Wata Sakayya Hausa Novels page 21 - Novels Elite

Wata Sakayya Hausa Novels page 21 - Novels Elite

Wata Sakayya Hausa Novels page 21 - Novels Elite

WATA SAKAYYAR

        (Sai a Lahira)

By

            *Nusaiba Alkamawa*

Free page 21

*****

Sosai tashin hankali ya bayyana a fuskokin likitocin, barema Muhseen shi kuka ma ya fashe dashi dama wannan abin yake gudu amma Jamal yaki saurarar sa yanzu gashi yana naiman rasa rayuwar sa, haka likitocin nan suka dukufa akan sa amma ina sun kasa shawo kan matsalar domin kuwa har lokacin bai daina jijjigar ba, da sauri Muhseen ya dauko wayar sa yana kuka ya kira wani babban likitan nasu dayake shi ba kullum yake zuwa ba sai asabar da lahadi yana daga wayar yaji Muhseen yana kuka tambayar  sa yayi da lfy? nan ya basa lbr abinda ya faru nan shima hankalin likitan ya tashi "Muhseen mai yasa baku bar aikin saina zo ba kunsan cewa dagani sai Jamal ne manyan likitoci a asibitin nan tunda Jamal shi za'ayiwa aikin kunga ai kamata ace to nima ina wajan za'ayi masa saboda gudun matsala irin wannan, gashi kuma wllhi bana gari naje wani aiki a london kuma kaga ba gari kusa ba, da saina taho yanzu amma duk da haka ayau dinnan komun dare zan taho insha Allah nasan gobe zuwa shabiyu na rana zan sauka, yanzu dai kuje ku cigaba da basa taimakon gaggawa" nan dai ya gayawa Muhseen abubuwan da ya kamata suyi masa kafin goben, fashewa da kuka muhseen ya kumayi yana kashe wayar jin babu nasara Doctor sadiq baya kasar ma, zama yayi akan kujera yana kara fashewa da kuka saboda hakikanin gaskiya Jamal abokinsa ne tunna kuruciya sunyi matukar shakuwa kuma yana matukar sonsa da kaunar sa tabbas idan wani abu ya faru dashi bazai taba yafewa kansa ba, daukar wayarsa ya kumayi domin ya kira Mommy ya gaya mata halin da ake ciki amma kuma sai yaga zai tayar mata da hankali ne kawai gashi shaikarunta sun karaja ga girma hakan zai iya sawa jininta ya hau saboda yasan yadda take matukar son Dr Jamal, saida Muhseen yasha kukan sa harya godewa Allah sannan ya koma cikin dakin tararwa yayi lokacin Jamal din ya daina jijjigar amma kuma baya numfashi kamar ma babu rai a jikinsa, da sauri ya dauko wannan abinda ake dannawa mutane a kirji mai kama da iron dinnan ya jonasa sannan ya hada bakinsu ya dannanwa Jamal a kirji, amma still numfashin bai dawo ba sake dannan masa yayi a karo na biyu nan ma babu labari, murzawa ya karayi zai danna a karo na uku, yasan cewa idan harya kara dannawa a karo na uku numfashinsa bai dawo ba to  tabbasa hakan yana nufin babu rai a jikinsa ya rigada ya mutu, runtse idanunsa yayi yana karantu duk addu'ar datazo bakinsa sannan ya kara dannan masa abin a kirji a karo na uku.

Hassana da yaranta duniya sabuwa ta dawo musu tunda annobar gidan ta mutu, karansu sukeci kawai babu babbaka hatta su Aminu sunyi farin ciki sosai da suka samu labarin mutuwar jidda har abokansa ya gayyato ya hada kwarya _kwaryan party na rasuwar jidda, matsalar Hassana daya ce yanzu a gidan itace takeyin aikin komai amma ta bada cigiyar a samo mata wata yar aikin tunda su Asabe sun gudu da gawar jidda kuma har yanzu ba'a sake jin duriyarta ba, gara a samo mata wata yadda zataji dadin rayuwarta fiye da a baya, Baban su Aminu ne ya sauko da shirinsa na tafiya wajan aiki Hassana ta taresa, "niwai na tambaye ka zanje na dubo babana bashida lfy amma bakace komai ba","nace miki ki shirya sai muje in aje ki nima daganan saina dubosa kinga kafinsu Aminu su dawo da schl kin dawo kar su dawo su tarar gidan babu kowa" wata uwar harara ta banka masa kamar idonta zai fado, "nace ni bazanje tare dakai ba kayi tafiyarka wajan aikinka idan  kaso saikaje ka dubosa nima yanzu na shirya naje","a dawo lfy" ya fada a takaice yana ficewa daga falon da harara tabi bayansa harya fita sannan taja dogon tsaki tana hayewa sama, ko minti talatin batayi da hawa ba sai gata ta sauko cikin shirinta na fita sai zuba kamshi takeyi kulle falon tayi sannan ta shiga motar ta, ta fice daga gidan bata zame ko ina ba sai shahara hotel tana zuwa Alhaji ashfaq ya fito ya rungumeta, "Sweetheart ai na dauka baza kizo ba harna fidda ran jin wannan dumin jikin naki" murmushi tayi tana shafo fuskar sa, "wllhi wanchan dan wahalar ne yaso ya hanani fita wai nace masa zanje in dubo Baba shine wai in shirya ya kaini ya dawo dani sai danayi masa jan ido sannan ya kyale ni","ai kin kyauta min wllhi" daga haka yajata suka shige cikin hotel din yana rungume da ita, wa'iyazubillah.

Share fisabilillah.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post