gajan haƙuri kesa wasu harsu fara neman duniya ido rufe, Allah dai yasa mu dace, Shiyasa ake so mutun ya dinga ziyarta asibitoci da wuraren da faƙiran talakawa suke yin rayuwa, Kodan ya ƙara imani, Allah dai ya tsare mu ya kare mu daga faɗawa tarkon halaka, kada amanta adunga taya ƴan uwan mu addu'a waɗanda ke a hannun kidnappers da kuma ƴan boko haram, da matsafa, muna roƙon Allah ya kawo mana ƙarshen wannan masifar da muke fama da ita a ƙasarmu badan halin mu ba, Alfarmar Annabi muhammad (SAW) addu'a takobin mumini ce da ita ne kaɗai zamu Iya yaƙar su, tun da mu bamu da yadda zamuyi, waɗanda keda ikon Yin sun gaza, saboda rayuwar mu bata da mahimmanci awurinsu, takansu suke yi, wanda nayi imanin da ace yau hada ƴa'ƴansu aka ɗauka da anga tashin hankali, cikin ƴan awanni sai sun san yadda zasuyi an dawo musu dasu, Akwai dai ranar ƙin dillaci, ranar da dukiya ko ya'ya ko wani muƙami na duniya bazai amfane su da komai ba, A ranar zasu shaida cewa ALLAH ƊAYA NE.


A hankali angel ta zame hannunta daga saman bakin deeja, 


"Deeja kodai in taimaka maki ki yi wanka? Naji jikin ki wani iri, daga gani baki jin daɗin shi" girgiza kai deeja tayi"a'a, bazan Iya yin wanka da ruwan sanyi ba, Jikina zai ƙara tsauri, ki barni kawai ahaka, " tsananin tausayinta ne ya ƙara kama angel.


"To Mu je mu kwanta, ko kin samu ki yi bacci ki huta" shiru deeja ta ɗan yi batare data amsa mata ba, har sai da angel ta ƙara maimaita mata, tukunna ta buɗe baki tace"bazan iya tashi ba, ki kije ki tada su daga bacci, ki faɗa musu cewa an dawo dani, su zo mu gaisa," maganar deeja ta yi matuƙar girgiza angel sai taga kamar bankwana ne take so ta yi dasu, muryarta na kerma tace"amma meyasa? Idan baki iya tafiya ne, ni sai in ɗauke ki abayana in kai ki cikin ɗakin ki kwanta, In yaso gobe da safe sai ku gaisa da su"  idanuwan deeja a marairaice take kallon fuskar angel,  da wata irin raunatacciyar murya tace"dan Allah ki kira mini su in gansu, kada na mutu batare da nayi tozali da ƴan uwana ba," girgiza kai angel tayi cikin shessheƙar kuka tace"In..sha.. Allah ba zaki mutu ba, har sai mun fita daga cikin kurkukun nan, Na roƙe ki ki daina Yi mini maganar mutuwa, kina karya mini zuciyata, Kinsa Jikina duk ya yi sanyi" hawaye ne masu ɗumi suka wanke fuskar deeja,  idanuwanta sunyi jawur sosai, la66anta na kerma tace"dan Allah ki kira mini su mu gaisa, inaso inga ƴan uwana."


Juya mata baya angel ta yi tare da cewa"Ki hau in kai ki cikin ɗakin, Sai in tada maki su ku yi magana" fashewa deeja tayi da kuka tana faɗin"bana ce maki bazan Iya miƙewa ba, Kije ki kira mini su ko so kike saina mutu ne batare da nayi bankwana dasu ba"? Yanayin da tayi  maganar yayi matuƙar girgiza angel, Hatta muryar deeja ta canza sosai, a ƙarshe ta sassauta muryarta tana yi mata magiya akan ta kira mata su, Muryar angel na rawa tace"shikenan ki jira dan Allah, yanzu zanje in tada su daga bacci kinji," Aruɗe ta yi maganar, ta miƙe da  sauri tana tafiya tana waiwayon deeja, fargabarta kada ta mutu kafin ta dawo daga kiran nasu, bayan ta cire jamlock ɗin ƙopar da gudun gaske ta faɗo Cikin ɗakin har kusan tuntu6e ta yi, tun kafin ta ƙarasa cikin ɗakin ta dinga kwala musu kira, Haris danish, naufal hanna hibba batool yasmin ku tashi an dawo da deeja, da alama sunyi nauyin bacci babu wanda ya motsa, gaban gadajensu taje tana bubbuga ƙafafuwansu tare da cire musu bargunan da suka lullu6a dasu, Wannan karan muryarta da sauti mai ƙarfi take kwala musu kira, a matuƙar firgice kowannansu ya farka Yana faman Yin hama, Ba ta bari sun wartsake ba, tace musu"ku tashi muje toilet, deeja tana aciki, An dawo da ita, amma bata da ƙoshin lafiya, ita ce tace in kira mata ku, tana son ganinku" Jiki na rawa suka sauko daga saman gadajensu, Haris yafi kowa zumuɗi, shine agaba sai naufal da mubeen da danish, tare da javed, Matan kuma batool ce agaba sai su hanna hibba eve da su Parveen, Mutun ɗaya ce  bata sauko daga saman gadonta ba, Azeeza amma ta farka tana ta kuka tana faɗin ita ba wanda zai kai ta wurin deeja, saboda anga bata da ido, har angel ta juya zata bi bayansu Batool sai kuma ta fasa jin muryar azeeza da sauri taje bakin gadonta ta ruƙo hannunta, tare da taimaka mata ta sauko daga saman gadonta, suka nufi toilet section ɗinsu, lokacin da kowannansu ya hallara acikin toilet ɗin da deeja take, hankalinsu Yayi matuƙar tashi, Ganin yadda jikinta ke ta kerma, wata irin zufa ce ke tsastsafo mata a jikinta, gaba ɗaya ta jiƙe sharkaf, a sukwane suka zuƙunna gabanta suka kewayeta, suna ambaton sunanta, hannu biyu haris ya sanya tare da tallabo fuskarta, daƙyar take iya buɗe idanuwanta da suka rune tana kallonsu, ita kaɗai tasan irin raɗaɗin azabar da take ji ajikinta, muryar haris a ruɗe ya ambaci sunanta"deeja! ke ce kika koma haka? me ke damunki? kina iya ganinmu"? jinjina ma shi kai ta yi alamar eh, Azeeza dake ta kuka tana faɗin su nuna mata deeja, angel ta zuƙunnar da ita agaban deeja, Ta haɗa hannun azeeza dana deeja, Sosai deeja ta ƙanƙame  hannun azeeza dake acikin nata, Cikin sanyin murya ta ambaci sunanta"Azeeza"! Amsa mata tayi"na'am, deeja ashe an dawo mana dake muna ta bacci bamu sani ba, Mun yi missing ɗinki sosai, " shafa fuskar azeeza ta yi da hannunta, nan take azeeza ta ɗan zabura tana faɗin"Zafi hannunki deeja, baki da lafiya ko"? Bata amsa mata ba, sai dai binsu da take yi da kallo, matsawa batool ta yi daga gefenta ta ɗaura hannunta saman wuyan deeja, da sauri ta zame shi, jin wani irin zafi na fitar hayyaci, hankalin ta ya yi matukar tashi tace"Yakamata mu kira tsohuwa ta duba jikinta, kwata kwata babu alamun lafiya atattare da ita" haris yace"me tsohuwa zata Iya yi mata? Ai kawai ku taimaka mata ta watsa ruwa ajikinta, zata ji sauƙi," girgiza kai batool ta yi tare da cewa"bazaka gane ba, kwara a kira ta, tun da ita tafi mu sanin meke damunta" Angel ta lura dasu kowa yana tofa albarkacin bakin shi, amma banda Danish tunda suka shigo ya zuƙunna na ɗan wani lokaci sai kuma taga ya miƙe ya jingina bayanshi jikin bangon da deeja take a zukunne, ya goya hannayen shi saman ƙirjinshi, ya ɗaga kanshi sama idanuwanshi na fuskantar ceilling, tsabar haushin shi ne ya kamata, shi da yake amatsayin babba acikinsu yaƙi buɗe baki ya yi magana, Koda lallashin deeja ne yayi duba da irin halin da take aciki,' 


 "Ko da ace kun kira tsohuwa, ba abunda zata Iya yi mini, nidai tunda na gan ku Alhamdulillah hakan ma ya wadatar" Deeja ce ta yi maganar, Hanna tace"pls ki tashi mu koma ɗaki ki kwanta," kallon hanna deeja ta yi, ƙarfin hali kawai take yi wurin yi musu magana"Ae bazan iya miƙewa ba, ƙafafuwana sun ruƙe," Juya mata baya haris yai tare da cewa"ki hau in goya ki, mu shiga" nan ma tace mishi bazata Iya motsawa ba,' lamarin yayi matuƙar girgiza su,  jikinsu yayi mugun yin sanyi, Rubina tace"nidai zanje na kira tsohuwa ne" tana kai karshen maganarta, da sauri ta juya ta buɗe kopar toilet ɗin ta fuce, gudu gudu sauri sauri ta ƙarasa bakin ƙopar ɗakin tsohuwa, Tasa hannu ta kwankwasa ƙopar, kusan sau uku tana yin knocking, kafin ta samu tsohuwa ta buɗe mata ƙopar ɗakin, fitowa daga Ciki tayi hannunta ruƙe da sanda, ta ɗago da ido tana kallon rubina, Muryarta na rawa tace"dan Allah kizo ki taimaka mana an dawo da deeja amma jikinta babu sauƙi, ko iya miƙewa bata Yi," duƙar dakai ƙasa tsohuwa ta ɗanyi batare da tace komai ba, "dan Allah ki taimaka badan halinmu ba, kada mu rasa ƴar uwarmu,"  kafin tsohuwa ta ɗago da kanta sai ga su Javed da hibba hada  yasmin sun fito daga Cikin sashen toilet dinsu, Hankalinsu duk atashe, ɗaya bayan ɗaya tsohuwa take binsu da kallo,  Gaba ɗaya suka haɗa baki wurin yi mata magiya akan tazo ta duba jikin deeja bata da lafiya, duk sun ruɗe bayin Allah, Girgiza kai tsohuwa ta ɗanyi fuskarta babu yabo ba fallasa tace"Ni da bani da amfani awurin ku?me kuma zan Iya yi maku? Ita uwar ta ku bata iya duba mata jikin nata ne"? Duk sun gane akan wa take magana wato angel, hibba tace"pls ki taimaka mana mu dai, ki manta da komai kizo ki duba Jikinta, mun gane kuskuren mu, bazamu ƙara ba" suna kai karshen maganarsu gaba ɗaya suka zube saman gwiwowinsu, suna roƙonta, Da buɗar bakinta sai cewa ta yi"zan iya taimakon ku, bisa sharaɗi ɗaya"! A ƙagare suka tambayeta menene tace"Su je su kira babarsu angel, tazo ta durƙusa agabanta ta  roƙe ta, idan har ta yi hakan ita kuma zata duba lafiyar deejan su," da sauri suka miƙe da gudu suka nufi cikin toilet ɗin, a lokacin Deeja tana kwance saman ƙirjin haris, ya ƙanƙameta da hannayenshi,  su angel duk suna a kewaye da ita, banda Maji daɗin gado daya ke atsaye kamar gunki, Yadda suka banko ƙopar toilet ɗinne yaja hankalinsu angel zuwa ga kallonsu, a fujajen suka faɗo, kusan atare suka haɗa murya wurin cewa"Ki zo angel, tsohuwa tace zata duba jikin deejan mu, amma dole sai kin durƙusa agabanta kin roƙe ta," Waro ido waje angel ta yi bakinta asake galala take kallonsu, lallai wannan tsohuwar ta ɗauko ta da zafi, taya zata ce saita durƙusa mata sannan zata duba lafiyar deeja?  Mamaki ya hana ta motsa, magiya su javed suka dinga yi mata akan tazo suje ta duƙama tsohuwa, ko sun samu ta duba Jikin deeja"  kasa tanka musu ta yi, Har saida batool tace"Angel ki taimaka ma rayuwar deeja, dan Allah badan halin mu ba, Kije ki roƙeta, wannan ce kaɗai damar da muke da ita, idan ba haka ba, deeja zata Iya mutuwa ki kalli yadda jikinta keta kerma yana zufa, duk ta fita hayyacinta" Batool na rufe baki azeeza ta fashe da kuka tana faɗin"Dan Allah angel kije kada mu rasa deejan mu, muna son ƴar uwar mu," ɗaya bayan ɗaya angel take kallonsu, a karshen ta tsayar da idanuwanta kan fuskar deeja dake kwance saman kirjin haris, la66anta sai kerma suke Yi, " ganin zata 6ata musu lokaci yasa suka nannaɗe hannuwan rigunansu, batayi wani aune ba, taji sun sunkuceta gaba ɗaya suka cuccu6ota suka juya da ita zuwa cikin ɗakin, tana ta kiciniyar ƙwace kanta amma sunƙi bari ta kubce musu, a haka suka shigo da ita cikin ɗakin, Tsohuwa na ganinsu ta saki wani irin bazawarin murmushi, dama tasan taurin kan angel da kafiyarta baza su ta6a bari ta tako da ƙafafunta zuwa gabanta ba,  su javed na ƙarasowa inda tsohuwa take a tsaye suka saki angel ta faɗi ƙasa, Idon tsohuwa na akanta, ɗagowa ta yi fuskarta a hargitse, saboda tsabar masifa ta rufe idanuwanta tana zazzaga masu masifa tana faɗin don me zasu je su ɗauko ta? Ita fa bazata ta6a duƙama wannan tsohuwar najadun ba, mai kafirar zuciya wadda batasan Allah ba, 'ta inda take shiga bata nan take fita ba, Hankalinsu Rubina ya ƙara tashi ganin tana ƙoƙarin 6ata musu lokaci, ga deeja can tana jin jiki ita kuma da suka ɗauko donta taimaka masu gashi tazo tana ƙara Kwafsa musu,  Zuƙunnawa su ka yi gaba ɗayansu saman gwiwowinsu suna roƙon angel akan ta taimake su badan su zata yi ba, ta dubi girman Allah ta roƙi tsohuwa taje ta duba lafiyar deejansu, " tsananin tausayinsu ne ya kama angel ganin hada hawaye akan fuskokinsu, saboda tsabar jaraba da jin takaici ta fashe da kuka tana faɗin"wayyo Allah na na shiga uku, yau zan aikata babban zunubi arayuwata, wlh na tsane ki kamar mutuwa ta, bansan ganinki,  muguwa azzaluma, mai zuciya irinta kafiran farko, ke daga ganinki kin hada iri da jinsin fir'auna, saboda rashin imani taimakon ne bazaki iya yi mana ba, dole saina roƙe ki....." Bata ƙarasa maganar ba,  yasmin ta sanya hannu biyu ta toshe mata baki, Cikin shessheƙar kuka tace"dan Allah angel kidaina, idan baxaki Iya ceton ran ƴar uwarmu ba, bai kamata kina ƙara fusata tsohuwa ba, so kike ta fasa taimakon mu" A tsiyace angel ta buge hannun yasmin data toshe mata baki dashi, idanuwanta sun yi jawur tamkar garwashin wuta, kallon kallon suka shiga yi ita da tsohuwa, 


"Lokaci Yana ƙure maki, idan har kika bari na juya na dogara sandata na koma Cikin ɗakina, To ku fidda rai da zan sake fitowa, wannan ce kaɗai damar da kuke da ita"  tsohuwace tayi maganar, fuskarta ɗauke da shu'umin murmushi, mai nuna tsantsar farin Ciki, bata ta6a jin nishaɗi ba irin na yau,   a hankali angel ta kawar da idonta daga kan fuskar tsohuwa ta mayar dasu kan fuskokinsu Javed da yasmin da hibba dake a zuƙunne saman gwiwowinsu, fuskarsu sharkaf da hawaye, gyaɗa kai kawai tayi Jiki ba kwari ta maida idonta ga tsohuwa, murya na kerma tace"zan roƙe ki ne bada son raina ba, dan haka kada ki yi tunanin kin ƙasƙantar dani ne,  zanyi ne saboda waɗannan bayin Allahn, da kuma ƴar uwata dake acikin mawuyacin hali, Sannan kada ki yi tunanin kece zaki bata lafiya, Allah subhanahu wata'ala shine ya baki ikon yin hakan, domin kuwa saida yardar shi ne komai yake wakana" daƙyar takai karshen maganar ganin tsohuwa na ƙoƙarin juyawa ta koma Cikin ɗakinta, aikuwa da sauri angel ta ɗago ta zuƙunna saman gwiwowinta, Muryarta a disashe tace"Na roƙe ki dan Allah badan Ni ba, kije ki duba lafiyar Deeja" Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa ta fashe da ita, tamoji tamojin fuskarta har rawa suke yi, saboda tsabar yarda jikinta ke jijjiga, Angel kuwa wani irin ƙululun baƙin Cikine ya Turniƙe zuciyarta, har wani zazza6i taji ajikinta, Kusan atare su javed suka sauke ajiyar zuciya, saboda tsabar mugunta saida tsohuwa tasa angel ta maimaita maganar da tayi kusan sau uku tukunna tace"hakan ya yi mini, haƙiƙa yau na shaida irin ƙaunar da kike yi musu, ke ɗin uwace ta gari agare su, Ina ji araina cewa nan gaba har rayuwarki zaki Iya sadaukarwa akansu, don ba ƙaramin mamaki nayi ba ganin irin yadda kika sauke duk wani girman kai naki da kafiyarki wurin roƙo na akan lafiyar ƴarki deeja,  Naji daɗi sosai Albarka zata tabbata akanki, ni kuma yau ta kasance ranar tarihi arayuwata, wato ranar da the most arrogant young lady in the world ta zuƙunna saman gwiwowinta domin ta roƙe ni......"Tsohuwa bata karasa maganarta ba, muryar angel Cikin fushi tace"Kinga surutun ya isa haka, tunda nayi maki abunda kike so, kema saiki biya ni" cike da shaƙiyanci tsohuwa tace"To  gimbiya sarautar mata, Ai ko me kike so yau zanyi maki shi" Harara angel ta watsa mata kamar kwayar idanuwanta zasu faɗo kasa,


 Juyawa tsohuwa tayi zata koma cikin ɗakinta, muryar javed ta katse ta"deeja fa? Naga zaki koma Cikin ɗaki" batare da ta juyo ta kalle shi ba tace"Ku jira ni yanzu zan fito," Tsayawa su kayi suna jiran ta, Badajimawa ba sai ga tsohuwa ta fito hannunta ɗaya ruƙe da gorar ruwa ta gargajiya, miƙa ma javed tayi"Ruƙe mun nan, Mu je ciki ka nuna mini ita" da sauri javed ya sanya hannu biyu ya kar6i gorar ruwan, Suka shiga gaba tabi bayansu, angel dai bata bi su ba, A nan ƙasa ta kwanta zuciyarta na tafarfasa, Ji take yau ta bata kanta, tun da harta durƙusawa tsohuwa,


Lokacin da suka shiga Cikin toilet ɗin, Tsohuwa ta basu umarnin su fita waje su jirata, haris dai bai yarda da ita ba, ya ƙyaleta ne kawai yaga iya gudun ruwanta, ɗaya bayan ɗaya suka fuce daga Cikin toilet ɗin, kafin javed ya fita sai da ya fara ajiye mata gorar ruwan a kasa, Tukunna yasa kai ya fuce, Cikin ɗakinsu suka koma Kowa zuciyarshi cike da zullumi, daga Cikin toilet ɗin suka soma Jin kukan deeja yadda kasan ana zare ranta, hankalinsu yai matuƙar tashi,  gaba ɗaya suka gaza jurewa, Komawa su kayi Cikin sashen toilet, Koda suka je bakin ƙopar toilet ɗin a datse suka same shi, A dole suka zauna ƙasa zaman jiran fitowar tsohuwa, danish dai yana acikin ɗakinsu, bai bi bayansu ba, Saman gadonshi ya koma ya zauna, yana satar kallon angel dake kwance a ƙasa, Yana so yaje ya lallashe ta amma yana tsoron masifarta, don kuwa yau sai Allah, Taci ka ta batse, jira take kawai ta samu wanda zata huce haushinta akanshi,' wannan dalilin ne ya hana shi tunkararta, gudun kada yasha mari,


Yau fa babu bacci, Dare ya koma musu tamkar rana, azeeza ce kaɗai take gyangyaɗin bacci, tana atsakankanin Batool da naufal, ta ɗan ɗaura kanta saman kafadar batool, ga dukkan alamu bacci take so ta yi,  Naufal ne ya lura da ita, ruƙo hannunta yayi acikin nashi yace"azeeza tashi muje in raka ki cikin ɗaki ki kwanta, kada ki yi bacci anan" maƙe mashi kafaɗa tayi muryarta adisashe tace"ba yanzu zan kwanta ba, sai na jira an fito da deeja" Haris dake sauraronsu yace"naufal, Kada ka biye mata, pls ka ɗauke ta, ka kaita cikin ɗaki," rigima ta sanya musu, akan ita bazata je ta kwanta ba, sai ta ga deeja" Naufal bai tsaya sauraronta ba, ya sanya hannayenshi biyu ya sa6e ta, kamar wata ƴar baby haka ya ruƙota ya nufi Cikin ɗakin da ita, A saman gadonta ya kwantar da ita, tare da janyo bargonta dake a nannaɗe ya lullu6e mata jikinta, sai gashi ta yi shiru alamar bacci yai awon gaba da ita, ajiyar zuciya naufal ya sauke sai da ya fara ɗagowa ya kalli danish dake kishingiɗe saman gadonshi, Ya kuma kallon angel dake kwance a ƙasa, Ya ɗan girgiza kai, kafin Ya juya ya nufi Cikin sashen toilet ɗin, Lokacin da naufal ya shiga Ciki, Ya yi dai dai da buɗe ƙopar toilet da tsohuwa ta yi, aikuwa Jikinsu har 6ari yake yi wurin miƙewa tsaye idon kowa akan Ta, fitowa tayi hannunta ruƙe da sanda, Ta ɗago ta kallesu tace"Ina babar taku take Ne"?  Suka haɗa baki wurin cewa"Tana acikin ɗaki" tsohuwa tace"Ku je kuce mata ta ɗauko bargo tazo, ta ɗauki diyarta, " amsa mata suka Yi da toh, Batool ce taje cikin ɗakin ta isar da saƙon zuwa ga angel, atare suka dawo hannun angel ruƙe da bargo, fuskarta a kumbure take hararar tsohuwa,


Matsa mata Hanya tsohuwa tayi"Ki shiga Ki lullu6a mata shi ajikinta, ki fito da ita, " batare da ta amsa mata ba ta nufi ƙopar toilet ɗin ta shige Ciki, tsohuwa ta kalli javed tare da cewa"idan sun fito ka ɗauko mini gorar ruwan nan, ka biyo ni da ita" ya amsa mata da toh,'. Har ta fara tafiya ta dan juyo tana kallon fuskokinsu tace"Yakamata kuje ku kwanta, duk da ma naga kamar Lokacin ya ƙure garin ya waye" bata rufe baki ba, sai ga hasken ɗakin su Ya gauraye ko'ina,  sun yi matuƙar yin mamaki, maganar tsohuwa ta tabbata, har gari ya waye basu sani ba, Atare suka haɗa baki wurin yi mata godiya, bata amsa musu ba sai cewa tayi"bani yakamata ku yi ma godiya ba, Babarku ce ta cancanci hakan," Fuskarta ɗauke da murmushi tayi maganar, tare da juyawa ta fuce daga cikin sashen toilet ɗin ta nufi dakinta,


Fitar tsohuwa keda wuya, Sai ga angel ta fito hannunta ɗaya talla6e da deeja, da alama hada wanka tsohuwa tayi mata, uniform dinta na sanye a jikinta, Daga sama kuma bargon da angel ta lullu6a mata ne," wani irin farin Ciki ne Ya lullu6esu, Ganin ƴar uwarsu ta wartsake har tana iya taka kafarta, Sai faman sauke ajiyar zuciya suke Yi, wuce wa gaba angel ta yi suka bi bayansu, a bakin gadon deeja suka tsaitsaya, angel ta taimaka mata ta kwantar da ita saman gadonta, muryar deeja na ɗan kerma tace"Sanyi nake ji, ku ƙara mun wasu bargunan akaina, Ko jikina ya yi ɗumi,"  Da sauri kowannan su ya nufi gadon shi suka ɗauko bargunansu suka lullu6a mata ajikinta, Cikin ƙanƙanin Lokaci bacci ya yi awon gaba da ita, duƙawa angel tayi agaban gadon deeja daga gefe, ta soma karanto addu'o'i tana tottofa mata, bayan ta kammala ta ɗago da idanuwanta ta kalli su Batool dake a kewaye da ita, tace dasu suyi mata addu'a suma, kowa ya ɗan zuƙunno da kanshi saitin gadon, suka karanta abun da taɗan koya musu suka tofa mata, daga bisani haris yace dasu, Su koma su kwanta, ganin jiya basu samu isasshen bacci ba, ba musu suka amsa mashi da toh, kowannan su Ya wuce saman gadon shi, suka kwakkwanta, Ya rage  saura haris dake a tsaye sai angel dake zuƙunne agaban gadon deeja, wuri ya samu gefen gadon deeja ya zauna,  ba laifi yanzu hankalin shi ya ɗan kwanta, kallon angel yae tare da cewa"Ke fa? Baki jin bacci"? daƙyar ta iya ɗago da ido ta kalle shi, baiwar Allah damuwar duniya ta isheta, maganganun da deeja ta faɗa mata sune suke ta yi mata yawo a cikin kanta, 


(Akwai Sauran free pages amma yakamata ku fara yin payment, nayi kokari dai na baku book one kyauta, nima sai ayaba mini, Masu son shiga paid group na Facebook sun tuntu6i 08169856268, for whatsapp 08103884440) 500 ne, ta bank ake turawa koda pos, in mutun baida account, idan ƙaramar wayace in ka tura kuɗin zaka fadi sunan me banki ko mai pos din za'a duba.   alert,*3196407426*

Bature Hafsat Muhammad

First bank  


*Zaka tura da shaidar Biyanka ta wannan Numbers ɗin (0816985 6268) ko kuma ta (08103884440

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post