A Rubuce Take (K'addarata) page 42 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 42 Hausa Novel - Novels Elite

 

A Rubuce Take (K'addarata) page 42 Hausa Novel - Novels Elite

*H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*

      (K'addarata)


Page 42
Sanda ya dawo gidan babu kowa sai hajiyan tashi,nan yayi zamansa bayan ya fito daga sallar isha'i,yana cin abinci tana qara masa suna hirarsu


"Nidai don Allah zan riqo alfarma guda daya a wajenka abbas" tayi zancan tana ajjiye dan bowl din data qara masa miya,sai ya tattara mata hankalinsa gaba daya,har yana ajjiye spoon din hannunsa


"Hajiya badai alfarma ba,saidai umarni ko?"


"Ko alfarma koma umarni,nidai burina ka cika......don Allah ka kula da yarinyar nan kamar yadda zaka kulaa da hadiyya da kuke fito ciki daya" kai ya jinjina,can qasan ransa yana jinjina tarin qaunar da hajiyar kema yarinyar


"Na daukar miki alqawari hajiya"


"To Allah ya taimakeka,yaci gaba da dafawa al'amuranka"


"Ameen ya raheem,Allah ya qara lafiya da nisan kwana" sai ta bishi da murmushi kawai,kafin ta amsa masa da ameen.


            Yau din sassan Widad din ya fara isa,saidai latifa na bude masa qofa taja baya cikin girmamawa,har ya sanya kansa sai ya dakata


"Kuna lafiya?,baku buqatar komai?" Ya tambaya,kai ta girgiza,tana tsananin yabawa da irin kulawar da yake nunawa akan widad din


"Lafiya qalau alhmdlh,babu komai"


"Itafa?" Ya tambaya kai tsaye


"Tayi bacci tun dazu"


"Lafiya dai ko?" Ya tambayeta yana dan ritsata da ido,kusan bai taba zuwa ya sameta tana bacci ba,yafi samunta a daki,data ganshi zata fara tattare jiki waje daya,ta kuma sanyawa bakinta kwado da linzami,har sai ya gana zamansa na mintu biyu zuwa uku sannan ya fito


"Eh bata dan jin dadin jikinta ne wai"


"Subhanallah,amma me yasa ba'a kirani an kaita asibiti ba?"


"Ba zazzabi ko ciwon kai bane,kawai bata da kuzadi ne kamar yadda ta saba" sai yadan kada kai kadan


"Allah ya sawwaqe,ammmm..... Please,koda akwai wani damuwa,a kirani ko ta wayarta ne"


"In sha Allah" ta fada cikin girmamawa,cikin ranta tana yaba kulawa da sanin darajar dan adam irin nasa.


      Sanda ya shiga falon hafsa a zaune ya sameta,yaran na kwance a wajen saman carfet kowa d'ai d'ai,itama saman carfet din take a zaune,hannunta riqe da waya,plates din abinci ne da abincin da sukaci suka zuzzubar kaca kaca,saman kanta ba dankwali,gashinta dake samun qarancin kulawa qwarai da gaske daure a kyauro.


          Idonsa ya dauke daga kanta yana qarasawa wajen yaransa,saita janye qafafunta tana masa sannu da zuwa,qasa qasa ya amsa mata,yana dauke yaran daga qasa ya nufi dakinsu dasu.


         A hargitse ya samu dakin kamar ko yaushe,sai a gadon nawwara ya fara ajesu,ya karkade gadon mimi ya maidasu kai,sannan ya gyarawa nawwara nata gadon itama ya maidata kai,bayan ya duba cupboard dinsu ya canza musu wankakken zanin gado,ya tattara karikicen kayan wasansu dake tsakiyar dakin ya killace a drawer dinsu ya hade kayan wankinsu a laundry basket.


          Yana gab da kammala mopping na dakin ta turo qofar ta shigo,zuwa yanzu daurin dankwalin ture kaga tsiya ne a kanta,dinkin atamfa ce doguwar riga data bude sosai daga qasa,saidai idan ka kalli kayan sosai a jikinta zakasan ta dan sha jiki.


       "Ya daga shigowarka kuma dear?" Ta fada tana jin wani iri a ranta,shi ya fiya qaqale qaqale,banda hakan bataga wani shahararren datti da dakin yayi wanda zai hana mutum yin bacci ba,taga ko daxun kafin ta fita sai data tattare kayan wankin gefe daya,amma shi baima gani ba.


           Idanu ya aza mata kafin ya janye yaci gaba da qarasa goge wajen,sai jikinta ya dan mata sanyi daga kalar kallon da yayi mata,don haka ta saki qofar tana qarasowa ciki.


          Kafin ta qaraso ya gama,ya ajjiye mopping stick din,sannan ya goye hannayensa da tuni ya nade hannaun rigar xuwa sama yana kallonta,yadda ya aza mata kallon mayatattun idanuwan nan nasa duka sai taji nauyinsa ya sake kamata,don haka ta daburce gaba daya


"Samu guri ki zauna" ya bata umarni kai tsaye,sai tadan ja tunga,gabanta yana faduwa,bata qaunar fadansa gaba daya,yanzun nan zai sanya ka ka rasa abun fadi,bayan tasan bata da kalar kowacce hujja da zata kare kanta da ita,dole ta samu gefan gadon nawwara ta zauna.


            Daya daga cikin kujerun dake hade da teburin karatunsu ya jawo,ya ajjiyeta dab ds ita ya zauna akai.


           Shuru ya ratsa dakin,tana ta kasa kunne taji me zayace da ita,yayin da shi kuma bai furta komai ba,sai kallo da ya ritsata dashi,kallon dake sake sanyata jin cewa da gaske ita din mai laifi ce


"Hafsat" ya kira sunanta kai tsaye,wanda abune mawuyaci kaji ya kirata din


"Na'am" ta amsa masa ba tare data iya kallon qwayar idanunsa ba


"Ki gayamin me kika nema kika rasa a gidan nan,wanne nauyi ne nawa da bana sauke miki?" Motsawa tayi,kamar wadda ke zaune saman wuta,kasa bashi amsa tayi,har ya gaji da jiranta,sai ya sauke hannayensa qasa ya dafe kujerar da yake kai yana ci gaba da kallonta


"A iya sanina babu wani abu da yayi saura wanda bana miki shi,ci sha suttura,kudin kashewa,hatta da lighter da za'a kunna gas a gidan nan alhmdlh ban bari ko yarda ki siya ba,me kika rasa hafsat?,amma kin kasa tsaida hankalinki ki tsaftace gidanki,ki kula da yaranki,ki sauke hakkina dake kanki,zaki iya tuna when last da kika kawo kanki gareni?" Ys jefa tambaya mafi girma da taketa tsoron yayi mata ita


"Don Allah kada ka kawo wannan zancan,ka san dai ina iya bakin qoqarina ai......" Wani miskilin murmushin takaici ya saki


"Well......am listen to you" da qyar ta tattaro dukka jarumta da qwarin gwiwar ta,duk da cikin ranta har yanzu bata jin kanta a matsayin mai laifi


"Ina fa kwatantawa,ina qoqarina dear,aikin gida fa ba is not easy at all,sauqinta ma ace ina da 'yar aiki,amma yanzun komai fa ni nakeyin abina,ga yara,ga makarantar mimi,dole wania abun fa sai ana haquri" ta fada tana dan tsuke girarta fuskarta qasa qasa,ita ala dole bataji dadin gyaran da yakeson mata ba.


          Shuru yayi kawai yana kallon fuskarta, reaction din da ta nuna saman fuskarta ya isa ya gamsar dashi cewa bata dauki kanta a tana aikata wani abu na ba dai dai ba,an dade hakan tana faruwa a tsakaninsu


"Idan aiki ya hanaki gyara muhallin mijinki dana yaranki.....shi kuma kitchen da kika tara kwanukan wanke wanke fa?, harda na tuwon jiya?"


"Yau ai fita nayi,kuma ka sani dear,ban zauna gaba daya a gidan ba,amma gobe in sha Allah da aikinsu zan tashi,idan na gyara gobe zaka ga kamar ba'ayi ba,ba shikenan ba?" A hankali ya lumshe idanuwansa gaba daya yana kiran sunan Allah,mata nawa ne keda nauyin da yafi nata amma zaka samesu su da gidansu da iyalinsu tsaf?,wannan muguwar qazantar baisan ta yaya zai raba hafsat din da ita ba,tafi komai ci masa tuwo a qwarya,ya yiwa qazanta wani mugu tsana da har baisan iyakarsa ba,abinda hafsat din har kwanan gobe ta kasa ganowa,mai aiki dai mai aiki dai.....shikam ba sakaran namiji bane da zai daukoma hafsat mai aiki,ya tabbatar daga qarshe ita zata koma yin komai.na gidan,qarshe harda abincinsa da zaya ci.


       Miqewa kawai yayi,ya zura hannayensa a aljihunsa


"Duk abinda ya kamata nayi miki na miki shi,ya kamata ki canza for now.....yaranki suna girma,zasu kuma dauki jalar kowacce dabi'a daga wajenki,dama sau daya tak take zuwa ma mutum a rayuwa" yayi maganar yana daga yatsansa guda daya,sanann ya juya yana barin dakin.


          Gabanta ya fadi,binsa tayi da kallo har ya fice,to me yake nufi?,abbas din yana da wuyar fahimta wani lokacin,ta janye idanunta daga kallon qofar da tuni ya jima da wucewa,ta dawo da dubanta cikin dakin,komai yayi fea gwanin sha'awa,ta tabbatar koda ita tayi wannan gyaran bazaiyi kyau haka ba,to itadai bataga laifi ba,idan ma yayin ba duka yaransu bane shi da ita?.


        Taso sharewa itama,amma sai zuciyarta ta gaza nutsuwa da hakan,wannan dalilin yasa ta bashi kusan awa guda,sannan ta tattara kayan abincin tana ta mita a ranta na wahalar da ya bata na diban abincin tayi sashensa.


           Da sallama ta tura qofar bedroom din nasa,sassanyan qamshinsa ya fara mata maraba,babu wadataccen haske a dakin sosai,yana daga gefe saman dan table din da yake dora system dinsa yayi wasu ayyuka da suka shafeshi yana duba wasu takardu.


          Kallo daya ya mata ya maida kansa ga takardunsa,kallon da ya bata mata rai sosai taji kamar ta koma ita da abincinta,amma ta hadiye ta danne,tana da burika da yawa da takeso ta cimma,kuma anty ummee ta tabbatar mata sai ta iya mallakar kanta da kuma fushinta.


         Wani table qarami na glass ta jawo ta aza kayan a kai,tana shirin zama tace masa


"Ga abincinka nan"


"Am okay,ki kwashesu" ranta tadan bata,ta zumbura baki,kamar zatayi magana sai kuma tayi shuru,taci gaba da kallonsa,yayin da shi kuma ya aza dukka hankalinsa akan takardar dake dauke da wani zane mai kama da map,ya sani ba zata iya bashi haquri ba,abune mai wahala kaji kalmar haquri daga bakinta.


         Sai da ya gama abinda yakeyi ya ninke takardar sannan ya miqe


"Jibi zamu wuce kaduna in sha Allah" ya fadi mata don ya fita hakkinta,gabanta yadan fadi


"naji kace zaku wuce,kai da wa?"


"Widad" ranar farko da ya fara ambatar sunanta,idanu ta qanqance cikin mamaki da ba zata tace


"Na dauka a nan zaka barta ko"


"Saboda ke ba zakije ba,kowa ma haka ne?" Wani tashin hankali ne taji ya ziyarceta,me abbas yake nufi?,ita zai barta a nan,ya tasa qanqanuwar yarinya a gaba su tafi garin da yake aiki?,ita tana nan tana me?.


          Sai da tayi yaqi da zuciyarta sannan ta hadiye maganganun da su taji sunfi dacewa ta gaya masa


"Amma idan kun tafin me zata tsinana maka?,ka barta kawai a nan ta saba da dangi mu tafi tare" kai ya girgiza yana nufar wardrobe dinsa ya budeta sannan ya amsa mata


"Ai bana magana biyu,kinfi kowa sanin hakan,zancan tafiya kaduna mun rufe wannan babin dake har abada,abinda yasa na gaya miki yanzun ma don na fita hakkinki,duk weekends zan dinga shigowa in sha Allah" wani abu ya taso ya tsaye mata a wuya,wannan karon taji ba zata iya shuru ba,ta yaya zai sanya yarinya qarama a gaba su tafi har wani gari,ita din tana jingine a gefe,sai qarshen sati sannan yazo mata?,me ma tayi kenan?,abinda take gudun afkuwarsa tabbas zai afku


"Gaskiya ni ban yarda ba,saboda nice babba ni ya kamata ace na bika,ko ka bani zabi....."


"Wanne zabi zan baki?,ki manta tun kafin wanzuwarta kika yiwa kanki zabi?,hafsat kinga..... please bana son ciwon kai,zancan ya isheni haka.....ina underwears dina?" Ya jefa mata tambayar yana ritsata da ido


"Ban wanke ba" ta amsa masa tana miqewa cikin hucin bacin rai


"Good" yace da ita yana maida murfin wardrobe din ya rufe zuciyarsa na masa zafi,duk sanda yake da buqatar neat underwears saidai ya zauna ya wanke abinsa da kansa,ko kuma ya diba yakai mata,ya kuma jaddada mata amfani zaiyi dasu,wataran ta diba wasu daga ciki ta wanke masa,wataran kuma ta wanke duka idan taso.


         "Abban mimi...." Ta kirayi sunansa da kaushi, ganin bai qara bi ta kanta ba,ya nufi ma qofar toilet dinsa


"Duk haquri da kuma kawaicin da nake maka hakan bai hanaka gaza yimin adalci ba ko?,to wallahi bazan yarda ina zaune a tauyemin hakkina ba" zuba mata idanu yayi sosai fiye da dazu yana kallon zallar ainihin rashin kunya daga wajen hafsat din,eh rashin kunya mana,banda haka ta manta abinda tayi masa


"Tunda kika zabi zama a bauchi baki isa ki bini ko ina ba,kince na nema mai zama dani a kaduna kuma na samu fine....na dauka hankali kikayi kika fara gyaro kura kurenki,ashe ba haka bane,to a wannan karon ina mai gaya miki da kakkausar murya,kibi a hankali,don bazanci gaba da lamuntar halayenki ba,if not kuma.....mu zuba dani dake" daga haka yayi gaba ya bude qofar toilet din ya shige abinsa.


        Wasu qwalla masu zafi ne suka biyo kuncinta


"Wallahi zankai inda za'a qwatar min hakkina,nima na gaji" ta fadi tana juyawa da gudu gudu ta fice daga dakin.


          Sanda ta gifta sassan widad dake kulle sai taji kamar ta koma ta shiga ta shaqeta ko zata rage zugi da radadin da zuciyarta ke mata,amma wata zuciyar ta hanata,ta wuce da sauri sauri zuwa sashenta tana kuka sosai.


*Arewabooks:Huguma*


KI KULANI miss xoxo


DAUDAR GORA Billynabdul


RUMBUN K'AYA hafsat rano


IDON NERA Mamuhghee


A RUBUCE TAKE huguma


_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_


_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_


0022419171

Maryam sani

Access bank


Saiku tura shaidar biya ga

+234 903 318 1070


*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*

09166221261


*Al'ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number*

+227 96 09 67 63*Thanks for choosing us*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post