Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 12 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 12 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 12 - Novels Elite

πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 

 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)

πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍🦽

By

            *Nusaiba Alkamawa*

 *Godiya* ~ta musamman gare ki πŸ‘‰Aisha~ baby (waleeda) ngd bisaga nuna ~soyayya ga wannan~ littafin, Allah yabar xuminci, wannan _shafin nakine kiyi_ ~yarda kika so da~ shi ~much love 

😘~ 

 *Free page 12* 

*****

Tashi tayi daga barcin da tatafi 

Ta Bude idanu, kadan domin baccin bai isheta ba. 

Tana kwance  taji ana kiran sallar isha, a hankali ta tashi zaune ta janyo kekenta ta hau, a bakin kofar bandakin ta sauka daga kan keken kafafuwanta na rawa haka da bin bango ta shiga bandakin bayan ta gama abinda zatayi ta fito ta hau kan keken nata ta sake turawa,  sallaya ta shinfida ta tayar da sallah, bayan ta idar ta koma kan gado ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya a haka bacci barawo yakara saceta duk da ciwon da kafarta takeyi mata, Asabe ce ta shigo da plate din abinci a hannunta, "yauwa jidda tashi kice abincin gashi nan na kawo maki" jin shiru yasa ta leka kyakykyawar, fuskar ta ganin idonta a rufe hakan ya tabbatar mata da bacci takeyi, komawa tayi da abincin. 

Tana kokarin fitowa daga madafar abincin saboda ta gama aikin da takeyi taga Garzali ya shigo,yace! "Asabe ya jikin Jiddar" murmushi tayi saboda yadda ya damu da Jidda yake kuma bata kulawa, ka kwantar da hankalinka da sauki harma ta samu yin bacci" ajiyar zuciya ya sauke yanayi wa Asabe saida safe ya juya ya tafi, da kallo ta bisa tana fadin, "Allah ya baka ladan wannan dawainiya da kakeyi da baiwar Allah nan da mune kadai muka zama gatanta a gidan duniyar nan, sai kuma Allah ubangijin talikai" dakin ta shiga tayi shimfida a kasa kusa da inda gadon da Jidda take kai, tun lokacin da aka dawo da Jidda bayan gidan wajan dakunan masu aikin gidan, Asabe ta daina kwana a dakinta ta dawo dakin da jidda take kwana, gudun wai kar ciwonta ya tashi cikin dare babu kowa a kusa da ita.

"Zaune suke suna dinner cike da farin ciki Hassana tana zuba musu abincin, Hassan da Usaini da kuma Al amen sai Daddy su amenu bayan sun gama cin abincin, yaran suka tafi suka kwanta babu ko sallar isha, zama Hassana tayi a kusa da mijin ta suna dan taba hira suna labarin duniya suna dariya, babu ruwansu da ko Jidda taci abincin ko bata ci ba, bayan sun gama abin da sukeyi suma suka wuce dakinsu suka kwanta. 


washe gari daya kasance weekend yaran gidan basuje makaranta ba sunata wasan su a filin gidan, koda su Jidda suka tashi sukayi sallar asuba bacci Jidda ta koma ita kuma Asabe ta wuce madafa dan dora abin karyawa, sai wajan sha daya na safe ta ta shi wanka ta shiga tayi tana fitowa ta saka kayan ta, bedside drower ta kalla taga Asabe ta aje mata abin karyawa, dauka tayi ta fara ci, "Asabe ce ta shigo tana fadin harkin tashi" daga mata kai tayi tana murmushi wanda inba Garzali ko Asaben ba babu mai ganin sa.

"jiya na kawo miki abincin ki, na tarar har kinyi bacci, ki daina yin bacci sai kinci abinci kinji kada ulcer ta kamaki kinji yar albarka" sake daga mata kai tayi a karo na biyu, bayan ta gama cin abincin ne ta rarrafo ta hau kan keken ta, "ina zakije kuma?" alama tayi mata da zataje waje ne, "nifa banason kije wajan nan su bata miki rai wllhi ko su rika zaginki" alama ta kuma yi mata da babu abinda zasuyi mata insha Allah, "to shikknan kije" haka ta tura keken nata ta fita badan ran Asabe yaso ba sai dan taga Jiddan nason fita ne, tana fita ta tarar dasu Aminu( Al amen) da yan biyu suna buga boll gefe taja ta tsaya tana kallon yadda suke wasan gwanin sha'awa, basu kula da zuwanta wajan ba saida boll dinsu tayo ta wajan da take zaune, Aminu ne ya nufo inda take fuskar nan a hade kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa,yace "kee! wai ba Mommy ta hanaki fitowa waje ba, ko so kike abokan mu suzo suce kee yar uwar muce, wllhi yau sai nasa an zane min kee ta yadda bazaki safe fitowa waje ba, nifa ko wannan shegiyar fuskar taki banaso ina gani a inda nake" in banda kaddara wai ace har kaninta data basa shekaru  wai shine yake gaya mata maganar daya gadama, bacin rai ko akasin haka ko kada bai bayyana akan fuskarta ba, fuskar ta nanan cike da annuri kamar yadda ta fito, maganganun sa baisa yanayinta ya sauya ba, "Hassan, Usaini, kuzo in sakaku wani aiki" da gudu kannan nasa suka rugo zuwa wajan da suke, "so nake ku daka min yarinyar nan" ai kuwa batare da wani tunani ba suka fara dukanta ta ko'ina, babu baki balle tayi ihun a kawo mata dauki saide hawayan daka ambaliya daga idonta zuwa kan kumatunta, janyota sukayi daga kan keken suka fado da ita kasa suka cigaba da dukanta harda su tattaka mata kafa da karfin gaske, rufe idanuwanta tayi saboda wani irin azababban radadi daya ratsata lokacin da suke taka mata kafafuwa, Garzali da fitowar sa daga daki kenan yaga abinda yake faruwa yayo kansu da gudu har yana tuntube, suna ganin ya nufo su suka ruga cikin gida da gudu,hajiya Hassana dake zaune akan kujera ta dora kafa daya kan daya tana kallo taga sun fado falo kamar daga sama, "kai lafiyan ku kuwa kuka shigomin falo haka?","wllhi Mommy Garzali mai gadi ne ya biyomu zai dake mu","zai dake ku kuma, to mai kukayi masa","babu abinda mukayi masa kawai dan mun doki Jidda kuma naga Mommy kece kikace in tayi mana abu mu ci ubanta da duka","kwarai kuwa ni na fada, fatan dai kun mata dokan da zata bi iyayan ta wajan da sukaje","mun dai doke ta sosai, dan ma wanchan mai gadin yazo ne ai da saimun kusa kasheta zamu kyale ta","Allah yayi muku albarka yanzu nasan nayi haihuwa, ku shiga dakin ku bari naje wajan wanchan tsinannan inji akan wane dalili zaina takurawa yarana yana mai gadi tsabar xagewa " tana gama fadin haka ta tashi fuuu kamar zata tashi sama tayo waje, tararwa tayi yana kokarin dora Jidda akan kekenta da bakinta sai jini yakeyi duk ya bata mata gaban riga, bakin ciki ya cika zuciyar Garzali wai mai yarinyar nan ta tarewa mutanan gidan nan ne da sukayi mata wannan muguwar tsanar haka kamar ba yar uwarsu ba,

 "kai Garzali mai yaran nan sukayi maka daka biyosu da gudu zaka dakesu, "Hajiya kalli fa abinda suka aikata wa jidda, fitowa nayi na tarar sun janyota daga kan keken nata sunata dukanta, dubi yadda suka fasa mata baki" dariya ta kece dashi, "aini naji haushi ma da iyakar baki suka fasa mata da basu babballa mata kafafuwa ba, kuma da kaketa tada jijiyoyin wuya maine tsakanin ka da yarinyar nan ne da har in an mata abu kake fusata kode kana rage zafine da ita bamu sani ba" jiyai kamar ta tsoka masa mashi a kirji ba tare daya tanka mata ba ya tura keken Jidda zuwa dakinta yabar hajiya Hassana tsaye a wajan tana sababi, kuka Asabe ta fashe dashi ganin irin dukan da sukayiwa Jidda gaba daya fuskarta ta kumbura, "dama saida na gaya miki kar kije amma ganin kina son fita shiyasa na kyale ki yanzu jibi irin abinda suka aikata maki, Allah ya isanki wllhi" Asabe ta fada tana shafa mata man zafi ajiki ko zai rage mata radadin da takeji, nunawa Asabe kafar ta tayi, "ciwo takeyi maki?" daga mata kai tayi, maganin ciwon kafar ta dauko ta bata.

Shere fisabilillah.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post