Wata Sakayya hausa novels page 20 - Novels Elite

Wata Sakayya hausa novels page 20 - Novels Elite

Wata Sakayya hausa novels page 20 - Novels Elite

WATA SAKAYYAR

        (Sai a Lahira)

By

            *Nusaiba Alkamawa*

Free page 20

*****

"Anya kuwa Jamal ba kwaya yasha ba yasan kuwa hadarin dake tattare da aikin nan dazai sadaukar da rayuwar sa akan yarinyar da bamu sani ba sai yanzu , a gaskiya bazan bari inaji ina gani in bari abokina ya cutar da rayuwarsa ba" ya fada a fili yana fitowa daga office din fitowa yayi daga cikin asibitin gaba daya ya shiga motarsa ya bata wuta.

Yana tunanin anya kuwa kuwa mahaifiyarsa zata a mince wannan sadaukarwar, Amman dai zai gwada yagani. 

"Mommy dan Allah wata alfarma nake naima a wajanki, Mommy aikin alkairi zanyi kada ki hana ni dan Allah Mommy na, kuma dama a koda yaushe kece kike cewa na taimaki duk wanda naga yana bukatar taimako indai hakan bai sabawa Addinin mu ba shiyasa a yanzo nake naiman amincewar ki da yaddar ki kafin na aikata aikin alkairin da nakeso na aikata" murmushi tayi tana kallon dan nata da'a koda yaushe take kara godewa Allah daya batashi a matsayin danta, dayane amma kamar goma shiyasa take alfahari dashi a koda yaushe, "ina jinka Jamal wane taimako kakeso kayi da har kake rokana haka kuma kake naiman amincewa ta?" shiru yayi yana nazarin mahaifiyar tasa kafin cikin kwarin gwiwa ya fara magana, "Mommy inaso zan bawa wata bargona ne, yarinyar tana cikin mawuyacin hali na rai ko mutuwa idan har ba'ayi mata aikin nan ba nan da awa ashirin da hudu, kuma kinga samun wanda zai bata kafin wadan nan awowin abune mai matukar wahala shiyasa na yanke shawarar zan bata nawa idan har kin amince" tunda ya fara magana ta kafesa da ido harya dasa aya tana kallon sa batare data kifta ba, "ka tabbata da gaske kakeson bata, kuma dan Allah zakayi wannan taimakon bada wata manufa ba","na rantse maki da girman Allah Mommy saboda Allah zanyi bandan wani abu ba","to Allah ubangiji ya bada lada yasa ayi aikin cikin nasara" cike da farin ciki ya taso ya rungume mahaifiyar tasa yana amsawa da ameen godiya yayi mata yana fadin, "bari naje nayi wanka" dato ta amsa masa tana saka masa albarka harya hau sama, Jamal na hawa sama Muhseen yayi sallama a gidan, cike da ladabi ya gaishe da Mommy itama da fara'a ta amsa masa, "Mommy dama wata magana ce mai mahimmanci na kawo akan Jamal","ina jinka Allah yasa ba wani laifi yayi ba","Mommy wasa Jamal yakeso yayi da rayuwar sa kuma wllhi aikin nan yanada matukar hadari saboda in anyi aiki ita yarinyar zata warke amma shi kuma ba lallai ya samu wadatacciyar lfy da zai rika yin abinda yakeso kamar yadda yakeyi yanzu " nan dai ya bawa Mommy labarin Bargon sa da yakeso ya bawa yarinyar, ajiyar zuciya Mommy ta sauke tana kallon Muhseen, "yanzu abinda nakeso dakai shine kayi masa fatan nasara akan aikin alkairin da yakeso yayi, ni a matsayina na mahaifiyar sa bazan taba hanasa aikin alkairin dayayi niyya ba saidai in masa fatan alkairi Allah yasa kuyi aikin a sa'a" da ameen ya amsa sannan yayi mata sallama ya fito, yana shiga mota ya tayar ya fito daga gidan a cikin zuciyarsa ya fara tunanin anya kuwa uwa da dan suna da hankali kuwa? , in kuwa sunada hankali bazasu taba wasa da lafiyar sa ba, ya dauka in yazo ya gaya mata zata dakatar dashi daga mummunan aikin da yakeso ya aikata wa kansa, amma saiya tarar uwar ce ma ta bawa Jamal din goyan baya mana, yoo in ba mummunan aiki ba taimakon da zai iya yin silar farin cikin abokin nasa koma yayi sanadiyar rayuwar sa gaba daya aiko dole ne ya kirasa da mummunan aiki da wannan tunanin ya karasa asibitin nan yasa aka fara shirye_ shiryan shigar da Jidda aiki gaba daya haushin yarinyar ma yakeji ko fuskarta bayason kallo tunda zatayi sanadin farin cikin abokin sa Jamal, gani yayi Asabe tasa an turo Jidda a gadon mararsa lfy za'a fita da ita dan harta taro napep tunda basuda kudin da aka bukata gara su koma gida kona gargajiya sai suyi, da sauri ya tari gabansu, "ina zakuje kuma","likita zamu tafi gida ne saboda bamuda kudin da kuka bukata kuma kunce dole sai an biya wadan nan makudan kudadan sannan za'ayi mata aikin" cike da tausayawa yake kallon Asabe da Garzali da kuma Jidda da batasan inda kanta yake bama, amma fa yafi tausayin abokinsa akansu, ku mayar da ita nan da awa biyu zamu shigar da ita zamuyi mata aikin" wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyoyin su jin abinda Muhseen ya fada har kasa Asabe da Garzali suka duka sunayi masa godiya, "babu komai i" ya fada a gajarce yana wucewa sukuma suka tura Jidda zuwa dakin da suka fito da ita zuciyoyin su fes.

____Kusan awa daya ya dauka yana salla tare da rokon Allah yasa ayi aikin nan cikin nasara, koda ya fito zai tafi Mommy har bakin motarsa ta rakasa tana masa addu'a saida taga fitarsa sannan ta juya zuwa ciki tana share hawayan tausayin dan nata, yana zuwa Asibitin ya tarar an gama shirya komi zuwa yayi ya chanza kaya zuwa kayan da aike sawa idan za'ayiwa mutum aiki sannan ya shiga tiyata room din tararwa yayi manya manyan likiticin asibitin su bakwai a wajan sunata harhada kayan aiki, kwanciya yayi akan gadon dake wajan sannan suka dauko wata allura sukayi masa a gadon baya daga nan bai sake sanin inda kansa yake ba, shigowa da Jidda akayi wacce ita tun a daki akayi mata allurar sannan aka hade gadonsu waje daya nan likitocin suka dukufa akansu anata aiki, su Asabe kuwa suna kofar tiyata room din daga wake sunata rokon Allah yasa ayi aikin nan a sa'a anyi aiki cikin nasara nan aka turo Jidda aka fito da ita aka maidata dakinta amma an gargade su da kada ayi wata hayaniya sannan suka koma wajan Jamal shima suna shirye shiryan fito dashi ya fara wata irin jijjiga nan fa likitocin hankalinsu ya tashi suka dukufa akansa wajan ganin sun ceto rayuwar sa.

More comments and likes more posts.

Share fisabilillah.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post