Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 2 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 2 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 2 - Novels Elite

*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*


   *PROFICIENT WRITER ASSOCIATION*

_Kokarin azawa akan tafarki,shi ne abu mafi muhimmanci da yakamata marubuta su kware akai,mu proficient writers association za mu yada wannan manufa._


 👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽😭😭😭😭😭😭 *😭*WATA SAKAYYAR....*

             (Sai a Lahira)

* 👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽

  Nusaiba Alkamawa                  PAID BOOK

free page


••••{2}

Jiddah point of view


Komawa nayi na kwanta da baya, akan gadon ina kallon cilin ɗin ɗakin wanda dama hakan yakasance kaman ɗabi'a ta ce,musamman idan yakasance ina bukatar yin tunani.


Shiru nayi da tunani da kuma sakin dogon numfashi domin bawa gangar jikina damar yin relax akan gadon,saboda fitarwa gajiyar da na ɗauka na yini guda ina wheel chair.

Kunnuwana shiru sukayi ba abinda suke ji sai kukan ƙwarin da suke yin ƙara lokacin da aka ɗauke ruwa da damina,da kuma sauran yayyafar da take sauƙa a hankali,wacce take bada alamar ruwa yagama sauka.


Wani kalar nau'in tunanin ne ya bugo cikin birnin kwakwalwarta,yanzu fah duk fadin gidannan da kuma yawan ɗakunnan sa ammma bani  da kason ko daya sai quarters kawai,babu wani ɗan adam mai numfashi a kusan wajen sai ni kadai.

    ***           *****       *****


A daidai tacciyar rayuwa wacce take cike da farin ciki gameda walwala ,akan haifar yaro ko yarinya ya faɗo duniya cikin hanneyen mutane biyu wanda yafi soyuwa a ransu fiyeda kowa,wato uwa da uba.

Sannan wani abin burgewar shine jinjiri kan zuwa da kukansa na farko da kuma koshasshiyar lafiya,nan zakaga wani ma yana murna bare kuma inaga wanda kaine tamkar xinare mai haskakawa a cikin idonsu?.

Amma idan yaro yazo duniya cikin wani hali na rashin lafiya anya kuwa kawai wanda ya kaisu damuwa a duniyar nan?!!!!

Ni Hauwa Abdullahi Alkamawa laƙabin suna Jiddah .

Nazo duniya a hannun iyayena sanann na samu wannan soyayyar da kowane yaro yake samu a wajen wannan mutane biyu masu daraja,abin tambayar ɗaya shine shin ni na basu farin cikin da yara ke bawa iyayensu kuwa?,anya maimakon basu farinciki ni ba nasu farincikin na ɗauke ba kuwa?.

 

 Nazo duniya da matsaloli guda biyu wanda suka kasance sun zamemin nakasu a cikin rayuwata,na farko ina da matsalar MUTENESS wanda shin an haifeni dashi ko kuma daga sama na samu ,wannan shine abinda bani da masaniya akai,hakan bai dameni sosai ba sai ta waje guda daya shine yanda zanyi magana mutane su gane mai nake nufi,sannan duk lokacin dana ga mutane suna magana na kan ji sha'awar hakan ta kamani,musamman ma yara kanana,sai nayi tunanin su Khan,sunji dadinsu,saboda suna iya magana kowa yagane kuma yayi musu abinda suke bukata.______Wannan disorder bata dameni ba kaman dayar,wacce bayan nakasunta har yau kuma ina fama da wahalar ta da kuma ciwonta.

Ita ce APLASTIC ANEMIA,karancin bargon kashi(bone marrow),abubuwa daya wa bana iya irin wanda mutane sukeyi,musamman ma tafiya,sannan kuma ga uwa uba yawan cututtuka irin su infection din sanyi da kuma saurin kamuwa da kananan cututtuka.

Tun ina yarinya abinda iyayena suke tsoron ya tabani shine ruwan sama,sannan basa barni na fita waje,a lokacin ina yarinya nayi zaton dan suna kunyar ace yar su tana keken guragune,sai daga baya bayan na rasasu a duniyata na gano cewa ashe suna gudun kada nasan abinda yake wajen duniya ne,musamman dana kasance tamkar tangaran wajen fashewa,(fragile).Su din mutanene da suka nuna min so duk da cewa ban karesu da komai ba sai wahala da tashin hankali a rayuwarsu.

Sun ki nunamin duniya saboda abinda yake cikinta,basu san cewa mutanen da suke gudu sune wanda suka mutu suka barni dasu,abinda suke yimin ko wanda yake ba ahalina ba bayamin irinsa.


Hawayen dayake gangarowa daga kan fuskata nasaka hannu na share,kafin na dauke idona daga kallon cilin din danake yi najuya domin sauka daga kan gadon saboda kiran sallah da akeyi na magriba.

Kujerata na dauko karama wacce zan iya yawo da ita a cikin daki mai tayoyi.


Hawa nayi na tura zuwa bandakin dayake dakin,buta na dauka na yi alwala kafin na fito na tada sallah.


Na Dade akan sallayar ina addu'a,wata ma bansan mai nake fada ba,saboda ina da abin fada sosai har vansan abinda zan fara roko daga farko ba,daya daga cikin burina ina neman canji a wanann rayuwar,nasan babu wanda zayyimin magani saboda a duniyar nan wazai iya yimin maganin irin wannan cutar mai matukar tsadar magani?,hmmm.

Rabona da zuwa asibiti tun lokacin da iyayena sukayi kwana arba'in da mutuwa,shima nasan dan mutuwar na kan sabonta ne.______Likitoci sun tabbatar cewa rashin lafiyata na Aplastic Anemia tana kan stage din warkewa,saidai tundaga ranar babu wanda ya sake maganar zuwa asibiti bare kuma fara dorani kan magani.

Nima ban saka hakan a raina ba dannasan babu wanda zai dubeni akan hakan,na bar komai ga ubangijina ina jiran ikonsa akaina,komin dare zan jure ciwon danake ciki har zuwa ranar da ajalina zai riskeni na bar wannan duniyar.

Da haka na kokarta na tashi na hau kan gadon dan ma katifa ce batada tsayi,nasan yanzu tashi na tsaya ma yana min wuya sosai,idan har ban shiga ruwa ba kuma na ci abinci mai gina jiki har bandaki nake zuwa da kafafuna,duk da suna rawa amma yafidai yin komai akan kujerar kaddarar tawa.


Jan numfashi nake a hankali har bacci barawo yayi gaba dani,sauƙinta ma ciwon ya lafa,saboda maganin dana sha.WAIWAYE ADON TAFIYA..............


Hafsat salisu bunu haifaffiyar Jihar bauchi saidai garin mahaifinta ne ba kuma garin data kasance suna zaune ba.Alhaji Abdullahi muhd Alkamawa, ya gamu da mahaifiyar Jiddah a lokacin dayake koyarwa a makarantarsu ta secondary lokacin yana service a wajen.


Hafsat macece da magana bata dame ta ba har wasu ma suke cewa ko tanada matsalar magana,saidai abinda basu saniba shine haka halinta yake,in ma da akwai wani disorder to ta haɗune da hali.


Hafsat da aka fi saninta da Hala tana da kanne guda biyu wanda suke tagwayene mace da namiji.

Ibrahim da kuma shafa'atu ,wanda shi ake kiransa da barade ,ita kuma shafa'atu ana kiranta da sunan ta.


Kasancewar Hala ta fisu da kusan shekara biyar saboda tsaikon haihuwa da mahaifiyarsu ta samu,sai ya zamana koyaushe ita ke kulada su,sannan saboda tazarar tsakaninsu basa zama suyi hira saidai su a tsakaninsu.


Kawar Hala ɗayace fateema ,itama ba wani surutu suke tareba,saidai idan ta gama yi mata zance tace uhm uhmuhm,duk da Fateema  tana da surutu amma tasan yanda take hakuri da halin Hala da kuma yanayin zama da ita.Rayuwar Hala tafara sanjawa ne lokacin da zuciyarta tafara fadawa wani sabon abu wai shi soyayya,da farkon bata fara gane wani hali take ciki ba saboda batada experience akai sannan ba shiga cikin kawaye take ba ballan tana tasan mai take ciki.


To haka shi ma a bangarensa saida sukayi dan ja inja da mahaifinsa wanda yake rike da kamfanin Alkamawa ,da suke sarrafa man shafawa da kuma yoghurt, Abdullahi yayi karatunsa a bangaren engineering maimakon yin karatu a bangaren Food microbiology,hakan shi yafara kawo sabani tsakanin sa da mahaifinsa.


Hakan bai damu Abdullahi ba na nuna banbancin dayake nunawa a tsakaninsa da sauran yan uwansa,saboda ya yarda da cewa baka iya achieve a rayuwa idan abin baya cikin ranka.


Sannan tun daga haihuwarka zuwa komawarka wajen ubangijinka abinda Allah ya kaddara maka shine zaka samu.


Sannan in Allah ya daga maka babu mai durkushe maka.


Cikin ikon Allah kuwa haka ya gama karatunsa har ta kaishi ga yin service a garin su Hala wato ainihin cikin bauchi .


Lokacin da Abdullahi ya dora idonsa a kan Hala bai tsaya bata lokaci ba ya tuntubi iyayenta akan maganar neman aurenta.


Da farko mahaifin Hala bai nuna amincewarsa saboda yanda iyayensa suke da kudi,shikuma basuda kudi sai rufin asiri. Saidai aure nufine na Allah musamman ma sha'ani na aure,sannan kuma duba da yanda ita ma Halah 

 tana son Abdullahi sosai,gashi kuma yarone na kirki na gari da kowanne uba zai so hada jini dashi.

Mahaifin Hala ya amince da auren yayinda shima mahaifin Abdallah ya yi na'am da zancen,saboda ya yaba da dattako irin na gidan su Hala .___Inda aka samu matsala shine bangaren mahaifiyar Abdullahi ,fafur ta nuna hakan bai yi mata ba saboda tana son ya auri yar kanwarta ba wata bare ba.

Saboda tun kakanninsu da iyaye ake hadin dangi a gidan,sai yanzu karon farko a kansa zai fara kawomusu bare cikin dangi.


Tayi iya kokarinta wajen hana auren,amma saboda bata da karfin iko irinna Alhaji Alkamawa ,sai ya zamana cewa dole ta hakura da nata kudurin,musamamn ma daya kasance cewa shima kansa uban gayyar yafi son Halah akan rabiatu wacce mahaifiyarsa take son ya aura.Itama kanwarta hajiya bilkisu da taga cewa Abdullahi ba yar ta zai aura ba sai ta fara zuga hajiya innah wato mahaifiyar su Abdullahi ,dama zani ce ta tadda mujemu,haka ta hau ta zauna akan lamarin,duk da cewa sunyi shiru akan hidimar bikin amma hakan ba shi yake nuna cewa sun amince da zaman Hala lafiya a cikin danginsu ba na Alkamawa family.
"Ba ayi wani shiri sosai ba na karya da hidima,saboda mahaifin Hala bai yarda akawo masa komai gidansa ba bayan sadaki,a cewarsa duk abinda yake so yayi mata a gidan sa lokacin da ta zama mallakinsa.

Suma kuma dama familyn Abdullahi basu da burin yin komai a bikin,tunda ba zabin ransu yaje ya auro ba sai  zabinsa.

Ranar juma'a aka daura auren Hafsat salisu bunu  da kuma Abdullahi muhd Alkamawa  akan sadaki naira dubu ashiri ajalan ba lakadan ba,bisa kuma yarjejeniyar zai kula da ita da kuma bata hakkinta kaman yanda Shari'ar addinin musulunci ta koyar ayi.

A ranar ba'a wani bata lokaci ba aka dauki amarya zuwa gidan ta dake cikin garin kano , daga ita sai kawarta guda daya da kuma kanwar baban ta.

Tun daga shiga gidan hankalin babar Hala ya tashi lokacin da taga irin tarbar da uwar mijinnata tayi musu,haka suma matan yayunsa da kuma kannensa babu wanda yayi musu kallon arziki,abu daya suka samu shine nuna musu kofar Abdullahi din da akayi,daga nan kowa ya kama gabansa.


Tausayin Hafsat ne ya kama Fateema musamman yanda tasan halinta da rashin magana da kuma rike abu a rai,ta san sai wani ikon Allah taji dadin zama a gidan.

Musamman ma a wajen uwar gayyar wato hajiya innah.


Babu Laifi kam sashen da aka nuna musu yayi matukar yin kyau,gashi wajen da shuke _shuke da tsarin muhallin yan gayu.ko ina sabon fenti ne wanda jiya aka yishi sakamakon da yayi niyyar su zauna a gidansa amma kuma hajiya inna tace bazai yiyu ba sai taga halinta kar ta illata mata yaro.


 Tun yamma dada sa'a suka kawo Hafsat amma har suna kokarin kwantawa babu wanda ya lekosu koda ruwan sha ne,abin yayi matukar basu mamaki kowa sai uhm yake cewa.__________Misalin wajen karfe takwas suka ji ana kwankwasa kofar shigowa falon gidan,tashi Fateema tayi domin zuwa bude kofar falon,hada ido sukayi da Abdullahi wanda fuskar sa dauke da damuwa da kuma kuloli guda biyu a hannunsa.


Komawa tayi cikin dakin yayinda shima ya bita a baya suka isa dakin da suka kwana a gidan.


Gaishe da Dada sa'a yayi wanda duk sonta ta binne bacin ran dayake cikin ranta hakan abine daya faskara,da kyar ciki ciki ta amsa masa gaisuwar,shima jikinsa sanyi yayi matuka,kana ganin tashin hankalin dayake ciki akan fuskarsa.Dayake ance mata da miji sai Allah ,duk da bacin ran da itama take ciki lokacin da aka sharesu,amma ganin yanda damuwa ta kwanta a cikin ransa,ga kuma yanda laifin da ba nasa ba yake kokarin komawa kansa sai tausayinsa ya kamata sosai.


Haka dai cikin sanyin jiki ya ajiye abincin tareda yimusu sallama ya tafi.


Washagari da safe su Fateema suka fara shirin tafiya ita da Dada sa'a,babu irin kukan da Hafsat batayi ba,saidai ya zatayi aure yakin mata,haka suka rarrasheta da lallashi kafin ta hakura hakan ma kadan kadan.

Mota guda Abdullahi ya bawa driver ya daukesu har garin bauchi .

Aka bar Hala da angonta Abdullahi ,daga ita sai halinta sai kuma sabin mutanen da zatayi rayuwa dasu.


Yanxu aka fara wasan 🤪

  Karku manta daga aunty nusee ne.


No 09030567767


Plx Like, Comment and share.

    _________✍🏼

[29/01, 3:07 pm] Nusaiba Alkamawa:Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post