Wata Sakayya page 15 hausa novels

Wata Sakayya page 15 hausa novels

Wata Sakayya page 15 hausa novels

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 

 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)


👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽


By

            *Nusaiba Alkamawa*

 *Free page 15* 

****

Office din Khalid ya shiga yana huci sai kace mayin wacin zaki, "Dr Jamal  yana ga kana huci?" banza yayi masa ya dauki ruwan jarka daya gani akan table din tunda ya kafa kai bai sauke ba har saida ya shanye ruwan tas, zama yayi akan kujera yana sauke numfashi Khalid ne ya sake tambayar sa a karo na biyu nan ya bawa Khalid labarin duk abinda ya faru" dariya Khalid ya tuntsire da ita harda fadowa daga saman kujerar da yake kai tsabar dariyar da take cinsa, "amma fa mutumin nan kana jin dadinka wllhi da nine na samu yan mata suna bibiyata kamar yadda sukeyi maka ai wllhi dana shana, to maize hana ka amshi tayi Yesmeen din kawai danka shana" wani banzan kallo ya watsa wa Khalid, yace "kasan ni ai ba mazinaci bane, hasali ma na tsani maiyin zina ina kyamar duk wanda yake aikatata, da farko yadda naga yarinyar tana nunamin soyayya naso in amince da soyayyarta saboda banaso wani yasha wahala akaina amma saina saka akamin bincike a boye akanta anan na gano ashai itadin karuwa ce tun daga lokacin nayi deleting dinta kuma dama ba wani birgeni takeyi ba","amma lallai Jamal to ai mata karuwai anfi hutawa dasu ni bari naje ko zata aminta dani kaga yau da daddare saitazo gida ta tayani kwana" bai jira amsar Jamal ba ya fice daga office din, bayansa Jamal yabi da kallo yana jan dogon tsaki kwantar da kansa yayi akan kujerar da yake kai ya lumshe idonsa kamar mai bacci.

Koda Khalid ya fito a kofar office din Jamal ya tarar da Yesmeen tana kokarin fitowa daga office din Jamal, "Yesmeen" ya kira sunan ta a hankali, "dan Allah ka bawa Sir Jamal hakuri kada ya kore ni wllhi da wannan aiki iyayena suka dogara" ta fada idanunta rau_ rau kamar zatayi kuka."karki damu bazai koreki ba, amma mai kikayi masa da har yake kokarin korar ki" yayi maganar kamar baisan abinda ya faru ba, inda _inda ta fara tana sosa kai, "to tunda bazaki fada ba ni bari na tafi amma ki sani bazan basa hakuri ba saide ya koreki" ya fada yana kokarin rabata ya wuce kamar bai damu ba amma a cikin zuciyarsa addu'a kawai yakeyi Allah yasa ta tsayar dashi shi kuma ya fada mata bukatarsa ko zata amince, "Dan Allah Sir ka tsaya zan fada maka" nan ta labarta masa duk abinda ya faru, kare mata kallo yayi tun daga sama har kasa ita din kyakkyawa ce ga diri Allah ya bata amma ko mai yasa ta fada harkar karuwanci ohoo? "to maizai hana ni ki bani abinda kike so ki ba wa Dr Jamal din kuma yaki amincewa" da sauri ta dago tana kallon sa daga mata kai yayi alamar abinda taji dinde shiya fada, "in kin amince ga katina ki kirani da daddare zanzo na dauke ki sai muje ki tayani kwana, kuma ki kwantar da hankalin ki Jamal bazai kore ki ba zaki cigaba da aiki a hospital din nan" fuskarta dauke da murmushi tayi masa godiya ta kara gaba, office dinsa ya koma amma bai tarar da Jamal ba, "ko ina ya tafi" daga kafada yayi alamar shiya sani.

Yana fitowa daga office din Khalid daki_ daki ya rika shiga yana duba mararsa lafiya har saida ya tabbatar da ya gama dubasu sannan ya fito dan ya tafi gida zuwa lokacin har daya da rabi tayi, mota ya shiga driver yaja suka tafi suna zuwa gida driver yayi horn mai gadi ya bude masa ya danna hancin motar sa a filin da ake ajiye motoci, motar na tsayawa ya fito zuwa falon Mommy a zaune ya tarar da ita tana karanta daily trust zama yayi a kusa da ita ya dora kansa akan kafadarta, "lfy yau naga ka dawo da wuri","yunwa nakeji kuma kinsan bana iya cin abincin waje indai ba naki bane kuma inaso na dan watsa ruwa shiyasa","to kaje ka watsa ruwan Yusrah zata kawo maka abincin" tashi yayi ya haye sama darect dakinsa ya shiga tun daga bakin kofa ya fara cire takalmi yana watsar wa haka safa haka dai ya rika cire kayan yana cillarwa sannan ya fada toilet, Yusrah na shigowa da tray din abinci a hannunta ta fara cin karo da takalman sa murmushi tayi tana fadin "matar da Yaya zai aura tana da aiki komai nasa saiya cillar" ajiye tray din tayi akan center table sannan ta kwashe masa kayan ta kaisu inda ya dace da ajiyar su, yana fitowa ya shafa lotion tare da taje sumar kansa sannan ya feshe jikinsa da turaruka masu kamshin gaske, jallabiya ya dauko ya saka ya cire tawol din jikinsa ya shimfida sallaya ya tada salla bayan ya idar ya dade akan sallayar yana yiwa mahaifinsa addu'ar Allah ya jikansa da rahama, sannan ya dauko abincin ya zuba zanso kuga dan abincin daya zuba duk da kiran yana jin yunwar da yakeyi, yana gama cin abincin ya sake wani sabon shiri ya fito, "yanzu kuma sai ina" Mommy ta tambaye sa fuskarta dauke da murmushi, "zan koma asibiti ne","to agogo sarkin aiki a dawo lfy" da Allah yasa ya amsa yana ficewa, mota ya shiga driver yaja suka bar gidan sai asibiti.

            *Jidda* 

  __________________

Yauwa hassan, yanxu xansaka vaseline da man gyada a tayil din nan kai kuwa sai kabi ta window ka kira mana wannan miskiniyar kace momy ce take Kiran ta kafin kadawo na Riga da na kammala aikin. 


Ai kuwa da gudu hassan yatafi cike da murnar muguntar da xasuyiwa jiddah, 


Shi kuwa al'amin shafawa yayi daidai kofar da jiddah zata fito harsaida wajan yayi kyalli sosai, sannan ya buya awajan daining area. 

Zaune take akan keken kaddarta hannunta rike da wani xobe kamar na diamond, tsinkayo muryar hassan taji Ai kuwa da saurinta ta boye xoben, Allah ya taimaketa ta setin xoben bata nan ne wajan window ba, le ko da kan shi yayi yace keee miskiniya kike ko wa? 

To kije yanxu momynmu tana kiranki, yana fadan haka ya wuce, 

Ita kuwa jiddah me take inba mamaki ba, meyafaru, meyasa take kirana, to Allah yasa dai alkhairi ne, bara naje kar nayi lefi duk da kullum ni me lefi ce agurinsu. 


Fita nayi, innalillahi wainnailahi rajiun jinayi ina tafiya babu birki na kasa control din keken nawa, rintse idanuna nayi, cikin xuciyata ina kalmar shahada domin yau na saddakar inda iyayena suka tafi yau nima can xantafi, jinayi nabige wani Abu, numfashi na ya tsaya cak. 


Bansake sanin kaina inda yake ba, sai da asabe ta kwarara min Ruwa, sannan cikin sakin ajiyar xuciyar sa na Bude idanuna. 


Sai sannu asabe take tamin,tana cewa garin ya haka tafaru, duk da tasan ba Iya amsata mata xanyi ba, mikewa nayi da kyer, ina babu bakin magana da xan fada mata abinda yafaru dani. 


Zaunar dani tayi 

Sannan tafita "Asabe ce ta kawowa Jidda abinci mika mata plate din abincin tayi amma sai jidda ta girgiza mata kai alamar ta koshi da abincin, "nifa gaskiya na kasa gane rashin son cin abincin nan naki kwana biyun nan daga tea sai tea, to tea har wani abinci ne ma, to gaskiya zansa Garzali ya siyo maki maganin cin abinci" girgiza wa Asabe kai tayi wai kar asiyo maganin, "aiko dole ne a siyo taya mutum zaiyi lfy bayan baya cin abinci?" ita dai jidda shiru tayi har Asabe ta gama fadanta ta fice daga dakin, abinda Asabe bata sani ba shin kwana biyun nan jidda batajin dadin jikinta yanzu ko dan taka kafar da takeyi da. 

yanzu bata iyawa amma taki fadawa su Asabe kuma taki bari su sani saboda tasan irin dawainiyar da sukeyi da ita.

Shere fisabilillah

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post