A Rubuce Take (K'addarata) page 33 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 33 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 33 Hausa Novel - Novels Elite

H U G U M A


A RUBUCE TAKE

       (K'addarata)

Page 33

         Table guda ya kama shi kadai,sanye da fara sol din shirt me gajeran hannu,sai wani lafiyayyen trouser daya dace da boots din qafarsa,coffee kawai yake sha,duk da yana da buqatar abinci,loneliness yake da buqata,yayi hayaniya har baisan iyakar adadinta ba,abinda ba dabi'arsa bace,yana tsoron hakan ya haifar masa da ciwon kai,wannan yasa ya zabi ya kebe shi daya ba tare daya gayawa kowa inda yake ba idan ka dauke suraj.


         Tun jiya suke karbar baki,ko kusa ko alama bai dauka wani sabon bikin zasuyi ba,sai da yaje gidan hajiyarsa yaga yadda ta tashi gagarumin biki,ya koma gida bisa ga mamakinsa hafsat ta zauna tayi masa lissafi ta kuma karba kudade sosai daga hannunsa tana shaida masa itama taro zatayi


"Ko yaya ma dai nakai ga qinta,tunda har an daura ta zama matarka,ina da ikon maida abinda ya faru ya zamana ba wanzajje ba?" Kai ya gyara cikin gamsuwa,ransa na masa dadi,yana sake samun nutsuwa,mamakinsa na sake daduwa akan hafsat din,fatansa da burinsa na dorewarta a haka na sake hauhawa,wanann abun yasa ba haufi ya ajjiye mata abinda ta buqata harda ma qari.


            Kusan komai mamaki yake bashi,auren yazo masa a hagunce,yanata kuma zuwa da abubuwan mamaki,bai dauka wani aure bane na azo a gani ba,amma sai gashi anata shirye shiryen daga kowanne bangare.


            Wayarsa dake yashe saman table din ta soma haske,saboda tuni ya maidata silent,idan kira ya shigo sai.ya duba ya tabbatar mai muhimmanci ne kafin ya daga,a yanzun ma suraj ne don haka ya danna green ya kuma maidata handsfree ba tare daya dauki wayar a hannunsa ba ya barta nan saman table din.


"Baka dawo bane?,kana ta ina?"


"I will be back......akwai damuwa ne?"


"Babu,kusan ma an kammala komai,har presidential lodge din da za'a zuba sauran baqin ya zama ready"


"Good,thank you suraj"


"What are friends for" murmushi ya saka ya kashe wayar.


         Har ya daga coffee din zai sake sipping tunanin kiran Samuel yazo masa,ya lumshe manyan idanunsa kadan sannan ya budesu yana tuna yadda hajiya ke bashi amanar yarinyar,tun ranar da aka daura aurensu har yau din nan,ba ranar da zata fito ta fadi bata ambata masa cewa amana ce ta iyayenta ba,sannan amanace ta ita kanta hajiyan,farincikin da yaga hajiyar nayi da auren kawai ya isheshi shima,bashi da burin daya wuce ganin walwalarta,da kuma farincikinta,wannan ya qara masa qaimi ya danna number samuel din.


         Cikin girmamawa da kuma nuna respect yake amsa kiran ogan nasa,ya tambayeshi hanya yace komai lafiya,ya gaya masa a inda suke a yanzun,ya kashe wayar yana irga adadin mintunan da suka rage musu su qaraso bauchin,sai ya shanye sauram coffee dinsa ya miqe yana maida wayarsa aljihu,ya dauki key dinsa ya nufi parking lot na gurin shan coffee din.


°°°°°°°Cike gidan yake da 'yan uwanta da abokan arziqi har zuwa compound na gidan,wani abun mamaki ko kuma rashin sabo ga duk wanda yasan gidan ko kuma ya saba wucewa ta gaban gidan,ko gari banza da wahala kaga tayi baqo,don ita din mutum ce mai tsananin rowa da tsumulmula,rashin kyauta rashin faran faran da rashin iya tarbar baqo.


         Daga cikin gidan kuwa,cikin bedroom din,hafsat din ce zaune a gefan gadonta,sai anty ummee da tayi tsaye gaban cupboard dinta tana zaqulo mata kayan data saka,sai mita takeyi cikin masifa


"Duk wannan uban suturar bansan me kike dasu ba,ke baki saka ba ke baki bayar ba,duk kayanki na fadan kishiya kuma bansan gidan uban da kika kaisu ba,kudin dinki da gyaran daya baki suma ina kika kaisu oho"


"Don Allah anty ummee kawai ki dauko kayan da zaki dauko ki barni naji da abinda nakeji" hafsat ta dago kanta da takejin kamar zai cire ta fadawa ummee din,sai ta waiwayo ta dubeta,idanunta har sun kada sun canza kala,tabe baki tayi,ta juyo hannunta riqe da wani lace,wanda a ido yayi mata kyau sosai,tana kuma saka ran zai zaunawa hafsa din


"Da wannan raunin naki da kuma rashin juriyarki bana jin zakici nasara maganar gaskiya,yau kawai.....tun bata kai ga shigowa gidan ba?,ina ga ta shigo?,ta wanzu a cikinsa?,zakici nasara kuwa?,wannan siradin ba na raguwar mace mai raguwar zuciya bane,hanya ce mafi sauqi ta mallakar kowa da komai......saidai.....tana yiwa yawa yawna mata wahala,ciki harda ke da alama"


        Hannunta dake dafe da kanta ta saki,ta sake daga kanta tana kallon anty ummee da kyau,muryarta a mugun karye,ita kadai tasan me takeji tsakanin zuciya da qirjinta


"Wanne qoqari zanyi anty ummee bayan wannan?,kinsan me nakeji kuwa?,har na fara nadamar daukan shawararki,qila da ace abinda zuciya ta ke gayan nayi na aikata.....wala'alla da ban fuskanci zafin da nakeji a yanxu ba....."


"Da kuma kinyi biyu babu ba.....da baki samu darajar da kike ganinta a idanunsa ba,da nutsuwar da kike qaryatawa a yanzun a yadda kike ganin babu ita tayi qaura dake kwata kwata..... tashi kiyi abinda zai fishsheki,ki yiwa zuciyarki qarfa qarfa,kici galaba a kanta,don ki cimma muradinki" ta qarashe maganar tana watsa mata kayan data debo din,sannan ta juya ta fice tabar mata dakin don ta bata damar shiryawa.


        Bin anty ummee tayi da kallo harta fita,sanann taja gauron numfashi ta miqe ta soma daga kayan tana kallonsu,tana jin qirjinta na mata wani zafi,tana jin kamar ta cinnawa gidan wuta gaba daya,sauqi sauqi daya takeji a ranta,idan ta tuna qaramar yarinya za'a kawo mata,tana da ikon juyata duk yadda takeso,amma ta wani bangaren tana jin zafin yadda ya dauko yarinyar da ta kusa haifarta, tabbas banda gidansu ana zaman karatu ta haifi yarinyar,idan ta zauna ta lissafa shekarunta da nata.


         Bata damu da canza undies ba,tunda a nata ganin basa cikin abinda zaka damu da canzasu koda yaushe,ta riga data saba,sometimes abbas ke sakata canzawa,idan ta tarasu zaiyita fada sai ya tilastata ta wanke,idan kuma yana free ma baya jin qyashin wanke mata su.


         Tana gama shiryawa mimi ta shigo da gudu riqe da hannun nawwara,bin yarinyar tayi da kallo,tunda aka fara hidima a gidan taga jama'a taketa murna,rabonta da ganin mutane haka a gidansu tun haihuwar nawwara,a sannan kuma bata da wani wayau sosai


"Anty jamila tace ki canza mana kaya,wai anty amarya tazo,yanzu motarsu ta shigo" gaban hafsat yayi mummunar faduwa,tabbas dirin motoci takeji daga harabar gidan,hakan yana gaya mata MUGUN IRIN ta shigo gidanta kenan,zuciyarta na wani irin zafi ta rufe mimi da fada


"Anty amaryar ubanki,kike rawar qafa a kanta,ki cewa jamilan ba za'a canza miki kayan ba,tafi ki bani waje tun banyi ball dake ba" tsoro ya kamasu duka su biyun,bama kamar mimi da tayi tsilli tsilli da ido tana shirin saki kuka,dai dai nan anty ummeen tashigo,a bayanta kuma anty atika ce yayarta da suke uba daya


"Yauwa,kin gama shiryawa ko?,maza fito gasu sun iso,fito" fuskarta tamkar wanda aka yiwa bushara da rasuwar wani makusancinsa


"Na fita nayi musu me?" Kafin anty ummee ta amsa anty atika ta rigata


"Ki tarbeta,ai haka akeyi" ta amsa mata tana shigewa toilet din hafsan,don fitsari ne ma ya shigo da ita,banda haka saitayi zuwa dari bata shigo dakinta ba,duk da dama bawai zuwan takeyi ba.


             Cikin wani madaukakin murmushi take takawa zuwa bakin motocin da sai yanzu suka gama tsaiwa,dai dai sanda anty deena ke tsaye a bakin qofar motar tana karantowa widad addu'o'i tana maimaitawa


"Sannunku da zuwa,ma sha Allah" hafsat wadda ta lullube jikinta da kyakkyawan mayafinta kalar lace din jikinta ta fada,fuskarta wadace da fara'ar da takejin dai dai take da kukan mutuwa.


           Anty madina anty deena anty halima batulu da momma dake wajen dukkansu suka waiwaya suna duban inda maganar ta fito,hafsat din da mutum takwas dake tare da ita,anty ummee da anty uwani ne kawai 'yan uwanta,sauran duka 'yan uwan abbas ne


"Yauwa sannunku"


"Kun sha hanya barkanku da sauka" qanwar hajiyan abbas din mace mai yawan fara'a karamci da sanin ya kamata ta fada,don kwata kwata takun hafsatun bai mata ba,hausawa sukance wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi,sai ta matsa tana kamo hannuwan widad da anty madeena ta jawa mayafin ta lullubewa fuska sosai,banda kuma tayi mata hakan ita ba sanin anayi tayi ba,ba lallai ta kula da wannan ba


"Lale maraba diyarmu,taso a hankali" ta sake fada tana tayata tasowar,ta cikin mayafi widad take mita ita kadai,kawai an qunshewa mutum kai?,wannan ai rashin gaskiya ne,ita me tayi daga zuwanta ba za'a barta bama taga hasken garin daga baya sai a rufe mata kan,da wannan tunanin tabi bayan gwaggwo mero qanwar hajiyan zuwa cikin gidan,duka sauran jama'ar suka bi bayansu.


          Kusan hafsatun ce a qarshe qarshe,tana biye dasu, idanunta da zuciyarta kamar zasu fado,sai data cewa anty ummee ba zata fito ba ta tilastata,ta fuskanci akwai munafukai cikin 'yan uwan abbas dake murna da wannan auren,amma koma meye zatayi maganin kowa,bata ta yarinyar,don kallon farko tun bataga fuskarta ba ta tabbatar yarinyace din sosai kamar yadda akace.


          A babban falon hafsat da abbas yasa aka gyara mata shi duka don ya danni zuciyarta aka fara yiwa widad masauki,hafsat din ta shigo sai idanu sukayi kanta,wasu nason ganin launin fuskarta ne,yayin da wasu ke mamakin shigowar ta a qarshe,tayi ta maza ta aro dakiya da juriya tana sake musu sannu da zuwa da kuma sannu da hanya.


           Duk da cewa AKWAI WATA A QASA amma SANIN GAIBU sai Allah,hakan sai ya yiwa su anty deena dadi,ya kuma dan sanyaya musu zuciya,ko banza awajensu tayi abinda mata dubu suka gaza yi,a  irin wannan lokacin wasu suke fara rabar da halinsu.


          Kanta tsaye ta wuce daura da inda aka zaunar da widad tana murmushi,tana zama sassanyan qamshin da fata da kuma sutturar widad din ke fitarwa ya ziyarci hancinta


"Sannunku da hanya" ta sake fadar kalmar da tun dazu ita take maimaita wa,sannan ta dora


"Sannu qanwata" idanunta nakan fuskar widad ta cikin mayafi,don har yanzu bata samu nasarar kallon fuskar tata ba,bata amsa ba kamar yadda bata motsa ba,anty halima data gama qarewa hafsat kallo a fakaice ta motsa,tace ayi salati ga annabi.


         'yan addu'o'i aka yi sannan suka gabatar mata da amanar widad din.


        Wani murmushi ta saki,inda ace ba akan plan take komai ba....ashar shine abu mafi dacewa ga wadda tace ta riqeta amana,amma babu komai,akwai lokaci,a juri zuwa rafi...


"Ai Allah ne ya hada zamana da ita,ita din koda baku fada bama ai tamkar qanwa take a gareni,ai babu komai,in sha Allah,zaku yaba,Allah dai ya bamu aron rai" ta qarashe fadi tana kuma fadada murmushinta,cikin zuciyarta tana ayyana kwana nawa zata gudu da qafarta,ko su dawo su kwashe ragowarta.


             Addu'a aka sake rufewa da ita,sanann suka dunguma sassan widad,sassan da a lokacin aketa kaya kayan shigar da kayan jerenta,wanda motoci uku ne manya suka iya daukesu,irin kudin da ummu da alhaji suka fitar basu tana fidda makamancinsa ba akan bikin jika,gefe daya kuma ga abbanta shima da yayi tasa bajintar,abun da ya bugar dasu batulu sosai,suka kuma sake tabbatar da cewa hae yanzu yana qaunar fatima,daga yadda ya aurar da autarta cikin girma,saboda bai taba irin wanna hidimar ga sauran yaransa ba,da sukayi qorafi sai.ya gaya musu,ita din nesa za'a kaita,duka yaransa kuma babu wadda aka taba kaiwa nesa,bugu da qari duk wata dama da wani alfanu da mutumin dake kusa da gida zaya samu ita banda ita,sunyi mita sunyi qorafi har suka gaji suka godewa Allah.


           Babban falo ne dake dauke da dakuna guda biyu,sai kitchen dining area da kuma ventilation ta baya,ginin yayi kyau sosai gwanin qayatarwa,komai kuma a wadace babu matsi.


          Basuyi minti talatin ba hafsat tasa aka kai musu coolers din abinci da tasa akayi musu,suna fara ci kusan suka ajjiye,nujood wadda aka taho da ita tace kuma sai 'yan kano zasu koma zata wuce gida ta ajjiye nata plate din itama


"Nifa wallahi dana sani masauki nabi su na'eema,wannan abinci haka?" Ta fada tana yatsina fuska,harararta hajjaa tayi


"Bamason abun magana daga zuwa baqunta malama,idan zaciki kici,idan bakici ki ajjiye musu kayansu" 


"To nima dai shuru kawai nayi,abun dai to....." Latifa ta fada yana yatsina fuska,duk sai aka kwashe da dariya,ashe kowa shuru kawai yayi yake kaiwa cikinsa,kada ya fara magana aga gajen haqurinsa,musamman da yake inna laila qanwar ummu tana wajen,ita kuma ba kasafai ta fiya son ire iren wadan nan abubuwan ba.


*Arewabooks:Huguma*


KI KULANI miss xoxo


DAUDAR GORA Billynabdul


RUMBUN K'AYA hafsat rano


IDON NERA Mamuhghee


A RUBUCE TAKE huguma


_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_


_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_


0022419171

Maryam sani

Access bank


Saiku tura shaidar biya ga

+234 903 318 1070


*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*

09166221261


*Al'ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number*

+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post