Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 8 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 8 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 8 - Novels Elite

👩‍👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 


 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)


👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽


By

            *Nusaiba Alkamawa*


 Free page 8

Shiru _shiru suna ta kasa kunne amma basuji komai ba, daga karshe ma da Hajiya Inna ta kasa hakuri saita tura Rabi'atu taje ta dauko mata rahoto, amma mai tana zuwa ta tarar Abdullahi na bawa Hala abinci a baki, ita kuma sai shagwaba take zuba masa, da sauri ta baro bakin window din cike da takaici abinda ta gani, tana zuwa ta fara fadawa hajiya inna, "kinsan Allah Hajiya yarinyar chan ba mutum bace ba, duk abinda mukayi mata a banza yake tashi, yanzu haka gata chan tana zuba wa danki shagwaba shi kuma sai faman rarrashinta yakeyi" wani abune ya tasowa  Hajiya Inna me daci, ya tsaya mata a makogwaro, hartama rasa mai zatace, Haka dai suka cigaba da kulla makircin su, amma kuma babu abinda ya sameta.

A kwana a tashi babu wuya a wajan Allah, yanzu cikin Hala har ya shiga watan Haihuwa, haka zalika babu abinda ya sauya tsakanin ta dasu Hajiya Inna, wajan mijinta da yayan mijin ta kawai take jindadi, Abdullahi kuwa sai haukan siyo kayan jarirai yake, a kullum idan ya kalli Hala da cikin dake jikinta, sai yaji duk duniya yafi kowa morewa da mace ta gari, wata safiyar laraba Hala ta tashi da nakuda, inda Allah ya taimake ta ma Abdullahi bai fita aiki ba lokacin, wllhi dasai dai ta mutu dansu Hajiya inna abinda sukeso kenan, ba taimaka mata zasuyi ba, a gigice ya dauke ta ya nufi asibiti da ita, sai bayan an shiga da ita sannan ya samu nutsuwar kiransu Hajiya ya gaya musu, batare da tace komai ba tayi tsaki ta kashe wayar, da kallo ya bi wayar yana mamakin irin wannan kiyayya da mahaifiyar sa takeyiwa Hala, yayansa ya kira bugu biyu ya dauka, fada masa halin da ake ciki, tmby yayi wane asibiti ne? , yana gaya masa yace gashi nan zuwa, Hala tasha wahala sosai kafin Allah yasa ta haihu ta santalo santaleliyar yarta mai kama sak da ita,kyakkyawa tabugawa a mu jalla,wani abun mamakin yarinyar bata yi kuka, cikin kidima nurses din suka dake ta Amman batayi kukan ba, har saida akayi mata duka uku tukunna tayi kukan, karar kukan tane yasa hala tayi saurin Bude ido wanda da tausayin diyar tata da ake bugunta yasa ta runtse idanu, cikin farin ciki take kallon nurse din, gyara jaririyar akayi, itama ta gyara jikinta, sannan aka fito dasu zuwa dakin hutu, izuwa lokacin ameenu harya karaso, ana fadawa Abdullahi Hala ta sauka an samu mace, sujjada yayi yanawa Allah godiya da wannan kyauta daya ba

Shiga dakin sukayi, a kwance suka tarar da Hala, jaririyar na kwance a kusa da ita, cikin zumudi ya karasa bakin gadon ya dauki yarinyar yana kallon ta, yana jin wani irin sonta na shigarsa, ganin bashida niyar basa shima ya dauka yasa ameenu fadin, "in ka gama kallon ta muma a bamu mu dauke ta" dariya yayi yana sosa keya, mika masa jaririyar yayi cike da kunya, karbar ta yayi yana fadin "Masha Allah, Allah ya raya mana ita " Hala kuwa baccinta take sha batasan ma wainar da suke toyawa ba.

Kwanan su daya a asibiti aka sallame su,   a ranar Inna Gaje tazo gidan, saboda itace zatayi mata zaman wanka, Abdullahi yace bazataje gida zaman wanka ba, saide taje yawon arba'in, haka ta hakura badan ranta yaso ba saidan faranta wa mijin ta akan abinda yakeso, tunda akayi haihuwar su Hajiya Inna basu shigo sunga jaririyar ba, hakama Hassana, ita kuwa Rabi'atu bata ita akeyi bama, Abdullahi abin yayi masa ciwo sosai amma kuma babu yadda ya iya da mahaifiyar sa, ranar suna yarinya taci sunan hauwau Jidda, anyi shagali na gani na fada amma fa babu dangin Abdullahi ko daya, bayan kwana biyu dangin Hala suka tafi aka bar iya, Inna Gaje, bayan kwana goma Inna Gaje ta samu Hala a bedroom dinta, "Hala dama magana nakeso muyi dake","to inna inajin ki","wai mai yake faruwa tsakanin ki da dangin mijin ki, naga tunda nazo banga ko mutum daya daga cikin su sun shigo ba, haka ma ranar suna ko sirikar taki ma bata shigo ba, kuma naga gida daya kuke da ita, ameenu kadai naga yana shigowa lfy kuwa","babu komai Inna kawai dai kece baki fahimci lamarin ba, amma lafiya kalau nake zaune dasu" ta fada fuskarta cike da fara'a yin duniya Inna Gaje tayi da hala akan ta fada mata, amma Hala taki fada, haka ta rabu da ita badan ranta yaso ba, Abdullahi dake tsaye a bakin kofa tun lokacin da Inna Gaje ta fara tambayar ta, wani irin farin ciki yaji ya lullube sa, Tabbas Hala matar sirrice kuma matar rufin asirice, jiki babu kwari yabar bakin kofar tausayin Hala fal ransa.

Like

Shere

Comment

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post