Wata Sakayya page 16 Hausa Nivels - Novels Elite

Wata Sakayya page 16 Hausa Nivels - Novels Elite

Wata Sakayya page 16 Hausa Nivels - Novels Elite

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 


 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)


👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽

By

            *Nusaiba Alkamawa*

 *Free page 16* 

*****

Kwanci tashi ciwo sai kara cin jikin Jidda yakeyi ba tare da kowa ya sani ba hatta Asabe ma bata sani ba kawai dai tasan yanzu jidda batason cin abinci saide tasha tea, shima din sai Asabe ta matsa mata sannan take sha yanzo ma Asaben ce a gaban gadon jiddar tana tambayarta, "anya kuwa Jidda lafiya kike" alama tayi mata da hannu akan maita gani, "naga duk kin rame ga wani haske da kikayi dadin dadawa bakison cin abinci, inaso na kaiki asibiti likita ya duba min ke amma kuma yanzu wata uku kenan Hajiya Hassana bata biyamu albashin mu ba dagani har Garzali da tuni na kaiki an dubamin lfy ki amma kuma banida kudi, ni wllhi badan shegiyar matar chan nake zaune a cikin gidan nan ba, danke nake zaune nasan inna tafi zalintar ki su Al'amin zasu tayi badan haka ba da tuni na koma garin mu wllhi amma bazan iya barinki ba innayi haka ban sakawa iyayanki da alkairin da sukamin ba amma babu komai wata rana sai labari, karki damu da zarar ta biyamu kudinmu zan kaiki asibiti kinji ko" daga mata kai Jidda tayi, "bari naje na karasa girkina kinji ko" nan ma dai daga mata kan ta kumayi a karo na biyu, fita Asabe tayi zuciyarta fal tausayin yar baiwar Allah Jidda, lumshe ido Jidda tayi har baccin wahala ya dauke ta saboda yadda takejin kasusuwan jikinta kamar ana sassara mata su, yanzu harta ma saba da kwanciya bama sosai take iya zaman bama yanzu .

"Wllhi kuwa kawata ai ina fada maki tunda watarana ta fito Al'amin yasasu Hassan suka kwara mata ruwan sanyi sannan suka jefe shegiya da duwasu suka farfasa mata fuska kinga yanzu wata shida kenan  harda yan kwanaki amma mayyar bata sake fitowa ba kamar ma bata gidan, a duniyar nan babu abinda na tsana sama dana bude idona naga yarinyar nan shegiyar mai kama da aljanu" dariya sosai Shamsiya tayi, tace "to aike kawata tantirancin naki karami ne in nice ke kawar da ita kawai zanyi na huta, kin tuna Laila kanwar mijina danaga zata hanani rawar gaban hantsi ai kawar da ita nayi daga duniyar kuma har yanzo maganar da nake maki ba'a gano nice na kasheta ba, kinsan fa so tayi ta tona min asiri Alhaji baya gari Yusuf yazo wajena muna jin dadin rayuwar mu ashe yarinyar tasan ina kawo maza cikin gidan, ranar mun fito nida Yusuf zan rakasa waje kawai na ganta a labe a bakin kofar bedroom dina aiko a ranar na aikata barzahu","to aini kawata bazan iya kashe mutum ba ","ai shiyasa nace miki tantirancin naki karami ne amma da zaki jarraba kawar da ita da kin huta kawai","to zan gwada dai naga kozan iyayi","waini ya mutumin naki ne","wafa","Ahmad mana","ohoo jiya ai tare muka wuni dashi a shahara Hotel kinsan cewa Aminu nayi zanje gida Innata batada lfy shine fa naje muka wuni dashi ko gidan ma banje ba, muna rabuwa dashi nayo gida saboda ganin magariba ta kawo kai" ,"gaskiya ne Hassana kina sha'aninki" wani irin makirin murmushi Hassana tayi, "yoo shamsiya in kace zaka zauna da namiji daya ai kana tare da wahala","to aike gwara mijinki yana gari nifa nawa sai inyi wata biyu batare dana ganshi ba, yana chan wajan aiki, shiyasa nake holewata da yara kanana yan ashirin zuwa ashirin da biyar" haka dai suka cigaba da yar iskar hirar tasu har Shamsiya tayiwa Hassana sallama ta rakata wajan motarta ta tafi

         *Jamal* 

________Yauma kamar kullum da wuri yaje asibiti dan lokacin daya je ma lokacin aketa sharar asibitin, kai tsaye office dinsa ya nufa yana zuwa ya tarar an gama gyara masa shi, zama yayi yana duba wasu file na wata yarinya yar kimanin shaikara goma sha hudu da sukayiwa tiyata jiya da daddare sun gargadi  iyayenta akan karta ci abinci ashe shine yarinyar ta damesu da kukan yunwa takeji shine suka bata biscuit taci aikin ya lalace toshi sam bashida lbr da yake baiyi aikin kwana ba jiya shidai yasan tare dashi akayi mata aikin suna fitowa daga tiyata room ya shirya ya tafi gida, da sauri ya fito daga office dinsa ya nufi dakin da aka kwantar da yarinyar harda hadawa da gudunsa, yana zuwa ya tarar yarinyar tana wani irin numfashi ga bankarewar da takeyi, lallai dole ne ya kori wanda ya rubuta bayani akan yarinyar amma yaki fadawa likitocin da suke duty dare su sake shigar da yarinyar tiyata a cire biscuit din dataci, da sauri ya kirawo sauran likitocin aka shigar da yarinyar tiyata sai da suka kwashe awa daya cir sannan suka samu komai ya dai daita turota akayi zuwa dakin da aka kwantar da ita, fitowa Jamal yayi yana goge zufar da take goshinsa gaba daya ransa a bace yake, yana shiga office ya duba wacece tayi night duty jiya? sunan Yesmeen ne ya bayya, sawa yayi aka kira masa ita jiki na rawa ta shigo office din dan ta rigada ma tasan laifinta, bayan ta rubuta abinda ya faru da yarinyar tana kokarin ta kaiwa  Dr Muhseen file din Khalid ya Kira ta akan yana jiranta a waje shine kawai ta aji file din a office din Jamal tay I tafiyar ta, tunda ta shigo yake watsa mata banzan kallo, "kece kikayi night duty jiya? " daga masa kai tayi, "zaki bude baki kiyi magana ko saina kira miki police kinsan kuwa kisan kai kikaso kiyi badan Allah yasa yarinyar nan tana da sauran numfashi ba da mutuwa zatayi, shine da kika rubuta baki kaiwa daya daga cikin likitocin ba shine kikayi tafiyar ki dan ba taki lfy bace ba ko" ya fada a tsawace, itadai ta kasa magana sai zazzare ido takeyi takardar sallama daga aiki ya rubuta mata ya mika maga, "dan Allah Sir karka min haka","zaki tafi salin alin ko kuwa na kira police su hukunta ki na kokarin kisan kan da kikayi" tana jin haka ta dauki takardar ta fito daga office din tana kuka, zama yayi akan kujera yana sauke numfashi.

Share fisabilillah.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post