*🌈TSINTACCIYA🌈*
NIMCYLUV
_FITATTU HUƊU 🔥_
_1.Meke Coursing Masturbation??_
_2.illar Masturbation??_
_3.Let's talk about NOMA, Amfaninta ga matasa!!!!!_
_4.Sharrin Aljanu, da hanyar da suke shiga jikin mutum_
_A kakkaɓe zani jama'a💃🏽 ki tabbatar kin kammala girki before you start reading my book....... Ready goooo!!!_
EPISODE1️⃣
http://wa.me/+2348119237616
Safiyar garin Lahadin yau ta kasance safiya mai ɗumbin tarihi ga dukkan jama'ar da suke yankin Kano kuma a sassa daban daban, Dalilin Kwantaccen baƙin hadarin dake garin, kasantuwar yanayin damu na da muke ciki, kuma farkon watan Agusta.
A hankali sassanyar iskar hadarin take Kaɗawa yayinda kuma dukkan baƙin hadarin yaywa samaniya tsinke, cikin nutsuwa baƙin hadarin ke joyewa zuwa jaa, alamar ko wanne lokaci ruwa na iya sauka.
Wata ƙaƙƙarfar iska ce mai tafiya da rufin gidaje ta fara fatali da dukkan wasu abubuwa marasa nauyi, ƙarfin isakar da rugugin hadarin ya wuce tunanin dukkan mai tunani da dukkan alama yau ruwan na musamman ne.
A hankali kuma gajimaren ke gudu yana haɗa jikinsa waje guda, cikin lokaci kaɗan samaniya tai wani irin jaa wanda ya wuce tunani mutane, ga wata ƙara da rugugi da hadarin yake, wanda ya haddasa tashin tsuntsayen daga saman bishiyoyi zuwa ma ɓoya.
Ƙarfin gudun isakar da kuma yadda take fatali da dukkan wani abu dake kan hanya, ya sanya dabbobi fara gudu suna kuka, yayinda abeben hawa suka shiga tsayawa a saman shimfiɗaɗɗan titin Sabon Garin!
"Shuuuu" haka sautin saukar ruwan saman ya bada Amo! Amon daya tsorata dukkan mutanan da suke waje, domin tunda aka fara damuna today is the first day! Da akai ruwa mai tsananin yawa wanda yake sauka da wata iska mai yaye dukkan rufin gidajen da basu da Kwari, saukar ruwan saman yay worse da yaywa al'amarin da yay Coursing wani irin hatsari mai munin gaske.
Saukar ruwan saman bai hanata ko da motsi ba, bare tayi Attempting na gudu zuwa wani wajan domin tsira da lafiyarta.
Tana zaune a saman wata kan bolar kasuwar Sabon gari, the way she's acting zaka san cewa akwai wani abu da yake tattare da ita.
Farar macace mai matsakaicin jiki, ƙyakƙyawa ce sosai saukar long dark hair ɗinta zuwa gadon bayanta zai tabbatar maka cewa ita ɗin ruwa biyu ce wato _(Half-caste)_.
Dukkan sassan jikinta rawa yake yana wani irin ɓari, na tsananin dukan ruwan saman, a dai-dai lokacin da kuma saukar ruwan saman ya juye zuwa saukar ƙanƙara yasa tai wani irin firgita tare da ɗago kanta sama.
”Yasubuhanallah!” hasken fuskarta shi kaɗai zai tabbatar maka cewa wannan ko a mahaukatan ita sabon kamo ce, idanunta sunyi jajirrr Jikinta na wani irin ɓari ta tashi tsaye _”Ya hayyu ya ƙayyum”_ ashe tsirara take babu komai jikinta sai dugun gashin daya rufe asalin kayan fuskarta.
Idanunta ta ɗaga sama kamar mai tunani a hankali kuma bakinta ke motsawa yadda babu mai iya jin abinda take faɗa.
Cikin nutsuwa kuma sautin maganar ke fitowa fili tana faɗin.
_“Allahumma Innakaa, Afuuwun! Tuhibbun Afu-afuu Anniii”_
Sune kaɗai kalaman dake fita a bakinta, wanda Ubangiji ne kaɗai ya sahale mata faɗar su, da kuma ƙarfin Imanin da Zuciyarta ke dashi, amma banda haka yaya cikakkiyar Mahaukaciya mai yawo tsirara wacce ta maida kan Bola wajan kwananta, ruwan kwanta ya zama abin kashe ƙishinta, yayinda abubuwan kan Bolan suka zama abincin sawa a cikinta zata iya wannan salati¿ _ONLY GOD KNOWS_.
A dai-dai lokacin ne kuma wata haɗaɗɗiyar mota Rolls-Royce Phantom mai tintak tai parking a wajan, cikin nutsuwa kuma aka buɗe Murfin motar aka fita, wani Babban mutum kuma attajiri ne ya fito yana gyara zaman laimar dake hannunsa.
Idanunsa ya juya tare da sauke ganinsa akanta, wani irin lumshe idanunsa yay yana siɗe laɓɓansa da harshe kamar tsuhun maye.
Cikin wata fitinannan Murya wacce buƙatar kasancewa da mahaukaciyar ya gama narkar da ita, ji yake J ɗinsa na wani irin fisga saboda ganinta da yay naked a gabansa.
Frm head to toe yake binta da kallo!
Cikin zaucewa ya ƙara ji J ɗinsa ta fara fisga to Yarinyar tai bala'in haɗuwa.
A zuciyarsa yake faɗin.
"Young innocent pretty gril aka haukata haka? She's different kyanta daban, komanta daban, that's illiteracy ji ɓeta kamar ƴar sarauta, so pretty my Lord! Yasubuhanallah, masu haukata Yarinyar nan sumbin gata, na samu full chances zaɓe zai zo min a dai-dai, kalleta her body is so soft ga idanu ka manyan kaya, look at her. Snatch waist wallahi zama ƊAN MAJALISA _(Members federal house of Representatives)_ Dole!”
Ya ƙare zan can zucin yana wani sauke ajjiyar zuciya da shafa ƙirji.
Motsin da taji a bayanta ya sanya ta juya da sauri ganin mutum dake can nesa da ita yasa ta razana sosai.
Tsoro, firgici ya haɗe mata waje guda, Ada kafin shigowar sa cikin rayuwarta _DAMUWA_ ce, amma shigowar sa cikin rayuwarta a yanzu ya zama _ƘALUBALE!_
Kai ta shiga girgiza masa ta nayi baya, jikinta na kyarma da ɓari amma hakan bai hana shi ƙara kusantu ta ba, yana zuwa yasa hannu ya fisgota zuwa wajan motar, yayinda shima jikin nasa ya ɗauki rawa saboda wata kalar tsawa da akai.
Kokawar kwace kanta ta shigayi, hakan yasa shima ya fara tayata kokawar it was like he is enjoying.
Tana gab da ƙwace kanta ya wani dannata cikin motar tare da sanyawa motar lock yana shiga yaja motar da wani irin speed yabar kam bolar.
http://wa.me
/+2348119237616
*_Domin magana da marubuciyar kai tsaye danna nan_*
*BAYAN SHEKARU 17*
WUDIL/KANO STATE
_Darki Lajawa Area_
Fitowa yay daga cikin ƙaramin ɗakin da yake ciki, hannunsu riƙe da Magirbi daya saƙala a wuyansa, Dattijo ne mai matsakaicin jiki, yana da kamala sosai.
Cikin sauri ya rufe ɗakin saboda gaba ɗaya hankalinsa yay kan gonarsa.
Yana ƙoƙarin fita yaji matarsa na faɗin.
"Innalillahi, Malam!Malam! Malam kana ina ne"
Da sauri wanda aka kira da Malam ya tsaya daga tafiyar da yake, gabansa na faɗuwa domin daga yadda ake kiransa kasan bana lafiya bane.
Kallon Matar tasa yay yace "Ya..Ya Rabi wannan kiran hak ince dai komai lafiya ne?" Girgiza masa kai tayi tace "Malam inafa lafiya" gabansa ne ya sake faɗuwa kafin yace "Assha,Meke faruwa to, kinga sauri nake zani gona, kuma yau muna da baƙi a garin namu zasu taimaka mana akan Noman mu"
Numfasawa tayi tace.
"Malam ban ganta ba, tun dana farka ko karin kumallo banyi saboda fargaba yanzu ma gajiya nayi da zullumi nace bari na faɗa maka"
Da sauri Malam yace "Kamarya? Babu yarinya kuma kikai shiru kamar baki san ciwon Yarinyar nan ba? Kamar bake kika haifa ba?"
Girgiza kai tayi tace "wallahi Malam na ɗauka taje makara...."
Da sauri ya tare ta hanyar faɗin "Wacce makaranta Rabi? Bayan satin daya shige ta gama zana jarabawar shiga aji huɗu na sakandare? Wallahi duk abinda ya samu Yarinyar nan ki kuka da kanki, ba zan lamunci wannan shirman a gidana ba, idan baki son riƙe ta saboda da lalurar da take da ita ina da inda zan kaita ta zauna har abada ko mai kamannin ta baki gani"
Yana faɗin hakan yay cilli da Magirbin tare da yin waje.
Shiru Baba Rabi tayi cike da zullumin halin da Yarinyar zata kasance.
Tunda ya fita ko mai kama da ita bai gani ba, babu ma yara sam a unguwar dalilin ruwan da aka shimfiɗa a daran jiya, ko'ina na unguwar ya cika da ruwa, ko shi ya shiga wannan ruwan sai yay jinya amma ina yarinyarsa taje a wannan lokacin?
Abu kamar wasa har ya fara shige tunanin Malam, al'amarin daya ƙara tayar masa da hankali kenan, yarinya ɗaya tilo da yake da ita wani ƙaramin kuskure yana neman yi masa nesa da ita.
Yama manta da batun gona da kuma baƙin daza suyi a garin, tafiya yake sosai harya ƙarasa wajan wani tafkeken ruwa _(Wudil river)_
Kana kallon ruwan nan kasa duk wanda ya shiga ko kuma ya faɗa, ya faɗa kenan sai dai wani bashi ba, ruwan yay wani sama dan ma wai a hakan ya tafiya.
Baka ganin komai sai haske da hayaƙin ruwan har wani ambaliya yake ya cika yay tafff.
Tana tsaye a gaban ƙaton ruwan, kanta a ƙasa Idanunta a rufe, yarinya ce ko kuma nace matashiyar budurwa, ƴar kimanin shekaru 17 a duniya, baka iya tantance yanayin dirin jikinta saboda babban hijab ɗin dake jikinta.
Fararan hannunta da kuma yatsun hannunta da take motsa su ne zai tabbatar maka da cewa farar macace irin farin nan mai mugun kyau, da ɗaukar hankali.
Kanta yay tudu sosai kamar wacce tai acuci, fafaran ƙafafuwanta ko takalmi babu.
A hankali ta ɗaga kanta tare da buɗe idanunta wanda eyes lashes suka kwanta luff a saman fatar idanun, hannunta ta sanya tare da kama gefen hijab ɗinta ta ƙanƙame Jikinta waje guda.
Dadai ace ta auri wanda bata so, Tabbas gwamma kowa ya rasata, rayuwarta bata da amfani a yanzu damuwa tai mata yawa.
Mene Amfaninta ne a yanzu? Ada rayuwar ta tambaya ce? Amma rayuwarta a yanzu ta zama Amsa, duk da irin wannan abun bai hana duniya tai mata wani irin kallo ba, mene yasa duniya ke son yin juyin wainar fulawa da ita ne?
A hankali ta share hawayen dake silaluwa daga cikin idanunta zuwa saman fuskarta, cikin siririyar muryarta mai raunin gaske tace.
"Am so sorry Baba, na kasa maka biyayya, I'm a bad girl ni ba ƴar ƙwarai bace, na ɗauka zan jure na ɗauka i can handle everything anything da zai farcing rayuwana, amma na kasa, Am sorry Ba..ba!!! Am sorry!"
Ƙafa ta ɗaga zata faɗa cikin ruwan taji ana faɗin.
"AKEELA! AKEELA!! AKEELA!!"
da wani irin sauri ta juya ganin Babanta a bayanta can nesa yana zuwa wajan, kai ta shiga girgiza masa ta kasa cewa komai.
Hijab ɗin jikinta ta tattare zuwa saman tana jan numfashi, Malam kuwa Murya ya buɗe ya shiga faɗin.
"Akeela ki tsaya bazan aura maki kuwa ba, Akeela Ruwa..."
Bai gama faɗin abinda yay niyya ba saboda wani irin bugawa da ƙirjinsa da yay ji kake "Tsundumm" ta faɗa cikin ƙaton kogin.
Wani irin suman tsaye Malam yay, komansa ya tsaya na wani lokaci, tashin hankali da makomarsa ya cika masa zuciya.
Da gudu har takalmansa na faɗuwa yay bakin Kogin duk da yadda idanunsa suke dishi dishi saboda ƙaran cin gani da yake da shi bai hana shi ganin wajan da Akeela ta faɗa ba, yana wani fidda ƙwayaye alamar numfashinta na fida saboda shigar ruwan cikin hanci da bakin ta.
Da gudu Malam ya kwasa zuwa bakin hanya yana faɗin.
"Jama'a ku taimakamin yarinta ta faɗa kogi, wai babu mutane a garin ne, jama'a!!!!"
Hannunsa ya ɗura akai har wani jiri ke ɗiban sa, babu mutum ko ɗaya a hanyar.
Sama da mintina 10 kafin Allah ya kawo wasu mutane wajan su biyar kana ganinsu kaga Manoma, da sauri Malam yasha gabansu yace.
"Bayin Allah ku taimaki ran baiwar Allah, yarinya ta na cikin ruwa, ko taimaka min kada ta mutu da haƙƙi na"
Kallon juna sukai kafin kuma gaba ɗaya suka bi bayansa saboda hannun wani da yaja.
Suna zuwa wani mai suna Isiya yace.
"Tab, ai wallahi idan kaga tayi rai sai ikon Allah"
Wani mai suna Sunusi yace "Wanne batun rai? Ai Isiya wannan Yarinyar Shikenan ta riga mu gidan gaskiya"
Wannan Maganar tasa Malam sakin kuka yana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, dan Allah ku daina faɗin haka wallahi yarinta tana raye bata mutu ba, gobe bikinta Tayaya ne za kace tamutu"
Isiya ne yace "To wallahi dai ku ruwa bai kashe ta ba, kifi ya cinye ta ko kada tab wannan maliyan ruwan ko ƙarshe bai dashi"
Jafar ne yace "To wama zai shiga wannan ruwan? Kasan bamu da wasu ƴan kwana kwana a wannan unguwar kafin su zoma komai ya faru" Sunusi ne ya ƙara leƙawa ruwan yace.
"Allah dai ya jiƙan musulmi, amma wannan Yarinyar tayi shahada mutuwar ruwa baiwar Allah kenan"
Da gudu Malam ya kwasa ya ƙara nufar kan hanya domin zuciyarsa ba zata jure jin wannan mugwayen alkaba'in akan Yarinyar kirki irin AKEELA ba.
Yana zuwa kan hanyar dai-dai lokacin da wasu haɗaɗɗun motoci suka danno kai cikin garin Wudil a kuma dai-dai Wudil river.
Motar farko wacce ta kasance Bugatti Veyron dark blue ce ta wuce da wani mugun sauri.
Kafin ɗaya motar mai ƙirar Lamborghini Aventador blue black ta marawa motar gaban baya.
Yana zaune a bayan motar idanunsa a rufe sanye yake cikin Modern fit suit nevy blue.
Sai wani Monk strap na shoe daya sanya, ya ɗaura Rolex Oyster Perpetual a hannunsa, ƙyakƙyawa ne amma baƙi, his Elegant black skin sai ƙyalli yake,
Babu wani abu mai haske jikinsa sai laɓɓansa da kuma idanunsa, he's dark-skinned yet handsome guy.
Wasu irin idanuwa ne dashi masu sparkling cikin idanun duk mai kallonsa.
A hankali ya buɗe idanunsa jin driver na faɗin "Subuhanallah" idanunsa ya gama buɗewa sosai ba tare daya kalli Driven yace.
"What happened with the car?"
Cikin girmamawa yace "Ƙaramin Mai gida wani bawan Allah yasha gaban mu Allah yasa ban taka shi ba"
Yana latsa Wayarsa yace "Ok! Check him muga"
Fita yay yana fita Malam ya miƙe yana riƙe ƙafa yace.
"Yarinya ta dan Allah ka taimakamin ita kaɗai nake da ita"
Da mamaki Driven yace "Bawan Allah lafiya, baka san hatsarin mota bane zaka sha gabanmu haka"
Cikin kuka Malam ya bashi labari tare da faɗin
"Dan Allah ka taimakamin tayi wajan mintina ashirin da faɗawa"
Baya Driven yay tare da faɗin "Bari na faɗawa Karamin Mai gida"
Yana faɗin ya nufi wajan motar back seat tare dayin knocking.
Idanu BARR ADNAN (MD) ya ɗaga kafin ya buɗe glass ɗin motar ganin Driven sa yace.
"Is everything okay?"
Ajjiyar zuciya Driver yay yace "Wai Yarinyar sa ta faɗa wannan kogin na Wudil gashi babu kuwa kusa, shine yake neman taimako"
Kallonsa kawai Md yay kafin yace "Is she a kid?" "Wallahi dai ban sani ba, amma hankalinsa a tashe yake"
Malam dake can gefe yay saurin ƙarasu wa wajan yace.
"Dan Allah ku taimaka"
Da sauri Md ya ɗaga idanunsa domin idan ba gizo muryar take masa sai yaji kamar muryar Baffansa.
Da mamaki Malam yace "A'a Adnanu kai ne? Maza fito maza kaji"
Buɗe ƙofa Md yay ya fito fuskarsa ɗauke da Murmushi yace.
"Baffa wacce ta faɗa ruwa kamar haka?"
Girgiza kai kawai Baffa yay yace "a fara taimakon rai sai ai magana da baya"
Gaba Baffa yay Adnan Md na biye da shi of course ya iya ruwa amma wannan ruwan ya wuce tunaninsa, gashi dai bai shirya mutuwa ba, Amma yay zai ne? da P.a yana kusa da sauƙi ma.
Zare jacket ɗin sa yay tare da cire necktie ɗinsa, yana tattare hannun rigarsa yace "Baffa babu alamun mutum fa a wannan ruwan"
Zuciyar Malam ya buga da ƙarfi kafin yace "Wallahi tana nan ta faɗa ka jarraba"
Zare takalmin ƙafarsa yay yace "I'll try my own best, firstly clam down kaji"
Gyara tsaiwa Md Adnan yay yana runtse idanunsa tsoro duk ya cikasa domin girman ruwan bana wasa bane da wani irin ƙarfi yay tsalle tare da faɗawa cikin Kogin....
*🌈TSINTACCIYA🌈*
NIMCYLUV
_FITATTU HUƊU🔥_
EPISODE2️⃣
http://wa.me/+2348119237616
“Tsundum” sautin Amon faɗawarsa cikin kogin ya bada, kafin kuma wasu manyan ƙwayaye su fara firfitowa alamar wanda ya shiga cikin ruwan yana fidda numfashi.
Malam ne ya sauke Ajjiyar zuciya tsoro duk ya cika masa zuciya, Musamman like Md Adnan did! Yay Wani good jum before he fall in to the river.
Cikin damuwa Malam ya kalli Drive yace "Yadai iya ruwan sosai ko? Nasan Adnanu gwamma shi da ɗan uwansa, bana son rasa rai biyu a lokaci guda, Akeela nada matuƙar muhimmaci a rayuwata haka Adnanu"
Shiru Driver yay domin like serious bai san komai ba amma dai yasan Adnan na yawan shiga wani ruwa.
Isiya ne yace "Uhm yadai iya ruwan ko?" Kallonsu driver yay kafin yace.
"Not sure! Amma Ƙaramin Mai gida yana shiga swwiming pool sosai yana son wasan ruwa, ta takalmin taya, amma dai ruwa kamar wannan bana da tabbacin yana shigarsa"
Malam ya kalli ruwan yace.
"Allah ka taimaka ni, ka duba lamarin wannan yaran"
Juyawa Driver yay yace "bari na kira taimakon kwanakwana incase"
Wajan motar ya nufa ya ɗauki Wayarsa tare da fara shiga goggle yana duba yadda zai samu impormation na ma'aikatan mafi kusa da garin.
Md Adnan wani numfashi yaja mai wahala yana jin yadda numfashin nasa ke wata fisga kamar zai bari ƙirjinsa.
A hankali kuma ya ɗaga hannunsa zuwa sama kafin ya ware legs ɗinsa, idanunsa dake a rufe ya buɗe yana kumbura bakinsa tare da fidda numfashi.
Girman ruwan da yadda yaga ruwa yay bala'in firgitar sa.
Cikin sauri kuma yay baya da hannunsu yana ware ƙafa tare da fara nutsu cikin ruwan yana ninƙaya, ya ɗauki good 10minutes yana duban Akeela amma babu ita, yana ƙoƙarin juyawa idanunsa ya sauka akan ta tana jin wani reshe na baƙin ruwan daya riƙe mata riƙa.
Hijab ɗin jikinta tuni ya zame yay gaba, gudun ya ƙara yana cimma ta yana gab da zuwa inda take wata igiyar ruwa ta riƙesa cikin kuma rashin Sa'a Wani irin ruwa mai yawan gaske ya tawo cure guda.
Wani kalan ware idanu Md Adnan yay kafin yay wani yunƙuri na guduwa ruwan yay gaba dashi ji kake "Shuuuuuu" sautin gudan ruwan ya bayar.
Dawo Driven yay yana faɗin "na kira, in sha Allah dukkan su noting will happen to them" Cikin damuwa Malam yace "Amma ko motsi babu, ji yadda ruwa ke gudu tsoro ya kamani sosai" "aifa da tsoro mutane har biyu ga wannan bawan Allan da gani bai saba da wahala ba" cewar Sunusi yana mai ƙara leƙawa cikin kogin.
A can cikin motar Md Adnan Wayarsa ce take ta ringing kira na wajan uku kenan amma babu respond! A hankali motar da fara shigewa wani matashi ya fara knocking Ƙofar motar hannunsa riƙe da wayarsa yana ƙara danna number Md Adnan yana mamakin abinda ya tsayar da shi har yanzu bai ƙarasu ba gashi lokaci na tafiya.
Daga cikin motar wani mutum ne mai kimanin shekaru 32 a duniya, yana zaune a back seat idanunsa maƙale da wani farin glass na haɗaɗɗun goyon nan.
Sanye yake da wata fitinanniyar Double breasted suit dark Maroon. Gashin kan nan nashi yay kwance har wuya daga gaba ya kwanto, sai ƙyalli yake yasha Ginger Geminal Oil hair.
Kakkauran laɓɓansa pink irin yirr ɗin nan lokacin zuwa lokacin yana taune su like his punishing kansa, fari ne tass irin farin nan da kai tsaye ba zaka iya tantance na wani ƙasa ko kuma jinsi ba, yana da kyau sosai looking soo damn sexcy and hot!
Irin manyan mutanan ne masu tashe da zamani irin definition of classic masu fama da mahaukacin kuɗi na halak.
Idanunsa ya janye daga kan haɗaɗɗiyar ƙaramar Apple system ɗinsa yana maida idanunsa Submariner Rolex ganin lokacin yaja ya ɗan saki siririn tsaki.
Deep down kuma zuciyarsa na wani irin bugawa da ƙarfi, like something bad gonna happen to him.
Irin mutanan ne da wahala ka fahimci sauyin fuskarsa, farin ciki da damuwa baya sanyawa kaga sauyi a saman fuskarsa.
Yana da kamilalliyar fuska mai cike da ilhama da kuma tarin nutsuwa abu guda ke sauya masa tunani yaji ana masa ihu a saman kansa, ko kuma yaga anci zarafin wani ɗan Adam.
Zame system ɗin yay tare da ajjiye ta a gefensa, cikin nutsuwa ya fara juyawa laɓɓansa yana motsawa a hankali.
A taushashe sautin fitar amon muryarsa ke tashi yana faɗin.
_“Asstagafirullah, Walahamdulillah, Wallahu Akbar”_ shine Amon kalaman dake fita a bakinsa.
A karo na wajan huɗu P.a dake tsaye daga baƙin ƙofar ya ƙara Knocking ƙofar, taɓe baki yay kafin ya ɗaga hannunsa tare da danna glass ɗin motar yay ƙasa.
P.a ne ya kalli mutumin cikin motar yace.
"5times ina kiran number Md amma no answer"
A karo na farko bayan sauke glass motar Dr. ABDUL-HAKEEM BUKAR BELLO ya ɗaga idanunsa tare da kallon P.a idanunsa kawai ya juya da sauri P.a yace.
"Ok lemme try it"
Ya faɗa yana ƙara danna number Md Adnan, kafin kuma gently ya miƙa hannunsa ya buɗe murfin motar, kamar bai so haka Dr A.b ya fito da ƙafarsa kafin kuma ya fito daga motar baki.
Lumshe idanunsa yay saboda iskar ƙasa da ƙamshin sabbin shukokin da akai da suke dukan hancinsa.
Yana da tsayi da faɗi jikinsa a murɗe yake ga wani faɗin ƙirji da yake dashi _(Physique chest)_ bayyanar ƙwayar idanunsa a yanzu ya tabbatar cewa shi ɗin _(Half-caste)_ ruwa biyu kenan.
Zare jacket ɗin yay ya saƙala a hannunsa yana mai sassauta necktie ɗin wuyansa.
"Sir har yanzu ga, gashi mun tara mutane sun taro mu kawai suke jira"
Taɓe baki yay walking slowly ya nufi wani ma dai-dai cin waje da aka gyara yay ta tass ga kujerar da aka sanya masa.
Maida wayar P.a yay zuwa aljihunsa yana mai mamakin abinda ya hana Md Adnan ɗaga wayar da kuma mamakin rashin ƙarasuwar sa is anything okay Babu damuwa ai rashin sanin dalilin shine damuwar.
Waje Dr A.b ya samu wanda wasu jama'ar suke kiransa da AKEEM ya zauna yana mai sassauta haɗewar fuskarsa saboda ganin duk manya ne a wajan wanda shekarunsu, suka ja ainun.
Cikin mutunci ya buɗe bakinsa a nutsu yace "Assalamu alaikum warahamatullah"
Gaba ɗaya mutanan suka amsa masa kafin yay Shiru yin shirun nasa ne kuma yasa P.a dake gefensa a tsaye yace.
Al'amarin ya girmi tunanin su Malam tashin hankali sosai ya bayyana akan fuskarsa yasan yadda ƙaninsa Bukar Bello ke bala'in son yaran nasa fiye da komai na rayuwarsa, yanayin komai saboda dasu ya hakan salwantar da nasa farin cikin just to see them happy, yaya zai kasance idan wani abu ya faru da Md Adnan? Wannan dalilin yasa baya barin su ko'ina sai companies ɗinsu da gida ko kuma ƙasar waje, he cares about his children yana mutuwan son su, ko zazzaɓin su baya jurewa musamman Mai sunan kawonsu.
Driven Md Adnan ne yace "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yanzu mene zance da Babban mai gida eh? Dan Allah? Yau warning ɗina akan na kula da driving ɗin Md Adnan ya kula dashi amma gashi shine ma yace ya shiga ruwan ƙilan dai yama kashe sa idan yaji labarin haka, domin yasan baƙar zuciyarsa.
Malam ne yace "Ubangijin sammai da ƙassai ya kawo mana ɗauki, Wannan wanne irin tashin hankali ne eh?"
Ya faɗa hawaye na zubu masa.
Kafin kace wani abu tuni mutane sun taro wajan yara da manya, a dai-dai lokacin ne kuma motar kwanakwana ta ƙarasu suna zuwa suka fara aikin su nan da nan suka shiga cikin ruwan, sama da mintuna talatin babu Md Adnan babu Akeela.
Tuni Driver ya fara kuka yana faɗin "shikenan wallahi na shiga uku wajan Babban mai gida, eh ina laifin ƴar kazar da nake ci na kwana katifa mai taushi ha banɗaki kamar ma kwanci, suttura kala-kala, eh? Duk banga haka ba ga ɗan ilimi dana samu na kan iya jin turanci ko yaya ne amma yanzu na tura masu ɗa cikin ruwa i can't forgive myself if anything happens to Ƙaramin Mai gida"
Wayarsa dake ƙara ya duba ganin sunan Alhaji yasa ya ɗaga jiki na rawa yace.
"Yallaɓai" gyara zama Alhaji Bukar Bello yay saman kujera hannunsa ɗauke da Mug yana shan coffee, yana sanye cikin Arabian Jallabiya mai taushi da laushi a ƙalla zai kai shekaru 63 amma jikinsa sam bai nuna ba, kyawunsa na samartaka na nan.
Cikin ɗan sakin fuska yace "Bala" da sauri Driven yace "Na'am Yay.. Yallaɓai" ya ƙare maganar muryarsa na rawa, gaban Abbu ne ya faɗi haka kawai yaji zuciyarsa na tsinkewa cikin ƙasa da murya yace.
"Bala where is my friends?" Shiru Bala driver yay yana zare idanu jin haka yasa Abbu miƙewa tsaye tare da goya hannunsa a baya a kaushashe Muryar nan babu wasa yace "Bala yarana" jin haka yasa Bala fashewa da kuka yace.
"Tsautsayi da kauɗin harshe, Allah na tuba ka yafan...," Da sauri Abbu ya katse sa da faɗin "heeyyy Bala this is the last time da zan tambaye ke where is my friends? Ina cute two kids ɗina? Suna ina Eh Bala?"
Haɗiye kukan Bala yay kafin yace.
"Yallaɓai Ƙaramin Mai gida ne ya shiga ruwa kuma..." Gaba ɗaya ya faɗa masa abinda ke faruwa. Tun kafin ya gama jikin Abbu ya hau rawa idanunsa suka Kaɗa ganin yana ƙoƙarin faɗuwa yasa da sauri matarsa mai suna Hajiya Ayusher suna ce mata Ummi tayi saurin miƙewa yana ganin ta ya faɗa jikinta ya rungome ta sosai jikinsa na wani irin rawa bakinsa na ɓari yace "My Adnan My Friends ya rana Ayushertu" ya faɗa yana ƙara matseta a jikinsa.
Jikin Bala Driver na rawa hannunsa wanda yake riƙe da wayar ya riƙe sosai yana faɗin "kai,kai! Ka tsaya mana wallahi yallaɓai bani da laifi idan ka kuran ina zan dinga cin shinkafa? Ina zan dinga cin naman nan naku mai daɗi da romo? Innalillahi wayyooo Ni Bala na shige su"
Shiru yaji babu maganar Abbu sai Ummi dake faɗin "Subuhanallah, Abbu Meke faruwa da yaran namu? Didi! Didi! Mami" ta shiga kiran sunan mutane.
Da sauri Bala ya koma wajan kogin har yanzu babu wani labari, ɗaya daga cikin ma'aikatan ne ya fito jikinsa duk ya jiƙe da ruwa.
Da sauri Malam yau wajansa yana faɗin "Yaya! Wa aka fara cirowa" girgiza ma'aikacin yay yana sharce ruwan fuskarsa yace "till now babu wanda muka gani, ruwa ne yake da ambaliya daga ƙasa, Amma we're still searching in sha Allah za'a same su"
Shiru kawai Malam yay tare da neman waje ya zauna yana ta sauke ajjiyar zuciya.
A hankali p.a ɗin ya kalli mutanan wajan yace "Kamar yadda kuka sani, kai ya waye lokaci yazo wanda ba sai munce dole sai gwamnati ta taimaka mana Sannan za muyi wani abun ba, ko zamu jira gwamnati at least we have to..." Gyaran Murya Akeem yay da sauri P.a yace "Yes sir" kallonsu yay yace "kuyi hqr bakina yana juye zuwa wani harshe daban, yana da kyau mu fahimci cewa idan muka ce sai mun jira gwamnati Tabbas zamu mutu babu mallaki komai na rayuwa ba, idan nace komai ina nufin, Ilimi both buko da Arabic, ƴan ci, ƴanci na nufin ka samawa kanka abinda babu wanda zai wulaƙanta ka, babu wanda zai kanka yace dan Meye ne kai Wannan? Ka zama komai kai updating kanka daga old version zuwa latest version something new haka" shiru yay yana kallon yadda Akeem ya yatsuna fuska kafin ya ɗura da faɗin "mun samu saƙon ku daga office ɗin mu dake AKEEM BETTER FARMING INSTITUDE A.B.I na samu sanarwar daga wajan H.o.d Ni kuma na faɗawa Md Adnan, Md ya faɗawa C.E.O na wannan makaranta zance maku ne ko ma'aikata? Bama duba messages ɗin da bana e-mail bane, amma muhimmacin garin da kuma albarkatun noma da muke dashi a wannan garin me albarka Sir Akeem kuma Dr Abdul-hakeem Bukar Bello C.e.o of Akeem better farming institute yace a shirya tafiya kafin yace fara gabatar da aikinsa da Za'ai a channel ɗin M.hausa dake GOtv and DStv yanzu muna son ɗaya daga cikin ku ya faɗa mana matsalar ku"
Wani babban kuma mai ɗan shekaru ya miƙe bayan yay godiya ne ya ɗura da faɗin.
"A kullum muna fuskantar barazana daga wajan manyan mutane wanda suka tsoratar damu da faɗin sunayen su"
Akeem da idanunsa ke ƙasa yana zuciyarsa na tsalle kamar zata faso ƙirjinsa ta fito saboda faɗuwar gaba ya ɗaga idanunsa ya kalli mutumin kamar bazai magana ba sai kuma yace "Uhm" yana faɗin hakan yay shiru da sauri kuma P.a ya miƙa masa gorar ganin yana shafa ƙirjinsa cikin ƙasa da murya cike da tsoro mutumin yace.
"Sunce mu bar masu gonakin mu akan kuɗi dubu ɗari biyar biyar ga dukkan mutumin daya sanya hannunsa a kan takardar, za suyi ma'aikata, da farko Bamu san wacce kalar ma'aikata bace, yaran mu masu tashi sune abin tsoro, mun yarda da noma, kuma itace arziƙin mu da dukkan wanda yake ƙasar Nigeria, Noma toshan arziƙin mu kuma kwanciyar hankalinmu mu manoma, wasu nayiwa noma kallon wani abu nada ban amma da ace mutum zai san amfanin noma da kuma ribarta to hatta samarin da suke da kwalin jami'a tabbas zasu ajjiye dugun buri su tawo gona domin yin Noma, babu buƙatar kuɗi gonakin mu muke buƙata, ƙauyen dake gaban namu sun amince bisa shawara dana masu har Abin yake neman juyewa zuwa tashin hankali, shine yasa muke neman taimako daga gareka ka shiga wannan lamarin muna buƙatar gonakin mu" ya faɗa yana haɗe hannayensa waje guda, ganin hakan yasa gaba ɗaya mutanan wajan suka miƙe suna haɗa hannayensu waje guda.
Da sauri Akeem ya miƙe yana fidda numfashi domin baya ƙaunar wani babba ya duƙa masa.
Wata haɗaɗɗan jotter da pen P.a ya bawa Akeem cikin sauri ya fara rubutu mai cike da tsari daga ƙarshe ya rubuta.
_From Akeem better farming institute_
To
_marasa tsoran Allah masu son ci da gumin wasu_
Sign ~Abb hero~
Yana gama rubutawa ya miƙawa P.a idanunsa ƙasa dan bai so ake ganinsa kafin a hankali cikin fitar wata Amon murya irin golden voice ɗin nan yace.
"Ku ɗauka ku Alhalin Abdul-hakeem Bukar Bello ne, babu abinda zai samu lafiyar ku, Alhalin ku, duniyoyin ku" yana faɗin hakan ya juya walking slowly irin tafiyar nan mai ɗaukan hankali.
Cikin sauri kuma a ransa ya furta "Adnan" da sauri ya nufi mota ganin hakan yasa P.a yabi bayansa motar ya shiga kana yana da gudu hankalinsa gaba ɗaya yay kan ɗan uwansa yana mutuwar son ganin nasa, he Loves him yafi son komai zai faru ya same su tare.
Wayar Md Adnan ya kira amma babu answer hakan yasa Murya can ƙasa yace.
"Uhm p.a drive faster"
Gudu ya ƙara suna zuwa dai-dai wajan taron jama'a Bala driver na ɗaga kiran Akeem ganin sunan Blood yasa Bala ya shiga uku.
Bai tsaya jiran jin abinda Bala zai faɗa ba, da sauri p.a ya fito daga motar yana buɗewa Akeem murfin motar, kai tsaye idanun Akeem ya sauka akan Baffansu.
Da sauri Malam ya miƙe ganin Mai sunan kawonsu yace.
"Kaga abinda ya faru ko? Daga zuwan Adnanu ya haɗu da aljalinsa" da wani irin kallo Akeem yabi Malam yama kasa gane mene sauke faɗa.
Ka kaff Malam ya bawa Akeem labarin abinda ya faru, nan da nan fuskarsa tai jajirrr saboda tashin hankali amma ko kaɗan babu wani alamar tashin hankalin cikin ƙwayar idanunsa saboda shegen shanye abune dashi a rai.
Zame jikinsa yay daga wajan Malam kai tsaye wajan ruwan ya nufa Malam na faɗin "A'a Mai sunan kawo kada mu rasaka dan Allah ka tsaya.." kafin ya gama magana tuni Akeem ya faɗa cikin kogin nutsu ya fara cikin ruwan cike da ƙwarewa yake sarrafa ruwan tamkar dai wanda ya san kanshi babu jimawa idanunsa ya sauka akan wani Abu mai duhu, cikin sauri yay wajan yana zuwa yaga mace saƙale jikin reshe ƙarasawa yay wajanta yana mai ɗan ƙara ware idanunsa ganin babu Md Adnan babu Labarinsa wani iri tsoro ya kamasa cikin damuwar ya nufi wajan Yarinyar yana zuwa yay wani irin.....
*🌈TSINTACCIYA🌈*
NIMCYLUV
_FITATTU HUƊU🔥_
EPISODE3️⃣
http://wa.me/+2348119237616
*_domin magana dani kai tsaye👆🏾_*
Tura kansa dake cikin ruwan zuwa waje yay yana haɗa numfashi, cikin wata kasalalliyyar murya mai cike da alhini yace "I got her" yana faɗin hakan kwanakwanan suka cilla masa duguwar igiya ya kama tare da ɗaura igiyar a ququnsa.
Cikin saurin ya nusa cikin ruwan kafin a hankali ya kama igiyar data riƙe ƙafar Akeela.
A hankali ya kunce igiyar gaba ɗaya Akeela tayi baya tare da fara yawo a ruwan zata matsa can gefe saboda ruwan da yake gudu sosai,
Fararan tafin ƙafafuwanta yabi da kallo, sunyi wani mugun haske kamar jini zai zuba a jikinta saboda farin da take dashi.
Tattausan hannunsa ya miƙa tare da jawo tafin ƙafarta "kittt" ya jata da zuwa inda take ƙarar tawowar wani ruwa ne ya daki kunnansa da sauri ya fisgota yana runtse idanunsa tare da sanya dukkan hannayensa ya wist ɗinta ya wani ƙanƙame idanuna da hannunsa dake bisa jikinta ko motsi ya ƙiyi.
Ya ɗauke dukkan Numfashinsa yana jin sanda ruwan ya shige ta gefensu kamar zai tafi dasu.
Zaro kanta dake jikinsu yay sai a lokacin idanunsa ya sauka akan fuskarta _Tsarki tabbata ga Ubangijin daya halicci sammai bakwai da ƙassai bakwai, Ubangijin daya halicci wannan duniya ya kuma halicci wannan surar dake hannun Akeem_ faɗin asalin kyan fuskar Akeela bata baki ne, tana da wani irin sahihin kyau, wanda ya wuce tunanin mai tunani, idanunta a rufe suke ruff amma eye lashes ɗin nan da suke dugwaye slick dark blck sunyi kwance saman kumburarrun idanunta, ga dugun hancin nan mai kyau sosai, wanda ya tsaya dai-dai tsagen laɓɓanta wanda suke da kauri sunyi jajir dasu.
Gashin kanta data ɗaure da ribbon tuni ya wargatse ya baje yana yawo cikin ruwa sai ta zama kamar wata aljanar cikin ruwan da mutanan suke faɗa.
Taɓe baki Akeem yay kafin cikin zafin nama yay wani cillata bayansa ya goyata sosai kafin ya gyara zaman igiyar jikinsa.
A hankali ya fara ta suwa sama cikin ƙwarewa kwanakwanan na ganinsa suka fara jawo igiyar ruwan.
P.a ne yabi Ubangidan nasa da kallo yana tuna wani abu daya wuce amma ya rasa ko menene, amma Tabbas ganin Akeem goyo da Akeela ya tuna basa wani abu mai mata tuƙar muhimmacin a rayuwarsa.
A fili Malam ya furta "Allahamdulillah biii rahmatiikaa"
Suna zuwa bakin ruwan yay wani irin baya yana daga tsaye yay wurgi da Akeela ta faɗi ƙasa ji kake "timmm" kanta ya bugu ƙasa amma ko motsi ba tayi ba saboda bata hayyacinta ta jima da sumewa.
Jikin Akeem na wani irin kyarma da rawa idanunsa sunyi jajir jijiyoyin kansa sun yi bala'in tashi sai wuci yake na zafin zuciya da kuma sayin ruwan daya gama ratsa dukkan kofofin jikinsa.
Kai tsaye wajan Bala driver ya nufa, ganin haka yasa P.a ya mara masa y domin yasan anything can happen idan Akeem ya ƙarasa domin a wannan karan ɓarin da jikinsa yake ya bayyana asalin zafi da kuma ƙuncin da zuciyarsa keyi, ya bayyana how sad he's.
Yana zuwa ya kalli Bala driver murya can ƙasa yace.
"Car keys?" Zare idanu Bala driver yay kafin ya fashe da kuka yace "Dan Allah dan Annabi kayi min suttura Babban mai gida, ka tausaya min kada ka kuran i don wanna lose my job dan Allah, dashi kawai nake kula da iyali na, na sani a made a mistake amma bani na tursasa Ƙaramin Mai gida shiga ru..."
Gigitacciyyar tsawar da Akeem ya daka masa yana faɗin "Heyyy, car keys nace kaban, kada ka tunzura ni ka bari zanyi Shari'a dakai da ita kanta tsinanniyar datai Coursing wannan abun i hate her, idan ina da rai da lafiya billahi I'll take a revenge, you'll see mene zan, common my friend bani" da sauri Bala driver ya miƙa masa tarin kyes ɗin, huci kawai Akeem yake idanunsa a ƙasa domin duk abinda zai bai fiya kallon mutum ba, gyaran murya yay jin haka yasa p.a faɗin Md Adnan's phone's, his I.d card" wayar ya miƙa masu kafin ya ɗauki walet ɗin dukkan wani card da ake amfani da shi ya bawa P.a.
Kai tsaye mota Akeem ya nufa zai shiga ko takan Yarinyar baibi ba, kafin ya shiga motar P.a yace "Sir" da sauri ya juya yana dafe kansa cikin haɗewar fuskarsa nan nashi yace "what again P.a Al'kaseem Yahya gama?" Yadda ya kira full name ɗin P.a yasa kowa na wajan kallonsa a sanyaye p.a yace "Abbu" ke kira.
Kamar bazai amshi wayar ba sai kuma ya amsa walking slowly yake tafiya yana baje gashin kansa wanda ruwa ya jiƙa daga can ɓangaren Abbu yace.
"Son" marai-raice fuska yay ba tare da yace komai ba, jin haka yasa Abbu faɗin "Are You okey?" Nan ma shiru yay bai ce komai ba hakan yasa Ummi dake gefensa faɗin "Is everything okay?" Didi dake tsaye riƙe da bakin zani tsohuwa ce sosai shekaru sun ja tace.
"Ihuu jama'a, bana faɗa ba? To kai dai Bukari ka haifi ɗa baka haifi halinsa ba, yaro baƙin hali yay masa yawa a to ai duk duniya ba sun shaida, jiya kana gani ilahirin tsiran daka kawo min ta tasss yabi dare ya sace, to ɓarawo ne fa? Banda maye waye ne zaice wani tsire ehe? Ai saini da cinsa ya zame min dole amma ina dai ba faɗin wasa wallahi Bukari ka nemawa ɗan ka magani bana son na fita ana min cune da baki ana gata can, jikanta maye ne, mece cin nama da zaro harshe waje....."
Shiru tayi Saboda saukar Muryar Akeem da taji ta wayar tana faɗin "Keeee!" Zare ido Didi tayi sai kuma ta fashe da kuka tana zare bakin zabi tana faɗin "to! A nan gidan duniya idan ban sawa Audil albarka ba wa zan sawa? Eh? Ta ka samu Iyaye da basu san komai ba ina nan ina jan casbie sai da nayi salati miliyan tamanin da shida to astagafirullah kamar dai bakai haka ba"
Girgiza kai kawai Abbu yay kafin yace.
"Friend ina son?" Ajjiyar zuciya Akeem ya sauke kafin yace "Abbu she killed my brother ta kashe mana Adnan" Miƙewa Abbu yay kafin yace "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Adnan ya mutu?" Wane kalar zabura Didi tayi sai ga zani a ƙasa tama ƙasa magana.
Ummi bakinta ta rufe saboda kukan da yazo mata da sauri tayi bedroom ɗinta, Mami kuwa idanunta kawai ta ƙurawa Abbu Allah yasa raguwar yaran duk suna makaranta Amani kuma tana bacci.
Cikin dauriya Abbu yace "Stay there Abdul-hakeem, in sha Allah on my way yanzu nan kuje gidan Baffa" yana faɗin hakan ya kashe wayar tare da nufar part ɗinsa..
Ƙasa Mami tayi da kanta sai sauke Ajjiyar zuciya take, Didi kuka kuka ta fasa tana faɗin "Wanne gantalallan ne Adunan? Laa Muhammadur Rasulullah S.a.w ku tare ni kada naje ƙasa"
Kwantar da Akeela akai a ƙasa Taɓa jikinta Malam yay yaji wani mugun sanyi, a dai-dai lokacin har sarkin ruwa yazo amma neman duniya babu Md Adnan gaba ɗaya suka rankaya zuwa gidan Baffa, suna zuwa Malam yace "Rabi maza haɗu min gaushi" babu jimawa ta dawo ɗauke da gaushi Miƙewa yay yana fita yace "maza sauya mata kaya Wannan na jikinta yay sanyi da yawa" Murmushi kawai Baba Rabi tayi yana fita ta miƙe tsaye tare da kunce bakin zani wata ƙaramar (Laya) ta ɗauko tare da samun kan Akeela wajan tsakiyar kanta ta haɗa da Layar ta rufke gashin wajan layar da shige ciki.
Wani Murmushin ta sakeyi ita kaɗan tasan abinda take kafin ta sauyawa Akeela kaya ta rufe ta da zani jikinta yay sanyi sosai kamar ƙanƙara.
Har lokacin Akeem bai shigo gidan ba, yana cikin mota sallah kawai ke fito dashi.
Wajejen Magrib Abbu ya ƙarasu daga kano da Wudil, har lokacin kuma Akeela bata farka ba, jiki a sanyaye Abbu yace "Baka da laifi, infact Adnan taimako yaje yi, Allah kaɗai yasan abinda ya samu Adnan, yana ruwan? Mutuwa yay? Tafiya ruwan yay dashi no one's know! Tabbas idan nace banji zafi da baƙin cikin abinda ya faru ba nayi ƙarya, amma ni musulmi ne waman ƙaddararllahu haƙƙa ƙadrihi, kuma Innallaha ba'assabirin zanyi addu'a zan saka ai idan har Adnan n raye Tabbas zai dawo gare ni"
Jinjina kai Malam yay kafin yace "haka ne, Ubangiji yasa Adnanu yana raye yaron ƙwarai" Miƙewa Abbu yay yace "Ina ita yarinyar ya farka ne?" Girgiza kai Malam yay yace "A'a muje ka ganta" gaba Malam yay Abbu ya bisa a baya cikin tafiyar nan nashi irin na Akeem yana sanye da wata bugaggiyar shadda dark Ash sai jaddara sai ƙamshi yake.
Malam ne ya fara shiga sai Abbu yana shiga idanunsa ya sauka akan Akeela gaba ɗaya tunaninsa ne ya tsaya cak, zuciyarsa na wani irin harbawa Kallonta yake tamkar zai cinyeta ko ya mayar da ita ciki, wani irin kallo ne mai kama da wanda ya kamo da soyayya! "Bukar! Bukar!" Da sauri yaja numfashi yana shafa ƙirjinsa kafin ya kalli Malam da sauri kuma ya juya yana kallon Akeela dafe ƙirjinsa yay ji yay wani mugun so da ƙaunar Akeela ya sauka a zuciyarsa har yana jin idan bai aureta ba zai iya mutu....
😂 Alhaji ka taro match, mata biyu? Eh? Yara sama da biyar kaga ɗanya sabuwar nona kace kana so? Jama'a me kukace anya Abbu bai so zuciyarsa ba????
ANJIMA DA FARA PAYMENT TUN KAFIN NA FARA POSTING
*TSINTACCIYA*
NRML GRP: ₦300
VIP: POSTING SAFE+YAMMA ₦500
ACCT NO: 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S
BANK NAME: UNION BANK
EVEDANCE OF PAYMENT
08119237616
*FITATTU HUƊU🔥*
TSINTACCIYA
Nimcyluv
Baƙar fata
Autar manya
DATTIJON ARZIƘI
Real ladingo
SULTAN
Mss flower
Gaba ɗaya 800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218
*SARAUTAR MARUBUTA* For more information😇
http://wa.me/+2348119237616
*🌈TSINTACCIYA🌈*
NIMCYLUV
FITATTU HUƊU🔥
_Dedicated to *ELEGANT ONLINE WTITER'S* Ina maku sahihiyar ƙauna mara algus❤️❤️_
EPISODE 4️⃣
http://wa.me/+2348119237616
*_domin magani dani kai tsaye_*
Jiyayi Numfashinsa na wata iriyar fusga lokacin daya sauke idanunsa a saman ƙirjinta, cikin sauri ya zame idanunsa yana shafa fuskarsa.
Bai taɓa ganin halittar da yaji yana mutuwar so, irin son nan mai zautar da mutane irin Akeela, at least zai iya good 35yrs ko sama da haka, kusan jiƙarsa ma take ba ƴar ba, ko zai haɗata da yaransa sai dai suyi age mate da Aleema.
Malam ne yay gyaran murya kafin yace "zauna mana Bukar" zama yay still idanunsa akan fuskar Akeela kamar zai haɗiye ta, saboda wani mugun kyau da tayi masa a fuska, ga ƙirjin nan dam, so Ma sha Allah, But even her lips are looking luscious succulent and irresitable every tensed man.
Shafa fuska ya sake yi kafin yace.
"Baffa badai Akeela tayi wannan girman ba?" Murmushi Baffa yay yace "Wallahi Bukar" "Allah sarki, the last time dana ganta tana primary 2 ne" cewar Abbu ya faɗa murya a shaƙe.
A sanyaye Baffa yace.
"Kayi hqr Bukar garin ceto ƴar dana haifa ɗan cikin ka yay asara nasa rayuwar" kamar Baffa zai kuka saboda damuwa cikin damuwar shima Abbu yace "haba Baffa, da abinda ka haifa da nawa ai duk ɗaya ne ko? Blood is thinker than water, koni i can do anything for this innocent gril, she deserved it" Murmushi Baffa yay zuciyarsa na masa zafi sosai Kafin yace.
"Ban san mene yasa Akeela tayi hakan ba, tana da hankali amma lalurar da Ubangiji ya jarabce ta dashi na neman zautar da tunaninta" da Mamaki Abbu yace "lalura?" "Eh! Tana da Amosa nin jini (SIKILA), wanda ke sonta tunda yaji labarin ciwonta yace ya fasa, bazai iya zama da mai ciwon SIKILA ba, haka nan taje ta shafa masa, shiyasa na yanke shawarar bawa wani auranta mai suna Malam Buba, yana da mata uku yara goma tsoho ne domin ya girme min, yace yaji ya gani zai zauna da ita a hakan, tun lokacin Akeela ta daina walwala na san bata son shi, to idan bata Aure sa ba wane zata aura? Eh? Kasan yadda ciwon SIKILA yake kamar Annoba a wannan lokacin musamman a wannan lokacin damuna da muke ciki, wannan dalilin yasa ta nemi kashe kanta ta wuta da bala'i"
Shiru Abbu yay Mamaki duk ya kamasa, yarinya like Akeela da ciwon SIKILA? Allah Al-hakkamu kenan bowayi gagara Misali.
Gyara zama Abbu yay cikin serious tone voice yace.
"Cutar sikila ko amosanin jini na ɗaya daga cikin cututtukan da za'a iya cewa na neman zama ruwan dare, saboda yadda ake yawan samun yin aure tsakanin masu rukunin jini AS da AS ko SS da AS, amma Abu mafi muhimmanci Shine babu yadda za'ai ba tare da gamayyar ƙwayayen haihu ba mutum ya samu SIKILA, babban jahilci ne ma gamai cewa za'a shafa masa, ai ba tari bane, ko H.i.v SIKILA zan iya haɗata da Asthma, amma Baffa batun zaka aura wa Akeela wani can banza bai taso ba, kai mata aure inda ake sonta kuma za'a kula da ita, na tabbatar he loves her just of her beauty and.."
Shiru dan baya jin iya cewa wani abun.
A hankali Baffa yace "To Bukar yay zan? Wayewar inda kuke da nan akwai bambanci sosai" idanunsa akan Akeela yace "Allow me to go with her, ka bani ita, zan haɗa ta da miji na gari wanda zai kula da ita, tai cikakken ilimi inda zakai farin ciki zan haɗa ta da yarana" ya faɗi maganar ba tare daya shirya ba, domin ji yake ko mintina goma bazai iya ba tare daya kalli Akeela ba, yay hakan ne saboda ya samu very close to her ya dasa mata masifafan son sa a Zuciyarta wanda Turawa suke cewa _ETERNAL LOVE_ yasan kuma soyayyarsa da ita ba zata taɓa zama _FORBIDDEN LOVE_ ba.
Jin muryar Sarkin ruwa a bakin ƙofa na sallama yasa Baffa Miƙewa cikin sauri yay waje.
Yana fita Abbu ya miƙe, cikin tafiyar nan wacce ya kejin kansa ontop, a hankali ya ƙarasa inda Akeela ke shimfiɗe kamar ma matacciya,
Ƙirjinta dake sama da ƙasa ya kalla ganin hakan yasa ya tabbatar she still alive.
Tsaye yay a kanta yana sauke numfashi tare da lumshe idanunsa slowly kuma ya ƙara buɗe idanunsa, kamar zai juya sai kuma ya sunkuya dai-dai kanta yana Kallon Zallar kyan fuskarta.
Hannunsa ya sanya ya ɗan ƙara zame zanin kanta nan take sumar kanta ta bayyana irin sosai ɗin nan gata rabi baƙa rabi jaa.
Wani cute smile yay yana yin ƙasa da bakinsa zuwa saman fuskarta bakinsa ya manna a goshinta tare da bata wani special kiss wanda ya kejinsa best kiss in his whole life.
Baffa ne ya kalli Sarkin Ruwan kafin yace "fatan an samu Adnanu ɗin?" Girgiza kai Sarkin Ruwan yay yace "gaskiya babu wani labari, amma dai ga abinda muka samu" ya faɗa yana miƙawa Baffa rigar jikin Md Adnan karɓa Baffa yay yace "to mungode ƙwarai shi kuma Allah ya bayyana mana shi, idan yana raye ya kai sa hannu na gari" da Ameen Sarkin Ruwan ya amsa.
Har Baffa zai juya sai kuma ya nufi motar Akeem yana zaune zuwa lokaci ya zame rigar jikinsa daga shi sai singlet murɗaɗɗan ƙirjinsa ya bayyana, ga sumar nan har lokacin na zubda ruwa, banda sauke numfashi babu abinda yake.
"Mai sunan kawo" Baffa ya kira Akeem, gently ya ɗaga kansa tare da sauke ganinsa akan Baffa kallo guda yay masa ya ɗauke kansa yana taune leɓansa tare da lumshe gajiyayyun Maraitattun idanunsa.
"Nasan kana jin haushin na ne ko? Kana ganin kamar da gangan nai hakan ko, to wallahi tsananin son da nakewa yarinya ta yasa nai haka amma nama fika baƙin ciki a yanzu haka"
Shiru Akeem yana danna system ɗinsa ba zaka taɓa cewa dashi Baffa yake Magana ba, fuskarsa looking okay Babu wani sauyi.
Sanin halin Akeem yasa Baffa juyawa.
A tsaye Baffa ya samu Abbu yana kallon Akeela kafin yace "to ko dai kwana za kuyi ne?" Girgiza kai Abbu yay yace "A'a yanzu zamu tafi in sha Allah" da sauri Baffa yace "to bari na kwaso kayanta ko" kallon Baffa Abbu yay kafin yace "haba Baffa no need, Akeela is like my daughter zan mata komai" murmushi Baffa yay hawaye na saukar masa domin gani yake ƙanin nasa kawai daurewa yake rashin Md Adnan ba ƙaramin babban giɓi bane a rayuwarsa.
Baba Rabi ce ta shigo idanunta yay jaa sosai irin taci kuka ta ƙoshi, kafin ta kalli Abbu tace "Mungode sosai Alhaji Bukar Allah ya bayyana mana Adnanu cikin aminci" "Ameen" kawai Abbu yace domin sosai zuciyarsa ke masa zafi kuka ne kawai da bazai ba, amma ganin fuskar Akeela na yaye masa wani ƙuncin.
Baffa ya nufi wajan Akeela zai ɗauke ta da sauri Abbu yace "A'a Baffa, Ni da zamu tafi tare bari na ɗauke ta"
Hannu yasa ya ɗauke ta sassanyar Ajjiyar zuciya Abbu ya sauke yana jin zuciyarsa na sanyi sosai, wani mayataccen Murmushi Abbu yay tare da fakar idanun Baffa yay wani tura ƙasa tsakiyar wuyanta...
*🌈TSINTACCIYA🌈*
NIMCYLUV
FITATTU HUƊU🔥
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*
EPISODE5️⃣
Http://wa.me/+234811237616
Bayan sallar magrib motocin su suka fara shigowa cikin haɗaɗɗan titin _Railway quarters Nasarawa, Kano_
A gida mai number 112 suka fara shigar da motocin bayan gatekeeper ya buɗe masu ƙaton gate ɗin.
Motar Abbu ce a farko shida Bala driver sai Akeela dake kwance a baya.
Mota ta biyu kuma P.a a ciki shi ɗaya yana janta motar ƙarshe kuma Oga Dr Abdul-hakeem Bukar Bello ne zaune ya ɗura hannunsa guda ɗaya a saman string motar ɗaya hannunsa kuma ya tsakiyar kansa yana hargitsa sumar kansa, a hankali kuma yake sauke ajjiyar zuciya ajajjere.
Zafi da raɗaɗi da zuciyarsa ke masa na tawowa da Akeela da Abbu yay yafi komai baƙanta masa, cos she's the reason behind anything daya samu Md Adnan.
Bama ya so ya buɗe ido yaga yarinyar shiyasa yau zamansa cikin motar tare da lumshe idanunsa yana so Abbu ya shige da ita domin ta riga data zame masa mujiya.
A hankali Abbu ya buɗe back seat tare da zura kansa cikin motar, dim! dim!! dim!! Haka zuciyarsa ke bugawa aduk sanda ya kalli ƙyakkyawar fuskarta wata nutsuwa ta saukar masa.
Zama yay cikin motar tare da miƙa hannunsa gaba ɗaya biyun ya jawota sosai very close to him, hannunsa dake rawa yasa tare da yin baya da gashin ta wanda ya sauke wai wist ɗinta,
Lumshe idanunsa yay cikin ƙasa da Murya yace "Uhm baby na mai kyau, nine ko?" Ya faɗa yana shafa kanta sai kuma ya cireta sama tare da fito da ita daga cikin motar, dai-dai kunnanta kamar wacce ta kejin sa yace.
"I'm your dad, your boyfriend uhm baby kina cin abinci kuwa? You are so light Baby" ya faɗa yana tafiya da ita kamar wani mai sabon jini bayan yay jika da ita.
P.a dake tsaye ya ɗauke idanunsa a hankali kuma yabi bayan Abbu da some things na Md Adnan.
Tsayawa Abbu yay tare da danna wani ma danni a hankali ƙofar ya fara ja baya tare da buɗewa ciki ya shiga babban Parlo ne daga cikin ƙofar, iya haɗuwa ya haɗu komai na Parlo Ash ne daga kujeru zuwa Flowers da labulaye anything dai.
Ga ƙatuwar cineme kusan rabin bango sai deep frizer mai gida wajan uku,ga senter table a tsakiyar mai ɗauke da wata ƙatuwar flower jikin bangon parlon duk Album ɗin ayatul kursiyu ne, da fatha e.t.c
Daga can bayansa yaji ana faɗin.
"Ya..yah kamar dai ƴan gudun hijira kuka faɗo mana gida babu ko Sallama? A'a babu ruwana kuda Allah tun dai duk musulmai ne a gidan da haka nan kamar ƴaƴan arna zaku faɗu mana gida, ai ko ƴan dama ne ku kwayi sallama musan da zuwanku kuma musan abinda zamu baku"
Kallon Didi Abbu yay kafin yace.
"Afuwa Didi"
Taɓe baki tayi kafin tace "A'a astagafirullah mene kuma afuwa fisabilillahi kamar dai nace akan Bukari siya min tsire? A'a ni rayuwar duniya mai sauƙi na ɗauke ta, Wacece wannan kuma Aljanu take ko shan Inna ce ta kamata"
Ta faɗa Idanunta akan Akeela wacce take jikin Abbu.
P.a Murmushi Yay domin yana son dramer tsohuwar kafin yace.
"Barka da dare Didi"
Washe baki Didi tayi tace "A'a ƙasimu ince dai ka samu matar aure? Yooo ba Gwamma kai ba ko babu komai zan baka shawara mai kyau kabi, kaga dai babu dangi iya babu na baba jinƙai da tausayi irin nawa nasa aka baka aiki gashi kuma yanzu nace kaje wajan yarinyar idan ubanta har yanzu yaƙi yadda ta Aure ka kawai kayi mata ciki kaga ko babu komai dole a baka ita ka aura ni wallahi yarinyar ba tayi min ba" shi dai Shiru kawai yay yana Murmushi ita a dole shawara ta bashi idan kuwa haka ake bada shawara da an shiga uku.
Kwantar da Akeela Abbu yay a hankali kuma fara faɗin.
"Ummi!! Mami!!"
Mami ce ta fara fitowa idanunta ya kumbura sosai saboda kuka, baƙa kana ganinta kaga mahaifiyarsa Md Adnan zatai shekaru wajan 42 tana sanye cikin wani haɗaɗɗan lace, Zama tayi a kujerar dake farcing Abbu ba tare da tace komai ba.
Not too long Ummi ta fito daga part ɗinta hannunta riƙe da wata ƙyakkyawar Yarinyar zatai shekaru 4 haka fara ce sosai kamanin Akeem zane raɗau a saman fuskarta Amani kenan jika a wajan Alhj Bukar Bello ƴar kuma wajan Dr Abdul-hakeem Bukar Bello.
Zama Ummi tayi kusa da Mami tana sanye cikin wata orange ɗin lafaya tai mata kyau sosai zatai shekara 45 haka amma jikinta a murje yake sosai har tafi Mami gogewa da kuma wayewa.
"Barka da dare ya hanya" Ummi ta faɗa murya ƙasa.
Kallon su duk yay kafin fuska a ɗan haɗe domin bai fiya sakin fuska ba idan ba keɓewa yay da matansa ba yace.
"Kunga abinda ya faru da Adnan ko? Jikina yana bani yana raye kuma komai jimawa zai dawo gare mu, i believe cewa komai sai Ubangiji ya tsara mu ɗauki hakan a wata sabuwar ƙaddara daga Allah wacce ya jarabce mu domin gwada imanin mu, ko yarda na yarda cewa hakan ya faru ne dalilin shigarsa ruwan, amma ruwan ne dai kawai ya zama sanadi amma tuntuni Ubangijin AL-ARSHI ya tsara faruwar hakan a Lauhil Mahfouz..."
Da sauri Didi tace.
"Sadaƙallahul Azeem,amma dai Bukari ka cuce mu da baka zama malami ba ka rasa mai zakai sai siyasa, ai yasin naji daɗi daka sauka daga kujerar mulkin baki ɗaya, ai da wallahi har govmet hausi ɗin zani nace bada yawo na ni Uwarka idan suka zaɓe maka, haka kurum na fita waje a dinga shunani da baki ana gata can ɗan ta yana handime kuɗin jama'a"
Ta faɗa tana cuna baki gaba, shi dai Abbu bai ce komai ba domin yasan rikicin tsofa ne.
"To! Ubangiji ya dubi idanun mu ya sanya Adnan yana raye ya kuma dawo gare mu, Allah ka dubi halin da muke ciki"
A sanyaye Mami tace "Ameen" idanunta na ƙara kawo ruwa ajjiyar zuciya Abbu ya sauke kafin ya kalli Akeela yace.
"Ɗiyar Baffa ce da Baba Rabi dalilinta Adnan ya faɗa ruwan kuma Thank God Dr ya ciro ta..."
A nan ya kwashe labarin kakaf abinda ya faru ya basu.
Ihu da kuuu Didi tasa zani na faɗuwa tace.
"Kun kashe min Adnanu wallahi hisba zan kaiku"
Tana faɗin hakan ta nufi waje a hanya taci karo da Akeem dake shigowa fuska ya haɗe sosai ko alamun annuri babu.
Ganin haka yasa Didi washe baki tace.
"Yooo yanzu naji bayani ai cewa nayi bari na leƙa naji mai gidan Shiru fa"
Bai ƙara kallon ta ya matsa can gefe sallama ma ciki yay kai tsaye upstairs ya nufa wajan part ɗinsa.
Ganin haka yasa Abbu faɗin "Dr kazo ka duba Akeela" jin sunanta yasa Akeem yaji kansa ya sara Mami kam Miƙewa tayi domin tunda taji a kanta Adnan ya faɗa ruwa taji wata muguwar tsanarta ya cika Zuciyarta.
Da ɗan sauri Akeem ya ƙarasa haurawa saman ko takan Abbu bai bi ba ganin hakan yasa Ummi faɗin.
"Bari na duba ta"
Ɗaukan ta Abbu yay zuwa part ɗin yaransa mata, ɗakin duhu alamar duk sunyi bacci On yay na wutar bedroom ɗin Aleema,Afaf duk suna kwance wajan Ameera da take zuwa hutu ya kwantar da ita, lokacin tuni Ummi ta ɗauko kayan aiki, cikin sauri ta fara duba ta ganin har yanzu da ruwa a cikinta yasa ta danna cikin da sauri sai ga ruwa na fita.
Tana ƙara dannawa Akeela tai hau yin tari.
Wata Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya Abbu ya sauke tana gama tarin kuma bacci ya ɗauke ta, sai da Ummi tayi mata injection kana ta ɗaura mata drip Abbu yi yayi kamar bazai fita ba ganin kallon da Ummi ke masa yasa ya ɗan shafa kansa yace.
"Miss You dear, let's go"
Gaba yay ta bisa a baya kana ta jawo masu ƙofa,
Daman p.a tuni yay masu sallama ya tafi gida.
A hankali bakinsa ke motsawa yana tasbihi can ƙasa zuciyarsa, saboda zafin da zuciyarsa ke masa, cikin haɗaɗɗan parlonsa ya shiga komai na Parlon white ne.
Ya haɗu sosai har ba'a magana, kai tsaye wata corridor ya bi hadle ɗin ƙofar ya buɗe, wani irin lumshe idanunsa yay tare da sauke wani maraitaccen numfashi yaja tare da saukewa, saboda wani sassanyan ƙamshi daya daki hancinsa ya sashi lumshe idanun da bai niyya ba.
Tura kansa cikin bedroom yay bakinsa ɗauke da wata kamilalliyar sallama yana maida ƙofar ya rufe.
Derect bathroom ya nufa yana mai zare kayan jikinsa, a saman hanger ya saƙale tare da sakarwa kansa shower, a hankali yake sauke ajjiyar zuciya yana jin yadda ruwan yake dukan saman fresh skin ɗinsa.
Bayan yay wankan ya ɗaura alwala kana ta ɗauki wani long white towel ya dauraia wist ɗinsa, ko kansa bai tsane ba ya fito ruwa na sauka daga sumar kansa zuwa ƙwantaccen gashin ƙirjinsa.
Wani irin ɗaci bakinsa yake masa rabon da yaci abinci har ya manta wajan fridge ya nufa ya ɗauki Apple da cake ya fara ci bai wani ci da yawa ba ya ajjiye.
Wasu haɗaɗɗun nightwear slik Pajamas milk colour, a hankali ya miƙe tare da goya hannunsa a bayansa ya ɗan fara tafiya yana mai karanta addu'a yana bin duk kusurwa ɗakin da tofi bayan ya gama ya kwanta saman bed ɗin tare da jan duvet ya rufe jikinsa, gaba ɗaya ya ƙasa bacci tunda matarsa ta rasu wajan haihuwar Amani baya iya cikakken bacci ya saba da jikin mace sosai duk da auran kamar na dole ne bai so amma ya saba da jikin matarsa ainun.
A haka bacci ya ɗauke sa.
Misalin 4 na dare ta shiga buɗe idanunta wanda sukai mata nauyi kanta na sarawa sosai, hannunta mai ɗauke da carnoner ta kala ɗan marai-raice fuska tayi kamar wata ƴar baby Wanda ya sanya manyan dimples ɗinsa bala'in lomawa.
A hankali kuma ta shiga bin bedroom ɗin da kallo sosai gabanta ya faɗi ganin bata dan ɗakin ba, jiki babu ƙauri ta miƙe tsaye tana Miƙewa gashinta ta sauka har wajan manyan ass ɗinta.
Da Mamaki tabi jikinta da kallo ganin wata Robe Nightgown silver wacce ta sauka iya laps ɗinta gaba ɗaya manyan gwayen ƙafafuwanta suna waje ga wani gashi da yay kwance lub a saman fatar ta.
Shanyayyun idanunta wanda kullum suke a Lumshe ta ƙara buɗe, jikinta babu ƙwari ta nufi ƙofar data gani, tana tafe ko'ina na jikinta moving yake kamar tarwaɗa.
A hankali ta buɗe ƙofar ta fita ita bama ta san dare bane sai da ta fito parlon daga duhu ga wani masifafan sanyi na Kaɗawa, da sauri ta matse jikinta waje guda ta shiga taune bakinta kamar wata ƴar turawa haka ta zama cikin nutsuwa take tafiya harta isa tsakiyar Parlo tana zuwa zata shige taji an sanya mata ƙafa baya tayi tare da hantsilawa zata faɗi wata kuma ƙyakkyawar Ajjiyar zuciya ta sauke jin ta faɗa saman ƙirjin mutum...
😂Abbu ya biyo dare jama'a