Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 10 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 10 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 10 - Novels Elite

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 

 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽

By

    Nusaiba Alkamawa

Wannan page din nakune, masoyan Wata SAKAYYAR sai alahira 🥰Ina alfahari daku bisa ga soyayyar da kuke nuna wa wannan littafin ngd

Free page 10

****

Hala ta cigaba da fuskantar kalubale a wajan su Hajiya inna, ga banbancin da ake nunawa tsakanin Jidda da kuma Al ameen Dan, da Hassana ta haifa, amma haka Hala taci gaba da hakuri bata nunawa Abdullahi, amma koda bata nuna masa yasan da wani abu da ake mata a cikin gidan, haka suka cigaba da kula da Jidda, gashi batada damar shiga cikin yara haka za'a fara tsokanar ta, ga arzikin Abdullahi kullum yana kara albarka har an fara fadan irin arzikinsa a cikin unguwa, ga katafaran ginin da yakeyi saboda yanaso ya tashi daga gidan ya koma wanda yake ginawa ko hankalin hala, dana Jidda zai kwanta, bakin ciki kuwa babu wanda Hassana bata nuna min ba, saboda tana ganin yanzu mijina yanata kara samun budi ga taimakon mabukata da takeyi, shima ameenu haka ya fara yiwa dan uwan nasa bakin ciki da budin da Allah yayi masa, duk kuwa da irin taimakon da Abdullahi yakeyi masa, har sabuwar mota da zata kai 8m Abdullahi ya siya masa, amma a kullum amenu bashida burin daya wuce yaga taya zai rabasa da dukiyar nan tasa,sbd anshiga tsakaninsu, ita kanta Hajiya Inna yanzu ta dan sakko ba kamar da ba.

Ansha gumurzu kafin Hajiya Inna ta yarda da tariyar da mukeso muyi a sabon gidan da Abdullahi ya gina mana, saida Abdullahi ya bata tushiyar bakin naira milyan biyu sannan ta amince da tariyar tasu, ranar ji nayi kamar na zuba ruwa a kasa nasha dan murna, koda mukaje gidan gidan ya hadu iya haduwa kamar wani gidan gwamna, ga komai sabo ne a gidan ya saka, haka dai ranar mukayi kwanan farin ciki, saidai matsalar jidda na yawan kuka, a haka dai muka cigaba da rayuwar mu a sabon gidan mu ba tare da kowa ya tsangwame koni ko jidda ba, haka na cigaba da kula da Jidda da kullum cikin rigima take, ranar muna zaune da daddare muna cin abinci, jidda na goye a baya na Abdullahi ya kalle ni cikin so da kauna da tarin tausayi na, "ina gani fa lokaci yayi da ya kamata in samo maki wacce zata tayaki kula da jidda da kuma wasu yan aikace_ aikace na cikin gidan nan" murmushi nayi nima ina kallon sa, "ina gani basai ka dauko kowa ba zan iya kula da ita","aa nasan ai kina kokari, kiyiwa  Inna Gaje mgn sai a kawo mana ko yar dattijuwa ce","tom shikkenan  zanyi mata mgn" ai kuwa washe gari na kira inna Gaje mukayi mgn, cikin sa'a kuwa tace akwai wacce take tunanin zata iya aikin insha Allah" ai kuwa a cikin kwana biyu aka kawo Asabe dattijuwa ce mai mutunci, haka take tayani muyi girki sannan mu kula da jidda, duk lokacin da aka gama abinci itace take  daukar na Garzali mai gadi ta kai masa.

Abinda ya kara tayar mana da Hankali shine, yanzu Jidda tanada shaikara bakwai amma har yanzo bata fara magana ba koda muka kaita asibiti sai aka sanar mana cewa, tanada matsala a makogwaranta shine ya hanata yin maga kuma ba lallai tayi mgn ba har abada, haka muka dawo gida jiki a sanyaye ashai bayan cutar rashin kwarin bargon kashi, tana da wata cutar ta rashin magana, a haka muka cigaba da kula da ita gashi ta isa a sakata a makaranta amma babu dama, inma mun sakata babu abinda zata iya koya ga tsokanarta da yara suke tayi, yanzu haka ma ko Garzali ya dauketa sun fita wani lokacin haka yara zasuta tsokanar ta, duk da wai tare da wani suke, inaga ita kadaice ai har dukanta yaran zasu iyayi tunda ba wani hankali ne dasu ba, haka dai Asabe da Garzali suka cigaba da taimaka min, duk da cewar Garzali mai gadi ne amma yanada kirki sosai, shiyasa Abdullahi yakeyi musu shatara ta arziki saboda kirkinsu da natsuwar su, ga kuma yadda suke nuna kulawa ga jidda da yadda suke sonta sabanin mutane da yawa da suke kyamar ta, wasuma har cewa suke mayya ce, wasu kuma suce aljana ce, izuwa lokacin Jidda ta fara fahimtar masoyanta da kuma makiyanta, saboda yanzo ta fara wayo da hankali, dan yanzu haka tanada shaikara goma sha daya a duniya.

A wajan iyayanta kawai take samun farin ciki sai wajan Asabe da kuma Garzali, kullum tana zaune akan keken guragu, sai kuma in tanajin bacci a kwantar da ita akan gado, ranar da sukaje gidan su Abdullahi sunsha wulakanci a wajan su Hajiya Inna da kuma Hassana harma da ameenu wanda ada baya musu, haka suka koma gida jiki a sanyaye jidda kuwa inka kalli fuskarta bazaka taba fahimtar yanayin da take ciki ba, na farin ciki ko akasin haka.

Shere fisabilillah.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post