Wata Sakayya Hausa Novels page 24 - Novels Elite

Wata Sakayya Hausa Novels page 24 - Novels Elite

Wata Sakayya Hausa Novels page 24 - Novels Elite

*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*


Kokarin azawa akan tafarki,shi ne abu mafi muhimmanci da yakamata marubuta su kware akai,mu proficient writers association za mu yada wannan manufa.


https://www.facebook.com/profile.php?id=100086156706062


https://t.me/+R7IGS941_bg3NDI0


  https://chat.whatsapp.com/GK9uG1er0mUFsuS1s5JE9K


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.

 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)

By

            *Nusaiba Alkamawa*

 *Free page 24* 


 *Happy Ramadan* mubarak 

*****

Fatalwa! haka suka rika fada suna guduwa, boyewa sukayi a bayan kujera jikinsu har rawa yakeyi tsabar tsoratar da sukayi da ganin Jidda musamman ma da su kaga tana taka kafarta , ita kuma mamaki ne ya kamata ganin suna gudu, Dan tama sha'afa da abinda yafaru da ita, ko gudun mai sukeyi oho? falon ta nufa amma bata gansu ba tana niyar fitowa ta hango kafar Al'amin a bayan kujera nufar wajan nasu tayi tana zuwa ta dan taba kafaɗar sa wata irin razananniyar kara ya saki yana sakin fitsari a wando, ita kanta Hassana kakkarwa takeyi tana fadin fatalwa, dariya Asabe tayi da ta shigo falon yanzu , "Hajiya Jidda ce fa naji kuma kina cewa Fatalwa","Jidda ai ta mutu ko ba da bakin ki kika fada mana cewar ta mutu ba, kuma wannan na tafiya ","Hajiya ai bata mutu ba na shiga daki ina kuka mukaga tana motsi shine fa muka kaita Asibiti gashi yanzu har aiki akayi mata ma gashi nan har tafiya takeyi" wani irin dogon tsaki Hassana ta saki tana mikewa cike da bakin cikin wannan rana da Jidda ta dawo,musamman ma cikin lafiya, shi kuwa Al'amin tsabar bakin cikin razanar da aka saka shi yayi,  bangad'e Jidda yayi yana shigewa dakin su domin ya chanza wasu kayan, "to uban waye ya biya mata kudin aikin da akayi mata" murmushi mai ciwo Asabe tayi, "wani bawon Allah ne ya bata bargon sa kuma akayi mata aikin batare da mun biya ko sisi ba","mtwsa dalla to tsayuwar mai kuke min ku fitar min daga falo" jiki babu kwari haka Asabe ta jawo hannun Jidda suka fito daga falon suka bar Hassana a tsaye cike da bakin ciki, suna zuwa bangaran su Asabe ta dan gyara musu dakin sannan ta shige bandaki, ita kuma Jidda kwanciya tayi rigingine tana kallon silin gaba daya hankalinta da tunaninta yana kan WANNAN bawan Allah daya taimaketa, shin ko yanzu wana hali yake ciki koya jikin nasa, da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita, ba ita ta farka ba sai ana kiran sallar magrib, lokacin Asabe bata dakin dan haka kawai saita shiga bathroom tayi wanka tare da dauro alwalla tana fitowa ta tada salla tana idar da sallar Asabe ta shigo hannunta dauke da kwanukan data zubo musu abinci ajiye musu abincin suka faraci Asabe nayiwa Jidda hira amma ita ina hankalin gaba daya ya tafi ko wane hali Dr Jamal yake ciki yanzu? 

 DR JAMAL

Satin sa biyu a asibiti jikinsa ya

fara samun sauki amma babban abin damuwar shine baya iyayin komai da Kansa komai sai Mommy ko Muhseen sunyi masa, hakan ne yasa Muhseen bada shawarar maizai hana a sallamesu su koma gida sai acigaba da kula dashi a gida inyaso ko mai kula dashi ne sai a samo, da sauri Jamal yayi na'am da shawarar da Muhseen ya bayar dama ya gaji da zama a asibitin badan Mommy taso ba aka sallamesu suka koma gida.

______part dinsa aka gyara sosai sannan aka samo wani namiji mai suna Sani wanda zai rika kula da Jamal, kamar kullum da gari ya waye Mommy ta shigo dakin taga ashe ma idonsa biyu, "my son good morning" murmushi yayi yana amsawa da "morning Mommy","ya jikin naka","Alhamdulillah","Allah ya kara sauki","bari na hada maka ruwan wankan sai na kira Sani yayi maka ko" turbune fuska Dr Jamal yayi tunda yaji ta ambato sunan Sani kuma wai harda yayi masa wanka, Allah ya sauwake ya bari wani ƙato ya gane masa tsaraicinsa, "a gaskiya Mommy ni banason aikin Sani sam bai iya aiki ba kinga dakin nan ma fa wai ya gyara sa a haka gaskiya ni banason sa a chanza wani" kallon dakin Mommy tayi taga ko ina  fes dashi amma wai bai iya gyara ba, "girgixa kai, kawai tayi, tace masa" tom shikkenan  Jamal insha Allah za'a samo wani" jinjina mata kai yayi yana lumshe ido ita kuma ta shiga bathroom dinsa ta hada masa ruwan wankan sannan tazo ta fara kiciniyar dorasa akan kekensa da kyar ta iya dorasa, tace "kaga abinda yasa nakeso Sani ya rika kula dakai ko, kaga ni tsufa ya fara kamani jibi yanzu fa dakyar na iya dora ka akan keken" shi dai baice komai ba saboda ya rigada ya saka a ransa Sani bazai kara masa aiki ba, bathroom din ta kaisa sannan ta cire masa kayan jikin sa ya rage daga shi sai gajeran wando sannan tayi masa wankan kana ta fito dashi ta shafa masa lotion ta taje masa sumar kansa, kayan sa marar sa nauyi ta dauko ta saka masa sannan ta dauko turare ta fesa masa, breakfast dinsa ta dauko ta fara basa a baki yanaci suna cikin haka Muhseen ya shigo dakin da sallama, "Mommy ashe kina nan ai nayi ta sallama a kofar dakin ki naji shiru ashe kina nan","wllhi kuwa ai mutumin naka ne Dan sa a hankali shima wannan mai kula dashin yace baiyi ba a chanzo wani","to ai Mommy sai a samo wanin kinga sai hankalinsa ya kwanta","hmm indai Jamal ne inka samoma daya kwana biyu zai kore sa, nidai tunda kazo zauna ka karasa basa abincin bari naje na dora girki " mika masa plate din tayi ta fita daga dakin, zama Muhseen yayi yana basa abincin suna taba yar hira har ya koshi sannan Muhseen yaje ya wanko hannunsa sannan yayi masa sallama dama wajan aiki zaije shine ya biyo ya duba sa.

 *By aunty nucy*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post