Feenart Hausa Novel Page 8 | Novels Elite

Feenart Hausa Novel Page 8 | Novels Elite

Feenart Hausa Novel Page 8 | Novels Elite

⚡ FEENART✨

 Proficient Writer's Asociation 💪

By  NUSAIBA ALKMAWA

🅿️8️⃣

"Nina fada masa yakai motar gurin gyara, sai yadawo gida yadauki wata"nace Momy kawai abani motar tunda kinga kodan irin haka",kema kinsan dadynku baxai barkiba

tashi nayi Ina turo Dan karamin bakina nashiga dakina nayi wanka nashirya sannan naje daining naci abinci tukunna na koma dakina nadauki wayata nahau chart. 

Sakonnin WhatsApp ne sukaita shigowa ,,,,,ciki kuwa harda na sahibina ,,reply nayi masa duk DA naga baya online ,,,tukunna nashiga group dayake group's dina hudu NE daga *maisikeli's* FAM  sai *rayuwarmu* sai *novelist* DA *late alhaji ** Abdullahi* FAM ,rayuwarmu nafara shiga natarar DA admin sir press ya turo DA labarin abin dariya. 

Aikuwa abun yasani nishadi sai dariya nake sannan nasauka daga online saboda indai aka biyewa group din to xaka wuni kana chart domin suna fadakarwa DA kayatarwa DA nishadantarwa. 

Washe gari haka nashirya natafi makaranta ,bayan nadawo natafi islamiya ,karfe biyar aka tasomu aikuwa Ina cire uniform din dake jikina nadauki wayata naga tarin missed called ciki harda na sahibina daily numbersa nayi tafara ringing aikuwa yakatse wayar yakirani,cikin shauki nayi masa sallama ya amsamin nan mukafara xuba love domin nidashi ba daga nanba wajan iya soyayya anan ma yake fadamin  baxai samu damar xuwaba xaije yakarbo wasu file ,,,,,nikuwa cikin rashin jin babu dadi na rashin xuwan nasa ,,,nace masa to nandai muka cigaba DA hirarmu irinta masoya. 

Yauma kamar kullum haka nashirya natafi makaranta wajan karfe daya driver yaxo yadaukeni ,,ina isa gida na tarar dayah ansar ,,da guduna nataho ina masa oyoyo xan rungumeshi.

tsawa yadakamin Wanda yasani raxana yace ke bakida hankali ,kina Abu kamar wata dabba ,,,mamakine yadada karuwa afuskata wato us din dayaje wulakanci yakaro DA Kalmar dabba ,abin yakona min raiii matuka,kamar ba jininsa baceba ,ni,,maganar Momy ce takatsemin tunanin DA nake tace,,kai kuwa ansar menene laifinta Dan taganka tana murnar ganinka ,yaushe rabon data ganka Ashe haryanxu baka rage xafin xuciyar nantakaba ?,,batarai yayi danme Momy xata masa haka agaban yarinyar nan salon ta raina shi. 

nikuwa kuka nafashe dashi na takaici nashiga daki na,photon Muhd nafara toxali dashi abangon dakin ,take naji xuciyata tayi sanyi duk wani bakin cikin danakeji ta yaye . 

Shikuwa ansar hakuri yayita bawa Momy ganin tahau sama saifada takeyi masa. 

Sai da ya tabbatar momyn tashi ta hakura sannan yatafi part dinsa. 

           Facebook alkamawas glow🥰

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

plx Share and vote ⚡

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post