*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 41
Latifa ce ta fara gaidashi,sannan ta kauce ta basu waje,falon ya zamana iya su yasu.
Cikin baqunta tadan motsa kadan tana gyara zamanta gami da hade jikinta waje daya,kamar yadda ummu ta koya mata duk sanda wani baqo ya shigo sassansu,koda kuwa cikin mazan gidansu ne yayyenta 'ya'yan kawunnanta
"Sannu da zuwa" itama fa fada kamar yadda su mimi suka fada,ba wani sakin jiki ko alamun sanayya a tattare da ita, yanayin da yayiwa hafsat dadi qwarai,ta kuma sake sanya idanu a tsakaninsu,tana kuma karantar yadda kowannensu ke nuna baqunta ga dan uwansa
"Sannunki,kin wuni lafiya?"
"Lafiya lau" ta amsa masa idanunta na a qasa,yayin da nasa hankalin yake kansu mimi,sai ya miqe dasu yana bare ma nawwara chocolate din daya shigo musu da ita.
"Babu wani abu ko?" Yayi tambayar a wannan karon yana watsa idanunsa a kanta,ta girgiza kai da sauri
"Ma sha Allah" ya fada yana kama hannun yaran,a sannan hafsat ta miqe,fuskarta fal murmushi
"Amarya ki dinga sakin jiku mana kinji?,ba haka ya kamata ki marabci angon naki ba" sakato widad din tayi tana jin nauyin maganar hafsat din,zancan kuma yana mata girma
"Ina zuwa bari.naje,ki shirya xamuci.abincin dare tare kinji ko?" Hafsat din ta fada tana danne dariya,yadda widad din tayi wuri wuri yayi mata dadi,bata amsa mata ba har ta fice.
Sam batasan yana tsaye a wajen ba sai da tazo giftawa tana sauri don ta cimmasa saiji tayi an damqo hannunta,ya kuma jawota xuwa gabansa.
Hannayensa ya sanya ya zage bayanta dasu,suka tsaya dab da juna suna ma juna kallon cikin idanu,ita ta fara janye idanunta,sabida bata fiya jurewa kallonsa ba,akwai wani irin kwarjini mai yawa cikin idanunsa,shi kuwa ci gaba yayi da.kallonta,irin wannan kallon yana tada masa feelings sosai a kanta,yana kuma karantar abubuwa masu yawa dake kwance a zuciyarta ta cikin idanun nata,saidai ya fuskanci ta koyi dabi'ar kaucema idanunsa din.
Dan gyata tsaiwarsa yayi yana sake matsota kusa da jikinsa,duk da cewa ba irin wannan yanayin da scent din yake son samu daga jikinta ba.......zaya so ace tana fidda kalar launin qamshin daya daga cikin turarukan da yafi so,yake kuma siya ya ajjiye mata komai tsadarsu
"Wai kin daina kishina ne?" Ya fada da wata irin cool voice,ita kadai tasan abinda ya saukar mata a zuciya,inda yasan yadda takejin zuciyarta a duk sanda yake magana kawai da wata macen,da wala'alla har ya mutu bazai sake kallon kowacce diya mace ba baya ga mahaifiyarsa
"To amaryar taka ce naga bata iya komai ba,kaima kuma baka iya rainon da aka kawo maka ba" yadda tayi maganar yadan sansano sautin kishi a ciki,duk da yaso jurewa amma saida murmushi ya subuce masa,sai ya saketa kamar yadda taketa kiciniyar qwacewa daga hannunsa,yasan zata ce masa kada yara su gansu
"Tunda gaki basai ki tayani rainon ba" baki ta tabe
"Saboda ni ka aurowa ita?,yanzun ma......" Maganarta ta yanke sanda ta fuskanci gangancin da take shirin aikatawa,saita waske
"Yanzun ma tausayinta nakeji,an aura mata tsoho" ta qarasa fada tana yin gaba,taku uku ya cimmata,sannan ya bata amsa
"Tsohon ashe yayi.kasuwa,tunda har ya samo qaramar yarinya ko?" Cikin Zuciyarta sai taji kamar.magana ya gaya mata,don haka taja bakinta ga tsuke,bata sake saka.baki.akan magabar ba,gudun kada ta tafka shirme tana samu tana tsallakewa da qyar.
Yana shiryawa yana mata magana cikin hikima akan ya kamata ra gyara dakin yaran dama nata dakin da kyau,baki ta tura,shi kome qoqarinka me yasa sai ya cika gyara?,sai yayi challenge naka?,duka ba hidimar dafa masa abinci ke cinye mata lokacin ba?,ita sai taji har ta qagu ya koma Kaduna,ta yadda zata samu ta miqe qafarta da kyau.
Tana gama sallar isha'i ta shiga wanka saboda tuna alqawarin data daukarwa anty deena,data fito ta shirya cikin kayan bacci kai tsaye,wasu riga da wando ne kalan pink da suketa burgeta cikin kayan lefanta,dama Allah Allah take ta sakasu,tana gamawa ta maida hijab dinta tabi lafiyar gado tana hamma,yau ma a nan dakin zata kwanta tare da latifa,idan suka kwana tare sai tayita jin kamar ummu.
Dai dai sanda take rufe bakinta sabida doguwar hammar bacci da taketa saki latifa ta turo qofar dakin,shigowarta kenan bayan ta maida kwanukan da sukaci abinci daki
"A'ah,me zan gani?,yauma?" Ta fada tana kama baki,sai widad din ta waiwayo tana dubanta
"Me nayi?"
"Ke da zaki wuce ki tafi dakin mijinki?"
"Dakin miji kuma umma latifa?,kamar wata 'yar iska?" Tayi maganar tana maida kanta saman pillow ta dora da cewa
"Yanzu da kanki kike cewa ma naje dakin wani" dariya taso qwacewa latifan,lallai da gasken gaske wauta da quruciya sun yiwa widad din yawa,saita qaraso gefan gadon ta zauna tana qoqarin fahimtar da ita.
Sam widad din ta gaza kai hankalinta kan abinda take nufi,sai ma tubure mata da tayi kan babu inda zata,dai dai lokacin hafsat tazo kiranta tazo suci abinci,nan ma tace ta qoshi ba zata ba,ran hafsat din ya mata dadi,amma duk da haka a gaban latifa dashi kansa abbas din saita nuna bataso haka ba
"Rabu da ita,yi serving dina" ya fada kansa tsaye sanda yake dan diban abincin kadan kadan yana baiwa nawwara a baki,wadda tayi dare dare saman cinyarsa,saita soma zuba masa abincin,amma bata rabu da zancan ba,don lallai ta nuna masa ita ba'a son ranta ba,har sai da yace
"Will you keep quiet madam?,ko sai na saka gum dina na rufe miki bakin?" Ya fada yana jifarta da hararar wasa
"Kai bakasan na fika farinciki da haka ba" ta fada cikin ranta,amma a zahiri bakin nata taha ta rufe,bata sake tashin zancan ba.
*********sannu a hankali kwanaki suka fara tafiya,widad cikin gidan har a sannan tana matsayin baquwa,baquwar dake ganin kulawa da damuwa daga idanun hafsat,harma taje ganin matuqar kirkinta fiye dana ja'afar,yadda su mimi ke kiranta da mommy haka nan itama take kiranta dashi,tana mata kallon da takewa anty madina ne,tana kallonta a matsayin uwa ko wata babbar yayarta,gefe guda kuma sabo ne ya shiga tsakaninsu dasu mimi da nawwara,musamman mimin,a nan sassanta suke kusan yini.
Idan ka samu widad din dasu mimi zakayi tunanin yayace da qannenta,kusan ko yaushe suna tare,sosai suke debe mata kewa,idan lokacin da zasu shiga kitchen yayi ita da latifa zasu shiga tare,to amma kusan fiye da rabin hankalinta yana kan yaran,don haka ba wani abun arziqi take tsaiwa ta koya ba.
Ta bangaren abbas shima tana masa kallo daya ne,matsayin uncle muhsin take kallonsa,saidai wani bangare na zuciyarta haka kawai yake cika da tsoronsa,ta kasa sakewa dashi kwata kwata,babu fashi,a kullum zai shigo da safe yaji basu da matsala,ya sake dawowa da dare ya tabbatar da komai lafiya,zaman cin abinci dasu kuwa ko sau daya bata taba yarda ta zauna din ba,hakan yana yiwa hafsat dadi matuqa,yadda yarinyar je tattare kanta waje daya,take kuma dari dari da komai nasa,wannan shike haska mata lallai komai zai tafi mata a sauqi.
To hakanan duk yadda latifa zata lallabata taje sashensa kona awa daya ne sai ta dawo taqi,sai tayi mata kamar bata ji ba,ta kwanta ta hau barcinta,tare suke kwana da latifa din a daki daya,gado daya,wannan yana debe mata kewar ummu qwarai da gaske.
*******A nutse cikin takun nan nashi dake nuna zallar karsashi da lafiya da tsiyayyar qirar jikin da yake dashi yake takowa zuwa harabar gidan,kunnensa maqale da waya yana amsa kira,hannunsa daya riqe da key din motarsa.
Sanye yake wani yadin kuftan mai kyau da daukar ido,anyi masa aikin hannu mai tsadar gaske,sosai kayan suka zauna masa,abbas din ba daga baya ba wajen iya saka manyan kaya,kowacce shiga daukansa takeyi,saika gaza tantance wadanne kaya ne suka fi masa kyau.
A hankali ya zare wayar daga kunnen nasa yana katse kiran, hankalinsa yana kaiwa kansu, suna daga gefan farfajiyar gidan,mimi ce da widad,widad din na daga zaune gefan wata tukunyar fulawa,sanye take da wata doguwar riga mai santsi mai dogon hannu,tana hade da hula ne daga bayanta,bata saka hular ba,tadai saketa,lallausan gashinta mai santsi da tsaho yana matse cikin qaramin band,jelar ta buya ta bayanta,fararen qafafunta na slipper blue din slippers,color din dake matuqar fidda hasken fatarta.
Mimi kedan garo mata ball,itama tana daga zaunen sai ta sanya qafarta ta maida mata,yau din tunda ta tashi bata da wani cikakken kuzari,shi yasa ma tace wa latifa ba zata shiga kitchen kallon girkin yamma ba,itama bata matsa mata ba,ta barta suka fito da mimi din,wadda hafsat ta tafi unguwa ita da nawwara,ta barta a nan,don qememe taqi binta,ba kasafai ta fiya damuwa da bin hafsat din unguwa ba,tafison zama da widad.
Idanunsa ya janye dsga kanta ya nufi parking space,yana hangosu har sannan ta cikin mirror din,shi kansa a yau sai yaga babu wannan kuzari da kazar kazar din daya santa dashi,idanunsa ya kuma daukewa yana rufe motar ya tayar da ita ya fice daga gidan a hankali.
A nutse yake tuqinsa kamar kullum,yana tafiya yana lura da abubuwan dake faruwa saman hanya,gidan hajiya ya nufa kai tsaye,don dama a yau din can yayi niyyar zuwa,sai dare kuma ya tsara zai fita daga unguwar.
A hanya ya tsaya ya siyama hajiyan abubuwan da yasan tana sha'awa kamar yadda ya saba,sannan ya wuce,mintuna qalilan ya iso unguwar tasu.
Tun daga farkon layinsu matasan da suka ankara da shigowar tasa suka biyo bayansa, mutum ne shi mai matuqar kirki tausayi da kuma taimako,wannan ya sanya masa farinjini sosai ga al'ummar unguwar,kamar ko yaushe,bai shiga gida ba sai da ya gama sallamarsu.
A bakin qofar dakin hajiyan ya duqa ya cire Black cover shoes din dake qafarsa mai matuqar tsada da kyau,sannan ya yaye kyawawan labulayen falon dattijuwar bakinsa dauke da sallama.
Su biyu suka amsa sallamar,hajiyarsa da kuma yayarsa yaaya bara'atu,fuskar hajiyan kwance da fara'a tayi magana
"Tun dazu akacemin kana qofar gida,a raina nace qila jama'a ne suka riqeka" yana qoqarin zama a gabanta saman carfet yace
"Sune hajiya,da qyar na qwato" ya qarasa maganar tsadadden murmushin sa kwance saman fuskar sa yana duban mahaifiyar tasa,saita jinjina kai
"Ma sha Allah,mafi alkhairin mutane shine wanda yake amfanar da mutane,Allah ya qara tsare mana ku a duk inda kuke"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu" ya amsa,yaaya bara'atu tana tayashi.
Sai da suka fara gaisawa da hajiyar sannan ya gaida yayar tashi,yana tambayarta mai gidanta,sannan suka shiga hira,kafin hajiya ta kira muneera ta kawo masa ruwa da lemo.
"A qoshe nake hajiya alhmdlh,saidai kafin na wuce"
"To shikenan muneera jeki", tsaiwa tayi ta gaidashi cikin girmamawa,sannan ta koma kitchen taci gaba da aikinta.
"Nace sai yaushe zaka koma kadunan ne ango?,ko cin amarcinne bai qare ba?" Yaaya bara'atu ta fada tana gyara zamanta sosai cikin lausasan royal chairs din hajiyar.
K'aramin murmushi ya subuce masa,banda yaaya bara'atun babu wanda zasuyi irin wannan maganar dashi
"Jibi nake saka ran wucewa,hutun da suka bani ya qare"
"Sun kyauta ma ai, duka duka yaushe ka koma kadunan ma,Allah ya sanya albarka sun kyautata maka kam"
"Sosai hajiya" ya furta yana gyada kansa.
"Tafiya dai ta kama hafsat zuwa yanzu,tunda dai ai ba zasu tattare gaba dayansu su zauna anan kai kana can ba" anty bara'atu ta sake fadi tana dubansa,duk da bata da tabbacin samun cikakkiyar amsa daga gareshi,ta sani ba kasafai ya fiya son hirarraki irin wadan nan ba.
Kaman hajiyan ta fuskanci bashi da niyyar yin magana din,sai tayi amfani da wannan damar ta isar da saqon da take ta son isar masa din
"Hafsat ai dama bauchi ta zaba,widad itace abokiyar tafiya Kaduna,ita ta riga ta yankewa kanta hukunci,bana jin kuma zata janye" tsaf ya gama karantar saqon hajiyan,saidai can qasan ranshi yana tunanin yadda zai dauki rigimammiyar yarinyar da bata da maraba dasu mimi har zuwa wata uwa duniyar da sunan matarsa
"Amma hajiya sai nakega ba zataji dadi ba,daga zuwan wata sai a tafi da ita ita kuma tana zaune?"
"A'haaannn,to daa waye yayi mata?,ita ta yankewa kanta wannan hukuncin,ta kuma bada zabin ya samo mai zama dashi,meye laifi yanzun dukka a cikin wannan lamarin?" Shuru bara'atun tayi,sai ta dan jinjina kanta
"Allah ya sawwaqe" .
Shigowar fanteka ya tasheshi,ya miqe yana zuba hannayensa a aljihun wandonsa
"Bari na danje bayanmu na dawo"
"Allah ya kiyaye,sai ka dawo" hajiya ta fada kanta tsaye,tashin da yayi yayi mata,don batason wata magana sam a gaban fantekan,tunda ta karanci inda ta sanya gaba.
Ba haka fanteka taso ba,amma saita rakashi da yaqe tare da addu'ar a dawo lafiya.
*Arewabooks:Huguma*
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥