Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 9 - Novels Elite


Health College

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 9 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 9 - Novels Elite

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 


 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)


👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽


By

            *Nusaiba Alkamawa*




Dedicated to my bloody sister *jiddah alkamawa* 🥰

                  



 *Free page* 9





*****



Ranar da Hala ta cika kwana arba'in da haihuwa, Inna Gaje ta shirya zata tafi, "yanzu Inna bazaki bari sai gobe ba" ta fada idonta na ciccikowa da kwalla, saboda tunda Inna Gaje tazo tadan rage shiga damuwa da zaman kadaici idan Abdullahi ya tafi wajan aiki, "kiyi hakuri Hafsat shi zaman aure haka yake, gashi ma Allah ya albarkace ku da nana hauwa  Wata rana itace zatana daibe miki kewa, kuma ta zamanto abokiyar shawarar ki"  haka dai tayi mata yan nasihohi da suka sanya jikinta yayi sanyi, Haka suka hadawa Inna Gaje shatara na arziki, sannan Abdullahi ya bada mota aka maida ita har gida, amma cikin ranta cike take da tausayin Hala saboda ta fahimci babu jituwa tsakaninta da surikarta, tun safe Jidda take kuka gaba daya Hala ta kasa gane maike damun ta, da sauri naje na dauko ruwa na bata ko zata sha, haka na zuba ruwan a fida na bata amma duk da haka bata daina kukan ba, muna haka har abban Jidda ya dawo daga wajan aiki, "Hala lfy kuwa take kuka","wllhi nima ban sani ba tun dazu take wannan kukan, na goyata ma har ruwa na bata amma taki daina kukan, kuma taki shan nono","subhanallahi, kawota muga" karbarta yayi ya fara jijjigata amma yarinya taki yin shiru, kamar ana mintsilinta, ranar dai haka muka kwana ba muyi bacci ba, yadda mukaga rana haka mukaga dare jidda nata tsala kuka,  karfe takwas Abdullahi yace ta shirya suje asibiti, koda sukaje asibitin babban likita suka naimi su gani, bayan ya duba jidda ya dawo ya zauna akan kujera yayi yan rubuce rubuce, "yace a gaskiya yarinyar nan batada cikakkiyar lafiya, tana da matsala ta rashin kwarin bargon kashi" rushewa da kuka nayi maganar ta dake ni , "amma doctor da akwai maganin da za'a bata ta warke" ki daina kuka kinji insha Allah jidda zata samu lfy, Abdullahi ya fada cike da tausayin jidda, "zata samu lfy, zamu dorata akan magana insha Allah zata samu lfy" takardar maganin ya mikawa Abdullahi, karba yayi suka fito daga office din yana dauke da jidda a kafadar sa da har lokacin bata daina tsala kuka ba, haka sukaje suka siya maganin daya rubuta musu masu balain tsada , suna komawa gida aka bata, haka muka cigaba da kula da Jidda amma duk da haka kullum cikin rigima take, wasa_ wasa kwanaki sunata tafiya, gashi yanzu har Jidda ta shiga shaikara ta biyu, amma abinda ya fara tayar musu da hankali shine, Jidda bata iya tsayawa da kafafuwanta,  gashi tanata kara girma dan yanzu haka tanada shekaru uku, amma da zarar ta yunkura ta mike sai kafafuwan ta su fara kakkarwa saita fadi, haka dai rayuwar gidan taci gaba da tafiya ga tsangwama da Jidda take sha a gidan, duk da a lokacin ko zaginta akayi batasan abinda hakan yake nufi ba, gata shiru shiru batada magana sosai.







A bangaran   Hassana kuwa tanata shirye_ shiryen mugun nufinta akan Hala wacce ma batasan tanayi ba, fuska biyuce da Hassan tunda ta fahimci in tana sukar Hala ameenu ransa yana baci, kawai saita dawo tana nuna masa ai tanason Hala, hasalima ai kanwace a gareta ai duk sun zama daya, amma fa ta ciki na ciki, ta riga ta kudiri aniyar wllhi_ wllhi koda zata tafi tsurara saita kawar da Hala a doran duniya, itafa tun farko Abdullahi takeso amma kuma sai Abdullahi bai nuna yana sonta ba, sai shi kuma ameenu ya fito ya nuna mata soyayya, to gudun kartayi biyu babu saita amince da ameenu har Allah yasa sukayi aure, amma saita kudirci cewa zata daina son Abdullahi amma kuma bazata taba bari ya auri wata mace ba, to lokacin da akazo da zanchan auran Rabi'atu ta shiga cikin bakin ciki, to amma da Abdullahi yace bayason ta sai taji ranta yayi fari sol, don harta fara tunanin kawar da Rabi'atun, ananan ananan sai Abdullahi yazo da zanchan auran Hala, ta dauka Hajiya Inna bazata bari ya aure ta ba, amma sai gashi ya aureta har Allah ya albarkace su da kyaukyawar diya mace, yanzu haka tana nan tana shirye_ shiryen batar da Hala daga doran duniya.




Watarana kwasam Hassana ta samu ciki, sai alokacin Hajiya Inna tace sai yanzu zatayi jika, dan wacchan mayya ba jikata bace ba, haka dai akai tayiwa Hala gori a cikin gidan, haka zatai ta kuka, ga kiran yarta da mayya da sukeyi, itako Rabi'atu ma cewa tayi yar ruwa ce yarinyar nan, dan da zasu kaita  tafki a aje da gudu zata shige cikin ruwan wajan yan uwanta yan ruwa, haka Hala take shan gori a wajan mutanan gidan, saide ta rungume Jidda taita kuka ga halinda jidda take ciki kullum cikin rigima, kuma koda wasa bata taba gayawa Abdullahi irin cin mutuncin da ake mata ba gaba daya duk nabi na lalace ta rame, cikin hassana yanata kara girma, gashi ya shiga watan haihuwa, ranar saita tashi da nakuda lolacin ameenu bayanan Hajiya Inna da kanta ta kaita asibiti, bata dade tana nakuda ba ta haifi danta namiji, sai kiran ameenu kawai Hajiya inna tayi, albishir tayi masa aiko ya rasa inda zai saka kansa dan murna.






Hassana tasha tarairaiya a wajan Hajiya Inna, dan da kanta ma takeyi mata wanka, saboda itama kamar diyace a wajanta, a haka har ranar suna yaro yaci sunan Al ameen , anyi shagali sosai da sosai, koda Hala ta shiga gidan sunan sai fitowa tayi tana kuka saboda zaginta da dangin su Abdullahi da sukeyi, karku manta Hassana mafa yar uwar su Abdullahi ce, da mahaifiyar Hajiya Inna da mahaifiyar Maman Hassana uwarsu daya uban su daya, to shine fa akayi musu auran hadi.












Shere fisabilillah

1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post