Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 1 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 1 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 1 - Novels Elite

*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*


   *PROFICIENT WRITER ASSOCIATION*

_Kokarin azawa akan tafarki,shi ne abu mafi muhimmanci da yakamata marubuta su kware akai,mu proficient writers association za mu yada wannan manufa._      👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 


 *WATA SAKAYYAR....*

        (Sai a Lahira)


👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽


By

            Nusaiba Alkamawa
Dedicated to my bloody sister *jiddah alkamawa* 🥰

                  


free page


••••{1}_______________Yanayin damina ne,garin ya daure tamau a kowane irin lokaci zai iya sake ruwan dayake kunshe a cikinsa kasancewar wata yayi tsakiya gashi kuma a yanayine na watan ruwa da nasara suke cewa (August),inda yayi dadai da yanayin marka marka inji hausawa.

Yayyafa aka fara da alama fah ruwa so yake ya goce a kowanne irin lokaci.

Hmmmm sarkakken gidannan mai cike da sarkakiya idona ya hangomini,kowa sai kokarin shiga gida yake domin kaucewa wannan baƙin hadarin da  alama zai iya yin awa biyar yana zubar da ruwa batare da ya gaji ba .

Kowane dan adam Allah yayi masa kafafunsa biyu wanda zai yi amfani dasu wajen gujewa abinda zai cutar dashi.

Saidai ga wanda basu da wannan ni'imar fah?? Su kuma ya zasuyi kenan?.Wata yar kyakykyawar

 matashiyar budurwace wanda yanzu take matakin farko a budurcinnata,ma'ana bazata wuce shekara goma sha uku ba kenan.

A zaune take a karkashin bishiyar gwaiba wacce take gefe da harabar gidan kadan,duk da iskar da take kadawa tana rishi da bishiyar da take zaune a kasanta bisa kan kujerar kaddarta,hakan baisa ta motsaba ko nuna wata alama daga kan fuskarta,duk da kuwa yanda fararen kayan da suke jikinta suke motsawa.

Idonta kyam yake yana kallon kan kofar babban falon shiga ainihin cikin gidan,duk gudun da yan gidan suke wajen kauracewa bugun ruwan dayake shirin zubowa duk akan idonta yake faruwa har saida ya zamo kowa ya samu nasarar shigewa cikin gidan.Na karshen Shiga ne ya rufo kofar gamm,yazamana babu wata halitta datake wanzuwa a tsakar gidan sai baiwar Allahn da take kan kujarar.


Kokarin boye abunda yake cikin zuciyarta takeyi duk da hakan kaman yana bata matukar wuya wajen yinsa.


Yayya fine yafara zuba fiiiiiii marasa karfi,babu abinda Jiddah take sai kiran sunan Allah a zuciyarta,wanda dama shine abinda kadai take da ikon yi a koda yaushe, 

Takun sawun mutum kunnuwanta suka jiyo mata kasancewar ruwan baiyi karfi sosai ba duk ya jikata jarab har yana zuba ta kasan kujerarta.


Sauke idon tayi akan mai gadin gidansu bawan Allah wanda samunsa cikin talikan bayi akwai matukar wahala.

Shi ma kallonta yake cikin sanyin jiki, idanuwansa suna nuna matukar bukatar san taimakonta amma kuma komai saida dama akeyi.Tsayawa yayi a gabanta yana kallon yanda hakoranta suke karafkiya da juna kat kat kat kaman suna fada,saboda tsabar yanda jikinta yake rawa.


Hawayene ya zubo daga idonsa kafin yace cikin karyayyar murya.


"Kiyi hakuri kinji uwata,tunda naga hadarinnan nake ta gudu amma kinsan abinka da jikin yafara gajiya"

Dago kanta ta fara da sauri tareda yimasa wani wahallalen murmushi tana lumshe ido,wanda hakan ya bawa ruwan dayake kan gashin idon ta damar gangarowa.


Baiyi mamakin ganin fuskarta ba dan dama yasan hakan ne zai kasance amsarta,tashi yayi a hankali ya koma ta bayanta tareda fara tura kujerata zuwa cikin gidan.______Tun kafin su shige falon wata mata dattijuwa bazata wuce shekara Arba'in  ba ta tsaida su cike da masifa tana cewa,

"Kai kai Garxali tsaya daga nan,miye haka zaka wani daukota ku bata mana falo,bayan ba iya gyarawa zatayi ba,a jiye ta anan idan ta bushe sai ta shige ciki  inyaso,gayyar tsiya kawai"

Kallon matar Garxali yake cike da takaici yana jijjaga kai,komawa yayi ya fita daga cikin falon ya bar jiddah a wajen wanda kanta yake sunkuye.Wani yarone ya bugo ball shida abokin wasan nasa wanda suke kama sak saidai yadan zartashi girma,da alama dan uwansa ne.

Zuwa yayi gaban jiddah  ya tsaya wanda take ta rawar jiki a kan kujerarta a gefen kofar falon,inda babu carfet a wajen.


Musguna mata baki yake duk daba wayone dashi sosai ba.

Kallonsa take kawai babu wata alama a kan fuskarta ta farin ciki ko bakin ciki.


"Ni kidaina kallona mayyah kawai,umma tace ke mayyah ce,ke ba mutum bace dan haka karki taba min kwallona"

Kallon kwallon take da take gefen tayar kujarta  sannan kuma sai ta kalli fuskar dan karamin yaron.


Jijjiga masa kai kawai tayi batare da tace komai ba,suna cikin hakanne garxali ya dawo da sauri dauke da bargo a hunnunsa a cikin leda.

Ware shi yayi ya lullubawa jiddah a jikinta kafin ya ciccibeta zuwa dakin ta, wanda yake can wajen wanki na gidan.


A hanyar wucewa ta madafar abincinne yayi wa wata mata wacce take wanke wanke a kitchen magana,

"Dan Allah idan kin gama aikin  Asabe kizo ki taimaka mata,ai bansan kina ciki ba,nayi zaton kin tafi gida"

"Ahah nagama sai naga ruwa ya tareni,shine kawai na tsaya rage aikin safiya"

Wucewa yayi ya fita ta kofar baya tareda bin wata rumfa wacce zata kaishi dakin dayake gidan na can baya.

Bude kofar dakin yayi ya zaunar ta akan katifar da take dakin.

Tsugunnawa yayi a gaban ta tareda sake jawo bargon yana sake rufemata jikinta.

"Nasan kina kokari da kuma hakuri,saidai kici gaba dayin hakuri kinji,wata rana zai kasance kaman bai taba faruwa ba,ni zan tafi amma zan je chemist na siyo miki maganinki,zan sake yiwa asabe magana ta taimaka ta cire miki wannan kayan kar sukara gudun hauhawar lalurarki"

Tunda yake maganar idonta kyam a kansa,saida ya gama kafin tayi masa alama da hannunta akan taji abinda yace,tana mai ɗaga kanta.


Shima jijjiga nasa kan yayi,dan zuwa yanzu yafara gane yanayin maganar ta ta kurame wanda asabe take koyamata,wasu kuma daga wanda malaminta ya koyamata a baya.

Har yazo fita suka ci karo da Asabe itama ta shigo dakin.

Kara yimata bayani yayi kafin ya fita domin nemowa maganin dayace.

Karisawa inda jiddah take Asabe tayi tana taba jikinta da yayi sanyi kalau,ga tsokar jikinta ta ko ina rawa take,sauke ajiyar zuciya tayi kafin tace,

"Kai abu bayyi dadi ba,ni duk na dauka kina dakinki banyi zaton kina waje ba har ruwa yafara dukanki,nasan yanzu ciwonki sai wani tsananin ikon Allah idan bai tashi ba,yanzu bari na taimaka miki ki cire wannan kayan"

Hannunta ta dauka ta kai kan kumatun jiddah tareda jin yanayin temperature na jikinta,sanyi Kalau taji kaman jikin gawa,kallon tausayi ta bita dashi tare yaye bargon da garxali ya nada mata a jikinta.

Zeef din rigar, ta ja tareda cireta a jikinta ya zamo saura best kawai a ciki wanda ta fito da kirgen dangi da ta farayi kadan.


Yi mata alama tayi akan ta kwanta akan katifar,babu musu jiddah ta kwanta a kan bayanta idonta yana kallon cilin din dakin,tunani ne barkatai suke yawo a cikin idonta,yayinda a bangare daya kuma tanajin yanda asabe take sauƙe dogon wandon dayake jikinta wanda ya jike da ruwa.


_____Barta tayi ga ita da best da kajeran wando kafin ta tashi zuwa dauko mata wasu kayan a cikin wardrobe dinta.

Wata doguwar riga mai kauri ta dauko baka mai adon golden da kuma wata hula itama ta sanyi.


Bayan sun gama shirin saka kayanne ta dauko mata man shafawarta wanda shima na maganinne wanda zai dunga kulada yanayin temperature jikinta,da kuma taimakawa cikin ƙashinta.


Bayan gama shirin kana kallon idon jiddah kasan taji dadin kayan da yake jijinta,saidai duk da haka numfashinta daddaya yake fita da kyar.


Tashi Asabe tayi zata fita jiddah tayi saurin riketa tareda nuna mata,kafarta ta dama tana runtse ido.
Dawowa tayi tareda matsa kafar kadan kafin tace,

"Nasan zasuyi miki ciwo Hawwer amma kidaure bari Garxali ya kawo maganin kisha,Allah yasa dai a yi sa'ar samun,yanzu ki jirani bari na kawo miki ko ruwan tea ne mai dan zafi "

Daga kanta tayi da alama taji dadin furucin Asaben.


Bayan fitar Asaben kafafunta ta zubawa ido daga kallon idanunta kasan akwai abinda take tunani a cikin ranta.


Fuskarta ta juyar kaɗan tana kallon  windon ɗakin ruwa yake zuba ta ɗaya bangaren,yayinda shikuma labulen dakin yake kadawa sakamakon ruwan da akeyi wanda yake zuba tareda iska mai karfin gaske.


Sake jan bargon dayake jikinta tana ƙara ƙame jikinta a ciki.

Shiru ne ya ratsa dakin baka jin komai sai numfashin Hauwa'u mai kama da nishi.

Inna Asabe ce ta shigo ɗakin ɗauke da tire mai ɗauke da kofi da kuma cincin a gefe.


Tsugunanwa tayi a hankali saboda kar yazube saboda bata rufe kofin da plate ba.

Jerawa tayi a gabanta tareda yimata kallon ta sakko,

"Saƙƙo Hauwa kisa wani abu a cikinki karki kwanta da yunwa,kinsan ita kanta yunwar zata iya jawomiki matsala,yakamata kidaina kwana da yunwa kinji"

Ɗaga mata kai tayi tareda sauƙe bargon ta matso gaban gadon, ziro siraren kafafunta tayi,wanda duk wanda yagansu yasan ba'a amfani dasu wajen taka ƙasa.


______Ƙarbar cup din tayi a hankali hannunta yana rawa,dan shi kansa hannun ba karfin sa ɗaya da sauran hanayen mutane masu lafiya ba,saidai duk da haka sunfi kafafun ta ƙarfi,tunda su takan iya amfani dasu wajen karbar abu marar ƙarfi sosai.

Bakinta takai ƙurbanta biyu ta sauke tana shirin ajiyewa,wani kallo inna asabe tayi mata wanda yasakata maida kofin bakinta tana ɗan cuna baki alamun anyi mata dole,itama Asaben murmushi tayi kafin ta mika mata cincin din shima.

Bayan ta gama ne har ta dauke tiren zata fita Hauwa'u ta ja hannunta ta baya,juyowa inna Asabe tayi dan ganin shin mai kuma take buƙata,wani ɗan card Hawwer ta daga an rubuta thank you a jiki take nunawa inna Asabe tareda ƙadashi tana yi mata murmushi.

Faɗaɗa dariyarta inna Asabe tayi tareda cewa,

"Ayyah ƴar nan banda abunki ai kinsan mukan boko sai a hankali,bansan abinda aka rubuta a jikin paper taki ba amma nasan rubutune mai nuna abinda yake zuciyarki,kisani inayi miki komai ne badan ki biyani ba jiddah saidan ɗa na kowane,sannan irin mutuncin da iyayenki sukayi mini bazan taba mantawa dashi ba a faɗin zuciyata,tsawon rayuwata zan kyautata miki Hauwa matuƙar inada ikonyi kuma ina numgashi,fatana da burina shine Allah ya kawo miki canji a rayuwarki,Allah ya dubi rayuwarki kar ya barki a wannan ƙangin wanda yafi bauta ciwo,ya kawo miki wani haske wanda zaki bishi zuwa wani mataki a rayuwarki kema,ya sawƙaƙa miki hanyarki jiddah ya dubi maraicinki..........."

Kuka inna Asabe ta fara wanda hakan yasaka ta barin dakin da sauri tana share kwallar da ta maƙale a gefen idanunta.


Kallon bayan inna Asabe Jiddah tayi wacce ta fita yanzu,duk da koyaushe cikin koyar yadda zata dunga boye emotion ɗinta a zuciya takeyi,amma duk da haka saida maganar inna Asabe ta dasu a cikin zuciyarta tareda tonowa bakin memoryn da ta binne a cikin zuciyarta,wanda hakan yasata dole komawa da baya zuwa waiwayen abinda ya faru a cikin rayuwarta shekaru sha uku da suka wuce,wasu wanda ta sanni da wayonta bai fi na shekara tara a baya,saidai duk da haka bata ƙaunar duk abinda zai sa tasake ganin wannan lokacin a rayuwarta,saidai me duk da haka abinda ya farun shine yake kuma faruwa,sannan bata cire tsammani ba kan cewa shine zai cigaba da faruwa matukar ba ikon Allah ne yayi tasiri a rayuwarta ba.

To amma tambayar anan shine yaushe wannan lokacin zaixo,wanene zai san inda take har yazo ya cireta a cikin wanann rayuwar,tunda take da wayonta bata taba taka filin kofar gidansu ba,sannan haka babu wanda yasan da rayuwarta a fadin duniya idan ka dauke mutanen da suke cikin gidansu.


Hawayene yafara zirarowa daga idonta,wanann lokacin kam kukanta har sauti yafara bayarwa tana jan zuciya ɗaya bayan ɗaya...................😥.


    Yanzune nafara  dasa sabon littafi mai suna WATA SAKAYYAR!!!,labarin inshaalllah yana da tsayi saboda abubuwan dayake kunshe a ciki suna da matuƙar yawa,sannan inshallah zanyi kokarin saka abubuwan masu amfanarwa inshaallah,kawai dai haɗin kanku nake bukata.

    

     *Daga Alkalamin* *Nusaiba Alkamawa*  ne.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post