A Rubuce Take (K'addarata) page 9 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 9 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 9 Hausa Novel - Novels Elite

H U G U M A

A RUBUCE TAKE

      (K'addarata)


Page 09


           Suna tafe a hanya uncle muhsin din yana janta da hira,ta saki jiki sosai sunata hirarsu da yake abokin hirarta ne dama,a nan ya fahimci interest dinta itama game da karatu,da yadda take da kaifin basira,tun suna hirar har suka gaji kowa yayi shuru,saita maida hankalinta ga kallon titi da yadda suke wuce dazuzzuka,can qasan ranta ta dinga jin wata kewa tana shigarta,zuciyarta ta karye,suna dada yiwa kano nisa.


           Tun tana iya bin hanya da kallo har baccin ya soma fusgarta,babu jimawa kuwa yayi awon gaba da ita,ta saki jiki sosai tana barcinta abinta.


          Bata tashi farkawa ba sai da uncle muhsin ya iso qofar gidanshi ya tsaya yana jiran mai gadi ya bude masa qofa,idanunta ta bude a hankali tana murzasu hadi da budesu da kyau tana qarewa wajen kallo.


           Tun a sannan tasan ta shigo baqunta,ta kuma shigo sabon waje,quaters ne dake da qarancin jama'a tare da qarancin gine gine,saidai kuma duka manyan gidaje ne ta wajen,tana nan zaune har ya buda gate din gidan ya dawo ya shigar da motar.


         Sanda ya kashe motar waiwayo yayi yana tsokanarta


"Yar qauyen kano yau gata a bauchi" kasa magana tayi saboda kewar ummu data fara shigarta,sai murmushi kawai data saki,dai dai nan matar gidan ta iso.


         "Kai kai kai.....abba wa nake gani haka?" Ta fada tana dariya gami da murza bdanunta,saboda baice mata da widad din zasu taho ba


"Wa idanunki suka gani?" Shima ya fada yana dariyar


"Tabdi,wai Allah na,anya kuwa ba gizo idanuwa kemin ba?"


"Shafa kiji dai" ya sake fada yana dariya gami da qoqarin fitowa daga motar yana duban widad din


"Fito mu shiga ciki" yace da ita yana fita daga motar


"Gaskiya na ciri tuta,abba wacce irin addu'a ne ka yiwa ummu ta baka widad?" Ta sake fada tana karbar jakar hannun widad din tare da sake bude mata qofar motar sosai.

   

          Tare suka jera zuwa ciki hadiyya matar uncle muhsin da yaranta ke kira hajjaa nata mamakin zuwan widad din


"Saurin me kike ne?,zakiji komai fa" cewar uncle muhsin.


          Tunda suka shiga falon gidan ta gane yaran gidan basa nan,da yake ranar makaranta ce,har dakin yaran hajjaa ta rakata sannan tace da ita


"Ki alwala ki sallah,ki shiga kitchen da abinci ki diba kici,su nujood din sun kusa dawowa,yanzun nan zaki gansu" a nan dakin ta barta ta koma wajen mijinta.


        Tun bai gama kintsawa ba ta sashi a gaba,yana shiryawar yana bata labarin dalilin tahowa da widad din,gyara zamanta tayi tana sauke ajiyar zuciya


"Gaskiya abba gwara daka taho da ita,duka duka nawa take da za'a dameta da batun aur,baya ga haka ma naga ko yayyen nata da aka yiwa auren duka sun fita datawa,tunda a qalla suna kaiwa sha bakwai sha takwas,sai ita tun tana 'yar sha hudu?"


"Nafi tunanin farinjinin da yaaya yaga tana da shi ne fiye dana 'yan uwanta ya daga masa hankali yakeso yayi ya kawar da ita,amma gaskiya ni dama nafi mata sha'awar karatu,da zan samu ummu tabarmin ita karatunta zatayi sosai"


"Gaskiya dai abba,Allah yasa ummu ta bari"


"Ba tabbas" ya amsa mata yana zura jallabiyyarsa


"Ki dauko system dita ki sakamin ita a charge,nabar ayyuka da yawa ban kammala ba,inaso na rage kafin gobe" ta amsa masa da to tana miqewa,shi kuma yana fita don zuwa masallaci sallar azahar.


           Hankalinta duka yana kan widad tunda ta barta a dakinsu nujood,widad din ba baquwarta bace,tasan yadda take da wahalar sabo da rashin sakin jiki,qilan yanzun tana can zaune a takure,kamar yadda ta zata kuwa haka ta sameta,tayi sallar dai amma tana zaune,cikin dariya tace


"Anya widad za'a zauna mana a bauchin nan kuwa?,taso muje kuci abinci kafin su qaraso,yau sunyi delay ma,Allah yasa ba school bus din tasu ce ta sake basu matsala ba,don haka tayi musu jiya".


          Tare suka fito tana biye da ita,a falo suka samu uncle muhsin din,shima shirin cin abincin yake,sai hajjaa ta zuba musu tare,tana daga gefe suna hirar kano da uncle muhsin din,jifa jifa suna sanya widad,har ta fara sakin jiki,da yake daga uncle din har hajjaa mutanenta ne.


        Basu ko kai ga gama cin abincin ba sukaji ana taba gate din gidan


"Tohm,ga 'yan makaranta nan"Hajjaa ta fada hayaniyarsu na ratsowa falon tun kafin sukai ga qarasowa.


   Tsam widad ta dauke hannunta daga plate din abincin cikin hanzari,kafin sukai ga qarasowa ita ta fita suka hade a farfajiyar gidan.


       Cikin murna nujood ta riqeta tana ta ihun murna kamar wadanda wani abu ya sama,banda uncle muhsin sun san abinda ke faruwa babu abinda zai hanasu tsorata,amma sai ya kada kai yana murmushi


"Allah ya shirya,kamar basusan sun fara girma ba"


"Banda abun abba ina hankali a nan,ai saidai aikin quruciya".


          A nan falo ranar aka wurgarwa da hajjaa kaya da jakar makaranta,sauqinta daya ranar babu islamiyya ta tabbatar da babu abinda zasu,baga nujood din kawai ba,har duka sauran 'yan uwanta sunji dadin zuwan widad din.


            Cikin kwanakin da basu da yawa taji ta qagu ta koma wajen ummunta,duk da cewa gidan yana mata dadi amma sam batason garin,hakanan take,ta fiya baqunta da rashin saurin sabo,abu daya ne yake sanyawa taji komawar ta fitar mata a ka,batun ma'aruf da kuma mahfood da taji rannan uncle muhsin suna zancan da hajjaa hadiyya sunayi cewar har yanzun bai haqura ba,yace idan Allah yayi rabonsa ce shikenan.


       Zumbura baki tayi gaba ba tare data baiwa zancan muhimmanci ba,duk da qarancin shekarunta amma ta fuskanci zallar nacin da mahfood ke dashi,ta rasa da wanne suna ya dace ta kirashi,takan kirashi da maye a ranta,taja tsaki ta dauki marker din zanen da tazo dauka suna wani zane ita da nujood ta fice zuwa farfajiyar gidan inda suka sanya kujeru suka zauna.


         ***

    Baqar mota ce wuluk qirar BMW take ratsawa a hankali ta saman titin,daga cikinta tana dauke ne da mutane uku,dukkansu sanye suke da police uniform (kakin d'an sanda,matuqin motar akkauran dan sanda ne baqi dake hakimce a mazaunin driver yana sarrafa sitiyarin motar cike da qwarewa,yayin da wanda ke zaune a gefansa ya kasance siriri sosai,hakanan kuma dogo ne,duk da cewa a zaune yake zaka fahimci hakan.


        Na ukun nasu kuwa yana zaune daga bayan motar,tashin farko zaka iya kiranshi da matashi,don duka duka shekarunsa na haihuwa ba zasu haura talatin da biyar ba,mara hasken fata ne da zaka iya kiransa sa chocolate color,irin fatar dake da tsada da kuma daukan hankali,saboda yadda take a kwance kadai zai nuna maka zallar jin dadin da ma'abocin fatar ke samu.


          Yana da matsakaicin tsaho,wanda inda ace siriri ne kai tsaye zaka iya kiransa da dogo,saidai murjewar jikinsa ta shanye tsahon nasa ta sanyashi a sahun matsaikatan maza,manyan idanu gareshi masu daukan hankali,girmansu bai hanasu lumshewa ba a duk sanda yaso hakan,kamar yadda yake da wasu irin lips kai kace na mace ne.


          Sosai uniform din suka zauna masa a jiki,kai kace saboda jikin nasa aka qerasu,qafafunsa da yayi crossing nasu socks ce kawai,boots dinsa na aje gefan qafafun nasa.


           Duk da hirarrakin da mutum biyun dake gaban motar sukeyi shi sam ko sau daya bai tsoma musu baki ba,hasalima tafin hannunsa ne shimfide saman fuskarsa kamar mai wani tunani,abinda kuma zai iya hanaka ganin ainihin fuskar tasa sosai kenan,sai kyakkyawan agogon Rolex dake daure a tsintsiyar hannunsa.


         Yanayin zaman da yayi kamar na mutumin daya gaji tubus,sam zaka zaci baya cikin motar ne,duk da hirar da sukeyi din ta shafi aikinsu,dukansu cikin zuciyoyinsu suna muradin ya sanya baki,saidai sunsan abune mawuyaci,shi yasa cikinsu ma babu wanda ya sanya rai da hakan suka ci gaba da hirarsu ba tare da sun daga sauti yadda zasu dameshi ba.


           Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana zame hannun nasa daga saman fuskar tasa,kyakkyawar zagayayyar fuskarsa dake cike da wani irin kwarjini gami da haiba ta bayyana,ya dan bude idanunsa kadan da nauyin gajiya ya cikasu.


           "Samuel" ya furta cikin muryarsa dake da kauri da nauyi


"Yes sir" mamallakin sunan wanda shike tuqin motar ya amsa a ladabce


"Ka saukeni gidan hajiya tukunna"


"Consider it done sir" ya sake amsa masa cikin nuna qarfin bin umarnin sa.


       Kafin wani a cikinsu ya sake cewa wani abu wayar dake tsakanin seat din gaba guda biyu ta dauki tsuwwa,mutumin dake zaune a kujerar dake zaman banza ne ya miqa hannu yana dubawa,kana yadan waiwayo kadan dai dai sanda yake qoqarin maida boot din qafarsa


"Sir,dan jaridar nan ne" shuru kamar bazai amsa ba,da alama ba ma'abocin son magana bane,sai kuma yace


"Ka katse kiran ka tura masa saqo,gobe qarfe biyu su sameni a zone one"


"Yes sir" shima ya amsa yana juyawa cikin qoqarin idar da umarninsa.


           Dai dai sanda ya gama sanya takalman yana gyara zamansa motar ta soma gangarawa cikin unguwarsu,sai ya juya gefansa yana daukar tarkacensa dake zube akan seat din gami da maida hularsa saman kansa yana dakon motar ta isa qofar gidan.



ZAFAFA BIYAR 2023


IDON NERA Mamuhghee


KI KULANI miss xoxo


A RUBUCE TAKE Huguma


RUMBUN K'AYA Hafsat rano


DAUDAR GORA Billynabdul


Account number


0022419171

Maryam sani

Access bank


Saiki tura shaidar biyanki ga

09033181070


VTU OR MTN RECHARGE CARD

09166221261


AL'UMMAR NIJER SU TUNTUBI WANNAN NUMBER


+227 90 16 59 91


Kuyi Comment, share sannan kuyi following blog dinnan pls.

Thanks for choosing us

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post