Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 5 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 5 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 4 - Novels Elite

 👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 


 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)


👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽


By

            *Nusaiba Alkamawa*
Dedicated to my bloody sister *jiddah alkamawa* 🥰

 _Free page 5 


*****

Wajan karfe 3 na dare suka isa gida, wanka sukayi sukabi lafiyar gado, basu suka farka ba sai wajan karfe goma na safe, brush Kawai sukayi suka fito falo domin su karya, babu ruwan su da sallah, dama sallar ba damunsu tayi ba, daining suka nufa domin suyi breakfest, bayan sun kammala, Hajiya inna tace, "yakamata fa muje mu dubo yarinyar nan, wata kilama ta haukace boye mana Abdullahi yayi" ta fada tana kallon maman Rabi'atu, "kuma fa hakane tashi muje" da wannan batu suka mike suka nufi part din Abdullahi, zuwa lokacin shi ya dade ma a office, koda suka shiga falon tarar wa sukayi tana shara, jiki na rawa Hala ta tsugunna har kasa tana gaishe su cike da ladabi.

Tsabar firgitar da sukayi na ganinta lafiya kasa amsa gaisuwar ta sukayi, maman Rabi'atu ce ma tayi karfin halin amsawa muryarta na rawa, hajiya inna, kuwa kasa motsi tayi, jiki na rawa suka fito daga part din, da kallo Hala ta bisu tana mamakin lfy kuwa, ganin yau basuyi mata abinda suka sababa, wato suci mata mutunci, haka ta cigaba da aikin ta, suna shiga falo Hajiya inna taja hannun maman Rabi'atu suka shiga daki, sannan ta sawa kofar key, "mai yasa boka na kan dutse zaiyi mana haka, cewa yayi fa zamu dawo mu tarar da ita a haukace amma gatanan lafiya lau, har shara ma takeyi","gaskiya ne amma ki kwantar da hankalin ki yaya , mu fara kiran boka muji ta bakinsa","to bari in kirasa muji" wayar ta dauka akan mudubi ta kira boka saida ta kusa katsewa sannan ya dauko, gaishe sa ta farayi, dakatar da ita yayi ta hanyar daka mata tsawa, "nasan abinda yasa kika kirani, to ki sani yarinyar nan ta rike addu'a da azkar da kuma karatun alkur'ani, dan hakan duk inda zakuje asiri bazai kama yarinyar nan ba, saboda tanada riko da addu'a" kit ta kashe wayar ba tare da ta jira jin abinda boka zai ce ba.

"Kina jin fa abinda boka yace" Hajiya inna ta fada tana kallon Maman Rabi'atu hankali a tashe, Hassana dake labe a bakin kofa da duk ta gama jin abinda suke cewa ta kwankwaso, a razane suke kallon kofar, "to waye yake kwankwasowa, Allah yasa baiji abinda muke cewa ba koma waye","Amin dai" kofar taje ta bude tana ganin hassana ce sai ta saki wata wawiyar ajiyar zuciya, "Hassana lfy kuwa","lfy lau Hajiya" ta fada tana murmushi, "naji abinda kuke tattaunawa, inada wani malami aikinsa kamar yankan wuka yake, idan kun amince saina kaiku wajan sa, kuga aiki da cikawa" cikin murna hajiya jummai tayi na'am da batun hassana, "yanzu yaushe zaki kaimu wajan sa","karki damu Hajiya basai kinje ba, kawai ki bayar da kudi saina kai masa na kuma fada masa aikin da zaiyi mana" cike da jin dadi Hajiya inna ta dauko kudi masu yawan gaske ta bawa Hassana, itama cike da murna ta fita tana fadin, "to Hajiya saina dawo","sai kin dawo" bayan Hassana ta fita Maman Rabi'atu ta kalli Hajiya inna , "anya kuwa yaya yarinyar nan ba yaudarar mu zatayi ba, kinga wani murmushi kuwa da takeyi","haba ke kuwa tasan halina sarai dan haka bazata taba tunanin yaudarata ba","Allah yasa ni bari na tafi gida nasan wanchan tsohon yana chan yana zuba idon gani na","to shknn kanwata saina kira ki" daga haka sukayi sallama ta tafi, ita kuwa kwanciya tayi akan makeken gadonta ranta fal farin ciki.

"Gaskiya sai yau na tabbatar Hajiya batada hankali, tana tunanin zanje na bawa wani banzan boka wadan nan makudan kudaden ne kawai dan yayi mata banzan aiki, nikam tsuntsu na samu daga sama gashishe" Hassana ta fada tana tuntsirewa da dariya, ajiya mai kyau tayiwa kudin sannan ta dauko jakarta ta fito ta shiga motar ta tabar gidan, sai yamma likis ta dawo, a daki ta samu Hajiya inna "Hajiya boka yace zamuga aiki da cikawa zuwa gobe","to Hassana Allah yasa, sai musa mata ido","to shknn hajiya bari na koma bangare na yaya aminu ya kusa dawowa" ,"tom shknn" fitowa Hassana tayi tana murmushin mugunta, "saiki ta zuba ido ai yar wahala"

Haka suka cigaba da zuwa wajan bokaye amma babu abinda ya samu Hala, Abdullahi sai kula yake da ita, ga wata shakuwa da ta shiga tsakanin su" gashi yanzu har sun kwashe wata hudu dayin aure, ta fanin su hajiya jummai babu abinda ya chanza na kyara da tsangwama da suke nunawa Hala, wata safiyar asabar bayan sun gama karyawa Abdullahi yacewa Hala ta sako hijjabin ta suje su gaida Hajiya, haka taje ta sako hijabin nata badan ranta yaso ba, amma hakan baisa ta nuna a fuskarta ba, saboda batasam mai zataje ta tarar a chan din ba, da sallama suka shiga falon, da sauri Rabi'atu ta taso ta rungumesa babu ko kunya a gaban hala, da karfi ya ture ta, tare da wanka mata mari, batare da yayi wata magana ba yaja hannun Hala suka haye sama, "wllhi tunda ya mare ni ta sanadiyar ki, saina dauki tsassauran mataki akanki zakiga kuma abinda zan maki" da sallama suka shiga dakin, amsa musu sallamar tayi babu yabo babu fallasa, kwanan farfesun kifi rike a hanunta tana ci, har kasa suka sugunna suna gaishe ta, da kyar ta amsa kamar wacce batason yin magana, kamshin kifin ne ya doki hancin Hala.


Amai taji yana taso mata, kafin tayi wani yunkuri ta fara kyala amai, a razane Hajiya inna take kallon Hala, "kee! badai ciki ne dake ba" Abdullahi ne yayi azamar riketa yana jera mata sannu, toilet din dakin ya shigar da ita ya wanke mata jiki da baki sannan ya fito da ita, lokaci daya harta jigata, kwantar da ita yayi akan gado sannan ya ciro wayarsa a aljiho ya kira family doctor dinsu, babu jimawa saiga Doctor yazo, lokacin da Doctor yazo har an gyara wajan da Hala ta bata, Hajiya Jummai kuwa ta kasa tsaye ta kasa zaune, koda likitan ya gama aune aunen sa ya fito fuskar sa cike da fara'a, "Abdullahi ina tayaka murna matar ka tana dauke da juna biyu na tsawon wata biyu" dam haka Hajiya inna taji kamar an soka mata mashi a kirjinta, wani irin hajijiya taji tana dibarta, luuu tayi zata fadi cikin zafin nama Abdullahi ya tarota yana tmby lfy kuwa.

Like

Shere

Comment.

3 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post