Wata Sakayya Page 17 By Nusaiba Alkamawa

Wata Sakayya Page 17 By Nusaiba Alkamawa

Wata Sakayya Page 17 By Nusaiba Alkamawa

WATA SAKAYYAR

        (Sai a Lahira)

By

            Nusaiba Alkamawa

Number marubuciyar : 07036162215 

Free page 17

**

Idonsa a rufe yaji an turo kofar office din an shigo ko bai bude idonsa ba yasan cewa tabbas daya daga cikin abokansa ne dan babu wanda yake shigo masa office kai tsaye ba tare da naiman izininshi ba saisu, waje Khalid ya samu ya zauna yana kallon Dr Jamal a hankali ya bude idonsa da suka rune saboda bacin ran da tashin hankalin da yake ciki yanzu da ace yarinyar nan ta mutu to da tabbas masu kula da hakkin dan adam sai sun rufe masa asibiti, asibitin da mahaifinsa yasha gwagwar maya dashi kafin Allah ubangiji ya dauki ransa, shi kuma ya dora daga inda mahaifinsa ya tsaya duk da irin jajircewar da taka tsantsan da yakeyi wajan ganin ya kula da asibitin sa daya shafe shaikara da shaikaru yana kula dashi sai yau rana tsaka wata banza zata lalata masa aiyukan daya shafe shakaru yana wahala dashi duk dan ganin asibitinsa ya samu lambar yabo shine cikin awowin da basu wuce sha biyu zata lalata masa komai, Khalid ganin Jamal yayi shiru yana kallonsa kamarma hankalinsa baya wajansa idonsa ne kawai akansa, "Jamal" ya kira sunan sa ya katse masa tunanin da yakeyi, "Jamal mai yasa ka kori Sweetheart dita daga aiki, ai kodan soyayyar dake tsakani na da ita yakamata ka dunga daga mata kafa koda kuwa mai tayi maka" sake da baki Dr Jamal yake kallon sa anya kuwa yarinyar nan ba wani abu ta bawa Khalid yasha ba, in ba haka ba taya zaice komai ta aikata bai kamata ya koreta daga aiki ba, "Jamal magana fa nakeyi maka amma kayi shiru kana kallo na","to ai maganar taka batayi kama da tamasu hankali ba shiyasa nake kare maka kallo danna tabbatar ba wani abun mayen kasha ba yasaka fadar haka, kisan kai fa tayi kokarin aikatawa da yanzo ace yarinyar ta mutu da mai kake tunanin zai faru? " shiru khalid yayi yana jinjina kisan kai taso aikatawa, amma shi ai ce masa tayi babu abinda ta aikata kawai yana zuwa ya mika mata takardar sallama daga wajan aiki ashe karya takeyi, "Jamal kayi hakuri ai bansan haka abin yake ba, ni bari naje na duba mararsa lafiya" ba tare da Jamal yace komi ba Khalid ya tashi ya fita daga office din da kallo Jamal ya bisa yana masa fatan shiriya na wannan biye biyan matan da yakeyi, yana komawa office ya tarar da Yesmeen tana safa da marwa jira kawai take ya dawo taji yadda sukayi da Dr Jamal din zama yayi akan kujera yana sauke numfashi, "Sir ya kukayi dashi?" da wani shegen kallo ya bita, "ashe kinsan abinda kika aikata ya chanchanci a kore ki daga aiki harma a hadaki da yansanda shine ni kuma kikace min babu abinda kikayi masa ashe wawa kika maidani wanda baisan abinda yakeyi ba, dalla fice min daga office kuma wllhi ko minti biyar kika kara a cikin asibitin nan to ina mai tabbatar maki da yan sanda zamu hadaki" sake da baki da hanci take kallon sa mutumin da yake ririta ta kamar kwai lokacin da yazo mata da bukatar sa shine yanzu yake mata tsawa har yana korarta daga inda yake, lallai namiji badan goyo bane ba dan kunama ne, "wato ka gama cin moriyar ganga shine zaka yarda kohonta ko? to wllhi baka isa ba, bari kaji na fada maka yanzu haka ina dauke da cikin yarka ko danka","ke dalla wace magana kikeyi taya zai zama cikina bayan ke motar kan titi ce duk wanda ya gadama hawa yakeyi, kinga fitar min daga office banason akuyanci" dariya ta kyalkyale da ita, "to idannan harni zan maka akuyanci to kai kuma buntsuranci kake min" a zafafe ya daga hannu zai wanka mata mari yaji an rike masa hannu, Muhseen ne ya rike hannun wanda shigowar sa office din kenn saboda cacar bakin da sukeyi yasa har ya shigo basu sani ba kuma duk abinda suke cewa babu abinda baiji ba saboda ya dade a bakin kofar office din jin abin nasu yana naima ya zama fada yasa shi shigowa, "kee bace daganan ko yanzu in kira a fitar mana dake" sumi sumi ta fito daga office din saboda gaba daya group din su Jamal ana mugun tsoronsu a asibitin. 

shima Khalid abinda yasa ta rainasa shine mu'amalar banzar data ringa shiga tsakanin su shiyasa raini ya shigo ciki, bayan fitar ta Muhseen ya dawo da kallonsa kan Khalid da yaketa huci, "yanzu Khalid ina ranar irin wannan abin, kai kenan bazaka daina mu'amala da mata ba kaga fa duk group dinmu kai kadai ne mai wannan dabi'ar ba dole yara kanana sa'anin kannan ka su rainaka ba dan Allah ka daina kaji abokina babu kyau Allah ya haramta mana mu'amala irin wannan indai bada matanmu wadanda suke maharraman mu, idan kuma bazaka iya dainawa ba to kayi aure" jinjina kai Khalid yayi ba tare da yace komi ba ya koma ya zauna shi kuma Muhseen ya fita daga office din, da kallo ya bisa yana ayyana tabbas fa abinda Muhseen ya fada gaskiya ne insha Allah zanyi kokari na daina ba'izinin lahi ta'ala.


"A gaskiya Jidda yau ko bashin kudi saina aro nazo na kaiki asibiti wannan kwanciyar da rashin cin abincin naki na kasa gane kansu gashi duk kin bi kin rame kin lalace, kullum ace mutum yana kwance kuma a hakan kice lafiya kike ina wllhi da sake" Asabe ta fada tana daukar hijabinta ta fito tanata zabga sauri hankali a tashe, "Asabe lafiya ina zuwa haka naga kinata sauri kamar zaki tashi sama","uhmm wllhi Garzali lamarin Jidda ne ya fara bani tsoro yarinya duk tabi ta fige ta lalace dazu fa har sandarewa ta rikayi amma duk da haka wai sai tace lafiya take, kuma ni gashi banida kudin da zan kaita asibiti kasan yanzu watan mu na hudu kenan Hajiya bata biyamu albashi ba yanzu ma aron kudi zanje ko Allah zaisa na samu" jinjina kai Garzali yayi na rashin imanin mutanan gidan ace babu ruwan su da yar marainiyar Allah ko mutuwa ma zatayi basu damu ba, "kuma kinga nima Asabe banida kudin wllhi da saina baki a kaita asibitin" ya fada cike da alhini, "karka damu nasan da ace kana dashi da zaka bayar bari naje ko Allah zaisa a dace" fatan dacewa yayi mata sannan ya koma kan benci ya zauna cike da jimami, saida Asabe ta kwashe kusan awa daya bata dawo ba chan saigata ta shigo jiki a sanyaye, da sauri Garzali ya miki yana tareta, "wllhi Garzali duk inda nake tunanin zan samu aron kudi amma naje ba'a dace ba kasan yadda ake wahalar kudin nan yanzu bansan yadda zanyi ba wllhi ga jikin yarinyar ya matsa wllhi","to maizai hana kije ki samu Hajiya ki fada mata halin da ake ciki ko Allah zaisa a dace","haba Garzali sai kace bakasan wacece Hassana ba kafi kowa sanin irin kiyayyar da takeyiwa Jidda","hakane amma dai ki jarraba zuwa","to ba'akin ta mutum bari naje" haka ta nufo babban falon gidan jiki a sanyaye tana shiga ta tarar da Hassana tana kokarin hawa sama, gaishe da ita tayi sannan ta kora mata bayanin abinda ya kawota, wata uwar shewa Hassana ta saki harda gud'a ma, "ashe har yanzo bakisan wacece Hassana ba" ta fada tana nuna kanta, "to bari kiji wllhi ko sisina baza tayi kuka ba akan wacchan miskiniyar, ni wllhi dama zata mutu kowa ma ya huta dana fi kowa farin ciki, kinga bace min da gani inada abinyi kinjiko" haka Asabe tafito daga falon ranta duk babu dadi lokacin data fito Garzali baya bakin get shiyasa ma kawai ta wuce bangaransu na yan aiki, da sallama ta shiga dakin amma mai zata gani Jidda ce sai jijjiga takeyi wani irin farin abu na fitowa daga bakinta da sauri Asabe ta karasa ta riketa amma bata daina jijjigar ba, chan kuma kamar wacce aka zarewa rai saita daina motsi gaba daya jikinta ya saki, babu inda yake motsi hannunta asabe ta kama amma saitaga ya koma lagob, wani irin ihu ta kurma tana kuka ta fito waje a guje da sauri Garzali ya taso wanda dawowarsa kenan saboda yadda yaga ta fito a birkice tana kuka, "shikkenan  Jidda ta mutu mun kasa rike amanar da aka bar mana kaico na da wannan rayuwa" shi kansa garzali suman tsaye yayi jin abinda Asaben ta fada.

Wata sakayyaar Fans kutaya jiddah da addua domin jidda ta rigamu gidan gaskiya 😭

Shere fisabilillah.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post