Feenart Hausa Novel page 1

Feenart Hausa Novel page 1

Feenart Hausa Novel page 1

⚡⚡ FEENART ⚡⚡

STORY ND WRITTEN 

             BY  

 NUSAIBA ALKAMAWA

PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION               

Bismillahi rahamanir raheem 

 FREE BOOK

🅿️1️⃣


"Momy dan Allah ki barni na raka Haleema hanya","kiyi hakuri Feenart bawai na hanaki rakata bane, kinsan halin yayan ki, in ya dawo bakya nan fa?",''  pls Mommy bazan dade ba fa" ta fada tana daddoka kafa,

"To shikenan kije amma karki dade","to Momy nagode" ta fada tana ficewa daga dakin, dan kada ma ta chanza shawara, da kallo Momy ta bita tana murmushi.

A kofar gida ta tarar da Halima, sai duba agogon dake tsintsiyar hannunta take, takun takalmi nane ya sanar da ita zuwa na, dama ni take jira, dagowa tayi tana hararata, "gaskiya Feenart bakida mutunci! kinsan fa jiran ki nakeyi, amma kikaje kika zauna, gashi kinsan zamu fita da Abra" ta karasa maganar tana huhhura hanci,

"Am sorry kawata Momy ce ta sani aiki shiyasa ban fito da wuri ba" ta fada tana hade hannayen ta alamar roko, murmushi Halima tayi, "is owk mu tafi" muna shirin tafiya motar Ansar ta shigo layin, dumm! haka ne sautin da kirjina ya bayar, saboda ganin Bro Ansar, 

"Feenart ga dodon ki" halima ta fada adai dai lokacin da yakeyin parking a gaban mu, ni kuwa inaa ban ma san abinda take cewa ba, saboda tunanin wahalar da zan sha inna shiga hannu Bro Ansar, Bro Ansar ne ya katse min tunanin da na lula, 

"Keee! ina zakije?" ya fada cikin kakkausar muryar sa, "am am dama ta kasa magana" saboda tsananin tsoran sa da takeji, "ba zakiyi magana ba sai na tattaka ki?" ya fada da yana daka mata tsawa, tare da kafeta da lumtsatsun idanun sa, cikin inda inda na fara magana, "dama bro Ansar zan raka Halima hanya ne" na fada ina sunƙuyar da kai,


"Shine kuma kike abu na marar sa gaskiya? stupid idot! "Yaya Ansar ina wuni" daga mata hannu yayi batare da ya ko kalli inda take ba, anan ya bar motar ya karasa gida a kafa, yana tafiya cike da izza.

Ajiyar zuciya nayi da karfin gaske, wanda ya saka Halima saurin kallo na, tuntsirewa tayi da dariya tana nuna ni da yatsa, "lgaskiya kina masifar jin tsoran mutumin nan, nuna kina jin tsoran sa yasa yake miki haka" ta fada har lokacin tana dariya,

"Halima kenan har yanzo bakisan wane Bro Ansar ba, shiyasa kike wanna maganar","nasani mana tunda gashi ya nuna min halin nasa, dan ma na saba shiyasa banji haushi ba"

"Kuma kinga da Naseeb ne bazai min haka ba","shiyasa na matsu ya dawo ko gidan namu yayi haske" murmushi sukayi, sannan suka fara tafiya suna cigaba da maganar Bro Ansar, saida na rakata har bakin layi, "kinga nikam a nan zan tsaya, ki gaida gida" hararata tayi tana fadin "matsoraciya na gode" ta fada tana murmushi,

Daga mata hannu nayi, sannan na juyo na dawo gida, ina shigowa falo mukayi ido hudu da dodon nawa, harara ya sakar min da sauri na sunkuyar da kaina, da sauri na shige dakina ina hamdala a cikin zuciyata, ina fadawa kan tangameman gado na cike da gajiya.

Wacece Feenarh?

Shere fisabilillah as much as u can.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post