Daudar Gora (Chiki Ka Shata) Hausa Novel, Chapter 14 - Novels Elite

Daudar Gora (Chiki Ka Shata) Hausa Novel, Chapter 14 - Novels Elite

Daudar Gora (Chiki Ka Shata) Hausa Novel, Chapter 14 - Novels Elite

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

     14

.........Wannan dare darene na tarihin da har abadan Iffah bazata taɓa mantawa da shi ba. Badan wani abu ya faru bayan wanda ya faruba, wanda ya farunne bazai taɓa zama shiɗaɗɗe a zuciyarta ba. Kwana ɗaya tak ta kasance cikin ɗimuwa da tsananin kewar ahalinta. Wanda ta riga ta gama sallamawa ta rabu dasu kenan har gaban abada. Sai dai bayan mutuwarta suzo jana'izarta batare da ko kan gawarta an barsu matsawa ba. Sam babu wani barci koda ɓarawo da yaci galabar ɗaukarta a wannan dare. Hakama abincin da aka biyo bayanta da shi na buɗa bakin azumin da tace batacisa ba. Kuka taci ta ƙoshi har kusan rabawar dare kafin ta miƙe zuwa bayi tayo alwala ta nutsu gaba ɗayanta gaban UBANGIJIN talikai maji roƙon bayinsa. Duk da tsananin tsoro da take a ciki na kasancewa ita kaɗai a katafaren sashen haka ta dinga jarumtar son dannewa a zahiri. Sai dai duk ƙanƙantar motsi yakan saka zuciyarta harbawa da tunanin anzo kashetane.

      Tana idar da sallar asubahi barci yafa ce ya shirya, dan duk yanda take faman turesa da son ƙin yinsa sai da yakaita ƙasa, dole takai kwance kan lafiyayyen kafet ɗin dake gaban gadon kafin ƙiftawar ido ta fara sauke numfashi....

        Barci sosai Iffah tasha na tsahon lokaci mai tsayi da har sai da aka tadata ta fahimci hakan. Ƙyawawan idanunta dake cike da barci ta buɗe da ƙyar akan matar dake tsaye a gabanta kanta a rissine. Babbar mace ce mai shekaru sosai, sai dai shigarta ta tabbatar da cewa ita ɗin bakomai bace sai hadima a masarautar. Amma kuma da alama hadima ce mai babban muƙami da matsayi....

       “Barka da safiya ya Zawjata-almilki”.

    Ta katse tunanin Iffah ta hanyar gaisheta. Yunƙurawa tai ta tashi zaune idonta na a kanta, kanta ta gyaɗa da faɗin, “Mama ina kwana”. Dan shekarun girma na matar ya wuce ta zauna saita gaisheta. Sosai ta ga ruɗewa da kiɗima a idanun matar. Cikin yin waige-waige na tsoron kar wani yaji ta zube ƙasa da rawar harshe. “Ranki ya daɗe na roƙeki dan ALLAH wannan sunan yabar fita a bakinki. Kece uwa a garemu, ke kika cancanta mu kira da sunan bani ƙasƙantacciyar baiwa mai miki hidima ba. Sunana shine Diwa, zaki iya kiran Ama (baiwa), ni shugabar hadimai masu kula da tsaftar sashen Malikat ce. An kawo miki abin karin kumallone tare da wanda zasu shiryaki da hadiman da zasu kasance masu hidima a gareki”.

       Idanu kawai Iffah ta tsura mata cike da tausayawa. Sai dai komai bata iya cewa ba ta kauda idanunta zuciyarta na ƙuna na raɗaɗin ƙasƙancin da su talakawan ruman ke fuskanta a ƙarƙashin waɗannan masarautu. Hadima Diwa miƙewa tai da sauri ta fita. Mintuna kaɗan sai gata ta dawo tare da wasu mata guda biyu.

         “Ranki ya daɗe, waɗannan matan sune zasu shiryaki a yanzu”.

    Yanzun ma iyakarta ɗago ido ta kallesu kawai, sai dai batayi musu ba wajen basu damar fara aikinsu. Amma a zuciyarta ta cigaba da yin addu'a sakamakon harbawa da ƙirjinta keyi da sauri-sauri tamkar mai tsoron tunkarar wani abu. Tsaf suka kwance kitson dake kanta, dogon gashinta da mafi yawan ƴan ƙasar ta Ruman keda ya bayyana. 

    “ALLAH ya ƙara miƙi tsahon rai da lafiya, wannan lokacine na wanka”.

   Komai Iffah batace musu ba ta miƙe, dan tanabin huɗubar Kaka ne daki-daki. Da zata shiga bayi dakatar da su tai daga ƙoƙarin binta da suke. 

      Hadima Diwa dake gurfane gefe tai saurin faɗin, “Ranki ya daɗe ki basu dama dan ALLAH, dan zasu nuna miki yanda zaki amfani da kayan wankan da aka shirya dominki a ciki, su kuma gyara miki kai kawai su fito”.

     “Karki damu zanyi da kaina”.

  Ta faɗa tana mai shigewa kafin ma ta sake cewa wani abu, sai dai bakinta ɗauke yake da addu'a. Wani irin harbawa zuciyarta tayi, tareda sarawar kai lokacin da take sanya ƙafa cikin toilet ɗin sai kace ba dashi tai amfani ba da asubahi, yanzu kuma da su Diwa suka shikago sun gyarasa da ajiye kayan wankan da suka shigo da shi tare da matan, hannu takai saman kanta tana karanto addu'a bayan ta shiga toilet da tayi sannan ta ƙarasa shiga. Shi kansa bayin abin kallone a yanzu fiye da ɗazun, dan yanzu an ƙawatashine da wasu irin fure da candles ta gefen jakuzzie ɗin. Sai wasu nau'inkan ruwan turare da aka ajiye domin tai amfani da shi, sam zuciyarta taƙi aminta da hakan, atake ta dinga ɗaga tasoshin da suke a ciki tana maidasu gefe guda ta hau wankanta tana mai zubda hawayen tausayin kanta dana iyayenta da batasan halin da suke ba a yanzun suma....

  

        Koda ta fito da tunanin samun matan data bari sai taci karo da akasin haka. Domin kuwa wayam ɗakin babu kowa, sai ƙamshi mai daɗi na turaren wuta da aka ajiye ke tashi. Numfashi ta sauke a hankali, badan samun nutsuwa na abinda ke gudana ba. Sai dan samun sassaucin nauyin da zuciyarta tai mata. Kusan mintuna biyar da fitowarta ta gagara tsinana komai, hasalima bata san ta ina zata fara ba.

     Knocking ƙofar da neman izinin shigowa ya sakata ɗaga idanunta manya takai dubanta, kafin ta bada izinin shigowa tana mai janye idanun nata. Hadima Diwa ta shigo sallama kanta a ƙasa, tun'a bakin ƙofa ta zube bisa gwiyawunta. Cike da tsantseni irin na tsakanin yaro da uban gidansa murya cike da rauni tace, “Ya Zawjata-almilki! Yanzu lokacine na shiryawarki da taimakon waɗan nan mata”. Ta ƙare maganar da nuna bayanta.

        Iffah dake saurarenta tare da zuba mata ido kallonta ta kai bayan nata, kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Tai ɗan shiru na wasu sakanni tamkar mai tunani kafin taja numfashi. “Ai zan iya shirya kaina su barshi kawai”.

      Ƙasa Diwa ta sake yi da kanta da sake gurfana ƙasa sosai. “Ki gafarceni ya Zawjata-almilki. An basu umarnine, saɓawa kuma a garesu tamkar bijirewa ne?”.

           Tsantsar tausayinsu da takaici mai gimtse maƙoshi ya sake baibaye Iffah, ta nisa tare da haɗiye abinda ya tokare ƙirjinta tana mai jin-jina kai wa hadima Diwa kawai. Tamkar ƙyaftawar ido matan suka shigo su biyu. Suma dai kallonsu kawai Iffah take cike da tausaya wa. dan cike da girmamawa a gareta suka zube gwiyawunsu a ƙasa domin gaisuwa a gareta kasancewar bana ɗazun bane. 

        “Dan ALLAH ku miƙe”.

Ta faɗa cikin wani irin yanayi daya saka matan ɗan ɗagowa suka dubeta. Su ɗin ababen tausayine, amma sai sukaji itace suke tausayi fiye da kansu. Umarninta sukabi duk suka miƙe ɗin, suna maiji da kallonta da matuƙar girma a idanunsu duk da ƙanƙantar ta, dan kuwa itace mafi ƙarancin girma a cikin Zawjata-almilki da aka kawo daular ruman.

         

       Sun mata shiri irin na Zawjata-almilki data isa a kirata da wannan sunan. Dan ƙwalliyar tata ta dace da halittar ƙyaƙyƙyawar surar jikinta da ƙyawunta. Ta cancanci a kirata Malikat Fareedah bayan Zawjata-almilki duk da ƙanƙantar shekarunta. Saboda duk da damuwar dake shimfiɗe a ƙyaƙyƙyawar fuskarta hakan bai hana bayyanar fitar kwalliyar ƙawata kwarjininta da cikar haiba ba. Su kansu hadiman dake zagaye da ita sai faman satar kallonta suke. Bawai dan tafi duk sauran Zawjata-almilki da suka shuɗe ƙyawu ba, kawai natan ya matuƙar ƙayatar dasu ne batare da sun san dalili ba. Ita a karan kanta kallon kanta take dajin tamkar ba ita ɗin bace, bawai dan ƙyale-ƙyalen gold da diamonds da aka ƙawata adon jikin nata da shi ba. Hasalima sune abu na farko da takejin tsantsenin gani a jikinta.

       Hadima Diwa data sake neman izinin shigowa ta shigo a gabanta ta sake zubewa tana mai satar kallonta itama. Cikin jinjina girma irin na UBANGIJI mai halittar abinda yaso a yanda yaso ta isar da saƙonta kamar haka....

          “Ya Zawjata-almilki! Yanzu shine lokacin karin kumallonki”.

      Iffah da takurar ta fara gundurarta ta saurin tarar numfashinta, “Bana buƙatar cin komai nikam Mama”.

     Tamkar hadima Diwa zatai kuka, muryarta har rawa take wajen faɗin, “Ki gafarceni ranki ya daɗe. Wannan suna bai dace da niba, jinsa a harshenki zai tabbatar da hukunci mai tsanani a gareni. Hakama rashin cin abincinki a yanzu”.

   (Ya rabba).

Iffah ta ambata a zuciyarta cike da takaici dajin sake tsanar Tajwar Eshaan dama duk mai faɗa aji na masarautar. Bata sake magana ba ta miƙe suka fito da hadima Diwa. Dan matan da suka mata kwalliya tuni sun fice su. Babu kowa a ƙaramin falon da Diwa tai mata jagora, inda aka shirya abinci kala-kala kai kace su goma zasu cisa. Ita a rantama tunani tai ko tare da Tajwar Eshaan ɗinne ma. Sai da taga har takai zaune Diwa na ƙoƙarin fara haɗa mata abincin ta tabbatar domin ita kawai akayi kenan. Komai batace ba, har Diwa ta gama buɗe abincin duka alamar taga wanda take buƙata kenan. Komai kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta, da ga ƙarshe ta nuna mata dafaffiyar madara kaɗai. Diwa tai jimm kamar mai tunani, sai kuma ta saci kallon Iffah ɗin tai saurin maida kanta ƙasa. Iffah da duk ke kallonta ta ƙasan ido ta cigaba da nazarinta harta kammala zuba mata madarar. Gabanta tazo ta ajiye, harta yunƙura zata miƙe ta dakatar da ita.

       “Bani zan sha ba ai mama naki ne”.

    A wani irin matuƙar hargitse Diwa ta ɗago tana duban ta, jikinta har wani karkarwa yake. “R....ran...ki ya daɗe w...w..wan nan ai ba hurumina bane”.

         Iffah data kafeta da idanu ko ƙyaftawa batayi ta janyesu a hankali tana mai miƙewa abinta batare da tace komai ba. Da sauri Diwa ta ƙara gurfana a gabanta tana hurwa. “Ranki ya daɗe dan ALLAH karkice bazakici komai ba, dan komai anan umarnine”.

      Bata zauna ɗin ba, ba kuma tace komai ba. Sai ma ɗakin da suka fito data nufa zuciyarta cike da nauyi. Batafi zaman mintuna biyarba wasu mata da batako musu kallo biyu ba suka iso da wata hamshaƙiyar riga mai kamar alƙyabba daga Malikat. Tare da umarnin tafiya da ita. Batai musu ba, dan a nata tunanin Malikat Bushirat suke nufi, sai dai zuciyarta ta kasa nutsuwa. Addu'a ta shiga ambato a zuciyarta har suka kammala saka mata ƙawatacciyar rigar alƙyabar mai tsananin ado da ɗaukar idanu, zasu kunna mata turaren wuta da suka shigo da shi a burner tai saurin dakatar da su. 

      Kallon juna sukai, kafin ɗaya tai saurin faɗin cikin ƙanƙan da kai, “Ya Zawjata-almilki wannan umarnine daga Malikat”. 

      Yamutsa fuska Iffah tai tana mai kallonta, kallo irin na wannan bata san wacece autar Babiy ba ta ɗauke kai. A karon farko tun shigowarta gidan tai magana da harshen ƙarfin zuciya ta ajiye rauninta a gefe. “Ni kuma wannan umarnina ne bana buƙata. Sai kumuje umarni na gaba”.

       Babu wanda a cikinsu baiji yayi sumar wucin gadi ba. Sai dai wani irin kwarjininta da jin shakkarta ya gama ɗarsuwa a zukatansu lokaci guda.. Iffah dake jin jininta na wani irin tsitstsinkewa ta sake dubansu da niyyar magana, tamkar wadda aka jefa da narkakken ƙarfe taji yafff! A ƙirjinta. Da sauri ta dafe ƙirjin tana mai rumtse idanunta. Rawar da jikinta ya farayi ya sata zubewa ƙasa tana mai ƙoƙarin ambaton sunan ALLAH, amma hakan ya gagara, dan tamkar an naɗe zuciyartane da harshenta a lokaci guda......


         Har rige-rigen fita hadiman nan sukeyi jikinsu na matuƙar rawa. Diwa dake zaune a falo tana jiran fitowarsu ta miƙe da sauri tana tambayar lafiya? Babu wanda ya saurareta a cikinsu suka fice. Hankalintane ya tashi, tai kamar zata bisu sai kuma ta fasa ta nufi ɗakin da Iffah take. Wani irin mugun bugawa ƙirjinta yay damm. Innalillahi..... ta shiga ambata dayin kan Iffah dake ta faman juye-juye a ƙasa, cikin ƙanƙanin lokaci ta jiƙe sharkaf da zufa tamkar an watsa mata ruwa koma an tsamota a ciki. Harta kusa kai hannu kanta sai kuma taja baya da sauri cikin tsoro. Ina bai kamataba, matsayinta na hadima hanunta ya taɓa Zawjata-almilki. A daburce tai waje da nufin isar da saƙo ga Malikat Bushirat duk da bata da tabbacin samun iso cikin sauƙi........✍


*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*



_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 90165991


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post