Wata Sakayya page 18 Hausa Novels - Novels Elite

Wata Sakayya page 18 Hausa Novels - Novels Elite

Wata Sakayya page 18 Hausa Novels - Novels Elite

WATA SAKAYYAR

        (Sai a Lahira)

By

            Aunty Nusy

Free page 18

******

Cikin tashin hankali da firgici Garzali yake kallon Asabe ga wasu hawaye masu  zafin gaske da suka zubo masa, Hassana ce ta fito da sauri jin kururuwar Asabe ta cika gidan "kee! lafiya kika cika mana gida da koke koke?","Hajiya Allah yayiwa Jidda rasuwa" wata uwar dariya Hassanata kece da ita harda rike ciki, cike da mamaki suke kallonta mutuwa fa akace anyi amma takeyin dariya basu karasa shiga mamaki ba saida sukaji abinda tace, "Alhamdulillah Allah na gode daka dauki ran yarinyar nan ko babu komai yanzu na huta da ganinta hankalina zai kwanta dama na tsani na bude ido na ganta a cikin gidan nan amma kunga daga yanzu komai yazo karshe" tana gama fadin haka ta juya ta koma falonta tayi zamanta, rushewa da kuka Asabe ta karayi jin rashin imani irin na Hassana, tashi tayi jiki a sabule ta koma dakinsu tana kuka mai ban tausayi da sauri shima Garzali ya rufa mata baya yana shiga dakin ya kurawa gawar Jidda ido yana kuka wiwi. 

 kamar a mafarki yaga ta dan motsa dan yatsunta kara murza idonsa yayi ko ba dai _dai yake gane masa ba amma sai yaga hannun ya sake motsi, "Asabe wllhi bata mutu ba, kinga tana motsa yatsunta fa" da sauri Asabe ta maida kallonta zuwa hannun Jidda motsi itama taga yayi, "maza jeka samo mana abin hawa mu kaita asibiti" da gudu Garzali ya fita sai Allah ya taimake sa yana fita yaga wani mai napep ya dauko wata yar budurwa tsayar dashi yayi yace , "dan Allah bawon Allah asibiti zaka kaimu wllhi wata yarinya ce rai a hannun Allah","to amma kaga na dauko wata" ba kowa mai napep din nan ya dauko ba sai Fadila kawar Yasmeen da sukeyin aiki tare da asibitin Dr Jamal kafin a kora ta daga aiki, "kaga babu matsala nima ma'aikaciyar asibiti ce yaje ya fito da ita" da gudu Garzali ya ruga gida yana ma Fadila godiya babu jimawa sai gashi ya dawo da Jidda a hannunsa Asabe na biye dashi a baya da sauri Fadila ta fito aka kwantar da jidda a bayan napep din, da sauri Fadila ta danna kirjin ta da hannu biyu aiko sai Jidda ta saki ajiyar zuciya da karfin gaske amma bata bude ido ba, fadila ce ta dago kan Jidda ta dorasa akan cinyarta ita kuma Asabe ta dora kafafuwanta akan cinyarta shi kuma Garzali ya zauna a gefen mai nepep din suka tafi tun kafin su karasa asibitin Fadila tayi waya suna zuwa aka dora Jidda a gadon mararsa lfy aka turata zuwa ciki, Asabe zata biya kudin napep din Fadila tace ta barshi zata biya godiya sosai Asabe tayiwa Fadila sannan tabi bayan gadon da aka dora Jidda akai dakin taimakon gaggawa aka shiga da ita saida suka shafe kusan awa biyu akanta kafin su samu linfashinta ya dawo dai dai sannan aka kawota dakin hutu, Dr Muhseen ne ya fito yana share gumin fuskar sa ya kalli Asabe da Garzali, "kune wadan da kuka kawo marar lafiyar nan","ehh likita mune","to ku biyoni office" binsa sukayi a baya har zuwa office dinsa zama yayi sannan ya basu umarnin su zauna kallonsu yayi na wasu dakiku sannan ya fara magana kamar haka, "kunsan cewa yarinyar ku tana fama da lalurar rashin kwarin bargon kashi ko?","mun sani likita","amma mai yasa baku kawota asibiti dan ana duba lafiyar ta" shiru sukayi suna zazzare ido domin basuda tacewa, "to yanzo haka zaku biya kudi naira milyan biyar domin yiwa yarinyar ku aiki" dafe kirji Asabe tayi saboda tunda take a rayuwarta bata taba ganin wadannan makudan kudade ba bare harta kawo ayiwa Jidda baiwar Allah aiki, "dan Allah likita ka taimaka wllhi yarinyar nan marainiya ce bamuda inda zamu samo wadannan makudan kudadan daka ambata ba","to ku dauki yarku ku kaita asibitin govnati munan asibitin kudi ne, zaki iya tafiya" jiki a sabile suka fito daga office din zuwa dakin da aka kwantar da Jidda kwance suka tarar da ita sai sauke nunfashin wahala takeyi.

Koda Hassana ta gayawa Ameenu rasuwar Jidda tsaki yayi yana fadin ni na dauka ma wani abun ne yasa kika kira ashe ma ba wani abune mai mahimmanci ba, yafada tare da kashe wayar sa, saboda ita Hassana batasan cewa Jidda tana raye ba har kuma sun kaita Asibiti ma, koda su Al'amin suka dawo daga makaranta Hassana ta fada musu cewar Jidda ta rasu harda tsallansu da murnar su nina rasa abinda Jidda ta tsare musu a rayuwar su da har suke mata wannan bakar kiyayyarnan koda su Hajiya Inna sukazo shine sukace a fito da gawar Jidda domin ayi mata wanka amma me? Hassana na zuwa ta tarar babu kowa a dakin ihu ta kurma tana fadin an sace gawar wllhi an saceta.

Share fisabilillah.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post