Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 13 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 13 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 13 - Novels Elite

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 

 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)


👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽

By

            *Nusaiba Alkamawa*

Dedicated to my  sister *jiddah alkamawa* and *yaya jamal* 

 Free page 13

*******

Haka Jidda tayi wunin ranar a kwance gaba daya jikinta ciwo yakeyi mata, abinci rana ma da kyar taci shima saida Asabe ta matsa mata sannan taci tasha magani sannan bacci wahala ya dauke ta, ba ita ta tashi ba sai la'asar tana tashi tayi sallar la'asar sannan ta zauna akan keken ta saboda ta gaji da kwanciyar, tana zaune ta tuno iyayanta da ace suna raye da babu wanda zai kaita jindadi a wajansu, amma ya zatayi da abinda Allah ya riga ya rubutosa, dole saiya faru "Allah ka bani ikon cinye wannan jarabawar" ta fada a fili hawaye masu dimi suka silalo da idonta zuwa kan kumatunta a hankali ta saka gefen hannunta ta goge, dole ne in koyawa kaina hakuri da juriya domin kuwa idan har zan rika saka abin a raina yana damuna sai hawan jini ya kamani bayan cutar da nake fama dasu, dole ne in koya wa kaina juriya da jajircewa, haka dai na cigaba da sakawa da warwarewa har aka kira sallar magariba, bandaki ta shiga ta dauro alwalla sannan ta fito ta tada salla, tana salla Asabe ta shigo itama ta tada sallar bayan sun idar ne Asabe take tambaya ta, "a kawo miki abincin ne" nuni tayi mata da bazata ci abinci ba, amma in akwai tea zata sha"to bari na hado maki da akwai a flasks" daga mata kai tayi ita kuma Asabe ta fita danta hado mata, a sace ta hado mata tea din mai kauri sosai ta kawo mata saboda Hassana ta hana a rika bata tea da madara, wai saidai tasha bunu tunda ba ubanta ne ya siya musu madarar ba, karbar tea din tayi tana sha a hankali Asabe kuma kara fita tayi danta kammala aikin da takeyi, Jidda nayin sallar isha tasha maganinta ta kwanta saboda har yanzun batajin dadin jikinta ga ciwon da kafarta takeyi, tun daga ranar da abinnan ya faru Jidda bata kara fitowa ba gashi yau har an kusa shafe wata daya da faruwar abin, duk da tanason fitowa amma sai Asabe ta hanata fita haka dole zata hakura badan taso ba, "Mommy kinga mayyar yarinyar chan bata kara fitowa ba ko","ai na gaya muku karku sake kuna barinta tana fitowa inba haka ba kuza tana kunya ta wa a idon duniya domin kuwa za'ana tsokanar ku yayar ku gurguwace kuma kurma ce bata magana, to garama kar kuna barinta tana fitowa yadda babu ma wanda zai ganta balle har asan tana gidan ba, duk kuwa ranar da kukaga ta fito ku lakada mata tsinan nan duka","nifa wllhi Mommy na tsani yarinyar nan, wllhi na tsani in bude idona in ganta a raye, kinsan Allah Mommy da za'a wayi gari yarinyar nan ta mutu da sai nafi kowa farin ciki" wani irin murmushin farin ciki ne ya subucewa Hassana ganin ta ruwan sanyi ta dasawa yaran nata kiyayyar Jidda a cikin zuciyar su.

"Jidda kinga Hassana ta aike ni bari naje na dawo, kuma dan Allah karki sake ki fito kinga Garzali bayanan kuma nima gashi zan dan fita duk da ba dadewa zanyi ba, kuma kinga marar sa mutuncin yaran nan suna gida, kiyi zaman ki a daki har naje na dawo kada ki fita suyi miki rashin albarka" jinjina mata kai Jidda tayi ranta fari sol saboda murnar yau zata dan fita taga hasken rana, "saina dawo inafa dada gaya miki karki fito dan ba dama ne da dake ma zan tafi kawai sai hankalina yafi kwanciya amma bazai yu ba" Asabe ta fada tana ficewa daga dakin tana tafiya sauri _sauri dan tayi ta dawo da wuri, saida ta bari Asabe ta fita da kusan minti goma sannan ta fito, tana fitowa ta tarar su Al'amin sun cika ruwa a cikin bokitai sannan saisu koma chan naisa da bokitan sai su wullo dutse cikin ruwan to inka jefo dutsan kuma ya shiga cikin bokitin to kaci wasan, da farko basu kula da ita ba saboda wasan da ya dauke musu hankali, juyowar da Al'amin zaiyi idonsa ya sauka akan wacce yafi tsana duk duniya, a fusace ya taho harta tsorata ta dauka wajanta ya nufo amma sai taga ya wuce ta ya shiga falo, ko minti biyar baiyi ba da shiga falon sai gashi ya fito hannunsa dauke da manya_ manyan kankara ta leda irin wacce ake daurawa dinnan, a cikin bokitin ya saka kankarar saida ya bari ta narke ruwan yayi mugun sanyi, sannan yace wa Hassan da Usaini "ku taho zamuyi wani kalar wasan" da sauri kannan nasa sukayo wajan da yake, yace '' ku kama min muje mu zubawa wacchan mayyar dama ba munce mata karta kara fitowa ba, shine saboda kunnenta na kashi ne ta fito to kuzo muyi maganinta" ya fada cike da mugunta, cikin murna suka kama masa bokitin Allah sarki Jidda baiwar Allah batasan abinda yake faruwa ba hankalinta nachan wani wajan sai jin saukar zuwa mai tsananin sanyi tayi a jikinta duk da yawan ruwan basu sauki bokitin ba saboda rashin tausayi duk da kakkarwar da takeyi saida suka juye mata shi tas a jikinta, wani irin nunfarfashi ta fara fitarwa idonta na kakkafewa amma duk da haka basu barta haka ba suka rika daukar duwasun da suke jefawa cikin ruwan suka fara jifanta basu daina jifanta ba saida sukaga ta daina motsi sannan suka kyaleta a wajan suka gudu zuwa cikin gidan, gaba daya duk sun farfasa mata fuska wajan idonta da bakinta duk ya kumbura idonta daya ma harya kumbura yayi sumtum, tsananin sanyin daya ratsata ne da azabar jefan da suke mata yasa ta suma a wajan tana zaune babu mai hanasu har saida sukaga ta daina motsi.

Asabe na shigowa idonta ya sauka akan Jidda da take cikin wani mummunan yanayi, a gigice ta koma kofar gidan ta tsayar da mai napep din daya sauketa, da taimakon mai napep din ta saka Jidda a cikin adaidaita sahun suka nufi asibiti, suna zuwa aka karbe su da gaggawa, dakyar likitoci suka samu ta farfado numfashinta ya dawo daidai, saida suka kara mata ledar ruwa sannan suka wanke mata ciwokan fuskarta, likitan na fitowa Asabe ta fara tmby sa ya jikin Jidda, "ki biyo ni office" yana fadan hakan yayi gaba ta biyosa a baya, saida ya zauna sannan ya maida idonsa kan Asabe yana kare mata kallo, a gaskiya yarinyar nan Allah ne yayi da sauran numfashinta a gaba, saboda ruwan sanyi daya ratsa jijiyoyin jikinta ya kamata a kiyaye ta daina amfani da abinda yake da sanyi kota sha saboda lafiyar ta, limoniya tayi mata mugun kamu, ga magungunan nan a siyo su, sannan inta farfado zamu sallameta amma ya kamata ku kiyaye" godiya Asabe tayi masa ta fito taje ta siyo magungunan daya rubuta Allah ya taimake ta da akwai kudi a jikinta, sai wajan karfe takwas na dare sannan aka sallame su suna komawa gida ta hada mata ruwa mai zafin gaske tayi mata wanka ko zataji dadin jikinta sannan ta hada mata tea mai kauri ta bata tasha sannan ta bata magani, "ki kwanta kinji" kwanciya Jidda tayi tanajin yadda cikin kashinta yake mata ciwo kamar ana daddatsa mata shi, fita Asabe tayi taje wajan Hassana, Hassana na ganinta ta mike tsaye a masifance, "waike gidan ubanwa kikaje, kuma ina aiken danayi miki","Hajiya su Alamin ne fa suka zubawa Jidda ruwan sanyi a jikinta sannan kuma suka farfasa mata fuska, yanzo haka likita cewa yayi rayuwar ta tana cikin hatsari saboda yadda sanyin ya ratsa kashi da jijiyoyin jikinta","toni mene damuwata a ciki, nama ta mutu kowa ma ya huta" tana gama fadin haka ta haye sama ta bar Asabe sake da baki.


Shere fisabilillah.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post