AUREN WATA UKU.!
*01*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Rayuwa tana zuwa ma bawa ta fuskoki daban daban cikeda jarabawa had’ida K’alubale. Ashe wasu mutanen Akan k’addarosu cikin rayuwan bawa ne matsayin jarabawa. Ashe Akan jarabci ‘ya’ya da nasu iyayen kaman yanda wasu ‘ya’yan ke zamtowa jarabawa ga iyayensu. Shin su waye ka tashi ka sani matsayin ahali.? Shin a ina k’alubalen take.? A ina gwagwarmayar take..? Tabbas wasu mutane da suka zamto jigo na rayuwar d’an Adam ka iya zama babban jarabawa a gareshi. Shin muna hak’uri da jarabawarmu ko kuwa dai bijirewa muke ga d’inbin rahamar Ubangijinmu garemu..? Bari mu tsunduma cikin labarin AUREN WATA UKU dan jin yanda ta kaya tsakani wasu ahali
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.!
Kano State, Nigeria.
Gida ne da za’a iya kiransa da gidan gandu sakamakon ahali guda dake rayuwa cikin gidan. K’ofofi ak’alla kuwa zasu kai takwas koma sufi. Yayye da k’anne dama makusanta na kusa wanda sukeda hakkin mallaka suke rayuwa cikin gidan.
D’aya daga cikin k’ofofin anyi cincirindo ana kallon abinda ke wakana. Dama dai abin kallo, magana harma da tsegumi basa kad’an a gidan yawa.
Ba komai akai cincirindo ana kallo ba sai akwatunan da ake fita dasu sahu sahu matan da sukazo kwasan kayan suna tofin Allah tsine.
D’aya matar ta kuma janyo k’aramar akwatin da k’arfin gaske kaman zata tsinke hannun jakan. Fad’i take “Alhamdulillah Allah Ya tsami d’anmu daga k’angin gori.. Me za’ayi da gayyan tsiya. Wllhi d’anmu yafi k’arfin wann sharan. Yaro d’an dangi, inyi.. Ina dalili.? Yarinyar da kowa Ya kwana da sanin sau babu adadi kenan ana amshe sadakinta. Kawai sai shi Zubairu sabida baida mafad’i mu bari Ya aureta.. Toh wllhi sam bazata saku ba wai bindiga a ruwa ehe.. Banda ma dai bani k’asa ina can birnin Saudiya da ina zan bari wann zancen banzan yayi nisa har akaiga kawo lefe..?” Ta d’anyi fasali tana kuma wangale bakinta yanda hakwaran makka har biyu suka bayyana cikin bakin nata, ta ko wani angle walwali yake.
“Aure dai mun fasa shi bama gayyan tsiya cikin zuri’armu..” Ta k’arashe d’aya matar da suke tafe tare tana tayata da fad’in “Wann gaskiya ne Hajjaju. Ai dama cewa nai kina dawowa za’a wargaza komai dama ganin babu idonki ne.”
Hajiya Dudu ta cab’e “Toh na dawo sai naga uban da zai d’aura wann gantalallen auren..!” Ta k’arashe k’iiii tana janyo trolley guda.
Wata mata ce da tin shigowan matan take sharb’an kuka an rasa mai bata baki ta isa da sauri ta rik’o hannun wann gabjejiyar matar. Cikin muryarta dake fita da kyar sabida kukan da taci take fad’in “Hajiya Dudu dan Allah dan Alfrman manzo Sallallahu alaihi wasallama ki rufa min asiri.. Kar ki bari a fasa auren nan.. Ki ceci d’iyata dan Allah..” Bata kai aya ba matar ta fincike hannunta tana ci gaba da huci had’ida aika mata muguwar harara ta gyara zaman mayafinta “Ke Suwaiba bari kiji na fad’a Miki wllhi idan ‘yarki itace autan mata Zubairu bazai kwashe ta ba.. Uban wa yasan abinda yasa ko wani manemi ke gudun ‘yarki.. Haka kawai a tashi a lik’a ma namu d’an.. Toh gari da yawa ga ‘yammata birjit masu jini a jika ba irin ‘yarki da ta girma ta rik’a ta tsofe gida ba.. Ke bari ma kiji cikin dangi zamu samar wa Zubairu matar aure dan gida bai k’oshi ba baza’a kai waje ba. Wajen ma ma bola shara irin ‘yarki..!” Tana ida fad’in haka ta fincike hannunta tana fad’in “Zinaru muje kinji kafin tsautsayi Ya hau kan kayan nan dan wllhi abu d’aya yayi ciwo tass sai an lale an biya.! Daga nan ma gidan Hajiya Atine muka nufa da kayan nan.. Ayyiriri D’anmu zai angwance da ‘yar dangi ba ‘yar bakin ruwa ba..” Haka suka fice suna guda suna watsa habaice habaice.
Matar da suka ambata da Suwaiba ta duk’a nan wajen tana cazgan kuka hannayenta biyu aka fad’i take “Na shiga uku ni Suwaiba Ina zan saka raina inji sanyi da wann bala’ai..”
Wata mata da ta d’an data dan ga dukkan alamu tafi ta tsugunnen a haife itace tai karaf ta cab’i zancen nata “Ohni Tani naga ikon Allah.. Aure ace ak’alla goma kenan ana karban sadaki ana anshewa idan ban b’ata lissafi ba.”
“Yaya bai Kai goma ba..!” Suwaiba dake duk’e wajen ta fad’i cikin gunjin kuka.
Tsaki Tani tai “Kayi magana ace kishi, na baki shawari ki d’auki yarinyar nan ki kaita baki ruwan Aljanun ruwa ne suka aureta amma kink’i ji kink’i d’aukan shawarina Suwaiba.. Waima har zigaki ake ana ce Miki ni ce nan nai ma ‘yarki asiri na hanata aure.. Toh ai idan ma asirin nai mata yazo gidan sauk’i sai ki d’auki k’afa kije gidan malamai a kwance miki sammun..” Ta kece da dariya had’ida rangad’a gud’a “Ayyyiriri nanaye Ayi dai mu gani.. Mun zuba ido mun baje kunnuwa..” Ta k’arashe tana gyara d’aurin zaninta da Ya karkace.
Su kaw sauran al’umman gidan dake tsaye suna bama idanunsu abinci tuni Sun soma tsegunta lamarin.
*
Cikin tsanaki ‘Yanmatan guda biyu ke takunsu gefen kwalta. Kallo guda zakai masu ka fahimci ‘yanuwan juna ne sakamakon kamanni ta fuskan halitta da su biyu din suke dashi.
Babban zata Kai kimanin shekaru 31 a duniya amma bazaka fahimci hakan ba sabida kyaun kira da Allah yayi mata. Sama bazakai zaton ta girme ma k’aramar wacce keda kimanin shekaru 20 a duniya har sai ka kula sosai. Sun karyo kwanan layinsu kenan suka hango wasu mata guda biyu jikin ginin wani gida Wanda garun baida tsawo sann duk ya murmushe abinka da ginin bani bani, idan da zakai tsalle d’aya zaka iya kamo katangar.
Wata mata ce da d’aurin k’irji daga nan cikin gidan ta dafe katangar ta lek’o suna tattaunawa da matan nan guda biyu dake daga waje. Aiko matar dake lek’en katangar da d’aurin k’irji tana hango ‘Yanmatan ta soma yima sauran biyun magana a hankali tanai masu nuni da ‘yanmatan da idanu. Tanai masu zindensu.
Gaba d’aya suka juyo suna duban ‘Yanmatan.
Sun kusan cimmasu k’arama daga cikin ‘Yanmatan tace “Adda Kinga magulmatan matan nan wllhi nasan bazai wuce zancenmu suke ba. Jibi yanda suke kallon mutane kaman mayu. Su ko kunya ma basa ji da girmansu da aurensu suna halin banza. Mtsw Allah ya kyauta halin matan unguwan nan. Mazajensu suna ficewa suma suke tafiya yawon gulma.”
Babbar ta murmusa tace “Ke wa yace miki gulmarmu suke.. Nidai dan Allah bana san tashin hankali Khulsum, nasan halinki sarai.. Gaisuwar fatan baki ya wadatar..”
Khulsum tace “Wllhi Adda ko kaffara bazanyi ba zancenmu suke. Tinda muka karyo layin nan suke mana kallon k’asa k’asa kuma wllhi mata tai mana zancen banza zataji babu dad’i tinda dai matan unguwan nan basu San su rik’e girmansu ba.”
Babban ta d’an tsare fuska “Ya isa Khulsumu. Kar ki sake cewa komai. Na san halinki sarai.. Kar ki ma wata mata magana cikinsu balle su samu abin tofawa.”
Khulsum tace “Ahaf wllhi Adda kema kinsan halina ba yanda za’ayi mata ta gaya mun bak’a na shanye ban rama ba. Ai sai nayi ciwo ma.. Tab.!”
Ita dai babbar bata kuma cewa komai ba sai girgiza kai da tai dan haka nan take ba mai yawan hayaniya bace.
Koda suka iso daidai yanda matan suke Babbar ce ta bud’e murya ta soma gaishesu cikeda girmamawa. Suka amsa yayinda Khulsum ta bisu da idanu.
Har sun wuce d’aya matar ta bud’e murya tace “UMMULKHAIRY..”
Daidai lokacin babba daga cikin ‘Yanmatan ta juyo tana dubanta “Na’am Maman Sahal..”
Matar ta murmusa tace “Ya batun aure ne wai.. Shiru shiru har yanzu ga Ummikhulsum har ta taddoki kodai tare za’a had’aku ne.?”
Kafin Ummulkhairy ta kaiga bata amsa suka sinkayo muryar Khulsum tana fad’in “Maman Sahal nace ba, idan gadon katako kikayi, to dan Allah ki canza kiyi na k’arfe kar ruma ya kama ko tsari da gara suci..”
Maman Sahal sai tai murmushi tana neman maida abun barkwanci “Oh su Khulsumu ba’aji ayi shiru.. Ai tambayan Alheri nai ba sai kin fad’a mun bak’a ba.”
D’aya matar dake lek’en Katanga tai karaf tace “Aff Lallai maman Sahal jaridu suna wuce ki kwanan nan, bakida labari har lefenta fah an kai kwanaki uku da suka shige.”
Ummulkhairy ta had’iyi abinda ya tokare mata mak’oshi had’ida aika ma ‘yaruwarta ummukhulsum mugun kallo. Ta shiga janyo hannun Khulsum zasu shige Khulsum ta kuma dogewa dan bataji bata mayar ba kaman dai yanda Maman Sahal tace.
Khulsumu ta murmusa tace “Kinji abokiyar gulmar taki ta baki amsa.. Ina kika makara baki sai jaridar ba.? Ko kudin sayan ne bakida shi na ranta Miki..?”
Nan fah Maman Sahal taja da baya ta Ware idanu tana nuna Khulsum da d’an yatsa “Ke kul wllhi ahir d’inki.. Koda wasa kar kimin rashin kunya ni ba sa’arki bace..”
D’aya matar ta bud’e murya tace “Wai dama Maman Sahal wa ya aikeki dogon hira da wann maras kunyar yarinyar.. Yarinyar da sam batada ta ido, ba ganin kowa take da gashin ido ba. Tanaji tana gani mata masu hankali ma yanzu ba auruwa suke ba ballantana ita maras kunya wacce bata mutunta kowa. Bazata d’auki darasi akan Yayarta ba. Kowa yayi shaidan Ummul a unguwar nan batada abokin fad’a tun tasowarta amma gashi nan ta kasa auruwa.. Sai anzo kaman za’ayi aure zance ya lalace. Ita wann kam inaga ba jinga ba saidai tayi bandaro ma.. Dan idan Har ba’a d’auki mai hankali ba banji za’a d’auki fitsararriya..”
Khulsumu kaw kafin matar nan ta rufe baki ta bata amsa da fad’in “Ai tinda mata gantalallu irinku basu rasa masu kwasan su ba bana Jin akwai kalar macen da bazata samu mijin aure ba.!”
Haba Nan fah Maman Sahal da gang d’inta suka nufo Khulsum Ummul na tsakiya tana janye Khulsum tana bawa su Maman Sahal hak’uri Wanda kaman zugasu take. Fad’i suke sai sun cire ma Khulsumu rashin kunyarta. Itama Khulsum d’in sai tsalle take tana fad’in dik matar da ta fasa dukanta ta raina Wanda take zaman aure k’ark’ashinsa.
Ana tsaka da wann kacaniya suka hango mata da akwatina nik’i nik’i aka sun dososu sahu sahu sai bala’i suke suna fad’in d’ansu bazai auri annoba ba.
Aiko nan suka ja wani wawan birki sakamo hango su Maman Sahal da k’awayenta d’aya da d’aurin k’irji sai tsalle suke yunk’urin cakumo Khulsum ga Ummulkhairy a tsakiya sai kuka take tana rok’onsu suyi hak’uri.. Garin janye Khulsum akaI watsi ma Ummulkhairy da mayafi ya fad’i gefe had’ida fincike mata d’ankwali tuni sumarta ya bayyana.
Salallami suka fara Hajiya Dudu tana masu nuni da su Ummulkhairy tana fad’in “Kunga abinda nake fad’a maku ko. Allah dai ya ceci Zubairu bazai yanka kazar wahala ba balle ya fige. wann ba matar aure bace.
Sauran matan suka shiga salati suna fad’in Sun shaida.
Hajiya Dudu ta kuma danna wayarta a kunne tana fad’in “Halo kai Zubairu nace wai kana ina ne haka da ka kasa k’arasowa..? Toh maza maza ka iso.. Alhamdulillahi tinda kana kusa ka gane ma idanunka. Kai sauri nace Jarababben banza..!”
Tana Ida wayan taci gaba da fad’in “Alhamdulillahi ai ni naji dad’i gwara dai yazo ya gane ma idanunsa.. Da banyi da gaske ba bazai bari azo a amshe kayan nan ba.. Toh gwara ya k’araso ya gane ma idanunsa. Me za’ayi da mace mai dambe a titi..!”
D’aya daga cikin k’awayen Maman Sahal kaw tana hango su Hajiya Dudu da akwatuna ta saki shewa tana gud’a tana jero baitukan ayye mama ayye mama har zuwa da aure yana raka aure da na biki mun tafi tare.
Haba nan fah waje ya kuma kacamewa kan kace mai anyi caa a wajen.
Mota ce k’irar Civic 2000 ta karyo layin hakan yai daidai da juyowan Ummulkhairy wacce idanunta ke zubda ruwa.
Karaf idanunta suka kafe cikin na Zaubair dake rolling glass din mota.
SameenaAleeyou📚
