Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 6 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 6 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 6 - Novels Elite

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  😭😭😭😭😭😭 


 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽

By

            *Nusaiba Alkamawa*

Dedicated to my bloody sister *jiddah alkamawa* 🥰


Free page 6

****

Amma gaskiya nayi saken da harna bari yarinyar nan ta samu ciki, ta ayyana haka a cikin zuciyar ta tana kallon gadon da Hala take kai, da harta samu bacci saboda allurar da doctor yayi mata, "Hajiya zauna anan kemah bakida lafiya yakamata kemah Doctor ya dubaki" wani banzan kallo ta watsa masa, "gara ace lafiyar ne bani dashi ai, akan wannan mummunan labarin danaji" yana kokarin ya tambaye ta wane mummunan labari taji yaji Hala tana motsi, da sauri yaje wajan ta, "ruwa, ruwa" shine abinda yaji ta fada, da sauri ya bude fridge ya dauko mata ruwan ya bata, "kaii! Auta dayake haka take kiranshi dashi, kaja wannan banzar matar taka ku barmin daki tun kafin raina ya baci" yasan halin mahaifiyar sa sarai na kiyayyar da take nunawa Hala, amma bai dauka zata ganta a wannan halin amma taki tausaya mata, haka ya kama Hala suka fito daga dakin, amma duk da haka Hajiya inna, sai zazzaga masifa takeyi.

Rabi'atu na ganin fitarsu ta hayo saman, saboda tun marin da Abdullahi yayi mata take shakkar haduwa dashi, kusa da Hajiya inna ta zauna, "Hajiya lfy kuwa naji kinata fada ke kadai" hmm "ki bari kawai wacchan yar iskar yarinyar ce take da ciki" ido ta zazzaro, "Hajiya wai kina nufin Hala","to in ba ita ba wa kike tunanin ina nufi, ita nake nufi mana, yanzo Doctor ya aunata cikin harya kai wata biyu, mu bamu farga ba, yanzun ma da ba agabana abin ya faru ba da saide muji ta haihu, yanzu ma idan bamu dauki mataki ba saide muji labarin haihuwar ta","Hajiya karki damu bazamu taba bari hakan ta faru ba, inada wani magani na zubar da ciki shi zamu bata tasha nan dake cikin zai zube" da mamaki Hajiya ta kalli Rabi'atu jin tace tana da maganin zubar da ciki, "to amma ke maiya hadaki da maganin zubar da ciki?" kame- kame Rabi'atu ta fara na rashin gaskiya, "umm dama na wata kawata ne ta bani ajiya saboda inta aje mamanta ta gani to zata shiga matsala shine fa na ajiye mata","tom shikenn amma ki rabu da wannan kawarta ki, dan gaskiya ba kawar arziki bace, tunda har take iya zubar da cikin data samu bata hanyar aure ba","to shknn Hajiya","yanzo dai kije ki dauko min maganin" da to ta amsa tana mikewa dan daukowa Hajiya maganin,

Abinda Hajiya inna bata sani ba shine, maganin nan na Rabi'atu ne, ta zubar da ciki yafi sau biyar yanzu hakama mahaifarta ta samu matsala saboda maganin zubar da cikin da take sha, aminu ne ya shigo dakin, gaishe da Hajiya yayi amsa masa tayi tare da fadin, "ya kowa da kowa","kowa da kowa inafa lafiya wanchan matsiyaciyar dana ciki harna tsawon wata biyu","Hajiya akan wa kike magana ne","wace kuwa inba wacchan shegiyar ba, matar Auta ","Alhamdulillah Allah ya raba lfy, ya kuma bawa Hala lfy","ba Amin ba, Allah yasa ta mutu kowa ma ya huta","subhanallahi Hajiya matar danki ce fa yakamata ki rage wannan kiyayyar da kikeyi mata, ko babu komi gashi yanzu, zata haifi jika a gidan nan, kuma ni banga laifin yarinyar nan ba, naga tana girmamaki, kuma wllhi Hajiya ita wacce kikeso ya Abdullahi ya aura wllhi batada tarbiya ke kina zaune a gida bakisan wacece  Rabi'atu a waje ba shiyasa, kuma wllhi muddin ya rabu da Hala bazai taba samun yarinya mai hankali da tarbiya irinta ba","dalla tashi kabar wajan nan banzaye wadan da basu san ciwon kansu ba, ai daga kai har Auta ba hankali gare kuba, sam bakusan inda yake muku ciwo ba","shknn Hajiya Allah ya huci zuciyar ki, yana gama fadin hakan ya mike yabar dakin zuciyarsa na suya, ya rasa wana irin haline wannan na mahaifiyar sa, haka Hajiya taci gaba da zazzaga masifa har Rabi'atu ta kawo maganin.

Boye maganin tayi saboda in tace zata bata yanzu, in cikin ya samu matsala yaranta zasu zargeta saboda yadda ta nuna kiri kiri batason cikin, koda su Abdullahi suka koma bangaransu kwantar da Hala yayi sannan ya hado mata tea mai kauri, da kyar ya samu tasha sannan ya bata magani tasha sai faman lallabata yakeyi, bacci mai nauyi ne ya dauke ta, shi kuma tsura mata ido yayi yana sa mata albarka farin ciki fal zuciyar sa, Hala na dauke da gudan jinin sa, tsason sa, wani fitinannen son tane yaji yana ratsa masa jinin jiki da bargonsa, bayan kwana biyu jikin Hala ya warware ga kulawar da take samu a wajan mijinta, dan a kwana biyun nan ma daina fita office yayi dan kawai ya kula da abinson sa da baigen sa wato Hala, 

Mahaifiyar Hala ce zaune a kusa da baban Hala, "ni kuwa Alhaji ina ganin ya kamata naje na gano yarinyar nan, yau wata hudu da auranta amma ban taba zuwa na gano ta ba, shine nake ganin ya dace naje na gano ta" murmushi yayi a kullum yanason matarsa saboda tsananin hakurin ta, bata taba tmby sa zuwa gidan Hala ba sai yau, yasan kuwa tayi hakuri, "yaushe kikeson tfy","duk lokacin da kace","to shkn, ki shirya ranar asabar sai kuje keda Gaje, kanwar sa kenn, tunda kinga yau litinin kinga zuwa asabar na gama shirye- shiryen tafiyar taku" ya fada fuskar sa dauke da murmushi, "to Malam Allah ya kaimu","Ameen saiki aika a gayawa Gajen","insha Allahu yanzo ma zan aika a gaya mata"to ni bari na fita"a dawo lfy malam" da ameen ya amsa ya mike ya fita, yaro ta samu ta aikasa yaje ya gayawa Gajen, aiko da sakon yaje mata ta shiga farin ciki marar masaltuwa da har ya kasa boyuwa, dama Hala yar dakinta ce, ko babu komi zataje ta gano ta, haka suka fara shirye shiryen tafiya, ranar tafiya kawai suke jira.

Kwanci tashi babu wuya a wajan Allah, yau asabar tun asuba maman Hala take shirye shirye, karfe bakwai dai dai suka dauki hanya tare da tarin abin arzikin da mahaifinta ya siya mata, karfe sha biyu dai _dai suka isa gidan, suna shiga gidan yayi daidai da fitowar Rabi'atu cikin wata yar iskar shiga, tsayawa kallonsu takeyi har suka karaso inda take, "kai ku dakata wajan wa kukazo ne, daga ganin ku daga kungurin kauye kuke ko" Rabi'atu ta fada tana watsa musu banzan kallo, "yar nan wajan Hala mukazo, wannan kuma da kike gani mahaifiyar Hala ce" wata yar iskar dariya Rabi'atu ta kwashe da ita, "koda nace ashai kudin iyayen wacchan banzar ne" kee! wacece banzar karki kara cewa yar yayana banza, inba haka ba yanzo kiga yadda ake banzanci" Gaje ta fada tana huci, Rabi'atu zata sake magana Abdullahi ya fito daga bangaran su, da sauri ya nufo inda suke, yana zuwa ya zube a kasa yana kwasar gaisuwa, da mamakin yadda yake rawar jiki wajan gaidasu Rabi'atu take kallonsa babu ko kiftawa, "Mama kuzo mu shiga daga ciki" haka yayi gaba suka bisa a baya suka bar Rabi'atu anan wajan sake da baki, fasa fitar datayi niya tayi ta koma cikin gida a fusace, Hajiya! Hajiya!! haka ta rinka kwalawa Hajiya inna kira, "lfy kuwa Rabi'atu kike kwala min irin wannan kiran","wllhi Hajiya dangin Hala sun rigada sun sanye Abdullahi, yanzun nan sukazo kinga yadda yake rawar jiki kuwa akansu, ladabin danaga yayi musu ko ke da kika haifesa bayayi miki irin sa" a fusace Hajiya inna taja hunnun Rabi'atu sukayi part din Abdullahi tana fadin, "yau za'ayi ta ta kare"

Muna son jin ta bakin ku game da yadda wannan littafin ya kasance, me ya burgeki ko menene baya burgeki a wannan littafin.

Shere fisabilillah.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post