Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 11 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 11 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 11 - Novels Elite

 👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 


 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)


👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽


By

            *Nusaiba Alkamawa*


Facebook, alkamawas glow 

 *Free page 11* 


*****

"hassana ta haifi yan biyu hassan da usaini, rabiatu kuwa tuni ta koma gidansu, sakamakon matsantawar mahaifinta da yayi akan ta koma gida, haka ta koma badon ranta yaso ba. 

Amman tace xuwan da xata karayi da babban shiri xataxo saita mallaki abdullahi kota wane hali. 

Shikuwa aminu yana nan yanajin haushin kanin nashi sbd arxikin da allah yabashi, matar sa hassana sai kara tunxira shi take. 

Hajiya inna Kuwa masifar ta, tayi sanyi sbd ciwo daya ciwo ta.


"Baba me gadi ne yake waya ya kebe guri daya da dukkan alamu Baya cikin nutsuwar shi . 

Horn ake ta yi masa Amman da dukkan alamu baijiba, da alhaji abdullahi yaji shuru, garxali baixo ya Bude masa gate ba, yace inaga yana wani uxurinne, cikin hanxari ya fito daga motar. 

Ya durfafi wajan Gate yasaka hannun yafara budewa, sannan yashiga da motor yayi parking a parking space, duk wannan budurin fa da ake baba mai gadi baisan anyi ba sbd maganar da ake masa, na wani makudan kudi Wanda bashi da su, kuma bashi da hanyar samun su, kwalla ce kawai take xuba acikin idanuwansa. 

Sallama alhaji yayi wa baba mai gadi Amman ina baima San anyi ba, har saida alhaji abdallah ya taboshi sannan firgigit ya dawo daga cikin hayyacinsa, ah alhaji sannu da dawowa bansan kadawo ba, Dan Allah kayahkuri yafada yana shirin durkusawa, saurin dagoshi abban jiddah yayi yace "haba garxali tashi mana da dukkan alamu kana cikin damuwa Dan haka ka gaggwauta fada min damuwartaka , shuru baba mai gadi yayi sbd maganar tana da mugun nauyi abakin sa, kamar Kuwa yagane yace" ahe inajinka karkaji shakkar gayamin,insha Allah idan ina da halin taimakonka xanyi idan kuma na addua ne xanbika da shi. 

Cikin xubda kwalla garxali yace, alhaji mahaifiya tace wllh bata da lfy shine da aka kaita asibiti aka ce saimun bada millions biyu da rabi, idan ba haka ba zamu iya rasata , yakarashe maganar yana kara xub da hawaye, "ya isa haka garxali dama sbd wannan ne yasa duk kashiga damuwa haka? nake ma taimakawa na waje ballantana kuma na cikin gidana, kasaka suturo maka da account number dinsu xan tura musu 3millions ,wani farin ciikine Mara misaltuwa ya mama ye , baba mai gadi, ya durkusa yana masa godiya. 

"alhaji nagode Allah yasaka da alkhairi, Allah yabawa hajiya inna lfy , yabawa jidda lfy ya rayata Allah yabaka duk abinda kakeso, tsugunnawa abban jidda yayi ya dago da baba maigadi yace, nagode da adduar ka, ai duk yiwa kaine, sannan kamanta baka fadi Abu daya ba, murmushi yayi yace menene alhaji? Kamanta baka fadi Allah yasa mucika da kyau da imani ba, alhaji Allah yasa mucika da kyau da imani, kuma Allah ya haskaka kabarinmu, yauwa garxali ko kaifa Amman Dan Allah kadaina kukan nan haka sannan kuma kashirya katafi ko kwana hudu kayi musu, Aa alhaji idan natafi kuma ai babu me tsoron gidannan, akwai Allah, Allah shixai bamu kariya. 

"Yana fadan Haka kawai ya juya yashiga cikin parlour, yatarar da jiddah tana wasa, nufar wajan ta yayi yadaga ta daga keken guragun da take ya Dora ta akan cinyarsa , ya shafa kanta cike da kaunar yar tasa, tsoka daya amiya, yace" jiddatul khairi kina nan kee kadai ina ummin taki, murmushi kawai tayi masa domin babu bakin yin magana, nuna masa kawai tayi da hannu ta nuna masa bedroom, inyeee yarinyata takusa Warkewa, yafada cikin jindadin fara warkewarta, kwalawa asabe mai aiki kira yayi aikuwa da saurin ta ta kara so, tana cewa alhaji gani, murmushi yayi mata yace yauwa Dan Allah asabe zama xakiyi ki kula da jiddah kafin na fito, naga anbarta it a kadai Dan Allah kadaina barinta ita kadai sbd banaso ta dunga shiga cikin damuwa, to alhaji xangyara insha Allah. 

Yana shiga Kuwa yana xama yaga sako yashigo wayarsa anturo masa da account number, Kiran garxali yayi ya tambayesa shikuma yace eh Shine, sannan ya katse wayar a take a nan yatura masa da millions uku, Kiran garxali ne yashigo wayarsa yana masa godiya, abban jidda yace Ai babu komai sannan ya katse wayar yashiga wanka,domin maman jiddah tana makwabta taje siyowa jidda wasu kaya da a kayi  order su.

____Bayan asabe ta kammala aikinta tafita waje domin dauko wani Abu, tahadu da baba garxali, yana hada kaya"aa garxali ina xuwa haka? Wlh xanje gidane mahaifiyata bata da lfy ne, ayya Allah yabata lpy yanxu sai kuma yaushe? Xanyi kwana hudu domin alhaji yace nayi kwana hudu na kula da mahaifiyata duk da Kuwa akwai kannena, asabe tace kai Allah yayiwa mutumin nan albarka akwaishi da adalci nima haka kwana ki fa yasiyawa iyayena gida da kuma kayan abinci kasan da haya ne, dakyar ma muke biyansa, nima kuma yabani kudi masu yawa yace na rike shi a hannuna sannan kuma idan ina da wasu bukatu na fada masa, murmushi garxali yayi yace ai kadan daga cikin alherinsa nima yanxu saida yabani kudade masu balain yawa Wanda kokaina idan aka siyar baxanyi kudi saba,  dashine xa a biya mata maganin, Allah sarki bawan Allah, Allah yabiya masa bukatunsa na Duniya Dana lahira haka dai sukaita masa adduoi kala _kala 

Haka suka cigaba da rayuwar su maidadi, suna kula da tilon yar tasu, suna kaita asibiti akai akai, cutar limoniyarma tafara yin sauki sbd ka idojin dasuke bi. 


 *Bayan wasu yan* *kwanaki* 

_____Yau mun tashi da shirin zuwa garin mu, sai murna nakeyi, amma kuma sai Abdullahi yace banda Jidda zamu tafi saboda matsala ta lalura da take dashi, "nifa ba wani abunne yasa banaso mu tafi da ita ba, kin fi kowa sanin irin lalurar da take dauke dashi, banaso muje da ita yara suna tsokanar ta, gara mu barta a gida wajan su Asabe sanin kanki ne Asabe zata kula da jidda kamar yadda zaki kula da ita, kuma fa a yau din zamuje mu kuma dawowa a yau","shikenan babu matsala,"Asabe ta kwala mata kira, "gani Hajiya","dama zamuje kauye ne yau zamu bar jidda a wajan ki, ki kula da ita kuma yauma zamu dawo insha Allah","to Hajiya Allah ya dawo daku lfy" da Ameen na amsa ina haurawa sama, bayan na shirya Jidda nima na shirya muka fito, Jidda sai kallo na take kamar akwai abinda takeson gaya min amma babu damar yin magana . durkusawa nayi a kusa da Jidda, "nace mu zamuje kauye amma yau zamu dawo kinji Allah yayi miki albarka, Allah ya albarkaci rayuwarki "kallonta kawai Jidda takeyi babu ko kiftawa, Abdullahi ne ya fito cikin shirinsa, shima durkusawa yayi a kusa da jidda da take zaune akan keken ta na guragu yanayi mata magana, cike da so da kauna, Hassana ce tayi sallama ta shigo, saida gabana ya fadi saboda ganinta danayi da sanyin safiyar nan, koda yake baza ace safiya ba tunda takwas ta wuce" mamaki da tsoron ganin Hassana ya kamani ita kanta Jidda boye fuskarta ta rikayi a jikin Abdullahi saboda ta gane Hassana itace wacce take zaginta tana ce mata mayya, tunda suka dawo gidan nan Hassana bata taba zuwa ba sai yau, gashi yanzo har sun kusa shaikara takwas da dawowa sabon gida, da fara'a akan fuskar Hassana ta fara gaishe su abinda ban taba gani ba kenan, "Abdullahi kai kuma ina zakaje naga ka shirya yau fa asabar babu aiki","zamuje kauye ne tare da Hala" dam Hassana taji gabanta ya fadi, "amma ai iya Hala akace zataje kauye mai yasa kai zakaje?" da ita kadai zata tafi, amma sai naga nima ya kamata naje na gaishe da iyayanta","Abdullahi dan Allah karka je"   da mamaki suke kallonta jin abinda tace, "yaushe na fara tambayar shawarar ki idan zanyi tafiya da zakice karna je" to waini a inama kikaji Hala zatayi tafiya" in'ina ta fara na rashin gaskiya chan wata dabara ya fado mata, "dama Hajiya Inna ce ta gaya min" banza yayi mata ya cigaba dayiwa jidda magana, mikewa yayi yaja hannun hala suka fara tafiya, juyowa nayi na kalli jidda sai kawai naji wasu Hawaye masu zafi sun taho min,nace mata Allah yakawo sauki cikin rayuwarki, yakawo haske cikinta, Abdullah man yace Allah yayi miki albarka hauwau jidda, sannan su kayi mata bye_ bye mota muka shiga muka fice daga gidan, da sauri Hassana ta fito tana bin motar da kallo bakin ciki fal zuciyarta batayi tunanin harda Abdullahi za'ayi tafiyar ba, itama motar ta tashiga ta fice daga gidan, "haba ke kuwa ki daina kuka , zuwa zamuyi fa mu dawo bawai shekara zamuyi ba, in kuma mu koma mu taho da jiddar to, indai hakan zaisa hankalinki ya kwanta","Aa kawai dai naga wanin irin kallo da take min ne, kamar akwai abinda takeson gaya min ne, naga sai motsa bakin takeyi amma ta kasa fadamin, gaba daya tausayin ta ya kamani" kiyi hakuri insha Allah zata samu lafiya kin manta abinda likita yace last month da muka kai ta?  yace fa ciwon rashin kwarin bargon kashinta yana matakin karshe na warkewa yana ma sa ran nan da wata biyu masu zuwa indai mun cigaba da kaita ganin likita zata iya fara taka kafarta tana tafiya kamar kowa","Allah yasa hakan" motar dayaga tayo kansu gadan_ gadan da gudun tsiya yaso ya taka birki amma birkin ya kwance yaki takuwa, Salati kawai suka farayi saboda yadda motar tayo kan tasu motar, kauuuuu! kakeji motar ta daki dayar mota, hada wannan mummunan accident ya faru gaba daya motar su Abdullahi tayi rugu rugu, da kyar aka samu aka zaro su, gaba daya jikinsu duk ya jike da jini, ko kafin a kaisu asibiti rai yarigada yayi halinsa.

Lokacin da labarin yasamu su Hajiya Inna sun shiga matsanan cin tashin hankali, haka suka garzayo asibiti sukayi cuku _cuku har suka samu aka basu gawarwakin da ko fuskar su ba'a ganewa saboda daga_ dagan da tayi, saboda hatsarin da sukayi ya munan ta, haka suka taho da gawar gida zuwa lokacin har dangin Hala sunzo gida ya cika sai koke_ koke ake tayi, Hassana ma tasha zunbulelen hijabinta tana share hawayen karya nan ko cikin ranta farin cike ne fal zuciyarta zasu mallaki dukiya, ita da mijinta da yayansu , Rabi'atu kuwa suma ta rinkayi saboda tashin hankali, aminu kuwa baka gane yanayin da yake ciki amma idanuwansa sun kada sunyi jajir, Jidda kuwa wani irin numfashi ta rika fitarwa idanuwanta suna kakkafewa dole sai asibiti aka wuce da ita gudun itama kar a rasata duk da babu wanda ya damu da ita, Asabe da Garzali ma sunji mutuwar nan kwarai da gaske,suma sunsha kuka. 

Haka aka shiryasu aka sallace su aka kaisu gidan su na gaskiya, haka aka cigaba da karbar gaisuwa har akayi sadakar bakwai, sai aranata takwas da rasuwar ne sannan aka sallamu Jidda daga asibity, iyayan Hala sunso su tafi da jidda kodan su cigaba da kula da ita amma Hajiya Inna ta shafawa idonta kwalli tace batasan zance ba,a bar mata jikarta domin ta dunga tunawa da danta mai kaunarta, haka suka tattara suka tafi badan ransu yaso ba, bayan wata daya da rasuwar lokacin basu fara nunawa Jidda komi ba suna dan kula da ita amma ba sosai ba, ranar da aminu yajewa Hajiya Inna da batun yanaso ya koma gidan late Abdullahi da zama saboda gidan babu kowa zaisa gidan ya lalace tunda babu mai kula dashi, da wannan yasa Hajiya inna ta amince suka koma gida, tunda Hassana taje gidan saita saka aka maida Jidda chan wajan da aka warewa yan aiki, yarinya da gidan ubanta amma tsabar zalinci sun kasa bata daki daya a ciki, saide a kaita chan baya wajan dakunan masu aiki.

Asibitin ma da ake kaita sai suka daina kaita ciwonta da yake a matakin warkewa sai gashi ta sanadiyar rashin kaita asibitin komi yazo ya kara tabarbarewa ciwon nata ya dawo danye shakaf, ga rashin kunya da dan gidan Hassana Al'amen yakeyi mata ga kiyayyar da aminu da matarsa Hassana suke nuna mata, amma bata iya magana saide tabi kowa da ido, Garzali da Asabe sune suka cigaba da kulawa da ita kuma sune suka maye mata gurbin iyayanta data rasa, saboda duk duniya a yanzo a wajan su kadai take ganin fara'a sannan kuma a lallashe ta, a kuma kula da ita.

Suma rashin nan ba karamin tabasu yayi ba, mahaifiyarsa Kuwa tasamu lpy ras. 

Ga wulakacin da aminu da hassana suke musu kai harda yayansu basu daukesu abakin komai ba, face baiwowinsu 

Shiyasa koda yaushe sai sunyiwa hafsat da Abdullah addua sunyi rashin su matuka. 

Back to story

Shere fisabilillah.

🤲 Ya Allah Dan girman mulkinka, Allah kabamu shugaba nagari Allah yaxaunar da garinmu da kasarmu lpy ameen dan shugaba

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post