A Rubuce Take (K'addarata) page 31 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 31 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 31 Hausa Novel - Novels Elite

H U G U M A


A RUBUCE TAKE

       (K'addarata)

Arewabooks: Huguma


Page 31

         Maganar ta qonawa anty madina rai sosai ta kuma bata haushi,sannan sai taji.maganar kamar tayi girma a kunnen widad,tana girmama dukka faccalolin nata saboda dukkansu sun girmeta,ita kadaice qarama a cikinsu,shi yasa take musu kallon yayunta,don haka ta tattara wayar da kudin ba tare data gama saita wayar ba ta miqawa widad


"Kaiwa ummu ta gani ta adana miki,anjima zan shigo saina qarasa gyara miki" karban kayanta tayi ba tare data ma fahimci maganar me momma takeyi ba,ko baqincikin dake manne a ranta ba ta qara gaba cikin doki da zumudi.


        Da kallo momma ta bita sannan ta tabe baki


"Kinga yarinya sai rawar kai take,Allah yasa bai lasa mata zuma a baki ba ya barmu da....."


"Kai.....kai momma" anty madina ta fada tana kama kai fuskarta na nuna zallar rashin jin dadi

"Wannan maganganun sunyi girma da yawa fa"


"Wanne girma?,a wajen wa?, yarinyar da yanzu keda ita dukka matsayinku daya?,tabdijan,kina wasa da yaran yanzu,ni da rannan naji tana gaya musu zata tafi gidanta itama ta dinga girki irin nasu anty dina,tayi.bacci a gadonta?,to billhuwallazi kada ma kiyi mamaki idan akace miki ya gama lallatseta kafin ya tafi,ko ya fara buda hanyarsa"


"To haka muke fata,aiba haram bane,me zan baki?" Tayi mai gaba daya saboda maganar ta soma isarta


"Yauwa,mai zaki zuba mana,nawa ya qare gaba daya jiya suka zube shi a dambu" karbar robar tayi kawai ta miqe ta wuce store dinta dake manne a kitchen, cikin ranta tana tur da Ala wadai da irin wanna dabi:ar tata,banda abinta meye abun kishi da widad?,me za'a yiwa baqinciki akanta,yarinyar da bata da maraba da marainiya?,bata taka muku ba bata zubar muku ba amma kunbi kun qwarzabi kanku a kanta,batama san me suke ba,bata wani ganewa halinsu idan ba takurata sukayi da kyara ko hantara ba,shine zaka ga ranta ya baci saman fuskarta,ko kuma ta janye jiki daga gurin ba kuma zata dawo nan kusa ba. °°°°°°duk yadda take ta so ta tursasata kanta da zuciyarta.....ta tafi da zuciyar tata da ruhinta bisa doron shawarar da anty ummee ta dorata akai amma abun yana ta neman yaci tura,daga sanda labarin AN DAURA auren mijinta abbas sa wata gaba daya ta birkice,zuciyarta nata gaya mata anya mafita ce anty ummee ke bata?,ta tsaya kawai tayi masa hauka,tayi tawaye ta tada masa hankali har ya aje auren,wannan shine shawarar da mafi rinjayen sashe a zuciyarta ke bata,yayin da wani sashen yake gaya mata ta haqura taci gaba da tafiya a haka,saboda taga alfanun hakan,ta samu alkhairai masu yawa daga jikin abbas din.


          A ranar ita daya ce a gidan,ta tura yaran gidansu,ko wankan arziqi bata samu yi ba bare ta kintsa gidan,sai ta zauna dirshan,ta soma bin status din dukkan wanda tasan ya tafi kano daurin auren.


          Irin kyan da taga abbas yayi cikin dukka hotunan,da yadda taga fuskarsa shimfide da qayataccen murmushin nan nasa sake matuqar burgeta da daukar mata hankali sai taji ta sake birkicewa,saidai kaf hotunan bataga fuskar amaryar da taketa lalube ta gani ba.


          Jefa wayar tayi gefe tana rufe fuskarta da tafin hannunta,kuka ya subuce mata,abbas ya cuceta,kuma ko meye zaiyi mata bazai taba wanke kanshi ba,ba haka tasan abbas ba,bashi sa kallon mata ko kadan,bai shiga shirginsu kwata kwata,ya akayi wata mace ta gilmawa idanunsa har ya qyasa yaji yana son yin tarayya da ita?, macen ma yarinya qarama kamar yadda aketa bata labari?,ya zuwa yanzu ka ta fara tantamar anya yarinyar ce kamar yadda aka ce?,tasan tsarika da zabin abbas,ta yaya zai aura yarinya?.


         Wayar ta jawo da sauri ta cireta daga flight mode din data saka mata tun jiya,dai dai lokacin da saqon abbas ya fado wayarta bayan ya gaji da kiranta yana jin wayar a kashe,tsaki taja tayi fatali da saqon ta shiga duba number anty ummee.


          Bugu daya ta daga,kamar mai jiran kiran nata dama,kuka kawai ta saka mata,tayita yi har kudinta ya qare kiran ya katse,anty ummee daga can inda take zaune a falonta taja tsaki


"Kuka ma yanzu kika fara,kishiya wasace,shegen son abun duniya irin naki,inda kin bada dama 'yan uwanki sunzo gidan an dan zauna dake aida an debe miki wannan damuwar,amma don kada mutum yazo yaci abinci da nama kika hana kowa zuwa,kyaci takaicinki ke kadai" ta fada tana bin kiran nata daya katse.


"Anty ummee anya zan iya?,wallahi bakiji abinda nakeji a qirjina ba" ta fada cikin muryar kuka


"Ke dole ki daure fa,saboda ribar ciki tafi rashin ribar yawa,wannan ce kadai hanya guda daya da zaki zauna salamun salamun a gidan,kuma kowa yayi miki.biyayya ba tare daya shirya ba,wannan itace kadai hanyar da zaki tankwabar da auren ma gaba daya ba tare da kowa ya zargeki ba,amma fa saikin jure sai kuma kin daure,in kikai haka gaba zaki godemin" Shuru tayi tana nazarin maganganun a kanta


"Ki kwantar da hankalinki,idan kin samu lokaci kizo zan sake shirya miki yadda komai zaici gaba da tafiya" ta sake gaya mata bayan sunyi maganganu masu yawa da suka dan saka hafsat din sake aro dauriya,duk da yadda take jin zuciyarta kamar wuta


"Zanzo gobe ko jibi ma"


"To shikenan,amma lallai lallai karki nuna masa wani banzan hali ko daya,kiyi kamar ba'ayi komai ba,zakiga yadda zai sake bude miki bakin aljihunsa"


"To shikenan" ta amsa mata tana sake share sauran hawayenta.


          Suna gama wayar saita koma ta duba saqon daya turo matan,gaisuwa ce yana kuma shaida mata suna kan hanyar dawowa gida,wani mugun tsaki taja,kamar zata ajjiye wayar sai kuma ta tuna da zancansu da anty ummee,tayi ta maza ta danne zuciyarta ta kirashi.


        Bugu biyu ya daga wayar,dai dai lokacin da har sun fara yiwa kano nisa,suna bayan motar da ake tuqasu shida muhammad da suraj a tsakiyar escort dinsa,sai ya gyara zamansa yana kara wayar a kunnensa.


         Tun daga sautin muryarta ya fuskanci akwai damuwa,duk da yadda tayi namijin qoqarin boyewa,to amma a yadda taji ta masa magana ba wani mummunan lafazi sai yaji hankalinsa ya sake kwanciya,da ya tambayeta mai ya sami wayarta tun jiya yake kira a kashe


"Kamar da gaske an damu dakai" ta fada a qasan ranta bayan tayi tsaki,amma a zahiri sai yace


"Nawwara ce ta jefamin ita bayan freezer,ruwa ma ya tabata,yanzu nakeson bada ita game gyara"


"Ya salam,shikenan,ki jira na dawo zan bayar a duba miki da kaina" tuni zuciyarta ta gama hasko mata abinda zatayi da wayar don haka tace


"A'ah,ai yaronma yana waje jirana ma yakeyi na bashi wayar"


"Is okay,yayi,saimun qaraso"


"Ala tsare" ta fada tana gintse wayar,saita maidata flight mode din,gobe ko jibi idan zata gidan anty ummee zata biya ta saidata ta sake hade kan kudadenta,ya sake kashe wani kudin ya siya mata wata,don ba imani ko daga qafa yanzun tsakaninta dashi.


            Zuciyarta nata gaya mata ta shiga kitchen tadan samar masa wani abun da zaici,amma sai tayi fatali da wannan tunanin,taja tsaki ta miqe kan kujera abinta tana cewa


"Bazan iya ba wallahi,wannan pretending dinma da nakeyi duka ya fara isata" ta sake jan wani tsakin tana rufe idanunta tanajin yadda ranta ke mata suya.


        Awanni kusan biyu tana zaune a wajen,sai data gaji don kanta,sannan ta miqe ta kom bedroom dinta,yanayin da jikinta yake ciki itama ya fara damunta,don haka ta hada ruwa ta shiga wanka,gaba daya hatta da yaran batason motsinsu ko bari bari da zasuyita sakata,don haka tun da safe ta aika gidansu dasu,wannan ne kadai zai bata damar zama tayi jinyar kanta da kyau.


          A nutse ya fita a motar bakinsa dauke da addu'o'i,samuel ya zagayo yayi saluting nashi sannan ya miqa masa key din cikin girmamawa,hannu yasa ya karba yana masa ban gajiya,sannan samuel din ya juya ya fita a gidan,zasu qarasa a ragowar motocinsu dake cikin layin.


         Jefa key din yayi a aljihun rigarsa,sannan ya juyo yana nufar gidan bayan ya sauke ajiyar zuciya,zuciyarsa na gaya masa ko me zaya tarar cikin gidan kuma?,sanin gaibu sai Allah,haka yaci gaba da takawa da kuzarinsa da qarfin gabban nan nasa da ya zama kamae signature dinsa.


         Da sallama a bakinsa ya yaye labulen falon yana qarewa falon kallon,as usual yana nan kamar kowanne lokaci,kamar yadda ya saba tarar dashi, matuqar sa'a ce zaici yayi wata tafiya ya dawo ya samu falon a kintse,har ya zame masa jiki,bawai ya dawo ya sameshi a hargitse ne abun mamaki ba a gareshi,babban abun mamakin ya sameshi neat,sai ya saki labulen ya kutsa kai zuwa ciki.


           Shurun da yaji yayi yawa sai ya dauka ko bacci yaran sukayi bayan ya kalli agogo,bakwai sa rabi na dare harda wasu mintuna,kansa tsaye ya tunkari dakinsu,amma daya tura sai yaga wayam babu kowa,dakin dai shima kamar ko yaushe,saiya maida qofarsa ya rufe ya sauya akalarsa zuwa dakinta.


           Tana tsaye bayan ta fito a wankan,daure da zanin jikinta wanda tayi masa daurin gaba(daurin qirji),tana ta qoqarin taje gashinta yana cije mata saboda taurin da yayi,ya turo qofar suka hada idanu,saita amsa masa sallamar ta maida kanta wajen taje kan nata,kamar ma batasan wayeshi ba.


          Kofar ya saka yana zare idanunsa daga saman gashinta yana takowa zuwa ciki,yasan kafin ya tafi ya ajjiye mata kudaden gyaran jiki da gyaran kai,yafi tsanar qazantar gashi fiye da qazantar komai,amma ita kwata kwata ba damuwarta bane,to ina takai kudin?,me kuma ya hanata zuwa gyaran kan?,jikinma baiga alamun an gyarashi ba, tun yana sanyata a gaba ya kaita har ya daina bata lokacinsa da kudinsa,tunda ya siya mata mota kudin kawai yake bata,cikin kaso goma kuma kaso biyu kacal take zuwa,kaso takwas din saidai ta adana kudinta,duk da shi baisan me takeyi dasu ba.


         Cikin juriya ya isa bayanta,ya kuma rungumota ta baya zuwa cikin jikinsa, hannayenta biyu ta saka da dukka qarfinta tana son janyeshi a jikinta,yasan zata aikata hakan,shi yasa bai mata qaramin riqo ba


"Am sorry" ya fada da muryar da yasan tana matuqar tasiri wajen karya lagonta,turjiya da tijara takeson masa koda zata rage zafin dake danqare a ranta,mugun guguwar baqin kishin da anty ummeen tasa ta danneshi bisa salo na kissa,amma sautin muryarsa data sauka a kunnenta ta karya dukka lagonta,sai ta sakar masa kuka,kuka kuwa sosai wanda ke bayyana ftsananun zafin da zuciya ke fuskanta.


           Ya sani,kishi yana da zafi,don haka ya fara lallashinta cikin wani salo da yasan yana saukar da zafinta,a hankali sai ya soma birkice mata,abinda yaja hankalinta kenan ta soma zame masa tana tureshi,cikin ranta tana mita,sai an fara abun arziqi dashi sai kuma ya canza hanya,shi din babu dama a hada jiki dashi sai wani zance na daban.


           Sosai yayi mata riqon tsauri,baisan meye damuwarta ba,bata taba iya karbar damuwarsa hannu bibbiyu ta bashi hadin kai ya sauketa ba,kamar bata da wani feeling,kuma qarya ne!, tabbas tana dashi,saidai ta sanyama ranta wani baqin rai da girman kan banza.


        Duk yadda taso tayi avoiding nasa amma ta kasa,dole ta bada kai bori ya hau,duk da ba wani hadin kai ya samu ba,ya saba da hakan,har kusan ya zame masa jiki,bayan komai ya kammala kuma ta shiga quncinta kamar yadda ta saba,baibi ta kai ba,hasalima kafin tayi wanka sai daya tabbatar ta wanke kanta da kyau,ya hadata da hand drayer sannan ya fito,ya wuce sassansa don ya shirya.


        Ko da ya gama shirinsa ya fito kitchen ya duba saboda yadda cikinsa ya rarake kamar an masa yasa,babu alamun an girka komai,sai kawai ya dauki key ya fita don yi musu takeaway ba tare da ya tsaya jiranta ba,yasan ba abinda zata dafa a wannan lokacin,a hanya yayi kiran hajiyarsa,har kuma ya qarasa wajen sunata wayar,yace mata gobe zai shigo da wuri kafin ya wuce,don a gobe yakeso ya koma kaduna.KI KULANI miss xoxo


DAUDAR GORA Billynabdul


RUMBUN K'AYA hafsat rano


IDON NERA Mamuhghee


A RUBUCE TAKE huguma


sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so


masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin


0022419171

Maryam sani

Access bank


Saiku tura shaidar biya ga

+234 903 318 1070


Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan

09166221261


Al'ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number

+227 96 09 67 63Thanks for choosing us

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post