Wata Sakayya hausa novels page 19 - Novels Elite

Wata Sakayya hausa novels page 19 - Novels Elite

WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)

By

            *Nusaiba Alkamawa*

Facebook alkamawaS glow 

                  

Free page 19


*****

Wata Sakayya hausa novels page 19 - Novels Elite

*

"Kamar ya an sace gawar kin duba dakin kuwa da kyau baki ganta ba, taya za'a sace gawa" Hajiya Inna ta fada tana rabawa ta gefen Hassana tana shigewa dakin itama duddubawa tayi har cikin drower da kar kashin gado saida ta duba amma babu Jidda babu alamarta da sauri ta fito daga dakin tana kallon yawon mutanan da sukayi cirko_ cirko a kofar dakin, "da gaske fa Hassana take banga gawar hauwa ba, to amma ke lokacin da ta rasu waya gaya miki? " Hajiya Inna ta tambaya tana kallon Hassana da tayi zuru_ zuru tana zazzare ido, "wllhi Asabe ce ta fito tana kuka wai Jidda ta rasu","to yanzu ina ita Asaben? "ita bata gidan nan tun dazu nake naimanta amma ban ganta ba, amma bari naje na tambayi Garzali mai gadi ko yaga fitar ta" ta fada tana nufar dakin Garzali koda ta shiga dakin nasa shima babu kowa a ciki a gigice ta fito tana fadin shima bayanan, "to wai a kirasu a waya mana" wani irin kallo Hassana tayiwa Hajiya Inna,sannan tace "ai basuda waya hasalima basu san yadda ake amfani da ita ba, sbd hajiya hassana batasan suna da waya ba","shikkenan  cewa zakiyi sun sace gawar sun tafi suyi tsafi da ita waya sani ma ko sune suka kasheta dansu gudu da gawar" Hajiya Inna ta fada tana rushewa da kuka kamar gaske sai kace son Jiddar takeyi da tanason ta ai dabata bari tasha wahalar datasha ba, hakuri aketa bata wasu na fadin aje asanar da yan sanda carab Hassana ta cabe zanchan ta hanyar fadin "aa mai zaisa a sanar da hukuma nasan garin su Asaben gara aje a naimota" saboda tasan indai akaje aka sanar da yan sanda itace zata kwana a ciki saboda in bincike yayi bincike za'a gano irin azabar data rika ganawa Jidda ita dasu Alamin daganan ma waya sani ko allura ta tono garma shiyasa tayi kicin_ kicin tasan yadda tayi har aka daina zanchan zuwa sanar da hukuma, daga nan ma zanchan zuwa garin su Asaban ya shirirance, cewa Hajiya Inna tayi maine abin wahalar dakai tunda dai yarinya ta riga ta mutu kawai ayi mata addu'a sukuma kome ma sukayi da gawar suje suda Allah, haka mutanan wajan da yake ba diyarsu bace ba sukayi na'am da shawarar Hajiya Inna da wannan batun aka fara zaman makoki batare da ansan inda kawar Jidda take ba.

"Malama wai har yanzu baku dauki marar lafiyar taku kun bar asibitin nan ba" Muhseen da fitowarsa kenan daga office yaga su Asabe sun zabga uban tagumi shine yayi musu magana, "rushewa Asabe ta kara yi da kuka a karo na babu adadi saboda a duk lokacin data tuna basuda kudin da zasu biya a yiwa Jidda aiki saita kara rushewa da kuka, Garzali na bata hakuri yanzun mu rushewa tayi da kuka, "dan girman Allah likita ka taimake mu kamar yadda Allah ya taimake ka yarinyar nan bata da kowa saimu sai kuma Allah subhanahu wata'ala" cike da tausayawa Dr Muhseen yake kallon Asabe matuka da gaske ta basa tausayi amma babu abinda zai iya yi musu, "na gaya muku asibitin nan na kudi ne, in taimako kuke naima to ku kaita asibitin gomnati sai ayi mata aikin na baku nan da minti talatin ku tattara kubar mana asibitin mu" yana gama fadin haka ya barsu anan wajan Asabe na kuka yayi office din Dr Jamal, "lfy kuwa naji duk abinda kuke fada kuda mutanan chan, bakaji tausayinsu ba na yadda matar chan take kuka" ya fada yana nuna Asabe ta window din office dinsa, "ni kaina dr Jamal sun bani tausayi amma babu abinda zan iya musu saboda aikin da za'ayiwa yarinyar da suka kawo aikine mai wahalar gaske kuma kaga sai an samu wanda zai bata bargon ma" kallon sa Jamal yayi kafin yace, "ni zan bata" cike da firgici da tashin hankali Muhseen yake kallon Jamal, "anya kuwa kasan abinda kake cewa? in kai kuma kazo ka samu matsala fa","nide na gaya maka a shirya kayan aiki nan da awa daya zaku shiga damu aiki" yana gama fadin haka ya dauki lap court dinsa ya fita daga office din yabar Muhseen cike da tsoro da tashin hankali daya kasa boyiwa a fuskar sa.

Daga taskar nusaiba alkamawa 


More comments more posts.

Share fisabilillah.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post