Abban Sojoji Takun Karshe (book 3) - Novels Elite

Abban Sojoji Takun Karshe (book 3) - Novels Elite

Abban Sojoji Takun Karshe (book 3) - Novels Elite

_Game duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata  zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari sannan a kula wannan itace numbar wayata,Wasu suna ɗaukar numbar Wanda suka bani tallarsu kayansu suna kiransu a matsayin ni,bayan ni ga numbar dana bada nan itace numberta_

*Nagode sosai da addu'o'inku agare ni,da kuma uzurin da kukayimun,har zuwa wannan lokacin,Allah yabar zumunci a tsakaninmu daga nan har gidan aljanna💃*


*nace ba Masu satar littafi suna fitarwa ta bayan fage,mai yasa baku ƙarasa masu labarin ba?kuma kenan saida kuka jira ni?ae nayi tunanin cewa zaku ƙarasa masu labarin ne ashe dai sai anjira Boss*😂🤣😅


Bismillah


Kai tsaye sautin ringing ɗin wayar ya daki dodon kunnan Aunty babba dake baje saman gadonsu tana Bacci,a lokacin ko yatsanta bata jin xata iya motsawa saboda baccin dake a idanunta,yatsina fuska tayi alamar an takura mata,
   Ishaq dake tsaye agaban mirror yana gyara jikinshi ya ɗan gyara murya tare da cewa"Madam ki daure ki tashi ki ɗaga kiran nan!da alama kira ne mai muhimmanci tun ɗazu wayar ke ta ringing,"
  Uban tsoki Aunty babba ta buga tare da yunƙurawa daƙyar ta tashi daga zaune,jikinta na sanye da sleeping dress,riga da wando purple colour,
  Fuskar nan tayi suntum kamar wadda aka nausa,hannu takai tare da ɗaukar wayar dake ajiye saman bedside drawer,duba screen ɗin wayar tayi ganin sunan Hayaam ya bayyana yasa ta ƙara tamke fuska kamar ta shanu,ɗaga kiran tayi tare da kara wayar a kunnanta,rai a6ace tace"Meyasa kika kirani fitsararra!ko kin kira ne don ki ƙarasa yimun rashin kunyar taki don ubanki,"
  on the other hand hayam tace"haba aunty laila,ni harna manta da abunda ya faru atsakanin mu.....'tunkan hayaam ta ƙarasa maganar Aunty babba ta katse mata hanzarinta da cewa"Idan kin manta ae ni ban manta ba,Ki faɗamun uban miyasa kika kira ni,idan ba haka ba ni zan kashe wayar,



  Zuba mata ido Ishaq yayi yana kallonta aransa yace"Zagi kamar ƴar maguzawa,ko kunyata bata ji,sae faman ɗura ashar take yi,ni dae Allah ya haɗani da Guyaba,'
     cike da damuwa hayaam ta sassauta muryarta,tare da cewa"Aunty laila,na shiga uku,ko ince mun shiga uku,Akwai gagarumar matsala,Gaba daya duk wani plan ɗinmu ya tashi aiki,'
  Tunda Aunty babba taji hakan,gabanta ya faɗi rasss,ƙasa ƙasa da murya tayi tace"Hayaam meya faru?wata irin matsala kike magana akai?
  "Aunty laila,Ashe yarinyar nan mai aikin gidansu,ɗiyar uncle ɗinsu ce Abusufyan!!!!!" tamkar saukar aradu haka aunty babba taji maganar Hayaam aikuwa a matuƙar gigice ta miƙe tsaye tana cewa
  "kutumar uba!inji ubanwa!yaushe Abusufyan ya ta6a aure,Wlh ƙaryane koma wani ɗan ƙaniyar ne ya faɗi maki hakan babban maƙaryaci ne....'



  Gaba daya hankalin ishaq ya dawo kanta,maganar dayaji tana fadi ta tsaya mashi aranshi,
   "Wani abusufyan din kuke magana akai,"
  Firgit Aunty babba tayi tare da ware ido tana kallonshi sam ta manta da cewar yana acikin ɗakin,
  Hankali a matuƙar tashe ta miƙe tsaye da nufin ta fuce daga cikin ɗakin,Saboda tsabar ruɗu ta nufi hanyar shiga toilet,
  gyaran murya ishaq yayi mata tare da cewa"kada fa ki shiga toilet da waya a kunnanki,'
  A zabure ta juya ta kuma nufi wardrobe da alama ruɗu yasa ta manta hanyar fita daga ɗakin,zuba mata ido yayi yana mai mamakin irin kiɗimar da tayi,to ko lafiya?ya tambayi kansa,
   Bata ankara ba sae da goshinta ya bugi jikin wardrobe din kayan nasu,sannan ta gane inda ta dosa,Rai a6ace ta kama hanya ta fuce daga dakin,saukowa downstairs tayi ta miƙi hanyar wannan tsohon store ɗin data ta6a garƙame su hosana aciki,anan corridor ɗin ta tsaya tana sauraran Hayaam,
  "Wlh Aunty laila da gaske ne,Ni shaidace,Naji komai lokacin da Uncle ɗin nasu yake korama junaid bayani,bama haka ba Aunty azmee da kanta ta gasgata mun hakan,Babban abunda yafi rikitar dani Yaran fa triplet ne ashe,kuma dukkansu Mata ne kyawawan gaske,kamannin su sak iri ɗaya,Kuma kina kallonsu zaki gane cewa ƴa'ƴanshi ne......'
  Hannu ɗaya Aunty babba tasa ta dafe tsakiyar kanta,yayin da dayan hannun ke ruƙe da wayarta data kara a kunnanta,



  "Hayaam bazan ta6a yarda da zancenki ba,Taya hakan ma zata faru!mutumin da bai ta6a yin aure ba,Shi za'ace yana da ƴa'ƴa har ƴan uku!Cikin shege kenan ya ta6a yima wata harya same su!Ni ban yarda da kalamanki ba,Hayaam kinsan cewa babu kyau tsoratar da musulmi,Idan wasa kike mun ki daina!!!!!
6acin raine yasa hayaam ta kashe wayar 
  Fashewa da kuka tayi saboda ƙululun baƙin cikin daya tokare mata maƙoshinta,ga zuciyarta dake ta faman tafarfasa,Gaba daya bata jin daɗin jikinta,
  Zubama wayar ido Aunty babba tayi tana kallonta.


Dannan Download a kasa domin sauke littafin.

Download

Zaku iya yin comment da irin littafin da kukeso wadanda bamu da su ana, in Sha Allah zamu Nemo maku.

4 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

  1. Abban sojoji part 2 pls

    ReplyDelete
  2. Continuation please takun karshe abban sojoji

    ReplyDelete
  3. Allah ya qara basira sis yaushe za,a cigaba awajen daurin auren rafyat na tsaya

    ReplyDelete
  4. Aslm please 🙏🥺 sis when zakiyi cigaba

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post