A Rubuce Take (K'addarata) page 22 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 22 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 22 Hausa Novel - Novels Elite

H U G U M A

A RUBUCE TAKE

     (K'addarata)

Page 22

Nujood da widad dake tahowa yake nuna masa,baiji abinda yace ba,yadai ci gaba da kallonsu,suna sarqafe da hannun juna,widad din tana jin gabanta na faduwa ne gami da sanyin jiki haka kawai,yayin da nujood ke tsokanarta,har ta daga qafa zata dan bi nujood din da gudu sai kuma ta tuna taga qofar setting room din a bude,wannan yasa takai idanunta ciki,bata hango wadanda ke ciki tar,saidai ta tabbatar suna iya kallonsu.

          Da sallama suka shigo,suraj ne ya amsa musu fuskarsa da murmushi,nujood din na riqe da hannun widad suka qarasa cikin falon.


          Nujood dince ta fara gaida abbas,fuskarsa kadaram kadaham ya amsa,already ta san halinsa,bai fiya fara'a ba don haka bata damu ba,ta maida akalar gaisuwar ta ga suraj


"Lafiya lau,ya karatu?" Ya amsa mata cikin fara'a da murmushi


"Alhmdlh" tuna abinda hajjaa tace da ita ya sanyata miqewa


"Saikin shigo" ta fada tana duban widad cikin salo na tsokana,wanda iya ita da ita ne kawai zasu fahimta.


        Maganar nujood din taja hankalin abbas harma da suraj,tunani iri daya ya darsu a ransu lokaci guda,kowanne dubanta yake,abinda ya sanyata taji kamar an aza mata wani nauyi,gaba daya ta jita kamar a daure,kallon da suke mata yana neman daburtata,tana takure a gefe tsakanin kujeru tana wasa da gefan mayafinta,saita nannadeshi ta wareshi,suraj ya fuskanci hakan,don haka yayi gyaran murya,cikin murmushi kuma yace


"Barka da fitowa 'yammata" muryar suraj din saita ankarar da ita mantuwar da tayi bata gaidasu ba,don haka ta daga kai in ta fara gaida suraj din,cikin sakewa da fara'a da kuma kulawa ya amsa mata,sa'annan ta koma ga abbas,idanu saika hada,take taji ya fiya kwarjini da yawa,tunda suka shigo kuma ta karanci fuskarsa bashi da yawan fara'a,sannan koda bata dade a wajen ba alamu su nuna yana da yawan shuru shuru,don ko daya bataji muryarsa ba tun bayan daya amsa gaisuwar nujood


"Ina yini" ta fada tana kaida kanta,sai daya lumshe idanunsa ya bude sannan ya amsa mata,'yammatan daya fada sai abbas yaji kamar gatse ne yake masa,zaqin muryarta kuma me cike da zallar quruciya na zaga kwanyarsa


"Kada dai ya kasance ita hajiya ta zaba masa?,anya kuwa?" Kamar suraj yasan tambayar dake yawo a ransa kenan,sai ya tsinceshi yana cewa


"Allah yasa kece wadda hajiya tace muzo mu gani?" Kanta a qasa kawai ta gyada kanta,amsar data tilastawa abbas maida bayansa jikin kujera ya jinginar kawai idanunsa a lumshe.


         Yana iya jin yadda suraj keta janta da hira,tana amsa masa da qyar,muryarta cakude da kunya da kuma tsoro hadi da rashin sabo,tunda suraj din ya kalleshi ya karanci yanayinsa,wannan yasa ya karbe hirar abinsa ba tare daya sanyoshi ba,kamar ma shi abbas din ya yiwa rakiya.


        Jinnta take a takure kota ina,musaman idan ta waiwaya inda abbas din ke zaune abinsa ya sanya musu kunne


"Wannan abokin nasa,ko me yasa yazo dashi?" Abinda tayita fada kenan a ranta


"To widad mu zamu wuce,sai kuma wani jiqon?" Suraj ya fada yana duba agogonsa,maganar data yiwa widad din mugun dadi,don kafin ma ya miqe ita ta miqe tana cewa


"Ku gaida gida" saita kada kai abinta tayi hanyar ficewa,a lokacinne abbas ya bude manyan idanunsa yana binta da kallo


"Minti daya mana malama widad" suraj ya fada yana miqewa da ledar siyayyarsa a hannu yana yiwa abbas sign din ya tashi mana,sai ya kauda kai kamar bai gani ba,don haka ya taka ya isa inda take tsaye ya miqa mata ledar,cikin ransa yana fadin siyayyar kuwa ta dace da ita


"Ga wannan ko babu yawa" sai data dora idanunta kan abbas dake zaune daga bayan suraj din taga ita yake kalla sannan ta saka hannu ta karba gabanta na faduwa


"Na gode" ta fada tana ficewa a dakin da hanzari gabanta na wani irin faduwa.


          Da baya suraj ya dawo a hankali yana hararar abbas


"Duk alamar da nake maka ka tashi ka miqa mata don ta fuskanci ma waye abbas din a cikinmu amma kayi banza dani?"


"Wai kanason kacemin wajenta mukazo zancan?" Abbas din yayi tambayar hankalinsa kwance,sai haushi ya kama suraj,ya watsa masa harara


"Ban sani ba,next time dama idan zaka zo kada ka sake ka kirani,idan kazo kai kadai zaka gane wajen wa kazo din,tashi mu tafi,ka barni ni kadai sai zuba nake".


          Cikin mota gaba daya kansa ya kwance,me yasa hajiya ta dauko masa wannan?,ta yaya zai samu sauqi ko kulawa daga wajenta,kansa kada,gaskiya bazai iya sake zuwa zance ba,yaje yace mata me?.


           Yana jin suraj yana ta hirarsa amma bai saka baki ba,saboda gaba daya tunaninsa na ata wani waje,suffarta da kamanninta yaketa qoqarin maidowa idanunsa ya hadasu waje daya,babu qarya.....tana da kyau,ita din kyakkyawace ta gasken gaske,to ko kyawun hajiya ta gani?,sai ya sake girgiza kansa,yasan hajiyan,tasan abun qwarai sarai,bai gano me ta hango masa ba,amma ya tabbatar akwai abinda ta hanga din.


           Saida suraj ya ajjiyeshi a gida sannan shima ya wuce,abbas din ya masa ban gajiya da godiya


"Ai babu wannan tsakaninmu,kawai dai next time ka tafi kai kadai,saboda ka samu ku fahimci juna sosai, she's too young,dole sai kana janta a jiki da dabaru sannan zata saki jiki da kai,amma kuma ina me tabbatar maka indai aka samu shaquwa sabo da kusanci tsakaninka da ita,ina me tabbatar maka.....ina sake fadi ina mai tabbatar maka anan zaka fahimci komai basai an gaya maka ba" abinda suraj ya gaya masa kenan,wanda ya tsaya masa a rai,ya kasa fahimta kuma,da wannan maganar ya kwanta.


          Ita kuwa widad tana fitowa ta qara da dan gudu gudu,wani irin tsoro takeji da faduwar gaba sosai,don sai data tsaya a hanya tadan saisaita numfashinta tana dafe qirjinta da hannu,batasan me yasa batason wancan abokin nasa yana kallonta ba,to amma itafa wallahi mai wanna zubar maganar indai shine wanda uncle muhsin ya turo mata baiyi mata ba sam,saita tabe baki tana buda ledar daya bata,murmushi ya subuce mata da taga masoyiyar wato chocolate,saita zabura tayi cikin gidan tana qwalawa nujood kira.


          "Iyyeee,yammatan ummu,da alama ciniki ya fada tunda naga kin dade da yawa" hajjaa ta fada cikin salon tsokana tana murmushi,baki ta tura gaba tana ajjiyewa hajjaa ledar,kanta tsaye cike da zallar wautar quruciya tace


"Ni gaskiya indai wannan mai surutun ne bana sonsa" dariya nujood ta sheqe da ita,kafin tace komai hajjaan da uncle muhsin ya bata aikin tuntubar widad din idan ta dawo aji ta bakinta tace da ita cikin tattara hankalinta


"Saboda me?"


"Ya cika siranta,kuma ya fiya magana" wannan karon nujood dariya harda fadowa


"Bafa uncle abbas take fada ba,uncle suraj ne wallahi take nufi" sai hajjan itama ta saki dariya,tasan suraj din,duk da ba sosai ba,amma sai da nujood ta fada sannan ta tuna tabbas yana da kirki yana kuma da hira


"To alhamdulillah,indai hakane uncle abbas yayi kenan?" Ta fada tana kallon widad,yadda suka tsareta suna jiran amsarta ya bata kunya,saita dauki filo ta cusa fuskarta a ciki tana dariya cike da jin kunya


"Allah nidai hajjaa...."kunya ta sanyata tashi da gudu tayi dakinsu,sai suka bita da dariya,hajjaa taja chocolate din ta ajjiye da nufin idan uncle muhsin ya dawo ta nuna masa kafin su taba,ta kuma hada da gaya masa yadda sukayi da widad din.


KI KULANI miss xoxo


DAUDAR GORA Billynabdul


RUMBUN K'AYA hafsat rano


IDON NERA Mamuhghee


A RUBUCE TAKE huguma


sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so


masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin


0022419171

Maryam sani

Access bank


Saiku tura shaidar biya ga

+234 903 318 1070


Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan

09166221261


Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number

+227 96 09 67 63


Thanks for choosing us

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post