A Rubuce Take (K'addarata) page 43 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 43 Hausa Novel - Novels Elite

 

A Rubuce Take (K'addarata) page 43 Hausa Novel - Novels Elite

*H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*

      (K'addarata)


Page 43          Gefan gadonta ta zauna hannuwanta rufe da fuskarta tana kuka sosai,me yasa abbas bazai fuskanceta su zauna lafiya ba?,yasha gaya mata zai bata mamaki,bata taba zaton irin wannan mamakin zai bata ba,ba ruwansa da harkar mata,kamar ma baida damuwa dasu,wannan yasa ta saki jikin cewa duk wani mataki da zai dauka a kanta bazai wuce ya qaurace mata ba,ita kuma bata da wannan damuwar,bata da yawan buqata,tasa buqatar ma damunta takeyi.


         Wayarta ta jawo dake gefan gadon ta soma laluba number kyawunta zatayi abinda ta saba wato kai qara,saidai tana kallon agogo taga dare yayi,wata zuciyar na ingizata ta kirashi,wata zuciyar na cewa tayi haquri ta barwa safiya,saita aje wayar,amma kuma yadda zuciyarta ta cika ta tumbatsa da bacin rai da kuma fushi,sai taji ba zata iya kwana ita daya da wannan baqincikin a cikin ranta ba,don haka ta sake daukar wayar ta kira number anty ummee.


          Cikin sa'a ta shiga,tana shiga din kuma ta daga


"Ke lafiyarki a wannan tsohon daren?" Ta jefa mata tambayar jin ta fashe mata da kuka


"Anty kaduna zai dauketa jibi su tafi"


"Ita wa?,au amaryar taki?" Kalmar tayi mata ciwo,amma saita gyada kai kamar tana wajen


"To sai kuma me ya faru?"


"Na gaya masa ni.ban yarda ba,shine yake wani gayamin wai aini na zabi haka, mukayi fada dai dashi na baro masa dakin" wani tsaki anty ummee taja


"Dadina dake wallahi baki da qwaqwalwa kwata kwata wani zubun hafsatu,ke da zaki nuna murna,kice hakan da yayi shine dai dai,zasufi sabawa da juna?" Ido hafsat ta zaro,kukanta ya tsaya cak


"Anty?,suje su kebe su biyu wani abun ya faru kenan fa?,kaduna fa nake gaya miki,gidan da daga shi sai ita"


"To ubanme ma zakije kiyi a garin da baki da ko kashi?,kibar kowa naki asalinki da tushenki a nan,suje sai sun dawo,sannan ma kuma sai akace miki haka zaki barta idan sun tashi tafiyar?,tsaya kiji,bude kunnenki da kyau" tarawa anty ummee nutsuwarta tayi,duk da tanajin babu wata mafita data wuce tayi masa bore,ko ya tafi da ita ko ya aje yarinyar a gida,saidai cikin minti biyar da fara sauraran anty ummee fuskarta ta washe da farinciki.


**********Tun daren jiya bai kwanta ba sai daya tabbatar ya hada duk kayan da zaiyi tafiyar dasu ranar asabar din,idan da sabo kusan ya zame masa jiki,a shekarun da sukayi da hafsat zai iya irga sau nawa ta taba hada masa kaya wai don zaiyi tafiya ko zai koma bakin aiki.


          Bai kwanta ba sai kusan biyu na dare,a nan ma tunani ya hanashi sakat,yayita juyi from side to side,yanata bitar halayen hafsat,ya yarda matar aure ta qwarai dace ne,bai taba kawowa hafsat din zata sauya haka ba,bai taba kawowa cewa haka halaye da dabi'unta suke a zahiri ba,bai samu bacci ba sai wajen uku da rabi na dare,asuba nayi yayi alwala ya wuce masallaci.


           Bai shigo gidan ba sai wajen qarfe tara na safe,ya tsaya taron magidanta da akeyi a unguwar duk qarshen wata,kafin sannan hafsat takai ta kawo a sassansa ya kusa sau uku,so take ta aiwatar da shirinta tun da wurwuri,plan din anty ummee yafi kwanta mata fiye da nata plan din,saboda idan tanason barin garinta to tana qaunar mutuwarta.


         Sunyi sabani,tana komawa sassanta yana shigowa gidan,kamar ko yaushe a matsayin widad na baquwa sai ya fara da sashenta.


          Dai dai lokacin suna bedroom din widad din,latifa ta gama musu breakfast,harma sunci,don basa iya cin abincin hafsa,wanna yasa ma basa jiranta,itama kuma ana kwanaki biyar ta daina kawowa,saidai ta aiko a kirata tazo suyi dinner,sai akaci sa'a widad din mai wahalar sabo ce bata zuwa.


          Sabbin kaya latifa ke ware mata,saboda ta soma shirin komawa kano,amma dai bata bari widad din ta sani ba,don kada ta birkice mata


"Wadan nan kayan dasu zakici gaba da kwalliyar,kinji dai abinda anty deena ta gaya miki?" Kai ta gyada


"Bakiga kullum sai nayi abinda tace din ba"


"Eh amma har yanzu baki qara zuwa wajen uncle din naki ba,kuma na gaya miki a can ake kwana" ido ta fiddo,waisu basa jin kunya suke mata zancan ta kwana da namiji?,bayan ummu ta gaya mata ko hannunta aka riqe ciki zatayi kuma mutuwa zatayi?,kafin tace komai anyi knocking qofar,latifan tasan ba wanda zai.shigo kansa tsaye saimai gidan,don haka ta zube kayan hannunta tana yiwa widad nuni da.hannu akan ta bude qofar.


          Itakam bata gane komai ba,ta sauko daga saman gadon,ta isa bakin qofar ya buda a hankali manyan idanuwansa suka fada cikin manyan fararen nata idanun,ta saki qofar cikin rashin sabo da d'ari d'ari taja baya tana cewa


"Ina kwana?"

"Lafiya qalau" ya amsa mata yana duban kayan jikinta,kayan bacci ne riga da wando masu taushi da kauri,wandon iyakarsa qauri,rigar ce ma mai dogon hannu,ya kauda ganinsa yana sanyo kansa cikin dakin,sai tahau raba idanu tana duban latifa dake jiran ya gama shigowa su gaisa ta basu waje,gabanta tana dan faduwa.


         Gaidashi tayi ya amsa,sai ta juya ta nufi qofa,widad din batayi qasa a gwiwa ba tabi bayanta zata fice itama cikin jin tsoro


"Zo nan" ya kirata a hankali,saita waiwayo fuskarta a narke kamar zata saki kuka,ya kalli siraran labbanta jajaye data tabesu


"Bari na dauko hijabi na" ta sake fada tana sanya jelar dankwalinta tana faman boyon na shanunta da suka fara bayyana kansu ta cikin rigar jikinta.


           Dariya taso bashi acan qasan zuciyarsa,ya fuskanci me take boyewa,ko me zasu sakashi ji wadannan qananun abubuwan oho,ya fada a ransa,saiya sanya hannu ya jawo hijabin da ya gani a gefansa ya miqa mata,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,tana ta faman cukuikuye gaban rigarta ta qaraso ta sanya hannu ta karba hijabin ta zura,sannan ya nuna mata waje ta zauna.


         "Kice ta shirya miki kayanki,gobe in sha Allah zamu tafi kaduna" da farko daya fara zancan hada kaya harta fara murna,ta dauka zaya ce gida zasu,amma sai taji yana kiran wata kaduna,ta fiddo manyan idanunta waje da suka fara hada hawaye


"Kaduna?....."sai ta kasa qarasa maganar,kai ya jinjina mata yana nazartarta,ta fiya tsoro, tsoronta yayi yawa,kuma ya lura maza kawai takewa haka


"Eh,gobe da safe" shuru tayi tayi qas da kanta qwalla na zuba,bai lura kuka take ba,yamiqe yana cewa


"Bakwa buqatar komai?" Saita jinjina masa kai kawai,ya taka a hankali ya fice,cikin ransa yana ayyana yadda zasuyi rayuwa a kaduna da ita ahaka a yadda take,itama din bata wuce raino ba.


           A haka latifa tazo ta tarar da ita,ta sata a gaba da tambaya,sai ta gaya mata,sannan ta dora da cewa


"Ni gida zan tafi ba wani kaduna,wajen ummu zamu tafi" zama sosai latifa tayi tana kwantanta mata lamarin aure,ta kuma gaya mata gaskiyar ta taho kenan,ita da gida saidai ziyara,saita rude mata,ta dinga rusa mata kuka tana lallashinta,daga qarshe dai sai data kai ga kiran alhj mahmud.


       Cikin hikima irin ta d'a da mahaifi ya dinga bata baki,tare damata alqawurin zaizo can din,kuma ta fadi kome takeso zaisa a kawo mata


"Ni banason komai,kawai komai a gidan,kullum shima sai ya tambayeni idan inason wani abu" wannan magana tata ta sake kwantar masa da hankali,ta kuma qarawa abbas martaba da bayyana asalin nagartarsa,abban nata bai barta ba har sai da ta sake sosai sannan sukayi sallama.


        Tsaf latifa ta hada mata kayan da dukka tasan ya kamata ta tafi dasu,itama ta faka nata kayan a boye.


          Bayan fitarsa sassan hafsat din ya wuce don yaga yaransa,a falon yayi sallama,sunata wasa da kayan bacci a jikinsu,babu alamun an musu brush da alwala ba bare wanka,fuskarsu duk jirwayen bacci da sauransu.


        Tana tsaye a dining area tana gyara kayan breakfast din data hada tun safe,bayan ta hana idanunta barci.


        Satar kallonsa takeyi,ya mata wani irin kwarjini da kyau,wani irin annuri ke fita daga fuskarsa,abinda ke qara mata soyayyarsa kenan da kuma kishinsa,kome ya sanyawa jikinsa karbarsa yakeyi.


        Cikin nutsuwar nan tasa ya duqa yana tarbar yaran nasa,suka shige jikinsa kowa a cikinsu yana son masa hira shi kuma yana biye musu,ta gaji da tsaiwa ganin baiko waiwayota ba,ta soma baro wajen zuwa inda suke tsugunne


"Ina kwana" ta fada ranta yana suya,a dakeka a hanaka kuka?,wanne irin al'amari ne wannann


"Lafiya"ya amsa a taqaice,ranta ya sake sosuwa,halin nasa ya motsa kenan,shi duk abinda ya faru kenan bai ga nasa laifin ba sai nata?.


"Ga abincinka nan an gama"


"Am okay alhamdulillah" ya bata amsa yana miqewa dauke da nawwara,sai itama ta miqe,zuciyarta na tafasa amma tana yunqurin danneta


"Amma kada ka yimin haka,tun dazu na tashi saboda kai fa?"


"Nace na qoshi" ya amsa mata bayan ya zube mata manyan idanunsa,abinda ya sage mata gwiwa ta koma baya ta jingina da kujera


"Abinda ya faru jiya ne kenan har yanxu bai wuce ba?" Waiwayawa yayi yana sake kallonta,shi take ma tambaya kenan?,bai amsa mata ba sai ta baiwa kanta amsa


"Kayi haquri,inasonka dole nayi kishinka,kishin ne ya sanya idanuna suka rufe,amma ya riga ya wuce,Allah ya tsare hanya" ta qarashe maganar tana jin kamar ta saki kururuwa,ita kadai tasan me takeji a zuciyarta,wani irin kisan mummuqe ne takewa zuciyarta,wadda bata saba da boye boye irin haka ba,komai nata gaba gadi take yinsa.


       Lokaci daya xuciyarsa yaji zuciyarsa ta karye,ta kuma sassauto,amma baiji gamsuwa akan lamarin hafsat din ba,ya santa,kamar hawainiya take akan wasu al'amuran,bashi da tabbacin ta fada din da gasken gaske


"Kaji?,nace kayi haquri" ta kuma fada,a wannan karon duk yadda taso tare qwallar baqincikin dake idanunta sai da suka sulmiyo,abinda ya qarasa karyashi kenan,son sam baya qaunar kuka,sai ya sauke nawwara yacewa mimi taja nawwaran suje dakinsu su dauko brush dinsu.


        A tausashe ya sanya hannunsa ya jawota zuwa jikinsa,tun baice komai ba ta saki kuka mai nauyi,wanda ke dauke da saqonni da yawa da zuciyarta keson fesarwa,baki da ruhi sun gaza amintuwa da hakan saboda burin cikar wani buri.


        Baice komai ba sai hannu da ya sanya a bayanta yana dan bubbuga wa kadan kadan,har zuwa wani lokaci,ya dagata yana duban fuskarta


"Is okay,wipe your tears" ya fada bayan ya miqa hannu ya yago mata tissue din dake kusa dashi,bata musa ba ta karba ta fara goge fuskarta ta,saidai zuciyarta har yanzu tana jinta kamar an fusgeta daga qirjinta an jefa gidan bread.


*Arewabooks:Huguma*


KI KULANI miss xoxo


DAUDAR GORA Billynabdul


RUMBUN K'AYA hafsat rano


IDON NERA Mamuhghee


A RUBUCE TAKE huguma


_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_


_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_


0022419171

Maryam sani

Access bank


Saiku tura shaidar biya ga

+234 903 318 1070


*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*

09166221261


*Al'ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number*

+227 96 09 67 63*Thanks for choosing us*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post