Wata Sakayya Hausa Novels page 22 - Novels Elite

Wata Sakayya Hausa Novels page 22 - Novels Elite

Wata Sakayya Hausa Novels page 22 - Novels Elite

WATA SAKAYYAR

        (Sai a Lahira)

By

            *Nusaiba Alkamawa*

Free page 22

******

Saida suka gama aikata alfashar su sannan suka fito rike da hannun juna, "tace, kaga bari nayi sauri na tafi gida nasan yanzu yara sun kusa dawowa daga makaranta" kallonta yayi yana murmushi, "yanzu kuma sai yaushe zamu sake haduwa" ha'ba ta rike tana kallon sama alamar tunani, "nifa kinsan idan koda yaushe zamu kasance tare bazan gaji ba, gashi kuma ko kiranki a waya kin hana ni yi kinga da ko muryar ki naji ai da zan rage zafi kafin mu hadu" fari tayi masa da ido, "aa nidai gaskiya karka kirani kada a samu matsala indai zan fito zan kiraka saimu hadu ai" badan yaso ba ya kyaleta sannan ya rakata har mota ta shiga saida yaga tafiyar ta sannan ya koma ciki ya dauki wayar sa ya kira wata number ringing daya a na buyun aka dauka, "hello masoyiyata Yasmeen wai sai yaushe zakizo ne?" daga dayan bangaren akace  "gani nan na kusa karasowa" babu dadewa kuwa sai gata ta karaso fitowa yayi itama danya shiga da ita, "yau bakije asibiti bane ba ko night duty kikeyi" tabe baki tayi sannan tace, "tsinan nan ya kore ni ai daga asibitin sa" nan dai ta basa labarin duk abinda ya faru, "karki damu indai zaki rika faranta min rai to ina mai tabbatar maki zan rika biyanki linkin abinda ake biyanki a wata sau uku" cike da jin dadi tayi tsalle ta rungumesa, "karka damu duk abinda kakeso zanyi maka kasan ni ai badaga nan ba" da wannan hirar suka karasa dakin.

******

Runtse idonsa yayi yana karanto duk addu'ar da tazo bakinsa sannan ya kara danna masa abin a kirjinsa a karo na uku, da karfi Jamal yaja wata doguwar ajiyar zuciya amma bai bude idonsa ba amma hakan ya tabbatar musu da yana raye hamdala Muhseen yayi yana fashewa da kukan farin ciki abokinsa na raye, abubuwan da Dr sadiq yace suyi masa dan basa agajin gaggawa kafin goben suka fara yi masa saida suka tabbatar komai ya dai daita hatta numfashinsa ma ya dawo dai dai sannan hankalinsu ya kwanta suka fito daga dakin a gajiye likis, kiran Mommy ne ya shigo wayar Muhseen da sauri ya dauka yana gaishe ta, "an fito dashi kuwa ko zan iya zuwa na gansa?" dan jim yayi dan harta dauka ma ko kiran wayar ne ya katse saida ta sake magana sannan yace, "kiyi hakuri Mommy yanzu babu damar ganinsa saboda yanayin aikin da akayi masa sai nan da kwana biyu zai dawo hayyacin sa, zan kula dashi yadda ya kamata Mommy insha Allah" godiya tayi masa tana kashe wayar ajiyar zuciya Muhseen ya sauke jin Mommy ta yarda da abinda ya gaya mata, bayaso hankalinta ya tashi sam da yake lokacin har an fara kiraye-kirayan sallar magariba yasa shi shiga office a gurguje yayi alwalla yayi sannan ya shinfida sallaya ya tada salla saboda ko azahar baiyi ba yanzu kuma gashi an fara kiran magriba, bayan ya idar da sallolin da ake binsa ne ya tada sallar magariba saboda ko yaje masallaci ba samun sallar zaiyi ba domin yanzu a raka'ar karshe suke yana idarwa yayiwa abokin sa addu'ar samun lafiya sannan ya mike ya dauki wayar sa yayi oder din abinda zaici, dan tun safe rabonsa da abinci shi ko yunwar ma bayaji saboda tashin hankali, ba'a dauki wani dogon lokaci ba aka kawo masa abinda yayi order ba wani sosai  yaci ba, abincin duk kuwa da yunwar da yakeji amma bashida kwanciyar hankalin da zaici abincin yadda ya kamata, bayan ya gama cin abincin ne ya dan dudduba wasu files, ana kiran sallar isha ya tashi ya nufi masallaci ana idarwa ya dawo cikin asibitin dakin da aka kwantar da Jidda ya fara shiga ya duba lafiyar ta duk da yanajin haushinta har zuwa lokacin dubata yayi yana shirin fita Asabe ta tare sa, "Dr lafiya kuwa naga har yanzo bata farfado ba" hararar ta yayi yana jan tsaki, "to ke a daukar ki ayi mata wannan aikin mai tsarin gaske kuma kisa ran farfado warta a yau, to bari kiji ko zata farfado sai zuwa gobe, goben mai sai anyi matukar sa'a dan zata iya kaiwa jibi, ke ko tambaya ma wanda ya bata bargo bakiyi ba wato ke ta yarki ma kikeyi shi kuma yana chan rai a hannun Allah bai zama  lallai ya tashi ba, yarki kuwa da muke da tabbaci dari bisa dari zata farfado kuma tare da cikakkiyar lafiya ta ita ma kikeyi, ni bani hanya na wuce" jikin Asabe ne da Garzali yayi sanyi hakika basu kyauta ba da basu tambayi lfy wanda ya taimake su ba amma gashi suna tambayar  sa lafiyar Jidda, yana fitowa daga dakin da aka kwantar da Jidda, dakin da Dr Jamal yake ya wuce yana zuwa ya sake dubasa ganin yana numfashi yasa hankalinsa ya kwanta sannan shima ya naimi dayan gadon dake cikin dakin ya kwanta saboda shi yakeso ya kwana dashi.

___Washe gari kamar yadda Dr sadiq ya fada wajan karfe sha biyu sai gashi ya shigo Asibitin yana zuwa basuyi wata- wata ba suka dukufa akan Jamal cikin nasara kuwa sukayi aikin domin kuwa komai ya dai daita, special dakin hutu aka kaisa sannan Dr sadiq  yaje ya duba Jidda yana shiga dakin tana farfadowa a firgice ta saki wata razananniyar kara.

Ina taya yan uwana musulmai murnar xuwan watan Ramadan Allah ya karbi ibadunmu ameen 🤲

Kuyahkuri da rashin posting da ba nayi muku kwana biyu ba na dakatane sbd  watan nan da yashigo mai albarka 

Amman 

Insha Allahu karfe goma na dare zandunga yi muku posting din wata sakayyar sai alahira 

Ngd matuka, 

 *Daga taskar anty* *nuseee*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post