Wata Sakayya Hausa Novels page 23 - Novels Elite

Wata Sakayya Hausa Novels page 23 - Novels Elite

 

Wata Sakayya Hausa Novels page 23 - Novels Elite

*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*


Kokarin azawa akan tafarki,shi ne abu mafi muhimmanci da yakamata marubuta su kware akai,mu proficient writers association za mu yada wannan manufa.

https://www.facebook.com/profile.php?id=100086156706062

https://t.me/+R7IGS941_bg3NDI0

 https://chat.whatsapp.com/GK9uG1er0mUFsuS1s5JE9K

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.

 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)

By

            Nusaiba Alkamawa

 *Free page 23* 

****

Da sauri Dr sadiq ya matso kusa da ita yana fadin "Alhamdulillah ta farfado,  ki natsu ki bude idonki a hankali ki kalle ni" a hankali ta fara bude idanuwan nata ta sauke su akansa, "yanzu inane yake maki ciwo? " nuna masa kafarta tayi, "sorry itama zata daina ciwo amma yanzu zaki sauko kiyi tafiya mu gani" a hankali ta zuro kyawawan kafafuwan nata kasa sannan ta mike tsaye duk da ciwon da kanta yake mata, abin da ya bata mamaki shine jin ta tsaya akan kafafun ta batare da sunyi kakkarwa ba ko kuma taji bazata iya taka su ba, "tako kije wanchan bangon mu gani" a hankali ta fara tafiya harta isa bangon sannan ta juyo ta dawo wajan likitan,kamar a mafarki "Alhamdulillah aiki yayi kyau yanzu haka zata iya tafiya zuwa ko ina takeso da kafafuwanta" sujjada Asabe da Garzali sukayi suna godewa ubangiji daya nuna musu wannan rana, mikewa sukayi tsaye suna yiwa Dr sadiq da Muhseen godiya tabe baki Muhseen yayi, "yarku ta samu lfy amma shi wanda ya bata bargon ga rayuwar sa chan a cikin hadari ai" ras haka gaban Jiddah ya fadi duk kuwa da farin cikin da take ciki na ganin yanzu itama zatana tafiya da kafafuwanta kamar kowa, ashai dama wanine ya bata bargonsa ta samu lfy shi kuma yana chan a kwance rai a hannun Allah ita kuwa dame zata sakawa wannan bawan Allah ganin su Muhseen suna kokarin fita yasa ta sha gabansu da saurin gaske, "dan Allah ku kaini na gansa naga lafiyar sa, ta fada a cikin xuciyarta 😜afili kuma tayi musu nuni da hannunta 

karan farko da tafara tafiya duk a lokaci daya, amma bata cikin farin ciki saboda jin wanda ya taimaketa ya kwance babu lfy, wani banzar kallo Muhseen ya bita dashi irin kallon up nd down dinnan, "kinyi sanadiyar kwanciyar sa babu lafiya yanzu kuma so kikeyi kije ki karasa sa ya mutu saiki fi jin dadi ko?","tace da yaran kura me, wllhi ba haka bane ba nide dan girman Allah ko daga bakin kofa ne na gansa ba dole bane sai naje kusa dashi ba" ta fada idonta na kawo ruwa "mtwss" yaja tsaki yana rabawa ta gefenta ya wuce kifa kanta tayi a jikin kofa tana fashe wa da kuka tausayi ta bawa Dr sadiq da yake kokarin fita daga dakin, dafata yayi yana fadin "zo muje ki gansa amma kiyimin alkawari bazakiyi kuka ba" da sauri tace "nayi maka alkawari wllhi ko tari bazanyi ba balle nayi kuka, ta fada tana nuni da hannu "  cike da farin ciki, shi kuwa lokaci daya yaji yarinyar ta birgesa sa'ar yarsa ce hajiya , jan hannunta yayi suka fita daga dakin sukabar su Asabe da kallon bayansu cike da mamakin ikon Allah wai yau Jidda ce da tafiya , har dakin ya shigar da ita sannan ya kaita har bakin gadon, "wannan shine Dr Jamal kuma shine wanda ya cece rayuwar ki" wasu hawayene masu dumin gaske taji sun zubo masa ita batasan ma sun zubo ba sai dumin su da taji hannu tasa tana share hawayan tausayinsa ganinsa a kwance kamar wanda babu rai a jikinsa sai cikinsa da yake dagowa da komawa alamar yana raye kenan, "amma Dr zai samu lfy kuwa? Duk fa maganar nan da take da hannunta take yinsa " kafin Dr sadiq ya bata amsa Muhseen ya karbe zanchan, "to in bazai samu lfy ba ai saiki kashe shi kawai kihuta" ya fada yana banka mata harara kamar idonsa zai fado sai kace wani mace, shifa tsakaninsa da Allah haushin Jidda yakeji saboda itace sanadiyar kwanciyar abokinsa mafi soyuwa a gare sa, "kinga diyata rabu da Muhseen zai samu lfy in sha Allah muje na rakaki ki koma dakin ki anjima kadan zan rubuta miki sallama amma da kici gaba da shan magunguna kinji ko" daga masa kai tayi tana share hawaye domin kuwa ta kasa manta yadda taga Jamal kamar matacce, saida ya rakata har dakinta sannan ya juya yaje ya dudduba marar sa lafiya sannan ya rubuto takardar sallamar Jidda ya kawo musu, "mun gode likita Allah ya biya ku da gidan Aljanna","babu komai  shi yayi dan Allah ne saidai kuyi ta masa addu'ar Allah ya basa lfy, idan taji wani chanji a jikin ta zaku iya dawo da ita wannan asibitin domin duba lafiyar ta" godiya suka karayi masa sannan ya fito daga dakin domin komawa office dinsa da sauri Jidda ta biyo bayansa tana kwala masa kira, juyowa yayi yana kallonta ganin itace yasa shi sakin murmushi, "dan Allah Dr ka bani number wayar ka sai ina kiran ka inajin halin da yake ciki" ba tare da wani tunani ba ya zaro biro da takarda a aljihunsa ya rubuta mata number sannan yayi mata sallama ta kara gaba, gam gam haka ta rike takardar a hannunta lokacin data koma dakin harsu Asabe sun gama hada kayansu fitowa sukayi tare da ita Garzali ya tare musu napep suka saka kayansu a ciki sannan suka shiga, kwantar da kanta tayi a kafadar Asabe har suka karaso gida, Asabe tana kokarin bawa mai napep kudinsa shi kuma Garzali yana sauko musu da kayan su, ita kuma Jidda ta shiga gida tana shigowa sukayi ido hudu da Hassana da kuma Al'amin , da gudu suka ruga daki suna ihu suna fadin Fatalwa! Fatalwa!! Fatalwa!!!

 Wata sakayyar

         Sai alahira 

 fans kuma karku gudu wannan jiddah alkamawa ce ba fatalwa ba 😄😜

Share fisabilillah.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post