⚡⚡⚡⚡⚡⚡
FEENEART
⚡⚡⚡⚡⚡⚡
BY
NUSAIBA ALKAMAWA
PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION
Dedicated to _nafeesat abubakar_ _alkaly_
🅿️2️⃣
Wacece fenart?
Nafeesat Abubakar alkaly shine cikakken sunan ta 'yace a wajan Alhaji Abubakar Alkaly (Dady) da Hajiya Fateema (Momy)
Su uku iyayensu suka Haifa Ansar ne babba sai kaninshi Naseeb sai kuma auta Nafeesat.
Alhaji abubakar Dan asalin jihar kano ne ,su biyu iyayensa suka Haifa shine babba sai kanwarsa Hajara tana aure ajihar Bauchi.
Ansar yagama karatunshi a US yadawo gida Nigeria, Yana aiki awata babbar court, shidin babban lawyer ne da ake ji dashi a fadin Nigeria.
Fenart yarinya ce kyakkyawa fara doguwa yar duma-duma, gashinta har gadon baya, gata da hanci, da idanuwa farare tass! manya manya, ga dimples ga kyan diri, Masha Allah domin Feenart kota ina ta hadu,
Amman saidai kash!tarasa Abu daya wato (farin ciki ).
Tayi saukar Al Qur'ani mai girma, sannan kuma tayi candy shekaru biyu da suka wuce, yanzo haka tana da shaikara ashirin a duniya, miskila ce ta ajin karshe,
Dan bata fiya magana ba, idan kaga tana hira to da aminiyar ta ne wato Haleema, kokuma Yaya Naseeb, kokuma Momy da dady.
Kullum tana dakinta, bata fitowa sosai, saidai tayita xama adakin tana tunanin abinda tasaba tunani, tunsu Momy suna mata nasiha harsuka dawo fada, yanxu dai sun zuba mata ido.
Shikuwa Yaya Naseeb Yana UK karatu, yanxu haka ma Yana final year, nan da two months zai dawo gida.
Mutum neshi mai fara'a da son yan uwansa, bayason abunda zai bata musu rai musamman ma Feenart, shiyasa indai yaganta cikin damuwa yake kokarin kawar mata da ita, shiyasa take cemasa hasken gidansu, Wannan kenan.
*Back to story*
Washe gari ina tashi wajan karfe 11 nashirya natafi makaranta, nakoma makarantar duk da kuwa cewa nayi graduation amma hakan bai hanani kara komawa ba domin Karin wani ilimin.
Ina xuwa akayi mana kari da wasu yan littattafan ,bayan angama mana aka taso mu daga makarantar, muna tafiya da Halima don ajinmu daya a makaranta.
Sallama nayi da ita domin xamuyi hanyar gidajenmu, ina shiga gida na tarar da monster akan kujera wato (ya Ansar) su Momy ma na parlourn dake yau weekend,
Sallama nayi suka amsa, Momy tace "daughter Momy zonan, yayanki Yana neman ki" amsa mata nayi da to, karasa shigo nayi cike da mamakin Neman da Yaya Ansar yakemin,
Shi kuwa gogan naku kara hade fuska yayi, meyasa Momy zatayi masa haka? shifa nasa nufin, Momy ce zata karbi laptop din shikuma saiyaje yakarba gurin ta, domin bayason kowace irin alaka yakara shiga tsakaninsu da yarinyar nan, shifa bayason raini!
Ni kuwa ina karasawa na gaida Momy da Yaya Ansar, Momy ce kawai ta amsa Amma shi ko kallon ƙurata bai yi ba,
Muryar sa ce ta, ɗoki dodon kunne na yace "keeeee jeki dauko min laptop Dinki" yafada cike da izza, saikace wani nasa ga wani irin bakin ciki daya lullubeni,
Saboda yafadamin Kalmar danafi tsana akirani dashi wato Kalmar "keee" saikace wanda baisan sunana ba, tashi nayi cikin bacin rai na nufi dakina, na kwanta nafada tunani akan abinda yafaru dani abaya Na irin bakin cikin dana shiga,
Na tsunduma cikin tunani naji mayataccen kamshin turarensa ya mamaye hancina,
Dagowa nayi da sauri domin tunawa da aiken da yayi min Dan wllh shaf namanta, saida naganshi yanzun na tuna
"Keeee Dan gidan ku ina Aiken da nayi miki? wato kin mayar dani sa'an wasan ki ko? kin barni a parlour inata jiran ki" yafada cikin fushi kamar yakaimin duka,
Aikuwa babu shiri natashi nadauko masa namika masa, fisgewa yayi, cikin sweet voice dinsa yace min,
"ba zaki kara ganin ta ba har abada, wannan shine hukuncin da zan maki na bata min lokaci da kikayi" mtwss! Yaja tsaki, tare da ficewa daga dakin.
Tsororo na bi kofar daya bi da kallo, ina fashewa da kuka bakin cikin kwacemin laptop da yayi, domin aduniya ba abinda idan nagani yake sani cikin farin sama da laptop dina,
Gwara ka kwacemin duk abinda na mallaka aduniya, akan ka kwace min Amman kabarmin laptop dina
Domin tana tuna min abubuwa da dama, kuma duk wani sirrikana Yana ciki,
Amman gashi wannan dodon gidan namu yakwacemin ita, haka nagaji da kuka nagoge hawayena nashiga bathroom domin nayi alwala,
Ina fitowa nayi sallah bayan Na sallame Na daga hannuna sama ina rokon Allah daya sassauta min abinda da nake ji acikin zuciyata,
Dakin Momy na nufa domin nakai karar Ya Ansar, zanyi knowking kenan, naji muryar Momy tana cewa.
Kash!laifin dadi karewa
Shere Fisabilillah.