A Rubuce Take (K'addarata) page 14 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 14 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 14 Hausa Novel - Novels Elite

H U G U M A

A RUBUCE TAKE

       (K'addarata)

Arewabooks:huguma

Page 14

           Ta tsakiyar mutane da suka cika a wajen 'yan kallo ya samu ya ratsa ya koma motarsa,yabar mutane suna ta tattauna maganar,da yawansu hakan da yayi ya sake burgesu saboda diban albarkar yaron tayi yawa,yan bani na iya kuma na ganin baiken hakan,suna ganin kamar yayi amfani da qarfin ikonsa ne.

        Abinda ya faru akan hanyar ya qarawa kansa zafi,ransa ya dinga sosuwa duk sanda ya tuna girman shekarun mutumin da abinda qaramin yaro yayi masa,a nutse yaci gaba da tuqinsa har ya shiga unguwar tasu,qofar gidansu yayi parking,yana shirin fita a motar sukaci kacibus da qanin mahaifinsa suka tsaya suna gaisawa,wannan yaja masa jinkirin shiga gidan,sai bayan la'asar sa wasu 'yan mintuna bayan sunyi sallar la'asar a masallacin qasan layinsu sannan suka taho tare da kawu hassan din,yanata masa godiyar uban gudunmawar daya bayar na auren diyar kawu hassan din,har suka iso gida,kawun ya shige gidansa dake jikin gidansu abbas din.

          Tun a harabar gidan ya fuskanci kamar gidan yau ba iya mutanen gidan bane kawai a cikinsa,muneera dake wanke alayyahu cikin famfon dake baiwa shukokin da suka qawata harabar gidan ruwa ta amsa sallamar tasa gami da gaidashi ya amsa mata,har yaa taka zuwa gaba sai ya tsaya cak ya waiwayo ga muneera

"Hajiya na ciki ne?"

"Eh sallah takeyi" fasa shigar yayi,saboda hayaniyar daya danji,a yanzun kuma ba abinda yake buqata sai zaman shuru,don haka ya juya akalarsa zuwa sitting room din baqi dake harabar gidan daga gefe

"Idan ta idar ki gaya mata na shigo,amma zan dan kwanta kadan"

"To uncle" ta amsa masa tana daukan kwandon alayyahunta tayi ciki,shi kuma ya murza key din daya gani a jiki ya bude falon ya shiga.

         Yasan tsaf falon yake,duk da ba shigarsa akeyi akai akai ba,babu inda hajiyarsa ke bari da qazanta cikin gidanta,koda kuwa ba'a amfani da wajen,bata lamutar datti ko qura,wannan yasa babu haufi ya nufi daya daga cikin kujerun Three sitter ake falon yayi kwanciyarsa,ya miqe bayansa sosai saman kujerar yana lumshe idanunsa hadi da sakin ajiyar zuciya,yanason baiwa kwanyarsu hutu,bayason tuna komai da zai dameshi.

          Minti kusan goma yana a haka,yanata kokawa da tunane tunanen dake kwanyarsa,saidai surutai da 'yan iface ifacen dake gilamawa kadan kadan ta wajen nadan damunsa lokaci bayan lokaci,bai wani dameshi da yawa ba,wannan ya sanya yaci gaba da barin idanuwansa a rufe.

          Gigitaccciyar qarar data cika harabar gidan ta sanyashi durowa daga saman kujerar ba tare daya shirya ba,muryar nada matuqar kaifi da zaqin da zata iya huda kunnuwan duk wanda ke wajen,zaman dirshan yayi saman kujerar yana rufe idanunsa jin yadda qarar taqi tsagaitawa,ya rintse idanunsa yana jin yadda kansa ke sara masa sanadiyyar qarar,tsaki yaja dabmugun qarfi ya kuma miqe a fusace ya nufi qofa yaje yaga wanda ke qarar kamar wanda ake cirewa rai.

        A hankali ya yaye labulen ranshi a bace idanuwansa a farfajiyar gidan yana son ganin wanne tashin hankalin ne haka yake faruwa,idanunsa suka sauka a kanta,a lokacin ta jima da fara tsalle tana runtuma ihu hadi hadi da hawaye face face saman fuskarta,tuni 'yar hular dake saman kanta tayi nata waje,gashinta da koda lafiya lau yake sabulewa daga jikin ribbom ya baje abinsa iska tana daukarsa.

          Idanunsa ya zube mata,yana qare mata kallo,me ya sanyata wannan tsallen a gigice?,kunama ce ta harbeta ko maciji ta gani?,saidai kunamar,don ya tabbatar cikin gidan nasu ba za'a samu maciji ba,sai ya rasa me ya kamata yayi,ihunta yana sake cika masa kunne,baikai qarshen tunaninsa ba hajiya ta iso wajen da hanzarinta ita da muneera,a rude take qoqarin kama widad tana tambayarsu nujood me ya sameta?,sai ya harde hannayensa a qirji,ya zauna a hankali saman hannun kujerar dake daura da qofar yana kallo da sauraren abinda yake faruwa


"Kyankyaso ne ya shigar mata riga" idanunsa ya lumshe yana jin wani haushinta yana cikashi,kyankyason takema wannan kamar wadda taga mutuwa?,bai bude idanun nasa ba yayi shuru yana sauraren muryar hajiya tana cewa


"Kyankyaso?,riga kuma?,garin yaya?"


"Musaddiq ne ya saka mata(qanin nujood dake binta)"

"Ashsha musaddiq baka kyauta ba" hajiya ta fada tana qoqarin kakkabe mata rigar.


        Hannu daya ya sanya ya sauke labulen,ya kuma tura qofar da qafa sannan ya koma saman kujerar ya kwanta kamar dazun yana sake jan tsaki,ko a ina hajiya ta samo su suka cikawa mutane gida da hayaniya?. Still idanuwansa suna rufe,yana jinta cikin sheshsheqar kuka tana gayama hajiyan yadda abun ya faru,ta yima musaddiq fada sosai sannan ta hada kansu suka wuce cikin gidan.


          Ana kiran sallar magariba ya wuce masallaci yayi sallah sannan ya shiga cikin gidan,zuwa sannan babu kowa daga hajiyan sai muneera


"A'ah,shigowar magariba kuma yau kayi abbas?"


"Ina nan tun sanda wannan tsanyar ke ihu" dan shuru tayi na sakanni,sai kuma ta saki murmushi


"Wai widad?,aikin musaddiq ne wallahi"


"Musaddiq din muhsin wai?,dama sune?"


"Sune,a nan hajjaa ke barinsu,idan ta taso daga makaranta take daukansu,widad kam ai bata da hayaniya ko kwaramniya,shaqiyancin musaddiq dinne,yasan yadda take tsoron kyankyason ya saka mata shi" kai ya jinjina kawai ba tare da yace komai ba,sai a sannan hankalin hajiya kuma ya dauku ga fuskarsa,ya akayi har ya shigo gidan tun yamma bai nemeta ba,fuskarsa ta nuna akwai damuwa tattare dashi


"Allah dai yasa lafiya" ta fada bayan sun gaisa,furzar da iska yayi daga bakinsa,ya motsa baki zaiyi magana ta datsi numfashinsa


  "Kada kacemin babu komai" shuru ya ratsa falon na wasu sakanni,sai ya buda baki a hankali yana gayama hajiyan zancan tafiyarsa kaduna da hafsat tayi tutsun ba zata je ba.


        Ran hajiyan ya dan tabu,tun ba yau ba tasan matsalar dake cikin gidanshi,ba yau ta fara gani da fuskanta ba,saidai batason shiga lamuran gidansa sam,hakanan a matsayinta na uwa bata da abinda zata masa illa addu'a da kuma bashi shawara na gari


"Kayi haquri ka tafin,kada ka matsa mata,duk sanda ka samu sarari ka dinga zuwa kana ganinsu,ta wani fannin tana da hanzarinta daya kamata a duba,ko don karatun mariya(mimi) da yanzu ta farashi kada ya samu tangarda,zama da iyali dan haquri ne,mahaifanku dukka haquri sukayi damu har zuwa sanda Allah ya rabamu,komai yayi farko kuma yana da qarshe" ajiyar zuciya ya saki,maganganun hajiyan sai suka sake kwantar masa da hankali da sanya masa nutsuwa,kalmominta masu tsada ne da baiwa zuciya da kuma ruhi nutsuwa,take yaji gaba daya dukka wani kwadayinsa na tafiya kaduna da hafsat din yakau a take


"Na gode hajiya" ya fada yana bude abincin data saka aka kawo masa,ya fara ci a hankali suna hira da hajiya,hirar da ako yaushe ita ke debe masa damuwa.


     Basu jima suna hirar ba babban yayansa ya shigo,wannan yaja hirar tasu,har yakai qarfe tara na dare,sai da zai tafi yace ya saukeshi a hanya,ya ajjiyeshin sannan ya wuce gida shima.


        Tun k'arfe takwas da rabi duka yaran sukayi bacci,ta kwashesu ta kaisu dakinsu ta kwantar dasu,ranta a jagule,kishi fal ranta,zuciya nata mata saqe kala daban daban kan inda ya tsaya din,don ba kasafai yake kaiwa dare haka a waje ba,koda zaikai din yana kiranta ya gaya mata zai kai dare din,tunda babu ta yadda aikinsu baya kamawa.


       Dakinta ta wuce bayan ta rage hasken falon,tanaso qwarai tayi wanka amma kuma tana gandar zuba ruwa a jikinta,saita zarme da zama gefan gadonta kawai taja wayarta ta fara chart.


        Batasan lokaci ya ja haka ba sai data ji qarar shigowar motarsa,ta sauke wayar tana duba lokaci,sai taci gaba da chart dinta,don tasan yawanci bai fiya dawowa shi kadai ba,kuma idan hakan ta kasance sai ya sallamesu kafin ya shigo cikin gidan.


           Duk da yasan babu lallai ya samu kowa a falon amma bai fasa yin sallama ba,ya dan bi falon da kallo,babu laifi,bai wani kacame can da yawa ba,duk da bai masa tsari yadda rai da zuciyarsa sukeso ba,kai tsaye dakin yaran ya wuce,ya tura qofa ya shiga,wutar dakin tana kunne,yabi yaran da kallo,ba alamun an musu wanka da zasu kwanta bare ayi maganar brush,kowanne cikinsu yana da kayan bacci qasa da kala goma goma,amma bazaice ya gansu dasu sau biyar ba,baima san inda take kaisu ba.


       Yadan jima a kansu yana musu addu'ar daya tabbatar bata musu ba,ya shafesu da ita,ya sake gyara musu kwanciyar ya lullubesu sannan ya kashe wutar dakin ya fito yaja musu qofar.


            Yana fitowa tana fitowa a nata dakin,kallon kallo sukayi a tsakaninsu,tanason ta karanci har yanzu ranshi na abace ne ko ya haqura?,duk da ba yau suka saba irin wannan ba,yayin da shi kuma yake kallon dressing din jikinta,kayan daya fita ya barta ne dasu,wanda tun safe suke jikinta,duk da yalwar suturu da take dasu masu tsada da kyan gaske,to amma fa idan ka gansu a jikinta wani babban sha'ani ya tashi da zata shiga dangi ko qawaye tayi bajinta


"Sannu da zuwa" ta fada tana dan basarwa"


"Yauwa,ya gida ya yaran?"


"Alhmdlh" ta amsa masa tana mamaki,a yadda ya fita bata taba kawo saukarsa a nan kusa ba,amma sai taga kamar babu abinda ya faru


"Anan zaka ci abincin naka?" Ta tambayeshi sanda taga yana takawa yana barin wajen


"Zan danyi wanka,kamar nan da minti goma ki kawomin sashena" dan yatsina fuska tayi can qasan ranta tana mita,bayan wahalar girkin da tasha kuma sai ya sanyata wahalar diban cooler din abinci ta bishi dasu?,me yasa bazai zauna a nan yaci ba?,bata amsa masa ba har ya fice,sai ta juya ta koma daki abinta taci gaba da charting dinta.


           Da sauri ta miqe sanda taji agogi ya buga,minti goma sai data ninkasu wajen sau hudu,ta qara ya zama minti arba'in da kusan biyar ba tare data ankara ba,ta jefa wayar gefe ta miqe tana gyara daurin dankwalin atamfar dake kanta sannan ta fito tana gyara daurin zaninta daya dangale tana qoqarin daidaita tsahonsa.


            Har ya gama shirinsa tsaf ba ita ba alamunta,ba wani yunwa yake ji ba ya riga da ya take cikinsa wajen hajiyarsa,don haka bai wani damu ba can,dama kuma idan da sabo ya riga ya saba,sai ya dauko luggage dinsa ya fara shirya kayan da zai tafi kaduna dasu.


          Ya gama hadasu tsaf ya debo wasu takardu nasa yana dubawa,sai ya koma kan sofa dake dakin ya zauna yana dubawa cikin nutsuwar nan tasa.


RIGIJI GABJI!🔥🔥

          

      WANI KAYA SAI AMALE🔥🔥🔥


FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU🔥🔥


JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA


  'YAN BIYAR DIN NAN NE FA


SARAKAN LABARUN



NISHADI

CAKWAKIYA

GWAGWARMAYA

BARKWANCI

TSANTSAR DARASIN RAYUWA


TARE DA


ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI


SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI   TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!


KIN SHIRYA MADAM?


MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN  KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA


DAUD'AR GORA Billynabdul


KI KULANI Missxoxo


IDON NERA Mamuhghee


RUMBUN K'AYA hafsat rano


A RUBUCE TAKE Huguma


ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number


09033181070


MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU


09166221261


Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe🙏🏾🙏🏾

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post