Daudar Gora (Chiki Ka Shata) Hausa Novel |
Domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
DAUƊAR GORA...
(Ciki ka shata)
Bilyn Abdull ce👌🏼
Page 1
1
.........Kwanakin mako uku kenan da shuɗewar komai amma komai ya kasa mantuwa a zukatansu. Kuzari ya samu rauni kamar yanda dukkan karsashi ya gujema gangar jiki. Duniya ta masu ƙunci, ƙunci irin wanda har ƙarshen numfashi da wahala su manta. Farin cikinsu ya zama fansar damuwar wasu, wasun da kansu kawai suka sani basa kallon na ƙasa da su. Da ace ƙarfin iko a hanun kowanne ruhi yake a zahirin rayuwa, da ita ce zata zama mace ta farko a duniya mai ƙarfin ikon da zai girgiza zukatan kowaɗanne irin azzalumai. Kafin shuɗewar makwanni uku masu ɗauke da kundun baƙin ciki rayuwar ahalin Mal. Zayyan tamkar dutsen lu'u-lu'u suke a cikin tsakkiyar zinare. Ba magana ake akan dukiya ba, dan tana a cikin jerin abu mafi rauni da suke ɗauka ko amsa sunan ko kallo farin ciki. ana magana ne akan kammaluwar ahali masu matuƙar ƙaunar juna zunzurutu mara gauraye. Masu kuka a yayin zubar hawayen ɗayansu, masu dariya a yayin farin cikin ɗayansu, masu jiyya a yayin ciwon ɗayansu, masu zama komai a lokacin da komai yake abu ɗaya a hanunsu.
𝕯𝖆𝖚𝖑𝖆𝖗 𝕽𝖚𝖒𝖆𝖓 babbar ƙasace a tsakkiyar wani babban tsibiri a wani ƙarni mai yawan arziƙin zinare dake a nahiyar Africa. Ƙasar Ruman nada babbar Daular mulki data ƙunshi manyan sarakuna masu ɗunbin tarihi kala-kala da labaransu bazai taɓa kasancewa shuɗaɗɗe ba a duniya. Ba arziƙin zinare ne kawai suke da shi ba, sunada nau'i-nau'in kayan itatuwa da wajajen noma harma da kiwon dabbobi da akan fita da su ƙasashe daban-daban ko'a shigo cikin ƙasar a saya. Al'ummar wannan ƙasa sun kasance wasu irin ƙyawawan mutane masu kwarjini da cikar haiba, sai dai duk da ƙyawun da mafi rinjayensu ke da shi hakan bazai hana a samu masu ƙarancin ƙyawun ba. Sunada yawan addinai da ƙabilu tamkar kowacce ƙasa, sai dai mafi rinjayen ƙabila sune masu yara yaren rumanci, sannan addinin musulinci yafi kowanne addini ƙarfi da rinjaye. Abu mafi mamaki a ƙasar ta Ruman shine, duk da ƙarfi da rinjayen da addinin musulinci ya samu suna girmama al'adunsu na kaka da kakani musamman ƙarfin iko. Ƙarfin iko nada matuƙar tasiri a ƙasar Ruman ainun, hakama al'adu da girman masautunsu na taka rawar ganin hana dukkan abinda turawa suka zo musu da shi taka rawar gaban hantsi a garesu bayan ilimin boko, duk da suma sun shiga cikin ƙangi na mulkin mallakar turawan a ƙarnin daya shuɗe. Babu wani mulki dake da tasiri sama dana sarautunsu tun a farkon ƙarnikan baya har zuwa yau ɗin nan da suke rayuwa bisa mulkin mallakar sarakunan dake mulkin mallakar su.
𝕯𝖆𝖚𝖑𝖆𝖗 𝕽𝖚𝖒𝖆𝖓 itace babbar masarauta da dukkan masarautu ke ƙarƙashin ikonta bama su talakawa kaɗai ba. Itace tamkar fadar shugaban ƙasa a wasu ƙasashe. A maimakon mulkin siyasa, su 𝐃𝐀𝐔𝐋𝐀𝐑 𝐑𝐔𝐌𝐀𝐍 itace babbar masarauta mai faɗa aji akan komai da kowa na ƙasar Ruman, komai yana tabbatuwa ko akasinsa da ƙarfin ikon sarki mai mulki a kujerar wannan daula. Bama gasu talakawa ba, babu wata masarauta a cikin kasar Ruman data isa koda ɗaga murya a bayan idon Daular Ruman saboda karfin ikon mulkin 𝐒𝐡𝐚𝐡𝐚𝐧-𝐬𝐡𝐚𝐧 (King of kings). Ƙarfin mulkin wannan Daula yakai a duk faɗi da ƙasar Ruman ke dashi babu wani mahaluki da zai iya faɗar siffa kai tsaye ko kamanni na sarkin da duk zai mulki daular ruman tun zamanin ƙarnikan baya, saboda tsantsar girmamawa da akema sarakunan wannan Daula ko iya ɗaga kai a musu kallon ƙurulla na kusa babu maiyi, daga nesa kuwa fuskokinsu ababen kwarjinine irin na masu mulki da a ranar wasan al'ada na kowanne shekara ake iya ganinsu a zahiri daga nesa bisa keken doki. A tsari da ƙa'idar daular ruman dukan yarima mai jiran gado daya shiga shekaru bakwai na girma za'a ɗaukesa kowa ya daina ganinsa, a sirrance zaiyi ilimin zamani dana addini dama duk wata rayuwarsa irin ta kowa. Bayan cikar shekarun girma a garesa za'a fara bayyanasa ga sarakunan sauran masarautu cikin shigar da ƙwayar idonsa kawai zasu iya gani. Nuna yarima mai jiran gado ga sauran masarautu na nufin alamar mahaifinsa zaiyi murabus kenan ya ɗaurasa a karagar mulki basai bayan ransa ba. Sarkin kuma da baya buƙatar hakan bazai taɓa bayyana yarima ba ga kowa har sai bayan mutuwarsa. 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐇𝐚𝐲𝐬𝐚𝐦 𝐢𝐛𝐧 𝐀𝐛𝐝𝐮𝐥𝐥-𝐌𝐚𝐣𝐞𝐞𝐝 shine sarkin daular ruman daya shuɗe aka ɗora ɗansa ɗaya tilo bisa karaga. Shi kaɗai ya haifa a duniya, shine kawai magajinsa sai mata huɗu da saɗaka daya bari. A yanda tarihi yazo ba'a taɓa 𝐒𝐡𝐚𝐡𝐚𝐧-𝐬𝐡𝐚𝐧 mai ƙarfin iko da daularsa ta gagari duk wani jar fata nunawa yatsa ba kamarsa, ya shimfiɗa mulki a Ruman dama yankin Africa gaba ɗaya, izzarsa da ƙarfin mulkinsa yasa ba masarautun Ruman kawai ba, dukkan masarautun Africa na biye da shi da girmamawa da tsoro mai ƙarfi. Ya tara arziƙi mai ban tsoro da ban mamaki, ya kuma shimfiɗa ayyuka da ba Ruman kawai ba, Africa gaba ɗaya bazasu iya mantawa ba. Kaf ƙasashen jajayen fata masu faɗa aji na tsoro da shakkar 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐇𝐚𝐲𝐬𝐚𝐦 𝐢𝐛𝐧 𝐀𝐛𝐝𝐮𝐥𝐥-𝐌𝐚𝐣𝐞𝐞𝐝. Sarki Haysam ya raini ɗansa ɗaya tilo tamkar sauran shuɗaɗɗun sarakuna koma fiye da su, dan saɓanin sauran yarima da tarihinsu ya shuɗe shi wannan yariman tun a shekara uku na haihuwarsa babu wanda ya sake ganinsa kojin labarin inda yake rayuwa. Sai dai a kullum akanji sunansa a bakin Tajwar Haysam fiye da sau goma, ambaton sunansa shine mafi yawan magana dake fita a bakin Tajwar. Hakan kan saka razani da tabbatuwar shi wannan yarima zai kasance na daban a dukkan sarakunan da suka shuɗe kenan. Tabbas hasashen mutanen ƙasar ruman ya rabbata, dan kuwa dai kam da gaske 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 𝐢𝐛𝐧 𝐇𝐚𝐲𝐬𝐚𝐦 𝐀𝐛𝐝𝐮𝐥𝐥-𝐦𝐚𝐣𝐞𝐞𝐝 ya zama sarki na daban a cikin dubban sarakuna, tare da labari mai ban tsoro da razani fiye dana mahaifinsa. Kamar yanda ƙa'idar daular ruman take bayan cikar shekara talatin da biyar yarima Eshaan ya bayyana a ƙasar haihuwarsa ta Ruman, sai dai kamar kowane yarima na baya babu mai iya ganin fuska ko suffarsa ta ainahi, hatta da idanunsa ma shi babu wanda zai iya ganin koda ƙwayar cikinsu sakamakon glass dake sakaye da su. Bayan gama bayyanashi ga masarautu da wata ɗaya kacal Tajwar Haysam bin Abdul-Majeed yay murabus aka ɗaura yarima mai jiran gado bisa kujerar mulkin daular ruman tare da auren mata huɗu galla-galla daga mabanbanta masarautu masu ƙarfin faɗa aji a kasar ruman. Kwanan 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 bakwai akan karagar mulki Tajwar mai murabus Haysam bin Abdul-Majeed ya kwanta jiyya, jiyya ce data girgiza kowa ta kuma bada mamaki, dan kuwa kwanansa ɗaya tak yace ga garinku nan. Kwatanta tashin hankalin da ƙasar Ruman ta shigama a lokacin bazai lissafu ba. Ƙura bata lafa ba mutuwar ɗaya daga matan 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 ta sake bayyana, kwana ɗaya da mutuwarta watama ta sake mutuwa a washe gari amare suka rage saura biyu. Al'amari ya fara saka zukatan jama'a hasashen da babu damar cewa komai. Wata biyu tsakani ɗayar matar ta uku ta sake mutuwa saura ɗaya. Tofa babbar magana. Abu mafi girgiza zukata shine mutuwar ɗayar data rage a shigar sabon wata. Kenan matan Tajwar 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 da mahaifinsa sun gama mutuwa kaf a cikar wataninsa uku da hawa karagar mulkinsa da kuma aurensa. Abun ya taɓa zukata aynun, sai dai babu wanda ya iya ko tari saboda tsoro. Sai dai abu mafi tsayawa arai a cikar wata na shidda aka sake ɗaura auren 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 𝐢𝐛𝐧 𝐇𝐚𝐲𝐬𝐚𝐦 𝐀𝐛𝐝𝐮𝐥𝐥-𝐦𝐚𝐣𝐞𝐞𝐝 da wasu matan biyu daga gidajen masarautun kasar ruman. Labarin bai canja ba, dan kuwa suma sun mutu ɗaya bayan ɗaya kafin cikar shekararsa guda da hawa mulkin. Abin al'ajabi aka kuma sake aura masa wasu biyun daga wasu masarautun, suma ɗin dai kamar ƙiftawar ido nasu labarin ya shuɗe a cikin shekara ɗaya. Haka aka sake ɗaurama Tajwar Eshan aure da wasu mata daga mabanbanta masarautu da tsoro bazai barsu hana auran ƴaƴansu ba, haka kuma suka mutu suma ya kasance duk ya auri yarinyar kowace masarauta goma da suke da su.
Zuwa yanzu ba shakka da tsoron ɗaga murya bane kawai a zukatan mutanen ƙasar Ruman, hatta numfashi suna yinsane tamkar ɓerayen dake a ƙarƙashin tsaron maguna. A tunaninku yaya sautin fitar numfashin zai kasance?😭.
★★_________★★
Sunanta shine 𝕱𝖆𝖗𝖊𝖊𝖉𝖆𝖍 na yanka, sai dai iyayeta da dukan jama'a na mata alkunya da 𝑰𝒇𝒇𝒂𝒉. Su huɗu iyayensu suka haifa, itace auta a cikinsu. Hanash! Shine namiji babba. Arfa! ita ke bi masa, Fariha! Itace ta uku, sai ita auta 𝑰𝒇𝒇𝒂𝒉. Sunan mahaifinsu Zayyan!, amma suna kiransa Babiy, mahaifiyarsu Jamaima! Suna kiranta Ummu. Ƙasar Ruman ƙasarsu ce ta gado tun iyaye da kakanni, nan kaɗai suka sani, anan kuma kaɗai suke rayuwa. Kamar yanda na faɗa muku a tun farko ƙasar Ruman ƙasace mai tarin arziƙi nau-i daban-daban da ake kaikawo da su a cikin ƙasa da wajenta, tun daga kan zinare, noma, kiwo, ƴaƴan itatuwa dama wasu daban lissafo ba. Sai dai duk da wannan tarin arziƙi da ALLAH ya basu hakan bai hana kasancewar wasu a cikin matsayin talakawa ba. Kamar dai su 𝑰𝒇𝒇𝒂𝒉, mahaifinsu talaka ne mai rufin asirin ALLAH. Manomi kuma makiyayi, a nomansa harda noman zuma yakeyi. Dukkan wani nau'in zuma zaka samesa a hannunsa, wannan yasa yake mu'amula da daular ƙasar Ruman. Duk da ba masu arziƙi bane su mahaifinsu mutumne mai tsantseni da taka tsantsan, sannan ya tsaya tsayin daka wajen ganin sun samu ilimin addini dana zamani irin na yara ƴan gata. Gidansu gidane mai ban sha'awa da birgewa a ɓangaren mu'amulantar juna mai cike da soyayya da ƙauna. Basu da wani buri sai na faranta ran juna, a koda yaushe zaka samesu cikin nishaɗi dan talaucinsu bai taɓa kasancewa damuwa ga rayuwarsu ba ko nakasu ga farin cikinsu. Idan ɗaya na ciwo sukan kasance tamkar su duka suke ciwon, idan ɗaya na farin ciki sukan kasance su duka cikin farin ciki. Sune abokai kuma kawayen junansu harda iyayensu. Sunada tarin burika na rayuwa dana kai da kai, wasu a rubuce, wasu a ƙayyade a cikin zuciya, wasu a bayyane, wasu a adane a ƙasan zukata. wasu sun cika, wasu ƙaddarorinsu masu ɗaci da saka zubar hawaye dake gudana a halin yanzun sun yanke igiyar kaiwa ga samun cikarsu. Labarin sauyawar tasu, da yankewar tasu ya farane daga wata rana dake dai-dai da cikar sauran kwanaki huɗu na zagayowar bikin al'ada da ƙasar Ruman ke gudanarwa. Ranar da tarihinsu bazai iya gogewa ba, zukata bazasu iya mantawa ba, lissafin faruwarsu da shuɗewarsu bazai taɓa daina maimaita kansa ba koda a bayan rai ne.😭
A kowane karshen wata Babiy ke kai zuma tulu uku daular ruman, amma a duk bikin shekara na al'ada tulu goma yake kaiwa dan shi kaɗai ne yardajje a manoman zuma da sarki ke iya amfani da zumar dake zuwa daga hanunsa tun zamannin Tajwar Haysam. Koda ya mutu kuma 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 bai daina amsa ba. Sai dai kuma duk da wannan yarda a kullum zagaye suke da tsaro ta fannoni daban-daban duk a dalilin zumar da Babiy kan samarwa Tajwar. A ranar data rage sauran cika kwanaki huɗu na bikin al'ada rashin jin daɗin jiki ya saka Babiy bama Hanash damar tafiya dasu duka cikin ƙaton gidan gonat da yake noman zuma domin ɗurasu a sabbin tulunan da za'akai daular ruman. Da'ace yasan anjimarsa ko ƙaddararsa data ahalinsa da bazai taɓa barin wannan lokaci zuwa ba koda a mafarki. Sai dai kash, ƙaddara ta riga fata inji masu iya magana. Cike da farin ciki suka fita, dan kuwa a shekara sau uku kacal Babiy ke barinsu shiga cikin lambunsa. Ba lambun kawai ba, hatta fita koda ta zuwa makarantace suna yintane cikin shiga mai lulluɓe dukkan kamanni, domin kuwa ƴaƴan nasa na ɗauke da wani irin sirrin ƙyawu mai ɗaukar hankalin duk wanda zaiyi tozali da su, dan haka kullum cikin shigar larabawa suke harda niƙabi, idanunsu kawai ake iya gani da tafukan hanunsu, a yau kam sai suka fita a asalinsu batare da sanin iyayensu ba duk da kuwa suna dai sanye da abayoyin, sai dai babu niƙabin. Su kansu da'ace sun san abinda ke biye da rayuwarsu da zasu ninka niƙabi kan niƙabi ne har sama da sau sittin idan zai nisanta zuwan almakashin daya datse walwalin zinaren farin cikin zukatansu.
Sun isa lambu sun gudanar da ayyukan da Babiy ya umarcesu cike da farin ciki da nishaɗi, suka tsinko tarin ƴaƴan itatuwa kowa da nasa da burin abinda zaiyi dashi a ranar bikin al'ada dake tunkarosu. shigarsu gida dai-dai da isowar tambura da bushe-bushen algaitu masu ban mamaki da al'ajab a cikin kunnuwansu dama dukkan sauran talakawan gari, dan abune da ba'a sabaji ba sai a wasu lokuta na gittawar Tajwar daga can kan hanya bawai a cikin anguwa kamar hakan ba...........✍
Page. 2
...........Cikin ƙarfin hali Babiy ya zabura hanyar soro domin dubawa duk da halin ciwo da yake ciki. Baya yaja da sauri saboda cin karo da suka kusayi da tawagar jama'ar Daular Ruman dake ƙoƙarin shigowa suma. Kansa ya rissinar alamar girmamawa a garesu. Hanash da Ummu ma a kusan tare suka zabura. Cike da girmamawa mai haɗe da matsanancin tsoro Babiy ya zube bisa gwuyawunsa. Hakan da su Ummu sukaga yayi ya sasu zubewar suma tare da risinar da kawunansu, jikkunansu na matuƙar tsuma dan abune da ba'a taɓa gani kojin labarin faruwarsa a tarihin ƙasar Ruman ba. Babban mutum dake jagorantar tawagar ya tsaida idanunsa akan Babiy. “Ya kai wannan talaka dake a ƙarƙashin mulkin daular ruman, munzo da babbar magana ne gareka bisa umarnin daular ruman”.
Ƙasa Babiy ya ƙarayi da kansa, tare da haɗe hannayensa waje guda. “Ina mai matuƙar farin cikin ganinku tare dani, ni mai biyayyane ga kowanne umarninku”.
Duk da maganar Babiy ta musu daɗi babu alamar hakan a fuskokinsu. Ya miƙe cikin rawar jiki zuwa ɗakin Ummu. Mintuna kaɗan ya dawo da babbar tabarma sabuwa ƙal data saya domin auren Arfa zai shimfiɗa a gabansu. Dakatar da shi Shugaban tawagar tasu yayi cikin ɗaga hannu.
*_“Munzo nan ne domin isar da saƙo ba zama ba ya kai wannan talaka dake a ƙarƙashin daular ruman. Umarni a gareka daga daular ruman, taga iri a gidanka kuma tana buƙata. Muna mai tayaka farin cikin zama ɗaya daga cikin surukan tarihin daular ruman”_*.
A matuƙar firgice Babiy da iyalansa duka suka ɗago cikin zabura da matasanancin rikicewa. Sai dai basu da ikon koda motsa bakunansu balle neman ƙarin bayani. Kasancewar ba amsa dama suke buƙata ba mutumin ya janye idanunsa daga Babiy ya maida kansu Arfa da suka ƙanƙame hannayen junansu.
“Wacece babba a cikinku?!”.
Kalamai huɗu masu ƙarfin razani da neman fasa zukatan mai saurare da har abada bazasu bar amsa sauti cikin zuciya da ɓargonsu ba suka fita daga bakin ɗaya daga firɗa-firɗan samudawan dake zagaye da mutumin. Babu wanda ya iya motsawa a cikinsu, dan kuwa sake dulmiya suke a cikin duhuwa.....
Saukar sautin wata zabgegiyar bulala mai adon jikin zakanya a jikinta ya sakasu zallo baki ɗaya. Babiy ya zube a ƙasa saboda azaba na raɗaɗin shigar wannan bahaguwar bulala a jikinsa, ganin basamuden mutumin dake riƙe da bulalar ya sake ɗagawa zai zuba masa Arfa ta miƙe tana mai fashewa da kuka jikinta na karkarwa tace..
“Nice!”.
Cikin daka tsawa basamuden hadimin yaba Fariha da Iffah umarnin suma su ɗago. Ɗagowa sukai jikkunansu na karkarwa ga hawayen tausayin mahaifinsu ya wanke musu fuskoki. Idanu ya zuba musu kusan na sakan goma, kafin ya janye ya maida ga shugaban tawagar tasu.... “Zancenta nakan gaskiya ALLAH ya ƙara maka lafiya”. ya faɗa cikin girmamawa ga shugaban tawagar tasu. Shugaban ya gyaɗa kansa shima idanunsa akan Arfa “Mahaifinta da ɗan uwanta zasu zama waliyyanta”.
Ya faɗa cike da cika umarni yana mai nufar hanyar fita batare da wani ƙarin bayani ba......
Har aka tafi da Hanash da Babiy babu abinda su Fariha suka fahimta, balle ma Iffah da kallon kowa kawai take. Kukan Ummu ne ya dawo da su hankalinsu, gaba ɗayansu sukai kanta. Ummu dake kuka kamar ranta zai fita ta haɗasu su duka ukun ta rungume jikinta na wani irin rawa......
★★_______★★
Tafiyarsu da kamar awanni uku Babiy da Hanash suka dawo gida da doki ɗaya da tarin kayayyaki, sai rakuma guda uku. Fuskokinsu cike suke da firgici mai tsayawa a zukatan masu kallo. Ba abinda sukazo da shi bane a gabansu Ummu, burinsu susan mike faruwa? Kawai. Basu samu amsa ba daga garesu har bayan shuɗewar wasu awanni, kafin Babiy ya basu amsa cikin dakewa....
“Na bada aurenta ga *_Shahan-shan_*, bamu baro ba sai da aka ɗaura musu aure, wannan raƙuman da dokin sadakinta ne”. Ya ƙare maganar idonsa akan Arfa.
Tamkar saukar aradu mai tarnatsa haka furucin ya isa cikin kunnuwansu, Ummu tai baya zata faɗi Babiy ya riƙota, kansa yake girgiza mata alamar kartace komai, suma yaran ya juyo garesu yay musu nuni da shiru ya jata suka shige ɗaki. Umarnin mahaifinsu shine mafi girman biyayyarsu garesa matsayinsu na waɗanda ke rayuwa a ƙarƙashinsa, badan sun so ba suka zaɓi shiru, sai dai shirun nasu bai hanasu haɗe kai a ɗaki suyi kuka ba su ukun. Kuka irin wanda za'a kira kuka a duk idaniyar da zubar hawaye ke kwaranya na rashin lissafin ƙididdiga. Mintuna sun shuɗe, hakama awannin da suka ƙarasa kalmashe wannan yinin. Bayan sallar magrib saiga motoci da tawagar hadimai tare da wasu hamshaƙan mata huɗu wai sunzo ɗaukar Amarya Arfa. Kuka suke tamkar ransu zai fita, haka sunaji suna gani suda iyayensu aka shirya Arfa cikin shiga ta alfarma aka wuce da ita Daular Ruman.
Dare ya riski zukatansu cike da damuwa, yayinda sai ɓarawo mafi iya satane ya samu nasarar sama musu nutsuwar wucin gadi wato barci. Sun wayi gari kunnuwansu a buɗe na jiran jin labarin mutuwar ƴar uwarsu, sai dai babu wani alamar hakan har sake shuɗewar kwanakin zuwan ranar bikin al'ada.
Babu fashi aka gudanar da bikin al'ada na ƙarshen kowace shekara. Sai dai su a zuri'arsu babu wanda ya leƙa koda ƙofar gida. Anyi an gama, kamar kowace shekara an samu rashin rayuka a wasanni daban-daban, da kuma haɗarin mota dana mashina suma a tituna daban-daban saboda cinkoson jama'a dalilin garin shine babban birni da Daular Ruman ke ciki. Bikin al'adar ƙasar ruman kuma yana ɗaya daga cikin biki mai tsananin ƙayatarwa da mutane daban-daban suke halarta daga sassan duniya ta ko ina. Shahan-shan ya fito zagaye tamkar kowace shekara cikin shiga ta alfarma, bashi a karan kansa ba hatta keken dokinsa ma abin kallo ne, sai dai a wannan karon ma babu wanda zaice ga kamanin Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed ɗin.
★ A haka lokaci ya ƙara turawar da kwanaki suka zama watanni kusan uku. Shuru na waɗannan watanni bai sama musu wata nutsuwa ba, dan a kallon farko da mai gani zaima gidansu zai san akwai matsala tattare dasu. Komai ya sauya, sauyawa irin wadda ƙaddara ta shigo cikin tarihinsu. Babu mai walwala a cikinsu, komai na ƙarfin hali sukeyi, abinci ya gagara ciyuwa yanda ya kamata a koda yaushe garesu, sai cin ƴaƴan itatuwa, tunkan a sanar musu alamominsu sun tabbatar da zaman makokinsu. A haka duhun wani dare na cika watanni uku da kwana uku da auren Arfa ya sake riskarsu, suka sake zama ƙarƙashin mulkin mallakar ɓarawo mafi iya sata koda shiri ko babu wato (barci). Daren da yazo ma Iffah da wasu irin munanan mafarkai masu firgici daban tsoron.
Har rige-rigen fitowa suke daga ɗakunan barcinsu sakamakon fitar sautin razananniyar ƙarar data karaɗe gidan mai ban tashin hankali. Su duka huɗun suka rufu a kanta kowa na ambaton sunanta da kai hannu jikinta. Duk da sanyi da akeyi jike take sharkaf da zufa ga illahirin jikin nata daya ɗauka zafi. Ummu ta rungumeta tana mai sakin hawayen da ke kwance a cikin idanunta. Ta riga ta farka dan haka itama ta ƙanƙame Ummun tana fashewa da nata kukan.
Ba yau ne karan farko da Iffah ke shiga irin wannan tsoron ba sakamakon firgici a mafarki, sai dai na kwanakin nan yafi razanarwa da saka ruɗani a zukatansu. Babiy ya kai hannu ya shafa yalwataccen gashin kanta, murya a raunane yake ambatar sunanta.. Kanta ta ɗago a hankali fuskata sharɓan da hawaye, ta dubi mahaifin nasu da Yayansu Hanash da Fariha, sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tare da haɗiye sauran kukan tana tashi zaune daga jikin Ummu ta share hawayen dake jiƙe da fuskarta. Matsawa tai jikin mahaifinsu tana mai kamo hanunsa.
“Babiy inajin tsoro, matuƙar tsoro a wannan mafarkin fiye dana kullum. Babiy itama Nina Arfa kashemana ita zasuyi kamar sauran matan daya aura?, itama zamu rasata na gani a mafarki na...”
Da sauri Hanash da dukkan rauninsa ya bayyana a fuskarsa ya shiga girgiza mata kansa cikin aro jarumta. “Mafarki ba gaskiya bane Iffah, ki kwantar da hankalinki Arfa na cikin ƙoshin lafiya tamkar mu insha ALLAHU...”
“Amma Akh Hanash nawa yasha zama gaskiya, a daren da Nina Arfa zata bar gidan nan irin wannan mafarkin nayi a kanta, yau ma shine na maimaita da ita babu banbanci a cikinsa na rantse maka”.
Har ƙasan zukata zancen nata ya dake su, ganin bayyanar rauni a fuskokinsu ya saka Babiy yin murmushin ƙarfin hali yana shafa kanta. “Shaiɗanu zasu iya dawo miki da makamancin sa ai Ibnati, dan haka ki kwantar da hankalinki Arfa na lafiya a gidan aurenta”.
Bazata cigaba dayin jayayya da su ba, amma tana cikin matsanancin damuwa tamkar yanda take hango tasu akan fuskokinsu. Maimakon komawarsu barci sai duk suka miƙe zuwa tsakar gida, alwala suka ɗauro, suka koma can runfar dake matsayin falon iyayensu suka fara salla da miƙa kukansu ga UBANGIJIN talikai da fatan hana tabbatuwar abinda zukatansu ke cikin tsananin fargaba. Haka suka kasance har sallar asubahi gaban mahaliccinmu, bayan idar da sallar asubahi maimakon kwanciya sai suka riski kansu a zaman jugum-jigum na jiran tsammani. Har fitowar rana babu wani yunƙuri daga ɗayansu. Sai ko ga isowar abinda suke fargabar ya riskesu ya iso garesun. Shigar bugun gidan a cikin kunnuwansu ta sakasu miƙewa a zabure gaba ɗaya kuma a lokaci ɗaya, kowanne cikin rawar jiki da fidda tsammani. Babiy ne yay jarumtar ƙarasawa ga soro cikin jan ƙafa. Tunda yay tozali da hadiman masarauta zuciyarsa tai wata irin masifar wulƙitawa.....
“Kun kasheta itama ko?!”.
Da shi da hadiman suka riski muryarta a cikin kunnensu a bazata. Sam babu tsoro ko shakka irin wadda akema duk wani mai alaƙa da masarauta a ƙasar cikin idanunta a yau. Sun soye sunyi jazur irin na tashin hankali. A harzuƙe cikin hadiman ɗaya ya daka mata tsawa da faɗin, “Hattara ɗiyar talakawa, bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane”.
“Idan yaron ya kasance rago ba!!”.
Ta bashi amsa itama a tsawace. Shimfiɗeɗiyar bulalar hanunsa ya ɗaga zai zuba mata Babiy ya kare cikin rawar jiki yana mai zubewa ƙasa a kan gwiyawunsa. Sosai a zaba ta ratsashi, ya rimtse idanu cikin aro dakiya da jarumtar dole, “A gafarceta ita ɗin yarinyace masu nasara”. Ya faɗa cikin rawar murya saboda azabar tasirin shigar bulalar.
Ƙasa Iffah takai durƙushe gaban Babiy tana mai fashewa da kuka, kafin ta ɗago ta dubesu zatayi magana Babiy yasa hannu ya rufe mata baki jikinsa na tsuma. Jikin nata itama tsumar yakeyi, sai dai ita bana tsoro bane na tsananin baƙin ciki ne da bushewar zuciya. So take ta amayar da abinda ke bakinta an hanata. Batare da hadiman sun sake bi takantaba suma suka isar da saƙon dake tafe da su.
“Kasancewarka mai biyayya da bin umarnin masarauta a karo na biyu an sake baka damar halartar jana'izar ɗiyarka kai da zuri'ar ka. Mun barka lafiya”.
Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un. Babiy ya shiga ambata, kusan a tare Ummu da Fariha suka saki razananniyar ƙara wadda ta jawo hankalin maƙwafta da mutanen dake tsaitsaye a ƙofar gida tun wucewar hadiman masarauta. Dan sun san dai labarin gizo bazai wuce na ƙoƙi ba........
*_WASA FARI GIRKI_*
Dole ne zuri'ar mal. Zayyan su ambaci rasuwar Arfa da kalmar WASA FARIN GIRKI a jerin zaren ƙaddarar da ta kutso a rayuwarsu mai ɗauke da almakashin da ya datse farin cikinsu. Sun rasata tamkar labarin hikayoyin marubuta ko wasan kwaikwayo na film. Ta tafi tafiyar da bazasu sake ganita ba, tafiyar da babu wanda aka bawa damar yin cikkakkiyar sallama da ita a cikinsu hatta mahaifansu. Ta shuɗe a ƙaddararsu tamkar yanda ruwan damuna kan tafi da duk wani yayin dakan tare masa hanya a lokacin wucewa. Komai ya faru tamkar ba'aiba. Babu mai iya koda tari balle bin ba'asi. Iyakarsu kukan idanu dana zuci wanda muryarsu kan tsayane kawai iya filin gidansu ko katanga basu isa bari ta haura ba. A yau ma dai Babiy da Hanash ne sukaje domin jana'izarta. Suko aka barsu da amsar gaisuwa a cikin gida wadda mutanensu talakawa na zuwa musu itane a ɗarare.......
Kwanaki sun cikagaba da shuɗawa tamkar ba'ai komai ba, yayinda ɗayar matar Tajwar da aka aura masa tare da Arfa itama dai ta mutu bayan wasu watanni. Bayan su Arfa ba'a sake jin Tajwar yayi wani aure ba, sai dai mutane na raɗeraɗin a duk randa aka kaisu domin ziyartar turakarsa babu fashi gawarsuce take fitowa. Hakan yasa kowa ke danganta mutuwar matan da tsafi yakeyi dasu.
Wata huɗu da sati ɗaya cif tarihi ya sake maimaita kansa, dan kuwa Fariha ta sake faɗowa a jerin matan da aka ɗaurama Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed aure da su. Batare da wani shawara ba a safiyar alhamis suna zaune kira ya riski Babiy daga masarauta, babu wanda bai shiga tsoro da firgici ba a cikinsu, sai dai babu wanda ya isa hana hakan a duk faɗin ruman. Sunaji suna gani babiy yay shiri ya amsa kiran. Tafiyarsa da awanin da basu gaza biyar ba sai ga hadiman masarauta sunzo sunma Fariha ɗaukar amarya itama babu wani bayani daga garesu. Ranar dai kam Iffah bata gazaba kojin tsoro wajen gwada musu hauka, dan bata bari an fita da Fariha ba har sai da basamuden nan ya zabga mata bulalar dorinar hanunsa data sakata zubewa, bata tashi dawowa hayyacinta ba sai bayan wucewarsu da kusan awa guda. Zuwa lokacin har Babiy ya dawo. Kamar dai Arfa itama Fariha an ɗaura mata aure da sarkin da kowa yake masa inkiya da fir'aunan wannan ƙarnin. Sai dai a ɓoye wannan suna ke fita a bakunan talakawan gari irinsu Iffah. Sakamakon bulalar da aka zabga ma Iffah bayanta yay mugun fashewa har akan mazaunanta, ga wani raɗaɗi mai azaba na ratsata har ta kasa riƙewa sai da ta saki ƙara. Babiy da Ummu suka rufu a kanta, hawaye suke suna jeramata sannu, Hanash na gefe zaune idanunsa jajur alamar tsananin ɓacin ran da babu ƙarfin ɗaukar mataki......
Tayi jiyya ta kwanaki uku, wajen ya warke, daga haka kwanaki suka cigaba da tafiya, inda a cikar watanni biyu itama Fariha mutuwarta ta riskesu tamkar ba'ayita ba. Sun sake rasa Fariha a dalilin auren Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed.............✍😭
3
.........A wannan gaɓar haukane kawai ya rage wannan ahali suyi, dan duk dauriyar Babiy ya kasa danne raɗaɗi da zafin da yakeji. Itako Iffah kalaman dake fita a bakinta kausasa sun saka kowa ke ɗaukar tama zare kawai. Daga ƙarshe maganin barci aka ɗura mata. Bata tashi farkawa ba sai a ƙauyen da kakanninsu ke rayuwa. Wato iyayen Ummu. Rayuwa a ƙauyen Jumna a gareta tamkar mai gushewar hankali ya zame mata. Domin bata gane komai sai sambatu da kalamun ɗaura ɗammarar ɗaukar fansa ga duk ahalin Daular Ruman. Ba ƙaramin dagewa da jajircewa kakannisu da su Babiy sukai ba a kanta wajen ganin ta samu lafiya ta dawo hayyacinta. A cikin watanni takwas ta rasa yayunta guda biyu, wannan babban tarihine da bazai gogu a zuciya da ruhinta ba har karshen rayuwarta. Bayan jiyyar watanni kusan uku ta dawo hayyacinta. Sai dai ta daina fira'a da kowa, an daina ganin dariyarta ko farin cikinta. Babu abinda ke'a ranta sai buri da ƙudirin ɗaukar fansa. Tama kanta alƙawarin ita da hannunta zata kashe *_Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed_*. Bayan nan idan itama an kasheta burinta ya cika na kawar da azzalumin sarki mai mulki irin na fir'auna a ƙasarta a cikin al'ummarta....
*_(Babbar magana. Tayaya wannan buri naki zai cika Iffah😱? Sarki mai cikakken iko irin Tajwar Eshaan, mai amsa sunan Shahan-shan da ko fuskarsa babu wanda ya iya sani a cikin kasar Ruman har yanzun. Anya kuwa....? To mudaije zuwa wai mahaukaci ya sai kura😬🤧🚴🏼)_*
★★★
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” bakinta ke ambata cikin firgici da rawar jiki sakamakon farkawar da tayi daga mummunan mafarkin daya risketa a cikin barcinta. Ta dafe kanta dake wata irin sarawa na ciwo tamkar ana mata luguden taɓaren daka a tsakkiyarsa, gaba ɗaya jikinta ya jiƙe da zufa tamkar tayi wanka. Kusan watanni biyar kafin mutuwar ƴan uwanta da fara canjawar salon mafarkainta saɓanin na baya, abu mafi tsoratarwa kuma kusan mafarki ɗaya ne ke maimaita kansa a kowane barcinta idan ta kwanta. Sai dai mafi tashin hankalin a yau yayi kamanceceniya da na wasu dare da tarihi bazai taɓa mantawa da shi ba a cikin rayuwarsu ita da ahalinta.
“Nina Arfa! Nina Fariha!”.
Ta ambata a zahiri zuciyata na ƙara ƙarfin gudu, yayinda hawaye suka shiga rige-rigen sauka a kumatunta. Tabbas irin wannan mafarkin tayi a daren da suka rasa Arfa, hakama daren mutuwar fariha. Yau kuma gashi ta maimaitashi akan kanta. Itama kenan zasu rasata?. Kai ta shiga girgizawa wani kuka masu ƙarfi na sake tahomata, hannu tasa ta toshe bakinta gudun kar sautinsa ya kai ga kunnen kakanninta. Sai dai aikin gama ya gama. Dan kuwa muryar kakanta takeji jikin ƙofar ɗakin nata a hankali yana ambatar sunanta. Da sauri ta shiga goge hawayen, kafin ta tashi daga shimfiɗar barcin nata wadda karan gado ne da katifar rimi. Mayafi ta ɗauka ta yanama jikinta, ta ƙarasa ga ƙofar ta buɗe...
“Kina lafiya kuwa ɗiyar nan?”.
Ya faɗa cikin kafeta da idanu. Kanta dake rissine ta jinjina masa, cikin son danne kukan dake yunƙuromata ta bashi amsa.
“Ina lafiya Kaka”.
Jin shiru bai sake cewa komai ba ta ɗago ta dubesa a karon farko. Shima dai kallon nata yakeyi tamkar mai nazari. Sake maida idonta tai ƙasa, hawayen da take faman riƙewa suka ɓalle mata da gudu. Bata san ta ambaci “Kaka nima zasu kashe muku ni ko?. Inaji a jikina nima zaku iya rasani nan kusa tamkar yanda muka rasa su Nina Arfa”. Rawar da jikinta ta fara ta sata zubewa a gabansa kuka na ƙwace mata. Kusan minti biyu baice da ita komai ba, ita kuma ta kasa tsaida kukan.. Jin saukar hanunsa saman kafaɗarta ya sata haɗiye kukan, ya ɗagota tsaye yana ɗan murmushi dake sake bayyana tsufansa. Gefen mayafin jikinta ya kama ya shiga goge mata hawayen. “Fareedatu! Ki kwantar da hankalinki, insha ALLAHU babu abinda zai faru da ke, mafarki ai ba gaskiya bane ba. Suma su Arfa kwanansu ne ya ƙare, koba komai kuma sun rasu a gidan aurensu. Wannan kawai ya ishemu farin ciki”.
Kanta ta jinjina masa tana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Ya cigaba da shafa kanta a hankali har zuwa wani ɗan lokaci. “Kije kiyi addu'a ki kwanta abinki da safe zamuyi magana”.
A hankali tace, “Kaka ina son zuwa naga su Ummu gobe to dan ALLAH”.
Da sauri ya girgizamata kansa. “A'a bazai yuwu ba Iffah, iyayenki sun kawoki nan ne domin kuɓutar dake, taya kike tunanin zan barki komawa cikin daular Ruman?. Tun ina ƙanƙanin yaro nake bauta wa masarautar Ruman, bayan mutuwar mahaifina na cigaba da bautar saƙa kayan doki a garesu kamar yanda mahaifina ya barmin gado, a haka na haifi ƙanin mahaifiyarku shima ya mayeni, gashi har girma ya riskesa shima yana bauta musu. Mun rasa ɗan uwan mahaifiyarku a yaƙin kare daular Ruman, mun rasa Arfa, da Fariha. Ke ɗaya da kika rage mana da yayanki wajen mahaifiyarku kuma sai muyi wasa da rayuwarki? Bazai yuwuba jeki kwanta...”
Batare daya sake bata damar yin magana ba ya juya ya koma bayan ya jamata murfin kofar. Da kallo kawai ta bisa hawaye na silalo mata. Duk yanda taso komawa barcin bayan tafiyarsa hakan ya gagara, zuciyarta ta kasa fita da ga ƙangin fargaba, da gaske tanajin matuƙar tsoro bayan rasa Fariha da Arfa da sukai watanni ƙalilan da suka shuɗe itama su rasata, tanaji zuciyar ahalinta bazata iya ɗauka ba idan itama suka rasatan. Wasu zafafan hawaye suka sake silalo mata masu raɗaɗi da saka ƙuna a ƙirji......
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
★★★
“Iffah! Iffah!!.....”
Sautin ƙwala kiran sunanta daga muryar kakarsu da suke kira Iyyani ya sakata fitowa daga banɗaki data zagaya domin yin fitsari. Turus ta tsaya tare da haɗiye maganar da zatayi tana mai kallon ɗan-uwanta Hanash dake zaune gefen kakar tasu a ƙarƙashin bishiyar ɗoruwa da take a tsakar gidan. Murmushin da yakemata ta maida masa, kafin ta ajiye butar hannunta ta ƙarasa garesa. Dab da shi ta zauna tana mai ɗan rungumesa ta gefe da faɗin, “Ina kewarku Akhi”.
Murmushinsa ya sake faɗaɗa yana mai kallon fuskarta. Ya kai hannu ya shafi yalwataccen gashin kanta da mayafin ya zame mai tsaho da santsi. “Muma muna kewarki Little angel. Gidan duk ya sake zama mana babu daɗi”.
Yanda maganar tasa ta ƙare cikin rauni itama sai idonta ya cika da ƙwalla. Amma sai ta dannesu da murmushin mai ɗaci tana kaɗa kanta kawai.
“Tashi ki bashi ruwa mana, k haka ake tarbar baƙo a garinku”.
Baki ta ɗan tura gaba da kallon Iyyani mai maganar, tayi hakane danta katse raunin data hanga a fuskokinsu. Ta miƙe tana bata amsa cike da shagwaɓa. “Iyyani laifinkine fa, ban taɓa ganin matar da bata tattalin mai gida ba irinki, dole Yayana ya miki kishiya”.
Daƙuwa tamata cikin gatsina fuska. “Ungo naki nan Fareedah, yo bandama lalacewa mizanyi da wannan faratun mai kama da jar tsada tuzurin banza”.
Hanash ya tsuke fuska yana kallon Iyyani. Murmushi Iffah tayi tun kafin ya faɗi abinda ke bakinsa. Dan dama inhar suka haɗu da Iyyani sai ta hasalashi take jin daɗi shi da Arfa akan ƙinyin aure, duk da bawani shekarune da shi ba, dan ashirin da shida ne kawai, Arfa nada ashirin da uku, Fariha nada ashirin da ɗaya. Iffah nada goma sha takwas....
Iffah ta dire masa abinci da ruwa ta sake kaiwa zaune kusa da shi sannan ta dubesa. “Akhi yasu Babiy suke?”.
Ya nisa a hankali bayan ya dire moɗar ruwan daya sha. “Duka lafiya suke. Suna gaisheki ke da su kaka. Duk da suma dai nan da kwana kusa zamu ma dawo nan ɗin muma. Yanzu haka nazo duba can tsohon gidanmu ne dan asan gyaran da za'ai masa”.
Sosai ta kafesa da ido ita da Iyyani. Kafin cikin ƙarfin hali Iffah tai magana. “Amma Yaya su Babiy basa ganin rayuwa zata mana wahala anan sakamakon bamu sababa sam. Sannan ayyukansu dake acan miye makomarsu? Da karatunmu muma?. Abinda ya faru ya riga ya faru, tunda hannayenmu bazasu iya maidosu ba, mi zaisa zukatanmu bazasu cigaba da haƙuri ba. Barowarmu cikin Daular ruman tamkar munji tsorone, ko sake sakin rayuwarmu a hanun waɗanda kansu kawai suka sani.......”
“Tsoro halak ne Iffah. Bama muba mafi yawan masu yara mata sunata barin daular ruman a yanzu domin tseratar da ƴaƴansu daga auren jeka nayika. Karatun ƴammata yana neman tsayawa cak, kowace na tsoron fitowa ta zama nama a hanun hadiman daular ruman. a yanda lissafin yake a yanzu an rasa mata goma sha huɗu fa, a tunaninki kafin ƙarewar wannan shekarar ba'a rasa fin hakaba duk da bawai ya cigaba da auren bane.”
Wasu hawayene masu ɗaci da ƙuna suka silalo ma Iffah, tai saurin saka gefen mayafinta ta share tana murmushin takaici. “Niko a ganina gudu bashine mafita ba, muryoyinmu ya kama mu ɗaga wa duniya kowa yasan halin da muke ciki, idan har a ƙasar Ruman babu wani sama da nasa mulkin ai a sauran ƙasashen duniya akwai wanda suka fisa...”
“Humm Iffah ke yarinya ce har yanzu.”
“Sosai kuwa Hanash. Shiyyasa bata gane komai sai abinda yanzu take zuwa da shi”.
“Humm Iyyani kenan”.
Iffah ta faɗa a yanayin jin raɗaɗi a maƙoshinta. Su duka kallonta sukai, sai dai ta ɗauke kanta gefe tamkar bata gansu ba. Daga haka babu wanda ya sake cewa komai har tsahon wani lokaci. Iyyani ce ta canja hirar da wani abu daban har Hanash ya kammala. Tare da shi suka fita wajen duba tsohon gidan da kakaninsu da suka haifi Babiy ne suka rayu a ciki, dan sudai tunda suka taso a cikin birinin daular ruman suka san kansu duk da a ɗan gefen gari suke acan ɗin ma. Sai dai su shigo cikin ƙauyen Jumna a matsayin duba kakannin nasu. zuwa yanzu su duk sun rasu, shiyyasa gidan ya kasance babu kowa. Duk ma ya rusa ya fita hayyacinsa dan ginine na jar laka tamkar yanda duka gidajen ƙauyen suke. Sun ɗan jima acan suka dawo, sun iske kaka ya dawo shima daga fitar da yay tun ta safe gona ɗebo sassaƙe-sassaƙen magunguna. Ƙara zaman tattaunawa sukayi iya su uku, ita dai Iffah bata cewa komai. Daga ƙarshe ma tashi tai ta shige ɗakin kwananta. Bata sake fitowa ba sai da kaka ya neme ta. Sassaƙe-Sassaƙen magungunan daya ɗibo ɗazun ne a gabansa, kowanne ya ɗauresa daban-daban. Ya turamata babban robar da suke ciki... “Zaki fara amfani da su Iffah, bana son kiyi wasa dan ALLAH. Waɗannan kuma hayaƙine, a kowacce duhun magriba ki tabbatar kinyi turarensu, wannan kuma a ruwan wanka ne, da kin idar da sallar asuba ki zubasu cikin ruwa kaɗan ki cire kayanki ki tabbatar duk jikinki ya samu”.
“Tofa kaka wannan ɗin kuma duk na miye?”. Iffah ta tambaya cikin nuna mamaki.
Idanu ya tsiramata na kusan mintuna uku tamkar mai nazari, sai kuma ya ɗauke kansa da wani yanayi mai wahalar fassara. “Faruwar ƙaddararmu bashi ke nuna baza'a sake jarabtarmu ba. Idan jiya ta shuɗe da ɗaci zata iya yuwuwa yau ɗinmu da dariya zata kasance, sai dai sanin mike a gobenmu al'amarine mai girman gaske, damin gaibunmu ce ita ALLAH ne kaɗai masanin mi zaizo.”
Kallon juna sukai ita da Hanash, Iffah ta ɗan ɗage kafaɗa cikin yanayin ban fahinta ba, shima sai ya kaɗamata idanu alamar shima hakan take. Atare suka maida dubansu ga kaka. Amma sai ya kauda kansa alamar baya buƙatar kowacce irin tambaya daga garesu. Iffah ta jinjina kai kawai alamar ko'oho. Sai kuma ta miƙe tana mai faɗin, “Ni dama fa na yanke shawarar zanbi Akhi mu koma. Tunda dai naji sauƙi gara naje na koma makaranta anata wuceni a darasi”.
Ba karamin waro idanu Hanash yay ba, zaiyi magana kaka ya dakatar da shi ta hanyar yin murmushi da kaɗa kansa. “Ita rayuwa rubutacciya ce tunkan halitta, an rubutatane da alƙalamin da ba'a goge rubutunsa, babu wani hannu daya isa gogeta koda da ƙarfin iko. Dole ne sai anyi hakan, ko muna so ko bama so mashin nan sai ya isa inda aka aikashi. Domin ita *KIBIYAR AJALI! SULKE BAYA TARETA SAI TA GITTA*”.
A rikice Hanash ya tari numfashinsa. “Kaka bana gane dunƙulallun zantukan nan naka, ka fito fili dan ALLAH ka sanar mana mi kake son faɗa...”
“Hanash! Lokacin faɗar baiyiba ai, nima kurman baƙin kawai na gani, fassarar sai UBANGIJI”.
Sosai Hanash ya sake tsare fuskar kaka da idanu, kamar yanda itama Iffah tai tsai tana kallon nasa. Su dukansu sun jima da sanin kaka mutum ne hatsabibi, dan kuwa mahaifinsa gawurtaccen masanine da azamaninsa akan kallesa tamkar matsafi ko wani mai gani har hanji, sai dai kasancewar bai ajiye buzu ya zauna akan iya wannan al'amarin ba yasa ake shakkar faɗa, yana bada taimako na magani akan abubuwa daban-daban musamman harkar aljanu komai ƙarfinsu da shaiɗancinsu. Sannan yana sana'arsa ta saƙa kayan kwalliyar doki. Kaka ya gaji abubuwa da dama a garesa, sai dai shi ya watsar da harkar bada maganin dan shima dai a karan kansa yana ta'allaƙa sanin mahaifin nasa da bokancin, duk da dai bai fito fili ya bayyana hakan ba kuwa, amma rashin maida hankali akan abinda ya shafi hakan zaisa ka zargi ko haka ɗinne. Akwai kayan aiki na mahaifinsa da yawa a killace a wani waje da shi kaɗai ya sani, kuma tun bayan mutuwarsa shi ya tattare su ya killace su............✍
Page 4
.........Iffah tayi mamaki da kaka ya bari salin alin tabi Hanash washe gari, duk da Iyyani taso borewa ita. Amma wasu lafuza daga cuɗaɗɗun kalamansa ya sata yin shiru ta bisu da addu'a. Kaka yayma Iffah gargaɗi matuƙa akan abubuwan daya bata, ya kuma tabbatar mata ko guda ɗaya taƙiyi zaiji hakan a jikinsa.
A hankali ta murza awarwarayen hannunta da shine ya sakamata, ta sake lumshe idanunta da sakin ajiyar zuciya. Haka kawai takejin awarwarayen da girma da kuma banbanci da irin wanda take sakawa a baya domin kwalliya, ko miye dalili oho.
Daga Ummu har Babiy a tsorace suke kallon Iffah da Hanash da suka shigo. Hanash ya girgiza musu kansa cikin sauri yana faɗin, “Wlhy ba laifina bane Babiy. Itace ta bore akan saita biyoni, kaka kuma ya bata goyon baya. Dan a cewarsa _(Babu wani nisa dake bada tazarar gujema ƙaddara. A wani ajin jarabawar data biyoka ma gara kai ka tunkareta. Dan ba kowane kogo bane ke zama kogo ga ma'abocin gudun ceton rai)._ Babiy na kasa fassarawa, akoda yaushe cirkuɗaɗɗun kalamai daga bakin Kaka masu tsaurine da wahalar fahimta. Dan ALLAH idan kun sani ku fassara mana”.
Maimakon amsa daga Babiy baya sukaga yayi tamkar zai faɗi, sai dai cikin sa'a ya dafe gini tare da dafe kansa alamar hajijiya. Ummu ma ƙasa takai zaune jikinta na rawa, hakan sai ya ƙara firgitasu. Da sauri duk sukai kansu suna mai tambayarsu suna lafiya kuwa?. Da kai kawai suka amsa musu, Babiy harda ƙoƙarin ƙaƙaro murmushi. Cikin son kwantar musu da hankali yake kallonsu. “Kunga karku sakama zukatanku wata damuwa, ba maganar Baba bace ba, kawai dai bana jin daɗine kwana biyun nan dama”.
Jimm sukai alamar tunani, sai dai kuma babu damar yin musu ko ƙin aminta da cewar tasa. Hanash ya taimaka masa suka koma cikin runfa, Iffah kuma tana riƙe da Ummu..
★★★
Washe gari batare da sun sani ba Babiy yay sammakon yin tafiya zuwa ƙauyen Jumna. Ya samu tarba daga surukan nasa ko ta girmamawa....
Ƙyaƙyƙyawan tsohon da Tattarowar fatarsa ta tsufa bai hana bayyanar ƙyawun cikar halittarsa ba ya sake kallon dattijon gabansa a karo na babu adadadi. Murmushi ya saki a karon farko, cikin karyar da kai da ƙanƙan da idanu ya kai hannu bisa kafaɗar dattijon. Numfashi yaja kakkaura da juyowa alamar dawowa hayyaci. Ya maida kansa ƙasa ya sunkiyar saboda girmamawa ta surukuta dake a tsakaninsu na tsahon shekaru.
“Humm Muhammadu Zayyanu!”.
Tsohon ya kira sunan tamkar mai sake bita a ranar da aka raɗa ga mai shi. Ɗago idanu ya sakeyi a karo na biyu sai kuma ya risinar tare da amsawa da “Na'am Baba”.
“Tun isowarka magana nake gani shimfiɗe a fuskarka amma bakinka ya kasa furtawa, ko wani abu ya sami Hanash da ƴar uwarsa ne a hanyarsu ta komawa gida jiya?”.
“A'a baba ko ɗaya, lafiya lau sukaje cikin ƙoshin lafiya kuma, sai dai.....”
Sai kuma yay shiru ya kasa ƙarasawa. Kaka dake kallonsa yay ɗan murmushi, “Sai dai baku so komawar Iffah ba ko?”.
“Hakane baba. Domin kuwa babu abinda ya canja a daular Ruman, muna jin tsoron rasata itama kamar ƴan uwanta, duk da bamu da tabbacin zasu sake waiwayrnmu, sai dai kalamanka sun sakamu a ruɗani har muka kasa rumtse idanu a daren jiya domin yin barc......”
“Hana ido barci bashi ke nufin damar iya sauya abinda bakai ka rubuta ba. Muhammadu Zayyanu! Da ace ƙaddararmu a hannayenmu take da kaf mutane bazasu zana zaman duniya ba a littafinsu musamman idan sun san koda daɗin busawar iskar dake cikin aljanna ce. Karka damu kanka da sanin sirrin cikin dutsen da ko'a kallo abin firgitarwa ne. Mumini yakan kasance mai azumtar yini daga UBANGIJI, ya kuma sallaci duhun dare daga UBANGIJI domin yaye damuwa ko samuwar nutsuwa a duniyarsa. Gaibu daga ALLAH take, zahirin da yaso mu sani kawai yake iya nuna mana ta isharar rayuwa ko canjawar tunanin zuciyo
yi”.
Nannauyan numfashi yaja ya fesar tare da jinjina kai, bawai kwanciyar hankalin da yazo nema ya samu ba, sai dai rashin zaɓi ko bakin zaren kamawa ya sashi fahimtar tsohon na masa nuni da shiru ne kawai a zubama sarautar ALLAH ido dan shine kawai gagara misali.....
_________________
★Kwanaki biyu kenan da dawowar Iffah gida, inda dawowar tata ta zame mata tamkar wani famin ciwo a jikinta. Dan a kullum takanyi hawaye sama da sau babu adadi akan rashin ƴan uwanta guda biyu. Komai ta kalla nasu yakan dawo mata da jiyansune mai cike da farin ciki da babu tunanin yankewa. Duk halin da take a ciki Ummu da Babiy na hankalce da ita, tausayi take basu matuƙa, wani lokacin Ummu har hawaye takan share itama.
Yau ma tamkar kullum tun bayan dawowarta tai shirin makaranta ta fice badan hankalin su Ummu ya kwanta ba. Kawai dai dan ta dagene akan komawar. Sun bartane ko komawar zaisa ta sake samun nutsuwa da farin cikin da ko'a fuskarta yanzu baka hangosa. Sanye take cikin skirt golden yellow da t-shirt fara da suka kasance Uniform ɗinsu, sai hijjab fari ƙarami shima ta ɗora niƙab ta yanda ƙwayar idanunta kawai ake iya gani. Bayanta goye da school bag. A nutse take tafiya kanta a ƙasa tamkar bata son taka ƙasar har ta iso bakin titi, tsayuwar da batafi ta mintuna uku ba ta samu abin hawa kamar sauran ɗalibai daketa ɓillowa a kowane kusurwa. Makarantarsu babbar makarantace mai ɗauke da ɗalibai masu hazaƙa, domin kuwa an tattarosu ne daga mabanbanta makarantu aka kawo nan saboda hazaƙarsu. Kowa bata kulaba ta shige aji tai zamanta, saɓanin da da kowa yasan Iffah mai tsiwa da surutu, gata ba'a kadata a himma. Kauɗinta yasa mafi yawan malamai saninta ga kuma ƙoƙari. Amma tunda ta dawo yanzu ta canjama kowa, magana ma saita zo har a tashi batai da wani ba. Kamar yanda malaman sukai mata uziri haka ɗaliban ma sukai mata, dan kowa yasan tana cikin yanayin da uzirin kawai tafi buƙata.
Duk wanda ya shigo yakan miƙa mata hannu su gaisa, itama babu musu take miƙawa tare da amsa sallamar da sukai mata. A haka har duk ɗaliban ajin suka kammala shigowa malamin farko ya shigo musu. Da farko ta nutsu wajen fara fahimtar darasin da yake musu, a hankali kuma tunaninta ya fara janyewa zuwa ga abinda taketa faman shiryawa da zuciyarta a kwanakin nan har malamin ya kammala ya fita babu abinda ta ɗauka. Haka na bayansa suka cigaba da shigowa basu darasi daban-daban, wani hankalinta na kai wani harya fita babu abinda zatace ta saurara. Ana tashi tana a ɗalibai sahun farko da suka fara fitowa, jitai kawai tana sha'awar yin tattaki da ƙafafunta yau, dan haka bata tsaya neman abun hawa ba ta miƙo titi da ƙafa ta fara tafiya kamar wasu tsirarun ɗalibai irinta da gidajensu ke kusa da makarantar. Tafiya tayi mai nisa sosai batare da nuna alamun gajiyawa ba, harta kusa isowa roundabout ɗin daya raba hanyar gidansu da ainahin titin hanyar masarauta daular ruman. Daga roundabout ɗin ana iya hango ƙaton tambarin ƙosashen zaki da akayisa da gold na tambarin Masarauta. Iffah taja wani kakkauran tsaki da ɗauke kanta zuciyarta na mata zafi. Harta kusa tsallakawa ta hango wata tsohuwa dake riƙe da wani yaro da Uniform a jikinsa da alama titin take so su tsallaka amma sunata inda-inda. Karan farko murmushi ya suɓuce mata ganin yanda yaron ke jan hanun tsohuwar sai sun tafi kamar zasu tsallaka saita fisgo yaron su dawo baya tana masifa. Sallama tai musu, tsohuwar ta amsa mata. Ta gaisheta da girmamawa tare da faɗin, “Ammi kuna so ku tsalla ne?”.
Amsawa tsohuwar tai da “Eh Ibnati ”.
Iffah ta sake murmusawa daga cikin niƙab ɗinta, kafin takai hannu ta riƙo na tsohuwar dake riƙe da yaron ita kuma. Suna gab da kaiwa tsakkiya yaron ya fisge hanunsa ya koma baya da gudu yana faɗin yabar abunsa a baya. Tsohuwar zata fisge itama tana masifa da kiran yaron ya dawo Iffah ta riƙeta gam suka karasa tsallakawa. “Ammi yi haƙuri barsa naje zan sake tsallako miki da shi. Rufe bakin Iffah yay dai-dai da taka wani bahagon birkin daya bada sautin ƙuuuuuu!!!. Sai sautin fitar ƙara mai razanarwa ta biyo bayansa.
Wani irin zabura Iffah tai na juyowa dan ƙarar har tsakkiyar kanta ta jita. Ai batama san sanda ta yaye niƙab ɗin fuskarta ba da waro manyan ƙyawawan idanunta waje gaba ɗaya ba tana mai ambaton sunan ALLAH ganin yaron nan tsaye cak a tsakkiyar titi hancin wata mota gab da shi allamar kaɗan ya hana ayi ɗanyen aiki. Kusan a tare suka isa kansa ita da tsohuwar data fashe da kuka da ƙwala kiran sunan yaron a matuƙar firgice.
Iffah da jikinta ke ɓari ta riƙo yaron jikinta tana duddubashi da sauke ajiyar zuciya a jajjere, ganin babu ko ƙwarzane a jikin nasa. Saurin sakin yaron tai ga tsohuwar tasha gaban motar ranta a ɓace ganin mai motar ko fitowa baiyiba ya ɗan leƙone kawai, ganin baima yaron komaiba ya maida kansa yanama ƙoƙarin barin wajen. A fusace ta buɗe murfin, ba saurayin daya kasance drivern motar ba hatta wanda ke gefensa hankalinsa akan lap-top dake saman cinyarsa sai da ya ɗago suka zuba mata idanu. Gaba ɗayansu ta haɗa ta dallama harara da manyan idanunta masu matuƙar haske tamkar madara.
“Kai malam baka san darajar mutane bane?....” Zazzaƙar muryarta mai taushi da nutsuwa a cikinta ta daki kunnuwansu cikin faɗa babu ko ɗigon tsoro a tare da ita. Batare data damu da yanda suka zuba mata ido ba ta murguɗa musu bakinta da sake dalla musu harara ta cigaba da masifarta, “Ka kusan bige yaro amma tsabar kanka ba'a daidai yake ba shine koka fito kaga yaya yake ma saboda ku masu kuɗin nan ɗaukar talaka kuke baida banbanci da titin da kuke gurza tayoyin banzayen motocinku da kuka saya da kuɗinmu”.
“Kai!”.
Drivern ya faɗa da maɗaukakin mamaki Iffah.
Harara ta sake dalla masa da zira hannunta ta zare key ɗin motar daya riga ya kashe tun ɓuɗe musu murfin da tayi.
“K! K! Dalla bani key kajimun fitsararriyar yarinya kinga mun taɓashi ne?”.
“Anƙi a bakun, wlhy duk sai kun fito kun dubashi kun bama kakarsa haƙuri zan baku key ɗin nan, inba hakaba sai dai mu kwana anan.”
Hannu saurayin ya kai da nufin warto key ɗin taja baya, sai dai duk da haka saida yaɗan taɓa skirt ɗinta kaɗan. Cikin matsanancin ɓacin rai ta jinjina yatsarta a kan fuskar matashin tamkar zata tsone masa ido. “Idan hanunka ya sake gigin taɓa koda hijjab ɗin jikina ne sai na karyashi, Sannan koda Shahanshan ne yay wannan aikin bai isa barin wajen nan ba balle kai shashasha driver”.
“K!!”.
Na gefensa ya faɗa cikin matuƙar waro idanu. A karan farko wanda ke hakimce zaune a sit ɗin bayansu lap-top a cinyarsa da tarin takardu a gefe da gefensa ya ɗago ƙyawawan idanunsa dake tattare da matsananciyar gajiya da ƙosawa yana yamutsa fuska. Baya ganin yarinyar, sai dai duk abinda take faɗa raɗam a kunensa zazzaƙar muryarta ke sauka. Baiko kalla yaran nasa ba ya sauke Lap-top ɗin dake cinyar tasa tare da kai hannu ya buɗe murfin. A tare suka zabura, sai dai kafin suyi wani yunƙuri harya fita a motar. Dolo suka fito suma da sauri...........✍
Page 5
........Kama hanun yaron da Iffah tai da nufin subar wajen duk da key ɗin motar mutanen har yanzu na'a hanunta yay dai-dai da isowar wani nutsatstsen taku mai tafiya da sassanyan ƙamshin turare tamkar shi kaɗai iska ke tsintowa tana busawa a hancinan mutane. Kamar wani magic wajen yay tsitt na wasu sakkani, tsirarun mutanen da suka taru a wajen tun furuwar abun duk suka zuba masa idanu. Ita kanta hajiya Iffah mai masifar ƙirjintane yay wata irin harbawa lokacin da mutumin ya sauke nasa lulu idanun cikin tsakkiyar nata. Da ƙyar ta iya fisgar su daga cikin nasa tana ɗan murguɗa baki da sauke niƙaf ɗinta cike da dakiya.
Idanun nasa ya janye daga kanta shima da matsawa gaban yaron ya kai tsigunne dai-dai tsayinsa dan ya fara ɗauka yarinyar nan aljanace ma dai kawai. Cikin sassanyar muryarsa mai zurfi da nutsuwa ya motsa lips ɗinsa kaɗan tamkar an fisgo maganar.
“Kana lafiya?”.
Kai yaron ya gyaɗa masa.
Ya ɗan ɗage gira da motsa bakinsa kamar zai taɓe. “Uhhm! minene sunanka?”.
“Amjed”.
Yaron ya faɗa cike da kwarin gwiwa.
A hankali ya sake kaɗa fararen idanunsa tare da jinjina masa👍🏻 ya saki wani sassanyan murmushi a karon farko da jan kumatun yaron. “Oh my Friend! nice name. Kana sona da aboki?”.
Da sauri yaron ya jinjina kai yana washe baki. Idanunsa ya ɗan sake fiddowa suka ƙara girma tare da ƙara sakin murmushi. Ya riƙo hannu yaron alamar suyi musabaha.
Al'amarin ya birge mutane da yawa, duk da babu wanda yasan wanene shi, amma ko makaho ya kalla wannan mutumi yasan babban mutum ne. Suit ɗin dake jikinsa farare tas ma kawai abin kallone. Balle shi a karan kansa daya kasance ƙyaƙyƙyawan gasken fatarsa da gogewarta har ɗaukar idanun mai kallo take. Ga wani ƙamshi na musamman mai saka nutsuwa ga mai shaƙa, yanayin kamewarsa da cikakkiyar isa irin ta manyan mutane ke ƙara kawata kwarjininsa da cikar kamala ga duk mai kallonsa.
A karo na biyu suka sake haɗa ido da Iffah dai-dai ya gama gaida kakar yaron nan da keta faman washe baki da jera masa godiya dan kuɗine dunkulallu sabbi ƙal ya damƙa a hanun Amjed. Harara ta balla masa da janye idanunta da sauri saboda wani abu mai tsananin sanyi taji yana tafiya daga ƙafafunta har saman kanta. Cike da takunsa na nutsuwa da ƙasaita shima ya juya ya bar wajen kai kace akan dole yake taka ƙasar saboda takun zaratan maza masu cikakkiyar isa da lafiya ce tattare da tafiyar tasa. Iffah ta jefama ɗaya daga cikin samarin nan biyu key ɗin motar, dan ɗayan ya tafi da hanzari ya buɗema ogansu ne. Dai-dai zai shiga ta ballama wanda ta jefama key ɗin harara da faɗin, “Daga yau ko daga nesa kuka hangoni to ku canja hanya koda a jirgi kuke kuwa”.
Shigar maganar tata a cikin kunensa dai-dai zai shiga motar da aka buɗe masa ya ɗan ɗago idonsa, sai dai wadda ya ɗago da nufin kallar da mamakinta ke cin ransa tuni ta nufi barin wajen tamkar ba ita ta haɗa dabar wajen ba... Suna ƙoƙarin shan shataletalen titin idanunsa ya sake sauka a kanta ta miƙe titi tana tafiyarta a nutse, sai dai fuskarta a rufe take da niƙab data saki tun bayan haɗa idonsu na farko....
🤔Wannan ƴa ta Babiy wataran sai ta saka an mata dukan sakwara a titi in har bata canja hali ba😬🚴🏼.
★★......★
“Badai a ƙasa kika tahoba auta? Na ganki a gajiye tamkar an koroki”.
Zubewa tai a taburmar da Ummu ke zaune, tare da ɗora kanta a cinyarta tana ƙara narke fuska. “ALLAH a ƙasa na taho Ummu. Haka kawai naji ina son na taho a ƙafan”.
“Ai gashi nan duk kin gajiyar da kanki, dama keba wata isashshiyar lafiya ba. Tashi kiɗan watsa ruwa dan sai warin rana kikeyi”.
“Kai Ummu warin rana fa?”. Tai maganar a shagwaɓe da kamo rigarta ta kai hancinta. Miƙewa tai tana tura baki gaba da faɗin, “ALLAH Ummu kinso dai yarfanine amma ƙamshin ma turare nakeyi”.
Murmushi kawai Ummu tai da girgiza kanta, ita kuma ta shige ɗaki sai faman cika baki take da iska a dole taji haushi.....
★Da daddare suna zaune a tsakar gida cikin hasken farin wata daya raba Hanash na koyama Iffah aikin makaranta. Daga gefensu Ummu da Babiy ne zaune yana cin abinci. Hira suke jefi-jefi akan kayan lambunsa da zai fidda a ƙarshen satin nan ga ƴan kasuwa. Iffah tai karaf jin Babiy yace zuma batayi kirki ba wannan karon bazata wuce tulu biyu ba.
“Babiy sai a bar mana mu shanye kawai a gida. Kaga dama Ummu zatamin alkakin saukar islamiyyarmu nan da wata biyu”.
Murmushi Babiy yayi, “Zanso haka Ibnati, sai dai bazai yuwuba dan dukanta zan kaita masarauta ne”.
Take murmushin fuskar Iffah ya ɗauke baki ɗaya. Kamar zatai magana sai kuma tai shiru ta maida kanta ga aikinta kamar bataji ba. Shima Babiy sai bai sake cewa komai ba akan zumar suka cigaba da maganarsu da Hanash da Ummu dake saka baki jefi-jefi.....
Tun wannan magana babu wanda ya sake tada zancen zumar nan. Babiy da Hanash suka duƙufa tattare kayan lambu da za'a fitar. Yayinda Iffah ta cigaba da zuwa makarantarta a zahiri kamar babu wata damuwa tattare da ita. Sai dai kuma a baɗini tun randa akai maganar kai zuma daular ruman zuciyarta sam bata huta ba. A duk motsinta cikin ƙullawa da kwancewa take game da babban burinta na ɗaukar fansa. Wanda tasan bata da wata hanyar yin hakan sai ta wannan zuma da Babiy ke kaiwa masarauta. Kuma tasha jin cewa Tajwar ne ke shanta kawai.
Har ana saura kwana biyu bata samu wata mafitaba akan ƙudirinta, dan haka tana zuwa makaranta taja wata ƙawarta da kafin yanzu da ta canja suke sabgarsu da rashinji tare gefe. Ikram da taji farin cikin ƙawarta ta fara dawowa yanda take babu musu ta bita suka koma can ƙarƙashin wata bishiya suka zauna.
“Ko kefa Iffah, ALLAH bana jin daɗin yanda kike shareni yanzu sam. Dan ALLAH ki manta da komai mu cigaba da yima su Akia Arfa addu'a”.
“Humm”. kawai Iffah tace da ɗan laɓe fuska. “Kinga ni ba wannan yasa na kiraki ba, tambayarki nake so nayi?”.
“To ALLAH yasa na sani”. Cewar Ikram tana gyara zama.
“Kinma sani, kwanaki bakin bani labarin sister ɗin mamanku tasha zuma taita ciwon ciki ba, kafin aje asibiti har hanjinta ya kakkatse?”.
“Yes anyi haka, bayan kwana huɗu ma ta rasu ai. Sai daga baya aka gane ashe saurayintane ya zuba mata wani magani a ciki. Sai dai har yanzu ma ana shari'an, dan a binciken likitoci sudai sunce basuga komai ba, abokinsa kuma da suka ƙulla tare ne ya tona masa asiri, ya kuma rantse sun zuba ɗin dan tare suka sayo maganin”.
Iffah dake saurarenta tace, “Anya kuwa ba abokin na masa sharri bane?”.
“To mudai bamu san dai-daiba sai ALLAH. Grand mother ɗinmu ma ita tace dan ALLAH abar shari'ar tunda UBANGIJI mafi sani ne. Idan anje garesa shi ya rarrabe ƙarya da gaskiya”.
“Uhm gaskiya kam tayi magana mai ƙyau. To amma ni abinda ya bani mamaki, shiko wannan wane kalar maganine haka da har za'ace likitoci sun kasa ganewa, bayan kuma gashi sunce ya kakkatsa mata hanjinta da kansu.”
“K nifa abinda na fahimta kamar an sayesu ne likitocin, kin sanfa ɗan manyan mutanene yaron. Amma abokin nasa ya faɗi sunan maganin sai dai na manta”.
“Komaima zai iya faruwa indai shegun manyan ƙasar nannne, kansu kawai suka sani azzalumai. Amma ina son nasan sunan maganin dan ina son nai bincike a kansa ma ni wlhy.”
“Kedai kawai wani abun adai rufesa kawai. Uhm kina nan da shegen son bincike-binciken nan naki, anya Iffah idan ALLAH ya cika miki burinki na zama ƴar jarida bazaki addabemuba? Dan na kula har hurumin aikin jami'an tsaro zaki dinga shiga tsabar bin kwaf-kwaf ɗinki”.
“Ƴar sa ido naji, nidai kafin a tashi ki tuno sunan maganin inba hakaba zanta addabarkine”.
Ikram tai dariya tana miƙewa. “Indai wannan ne zanyi ƙoƙari. Maganin ma fa ba wani na kirki bane ba ance ana zubama ƙananun ƙwari ne dakan damu mutane a cikin gida a ruwa haka ko abinci, dan basajin warinsa sam ko ami aka zuba sai kiga sunsha ruwa da shi ko abinci.”
“To kinga koda ba bincikeba ai zai mana amfani, dama mu da muke cikin lambu kullum cikin ganin macizai dama halittu masu cutarwa iri-iri dake iya zama a cikin gida haka.”
“Eh gaskiya kuma hakane, zai ko taimaka muku insha ALLAHU”.
Kafin a tashi kuwa Ikram ta cika alƙawarin samowa Iffah sunan magani. Takoyi farin ciki har haƙwaranta na bayyana wajen murmushi irin wanda ta jima batayiba a rayuwarta. Iya kuɗin motarta ne kawai a jikinta. Dan haka ta gama tsara ƙaryar da zatai ta samu kuɗin sayen maganin idan ta koma gida. Koda ta koma gida tun kafin takai zaune ta sanarma Ummu ai an basu wani Assignment mai wahalar gaske. Gashi bata da littafin dazai taimaka mata tayi har sai ta saya. Ganin yanda tai maganar a serious yasa Ummu yimata murmushin kwantar da hankali.
“Karki damu in har ana saidawa anjima sai Hanash ya fita ya saya miki kema, ko kuma ki bincika a kayan karatun su Arfa ƙila ki samu ai”.
“Ummu basu dashi sam, dan kwanaki ma da malaminmu yay maganarsa sannan suna nan ai. Kinga da suna dashi ai da sun bani”.
“Uhm hakane kuma kam. To ki bari Hanash ɗin ya dawo sai ya dubo miki”.
“Ummu ni kawai ki bani yanzu da nayi wanka sai naje da kaina na dubo. Ƙilama daga nan na ƙara ilimi”.
“Kai Iffah kin cika fitina, kin dai san ba son yawan fitarnan taki muke ba ai”.
“Na sani Ummu, insha ALLAHU babu abinda zai faru addu'arku na biye dani, kuma ina suturce jikina idan zan fita”.
Badan hankalin Ummu ya kwanta ba ta yarda tabar Iffah ta fita. dan ta dage akan gobe ake buƙatar sukai Assignment ɗin, idan tace zata jira sai Hanash ya dawo dare zaiyi tunta sunje babbar kasuwar cinikayyar ƙarshen watane ta daular ruman kai kayan lambu. Kamar kullum tai shirinta tsaf tare da rufe duk jikinta sai idanunta kawai da ake gani. Sosai ash color na abayar jikin nata mai adon duwatsu blue masu sheƙi sukai mata ƙyau duk da ba'a iya ganin fuskarta. Cikin nutsuwarta take takunta tamkar wata tarwaɗa. Dan Iffah tun tana yarinya irin yaran nanne masu shegen iyayi da kauɗi. Tun a shekarun baya mutane kance za'ai kallon ƴammata a wajen nan, dan tafi yayunta son kyale-ƙyale da tsantseni irin na ƴan gayun mata masu ji da kansu. Da ƙafa tazo har titi duk da akwai ɗan tafiya a tsakaninsu. Ta tare abin hawa tare da sanar masa inda zai kaita.
A ƙofar katon kantin da ake saida duk wani nau'in magani daya shafi gona dana kauda mugayen halittu masu cutarwa ga mutane dakan shiga cikin gida ya sauketa. Ta biyashi kuɗinsa sannan ta shige. Kanta tsaye ta miƙa takardar data riga ta rubuta sunan maganin dan karta manta. Aka faɗa mata kuɗin ta biya suka bata. Wani irin farin ciki takeji a ranta, tunin karta koma gida babu littafi ta zama abar tuhuma ya sata cema mai abin hawan data hawo ya kaita babban shagon littatafai. Koda suka isa cewa tai ya jirata yanzu zata fito su wuce. Gargaɗi ya mata akan kuɗintafa ya ƙaru, tace babu damuwa tana shigewa.
Ganin babu yawan mutane a shagon duk da ƙatone sosai ba kuma wajen da za'ai hayaniyar da zaka san adadin mutanen wajen bane yasata ɗage niƙab ɗinta yanda zataga komai da ƙyau. Kowanne littatafai da sashensu a rubuce kuma yanda bazakasha wahalar nema ba, maimakon ta nufi inda zataga irin nata kai tsaye saita fara zagaye. Sai da ta gama kewaye-kewayenta tamkar ta manta da wanda ta ajiye a waje kafin ta tsaida hankalinta ga inda zataga littafin daya dace ta ɗauka. Surutun yara takeji kaɗan-kaɗan ta bayan inda take, ta ɗan dudduba taga babu ta inda zata leƙasu sai ta haƙura cikin taɓe baki takai hannu kan wani littafi zata ɗauka. Daga can ɓangaren ma dai-dai an kai hannu akan littafin za'a ɗauka dan duk kanta ɗaya ce, littatafan ne kawai suka rufe wanda ke can baya ganin na nan. Iffah taja, daga can ma aka ja, jin za'a fisge saboda an fita ƙarfi dama tsaho dan ita harda su ɗiɗɗishe saita fisga itama a ɗan fusace saboda gani take wani keson raina mata hankali. Ta cikin ɗan space ɗin data cire littafin ita da shi suka zubama juna idanu, haka kawai taji tsigar jikinta ta tashi duk da ita bama wani ganesa tai da ƙyau ba saboda space ɗin bawai ya buɗe da ƙyau bane. Kamilalliyar fuskarsa da dama babu wani walwala a cikinta ya ƙara tsukewa dan shiko sarai ya ganeta...........✍
★ Shin wanene wai wannan dake neman zamema Iffah ɗan kaɗafi?.
★To wai mima zatayi da maganin data saya ne?.
★ Ko Iffah zataci nasarar cika ƙudirinta?.
★Idan taci nasarar minene zai biyo baya?.
★Mike kashe matan Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed ne?.
★Shi kansa Tajwar Eshaan ɗin wanene shi?.
★Yaya yake? Taya zamu san ainahinsa?.
*_Duka amsoshin nan na'a cikin gundarin labarin littafin DAUƊAR GORA. Masu iya magana kance (CIKI KA SHATA). To waima miye ma'anar kalmar Dauɗar gora ciki ka shatan ne?🤗. Kumuje zuwa kudai, karku bari a baku labari masoya🤸🏼, dan cakwakiya iya cakwakiya. Kundai san minene gidan sarauta, balle irin wannan na DAULAR RUMAN da Tajwar ɗinta ke amsa suna Shahan-shan. Ma'ana (King of Kings🤴🏻). Bafa cakwakiyar kawai bace, akwai tsumammiyar soyayya mai fasa zuciya😋._*
Dawa?.
A ina?.
Taya?.
_Duk amsar na cikin *DAUƊAR GORA CIKI KA SHATA🤗* dake a ɗaya daga cikin littatafai biyar na *ZAFAFANKU* abin alfaharinku. Kundai sansu kun san aikinsu babu wasa babu jan rai a cikinsa balle shiririta. Zamu gamsar da ku da salon labaranmu a wannan karon fiye dana baya insha ALLAHU. Kudai kawai ku kasance da zafafan naku biyar zakuce nina faɗa muku😋😁._
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA
+22799643131
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
Visit > https://www.novelselite.com.ng/
Facebook: Novels Elite
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.