Daurin Boye hausa novel Complete by Safiya Abdullahi HUGUNA

Daurin Boye hausa novel Complete by Safiya Abdullahi HUGUNA

Daurin Boye hausa novel Complete by Safiya Abdullahi HUGUNA

DAURIN BOYE* 🧣🧣

         *NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

HASKE WRITERS ASSO

(home of expert and perfect writers)✍

*_Dandano daga littafin DAURIN BOYE_*

        0⃣1⃣

      Sake gyara tsaiwarshi yayi jikin machine din nasa samfurin lifan kirar MOTO B,agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ya kalla yana sake qiyasta mintocin daya kashe tsaye a qofar gidan,tabbas banda wani babban dalili babu abinda zaya sanyashi zaman jira har kamar haka,babu abinda ya tsana a rayuwarshi kaman jira,mutum ne shi mai kiyaye qa'ida wanda bai yarda da samfurin wannan maganar da hausawa ke bawa lokaci ba na african time.

      Sauke hannun nashi yayi ya maida dubansa ga madaidaicin get din dake maqale da katangar gaban gidan wanda ya kasance shine kofar da zai sadaka da ainihin cikin gidan,kaman jiran hakan kuwa ake qofar ta soma yunkurin budewa,cikin sakannin kadan matashiyar dake yunqurin bude qofar ta bayyana.

     A hankali take takowa zuwa inda yake,sanye cikin dinkin atamfa riga fitted da skert wanda ya zaunawa jikinta das,ta lullube jikinta da mayafi wanda baikai matsayin medium ba,a hankali yayi kokarin mamaye fuskarshi da murmushi duk da yadda fuskarta take kadaran kadaham hakan bai dameshi ba duk da yana ankare,ba fara'a sannan ba kuma a daure take can ba,kallo take kare masa tun daga nesa kaman yadda ta saba masa duk sa'ilin da ya ziyarceta,shirt ce jikinsa ruwan makuba da bakin wando jeans mai matsakaicin kudi,kafafunsa saye da takalmi budadde dinkin hannu na kasuwar kofar wambai,fes yake hakanan kayan sun masa kyau babu laifi,sumarshi kanshi zuwa sajensa a gyare a taje wanda hakan ya sake bayyana sirrin kyan da Allah ya bashi,ba shakka banda wani abu guda tak muhammad ya cika mijin aure wanda za'a iya nuna shi a ko ina,saidai wannan abun daya rasa din ya sanya ta cireshi daga tsarin mutumin daya cancanci aurenta.....

Sauke littafin domin karanta complete.

DOWNLOAD

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post