A Rubuce Take (K'addarata) page 52 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 52 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 52 Hausa Novel - Novels Elite

H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*

       (K'addarata)


Page 52


      Har ta gama gyaran dakin kwance saman gadon tana chart


"Na gama" ta fada jikinta yana amsawa da wani irin ciwo,saboda wannan shine karo na farko data fara aiki mai yawa haka


"Akwai 'yan kayan da zaki daurayemin.....amma,bari nayi kiranki idan na tashi" da to ta amsa,ta juya tana fita a dakin,tana jiyota tana cewa su mimi


"Ku bita da Allah kuban waje na huta" da saurinsu kuwa yaran suka biyo bayanta.


         A falo ta barsu,ta shiga bedroom ta zarce toilet ta hada ruwan zafi tayi wanka,ta hado da alwala,farkon mkhtarin sallar azahar din ya shiga,sai kawai tayi sallarta,tana shafa mai gajiya tana bin jikinta,da qyar ta qarasa,ta shiga kitchen ta hada tea ta hado da bread ta dawo ta zauna tana ci,bata iya shanyewa ba taji ya fita a kanta,sai ta dire cup din ta wuce daki tabi lafiyar gado,bata jima ba kuwa bacci yayi awon gaba da ita,saboda uban gajiyar data tarawa jikinta.


           Tana tsaka da baccin taji ana dan dukan qafafunta,idanunta a rurrufe saboda nauyin da sukayi mata ta budesu kadan,mimi ce da nawwara


"Nawwara ce tayi pupu,mommy tace ki wanke mata" idanu tadan runtse,baccin sam bai isheta ba,amma tana jin ya zame mata dole ta tashi,hakanan ta miqe ta cirema nawwaran pampers ta wanke mata,ta maida mata wandonta,lokacin sallar la'asar ya shiga,don haka ta daura alwala ta bada farali,sanda ta idar cikinta yayi wayam,dole ta shiga kitchen,ta rasa me zata dafa,ta jima a tsaye tana tunani,daga bisani ta raya gwada dafa jallop rice.


         Nutsuwa tayi sosai ta fara hada jallop din,sai data gama hada komai ta rufe Sannan ta koma ta zauna cikin kitchen din tana taya su mimi wasa,wayarta dake daki ta dauki ringing,sai ta fito tabar kitchen din ta wuce bedroom din,ta dauko wayar dake saman madubi ta duba me kiran.


           Anty deena ce,saita saki murmushi ta koma bakin gadon ta zauna,daxun da safe da sukayi waya da ummun take cigiyar anty deena di,tace an dauke mata waya ne


"Shalelen ummu" baki widad ta tura gaba


"Ni wallahi ba haka bane anty deena,duk ku manta dani,kun kawo ni nan kun ajjiyeni" murmushi ta saka


"Banda abinki widad,ashe muma ba'a sonmu kenan, kowacce mace 'yar wani gida ce daman ai" 


"Amma ku ai kuna kusa da gida,kuma ana zuwa,ni kam ba wanda yazo,ummu ma taqi zuwa"


"To daga aure weedad sai muhau zirya?,kiyi haquri kinji?" Kai ta gyada kamar tana a gabanta ne,saidai anty deena ta fahimci ta amsa ne tunda taji shuru


"Komai lafiya ko?" Ta jefa mata tambayar,sai taji kamar ta tsokano ta,idanunta suka hada qwallar da itama ba zatace ga dalili ba.


         Ta bude baki tana shirin yin magana aka buda qofar dakin nata,ta daga ido tana duban bakin qofar dakin,hafsat ce ke shigowa,sanye da bubu na wani material,ta qulle kanta da dankwalin lace.


         Zubawa juna idanu sukayi dukka su biyun,abinda yasa hafsat din taji ta tsargu,bata kuma yarda da wayar dake kunnen widad din ba,ita kuma widad din taji wani mugun tsoro ya saukar mata,hafsat din tayi mata wani mugun kwarjini,tana ji anty deena na sake cewa


"Hello weedad lafiya ko?" Hadiye wani yawo tayi mai cike da tsoro


"Eh anty" muryarta ta sauya ba kamar dazun ba,tabi hannun hafsat da kallo wadda ta miqa hannu kai tsaye tana zare wayar daga kunnenta,ta duba me kiran sannan ta saka a nata kunnen,dai dai lokacin da anty deenan ta sake cewa


"Idan da wata matsala ki fada kinji,in sha Allah zan baki shawarwari,basai kin kira ummu kin daga mata hankali ba,ba kuma sai kowa yazo ba" idanu hafsat din ta sauke mata,sai ta dan daga wayar daga kunnenta nesa kadan sannan tace


"Bani mana mu gaisa" tamkar a lokacin ta karbi wayar,sannan ta mayar kunnen tana sallama.


             A sake suka gaisa da anty deena din,don basu manta da yadda ta tarbesu ba sanda suka kawo widad din ba,sun tafi suna yabonta,fargabarsu kuma na shigar widad din gidan kishiya tana raguwa


"Da fatan qanwar tamu dai bata da matsala?"


"Ah wallahi tana da hankali ga nutsuwa,komai lafiya alhmdlh" cikin jin dadi anty deena tace


"To ma sha Allah,muna godiya sosai"


"Aiba komai,yiwa kaine ai,bari na baku guri ku qarasabmaganarku" ta fada tana miqawa widad din,jiki a mace ta karba wayar,maimakon ta fita din kamar yadda ta cewa anty deena,sai kawai ta samu waje ta zauna nan saman madubin widad din tana qarewa dakin kallo,kunnuwanta kuma suna sauraren abinda take fadi,shegiya......shuwa ko sadakar yalla,sharrinsu yawa gareshi,yarinya mitsitsiya amma dakinta yana qamshin da nata dakin bai taba yi ba tun zamanin amarci?,take kishi ya kamata,ta maida dubanta ga widad din sanda suke sallama da anty deena.


       "Wani abu kika gaya musu?" Ta tambayeta tana hade rai tsam kamar tana magana ne da mimi,da sauri ta girgiza kai


"A'ah wallahi mommy,muna fara waya ma kika shigo" kai ta jinjina sannan ta sake cewa da ita


"Ko.meye yake damunki ni ya.kamata ki fara gayawa kina jina?,tunda yanzun mune muke gida daya dake kinji ko?,dani zaki dinga shawara" kai ta daga,sai hafsat din ta sako qasa tana sake nazartar dakin


"Wannan turaren kuma da kike bulbulawa dakin,so kike.aljannu su tare miki a daki su dinga hanaki bacci suna zuwa da daddare suna tsorataki?" Dukka manyan fararen idanuwanta weedad ta fidda waje,iya maganar da hafsat din kadai tayi ta tsoratata matuqa,tsoro sosai ya shigeta,ta fara kada kai


"To ki daina sakawa,kibar dakinki a hakama"


"Ba sakawa nake ba,haka dakin yake ai" ta furta muryarta tana rawa,a fakaice ta jefa mata harara ta yatsina baki, shegiyar yarinya sai shegen sanabe da kidifiri


"To shikenan,ki taso ki wanke uniform din mimi,idan ya bushe kiyi ironing dinsa" tana gama bada umarnin tayi gaba abinta,ai kafin ta kammala fita ma ta biyo bayanta,saboda zancan aljanun yayi mugun bata tsoro,a tsaitsaye ta kashe girkinta dake kitchen,bata ko tsaya dubawa ba tayo sashenta.


        Sai data gama komai kamar wata 'yar aiki,harda tsarabar sake goge mata falo dasu mimi suka bata,kafin dare ta gaji tubus,tana son komawa amma tana jan jiki,don har yanzu tsoron maganar mommy hafsa dince a ranta,saidai dole ta koma din,tunda a nan din ba wani sakin jiki takeyi ba sosai,kasancewarta mutum mara saurin sabo.


           Komai da takeyi da takatsantsan take yinsa,ta shiga kitchen ta juyo abincinta ta wuce daki dashi,sai da ta zauna taci mai yawa sosai,don har ita kanta tana mamakin yawansa,amma ba abun mamaki bane,saboda kusan yini tayi da yunwa,data gama din saita tube kayan jikinta ta daura towel ta wuce toilet.


           A parking lot na gidan ya tsaida motarsa,ya fito hannunsa dauke da ledar da uncle muhsin ya bayar yace a kawowa widad din,don jiya ya dawo daga kano,saqo ne daga mutanen gida,kowa da abinda ya bayar a kawo mata,amma shi abbas din baisan meye da meye a ciki ba,kawai dai ya karba ya taho dashi.


          Yau din tunda ya fita bai zauna ba,daga gidan hajiya ya dauketa sukayi ziyara sosai bayan sunje gidan makokin,basu dawo ba sai magrib,daga nan kuma yayo gida.


           Koda ya kashe motar kansa tsaye sassanta ya nufa,hankalinsa yana can,daya fita hajiya na tambayarsa lafiyarta,sai yaga kamar bai kyautawa hajiyan ba,don baisan ya tata tashi ba,wannan dalilin yasa hankalinsa ya dauko da zuwa sashen.


            A nutse ya buda qofar da sallama abakinsa cikin wannan kwantacciyar muryar tasa mai taushi,falon ba kowa,saidai wannan sassanyan qamshin da ya zaunewa falon daketa faman kadawa,jikinsa ya bashi tana dakinta,don haka kai tsaye ya nufi dakin.


          Sanda take fitowa daga bandakin lokacin shima ya turo qofar dakin ya shigo,bata ganshi ba saboda ta juya a hankali tana jan qofar toilet din tana rufeta,don ko kadan bata qaunar wani babban motsi,saboda yadda zuciyarta keta rawa,a tsorace take sosai,ta sauke ajiyar zuciya ta fara takowa tsakiyar dakin,sai a sannan idanuwanta suka gano mata shi.


           Baisan me ya tsaidashi ba daga bakin qofa ya kasa qarasowa ciki,yasan dai tunda ya dora idanuwansa a kanta yaji kamar an tsaidashi a wajen..... widad kuwa baya taja da sauri sanda sukayi ido hudu,jikinta ya fara rawa, idanuwanta suka fara tara hawaye,abu na farko daya zo mata a rai aljanine ya shigo mata part yayi mata suffarsa,fararen kaya ne a jikinsa na wani lallausan yadin filtex,hakanan jakar hannunsa itama farace....an kuma gaya musu a tatsuniya aljanu suna son shigar farare,don haka ta fara hawaye tana fadin


"Wayyo ummu na.....don Allah kayi haquri,wallahi na daina,don Allah kada ka yimin komai" haushi dariya da kuma takaici suka qumeshi,yau kuma shine abun tsoron?,lallai abun nata babba ne,quruciyar tata ta gaske ce,rasa abunyi yayi,ta kuma tubure sosai tana masa kuka da magiya,ya lumshe idanu hadi da sauke numfashi ya kuma furzar da iska,ganin yadda yaketa qoqarin yi mata bayani amma ta gaza fahimta.


           Idanunsa ya sanya cikin nata ya kira sunanta da qarfi,tamkar numfashinta zai fita daga qirjinta ta sandare a tsaye


"Kina motsawa anan inda kike zan batar dake,ki tsaya na iso gabanki saina tafi na baki waje" kai ta shiga kadawa,kamar zata saki fitsari a wando,qasan ransa kamar dariya zata qwace masa amma takaici ya hanashi,ya ajjiye ladar hannunsa saman madubi,ya soma takowa idanuwansa a kanta.


        Yana zuwa gabanta ya hade tazarar dake tsakaninsu,ya buda hannayensa gaba daya ya lullubeta tsam cikin qirjinsa,qamashin shampoo data wanke kanta hadi da shower gel dinta ya nutsa can cikin hancinsa,ya lumshe ido wani numfashi na fusga daga qasan zuciyarsa mai wani irin nauyi


"Ya Allah,what's happening?" Ya fada can cikin ransa,jin yadda gaba daya jikinsa ya saki,abun mamaki baiyi abinda ya zata zatayi din ba,a maimakon haka saita tsaya cak a jikin nasa,wani irin nutsuwa taji tana saukar mata, tsoron yana gushewa,ta lullube idanunta sosai,kukan yana dauke mata,ajiyar zuciya tana maye gurbin kukan.


           Sun jima a haka,kusan mintuna biyar ba wanda ya zame jikinsa daga dan uwansa,dole tasa ya fara neman rabata da jikinsa,saboda yadda dumin jikinta ya fara ratsa nasa jikin,tudun matasan qirjinta ya fara masa barazana,har numfashinsa na qoqarin sauyawa,baiyi mamakin faruwar hakan ba,saboda yasan yana cikin wani irin situation,bako da yaushe yake samun yadda yakeso daga hafsat ba, saboda dan uban qazantarta dake hana masa rawar gaban hantsi koda kuwa ta bashi dama,lokuta mafi yawa kuma takan tsuqe,tare da kawo masa qorafe qorafen


"Ni na gaji yau wallahi......bacci nakeji......bani da lafiya fa....." Ko sau daya bai taba waiwayawa yabi ta kanta ba,ya gwammace ya kama kansa,don baijin zai iya begging dinta akan abinda yake halalinsa,sannu a hankali ta fara cire masa sha'awar ta kwata kwata daga zuciyarsa,sai ya dauki lokaci bai waiwayeta ba,abun har ya fara zame masa jiki.


           Kamar raqumi da akala haka ya zaunar da ita gefan gadon,ya jawo kujera ya zauna yana fuskantar ta.


          Nazarinta ya fara,ya zuba mata idanu yana kallonta tun daga santala santalan cinyoyinta zuwa jiqaqqiyar sumar kanta da ta fara tsanewa,idanunsa suka tsaya ga fafaren kafadunta dake cikin farin towel,a lokacin ne hankalinta ya dawo jikinta,ta soma curewa waje daya sabbin qwalla suna cika mata idanu


"Mene ne?" Ya tambayeta ganin yadda hankalinta ya tashi lokaci guda


"Kaga fa....bani da riga" furucin ya qaraso fitowa da hawaye masu dumi daga idanunta,karon farko da yajin haushi ya kamashi


"To sai menene?" Kuka ta fashe masa dashi tana nuna masa hijab dinta


"Don Allah ka bani hijab dina na saka,Allah ummu ta hanani"


"Tace miki harda ni kada na ganki a haka?" Ya jefa mata tambayar,yau kam sai ya qure tunaninta,kai ta kada


"Ban sani ba,ka daina kallona don Allah" ta sake fada tana kuka,shuru yayi yana duban baby face dinta dake jiqe da hawaye,ya gama karantarta,a haka ta taso ba tare da tasan cikakkiyar ma'anar aure ba,kuma ko a yanxun indai yanason ta fahimci abinda zai gaya mata saidai ya bata hijabin yadda takeso,baisan dalil ba,sanda ya miqa mata hijab din,sai yaji baya buqatar ta saka,amma haka ya lumshe idanunsa harta gama sakawar,sannan ta tsareshi da ido tana jan majina.


          Shima ita din yake kallo,kafin daga bisani ya kauda dubansa,ba lallai ma ta gane meye miji ba bare aure,sai ya ajjiye wannan maganar ya soma mata wadda yake ganin tafi muhimmanci akan wadda da farko yaso yayi mata ita.


*Arewabooks:Huguma*


KI KULANI miss xoxo


DAUDAR GORA Billynabdul


RUMBUN K'AYA hafsat rano


IDON NERA Mamuhghee


A RUBUCE TAKE huguma


_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_


_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_


0022419171

Maryam sani

Access bank


Saiku tura shaidar biya ga

+234 903 318 1070


*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*

09166221261


*Al'ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number*

+227 96 09 67 63*Thanks for choosing us*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post